Showing 549001 words to 552000 words out of 557259 words
sannan ake barinsu su koyi rayuwa da hidimar rayuwar data zamewa kowa ya koyi yiwa kansa.
Idanun yara kawai ya hana ya rungumeta,amma qasa qasa yake fadin.
"Karki bata fuskarki,karki kashe mana farincikin yau" Ya fada yana dan bubbuga bayanta.
"Kita fatan muci gaba da irga wadannan shekarun tare" Abinda ya rada mata kenan.
Qaramin walima akayi a gurin da kayan maqulashe kala kala,kuma abunda ya bata mamakin shine,koda autar gidan iffa wadda tare suka shigo gidan sun tanadar mata gift din da zata bawa daddy jadda (yadda gidan suke kiransa kenan in general idan ba'a sassansa bane).
Farinciki da walwala ne kawai ya wanzu a gurin,inda daga qarshe dai bata haura samanta ba kota wuce sassanta ta lalace a nan tana tsakiyar family din nata suka zarce da hirarrakin bikin da zaa fara jibi jibi.
Wayarta ta ciro da zummar kiransu nadra taji inda suka dade haka da yawa sai taci karo da tarin miscal din jadda. Ta zaro ido tana mamakin tun yaushe yaketa kira bataji ba?,saiga shigowar wani kiran nasa.
"Sabrrrr" Kawai ya fada a narke,take ta fahimci yana buqatarta a kusa dashi.
"Banda abun hamma.....awa daya kawai ya rage ayi magriba fa?" Ta fada cikin mita tana tura katafariyar qofan master bedroom dinshi.
Bata gama ajiye qafarta taji an ficikota ciki,a zafafe ya manne bakinsu guri daya ba tare daya jira komai ba.
Har kullum har ko yaushe har kuma abada mantawa takeyi da shekarun dake wuyansu idan suna tare da jadda din. Wani irin mutum ne dake da baiwar narkar da zuciyar diya mace ya kuma mantar da ita komai. Abinda yayi imani dashi shine,yadda kowacce diya mace a kullum take fadi tashin neman hanyoyin faranta ran namiji da burgeshi,haka ya kamata kowanne namiji shima ya kasance cikin sanin hanyoyi da salon mallake zuciyar matarsa......wannan dabi'ar tasa ta sanya yayi zarra a zuciyar sabreen din.
Sai data tabbatar ta samar masa da nutsuwa sannan ta baiwa kanta hutu tana aje numfashi,ya birkitota yana maqaleta a jikinsa bayan sunyi alwala sun dawo. Shuru ne ya ratsa tsakaninsu,kafin daga bisani taji saukar numfashinsa a hankali bacci me cike da nutsuwa yayi awon gaba dashi.
Sai bayan sallar isha'i ta samu saukowa daga wajensa,a lokacin ya fita sallar isha'i,da wannan damar ta samu tayi wanka tayi kwalliya kuma cikin atamfa kaman yadda ta saba idan zasuci abinci nasu duka.
D'as d'as take takawa kaman ba wannan jikin bane ya fidda rai goma ba,har ta iso babban parlor din da anan aka gina katafaren dakin cin abinci.
Ta samu kowa yana gurin,kowa kuma yasan mazauninsa yana kai a zaune,sauran wadanda basu hadu ba sai a sannan irin musaddiq saddiq da farouq duka a nan suka gaisa suna tayata murnar ci gaban da aketa samu.
Kowa ya hallara kuma faud din ake jira,shine qarshen shigowa,yana takowa a nutse da wata irin haiba da kwarjinin da ya qara yawa sanadin shekaru da kuma riqo da addini da yake dashi,kwarjinin da yake hana mutum musu dashi ko yin abu ba daidai ba,kwarjinin da hatta sabreen a yawancin lokuta yakan daketa duk kuwa da cewa dazu dazu suka rabu a daki cikin wani sirrintaccen yanayi,amma yanzun data kalleshi kwarjinin nan ya dawo fes saman fuskarsa.
Kusan yara yaran a tare suka gaidashi,su sabreen huda fannah da amna suka fara serving na kowa da kowa a nutse ba wani hayaniya kaman ba taron mutum kusan talatin ba.
Cikin qauna da tsabar sabo da juna suke cin abincin,hirarraki suna gudana a tsakaninsu. Har yau har kuma gobe yana maintaining class dinta a idanunsa,bata duba an dade tare.....an jima da juna ta dinga wasu abubuwa da babu aji sam cikinsa a wajen diya mace( mata yana da kyau ku kula da wannan,stay classy please,karki dinga abu gaban miji wargazaza koda shekara dubu kukayi ki tabbatar masa ajin nan fa akwaisa,idan ba haka ba ya hango wadda bata kaiki ba nata ajin ya dinga dibansa yana burgeshi).
Shi dinma satar kallonta yakeyi,yanason gano meye ya banbantata da sabreen din shekaru goma sha baya?. Ya dade yana against in din maza da yawa akan suna da babban laifi da muhimmiyar rawa da suke takawa wajen wargajewar matansu,mace 'yar tattali ce.....'yar a bata kulawa ce,mace tamkar fure take,dole idan anaso aci gaba da ganinta sharshar a tsaya mata da ban ruwa,wato cima sutura muhalli abun sha me kyau,a debe mata damuwa daga zuciyarta.
Ta samu daman zama da amaren nadra da haneefa har kusan sha daya na dare,don shima sun kebe dasu musaddiq suna tasu tattaunawar,har suka kammala ya dawo ta parlor din.
Daga tsaye yake dubanta da lumsassun idanunsa,hannayensa cikin aljihun rigarsa.
"Madame.....baa kammala bane?".
"Saura kadan hamma" Agogo ya kalla sannan ya sauke dubansa.
"Kubar addan nan ta huta mana.....da safe sai a qarasa" Dariya nadra da haneefa suka saki suna miqewa gami da tattare kayan da take dubawa,haneefa tace
"Hamma babu ruwanmu fa,tun dazu mukace mata xamu qarasa gobe tace yau xaa gama.....saida safe" Ta shilla da dan qaramin gudunta tana bin bayan nadra da tuni ita ta fece.
Ta dawo da idanunta daga kan haneefa tana murmushin wai auta itace yau da aure?,saiji tayi kawai anyi sama da ita.
Wutsil wutsil ta fara yi da santala santalan qafafunta kamar qaramar yarinya.
"Hamma......please mana,kada wani ya ganmu mana?".
"Who cares?" Tunda taji ya fadi haka tasan zai wahala ya sauketa idan ba fita sukayi ba,don haka ta kwantar da kanta saman qirjin da duk duniya yafi mata ko ina dadi da samun cikakkiyar nutsuwa.
β
Kwanaki uku kacal da dawowarta aka fara bikinsu nadra din,iya events din data fada din kusan haka aka yisu. Saidai fa tun ranar bridal shower fu'ad din bai sake barinta taje komai ba,saboda wani irin sassanyan kyau da tayi me daukan hankali cikin wata butter color gown ita da iffa da tayi order dinta tun daga Egypt,tana yawo kuma da tag din bride sister daya sake bata ranshi. Lallaba kayanta kawai takeyi,tasan halinsa sarai a kanta baida sauqi,ta samu ta saukeshi ta kuma kiyaye dukka dokokinsa har aka gama bikin lafiya. Saidai ko bayan bikin still mitar bridal shower day din ya dinga mata,saida ta samu ta bashi wani zazzafan dare guda daya sannan ta wanke kanta.
*_GRADUATION DAY_*
*@KING ABDUL'AZEE INTERNATIONAL SCHOOL*
Triplet din 'yan qasa nigeria kuma haifaffun qasar madeenatul munawwara......wasu irin yara ne da sunansu dasu kansu sukayi fice cikin makaranta dama wajenta. Bawai don kawai farinjinin 'yan uku ba.....aah hatta da kaifin basira da Allah ya zuba musu,matsanancin nutsuwa da sanin ya kamata.....inda daga qarshe kuma suka zama dalibai madiya hazaqa da qoqari cikin daliban da makarantar ta fitar.
Sanda makarantar ta tasosu ta tsaidasu saman stage tana wassafa kyawun dabi'u da hazaqar yaran sai sabreen ta kasa daurewa,ta kifa fuskarta tsakanin tafukan hannayenta tana jin wani irin alfahari da yaran da kuma qaunarsu tana ratsata.......wani irin farinciki da batasan yadda zata misaltashi ba na kyauta da baiwar yaran da Allah yayi mata,wanda a yanzun haka cikin amsa kuwwa ake sanar da kowa cewa su din cikakkun 'yan qasa ne.....gwamantin saudiyya kuma sun dauki nauyin komai da komai nasu saboda girmamawa da jin dadin yadda suka zauna da kowa cikin makarantar dama qasar lafiya.
Da qyar ta iya isa tsakiyar yaran nata don karba musu kyaututtukan karramawa da suka samu,duk da jikinta a lullube yake kirif,baka ganin komai nata sai zagayayyar fuskarta,amma duk da haka wasu sun cika da mamakin cewa itace mamansu. Tun tana iya amsa har gifts din sukafi qarfinta saida jadda dake sanye cikin wata rantsatsiyar shadda ya tako da sanyin nan nasa da nutsuwarsa ya tallafeta da wasu kayayyakin.
Ranar wata rana ce da bazata gushe ba a zukatansu,cike da tarihin da bazai kankaru ba cikin rayuwarsu.
Already sun tsara ana kammala taron zasu koma makka su sauke umra gaba dayansu,saboda nuna godiyarsu ga Allah da kuma sake roqon ubangiji ingantacciyar rayuwa me dorewa.
*_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_*
08187255862
*_NACE BA......._*π§π½π§π½
*_Hajjaju a ina kike siyan turare?....._*
*_NACE A INA KIKE SIYAN TURARE?_*
*_Ga wani fa........TASTED AND TRUSTED ne.......mun gwada munga ingancinsa_*
*_Da yardar Allah saikin godemin_*
*_KUNSAN DUK INDA QAMSHI YAKE ZAKA SAMENI A GURIN,MAGANAR GASKIYA KENAN AHTO_*ππ
Golden oud
Hawi
Sandal balls
Sandal flakes
Cotton bakhoor
Kabbasine mix
Khumra(alba,alsuma,ebony,monarch,musk)
Deep crush (luxury khumra).
Signature oil
Kuleccham
Kabbasine spray
*_YA SUBHANALLAH.....hajiyata dukka wadannan zaki samesu a_*
*_PRIME SCENTS(the scents of royalty_*
*KE DAGA JIN SUNAN KINSAN ZA'A ZUBDA QAMSHI ME AJI DA DAUKAN HANKALI*
*SUNA NAN A*
*_No 3,kabiru sani lawan street,farawa layout,Maiduguri road kano_*
*BA'A KANO KIKE BA?*
*_karki damu,tuntubeta ta nan,TABBAS kayanki zasu iskeki a duk inda kike cikin aminci da yardar Allah,NA BAKI TABBACIN HAKA_*
*DANNA RUBUTUNNAN DON YIN MAGANA DA ITA KAI TSAYE*ππΎππΎ
wa.me/+2348103155915
KO KI KIRATA TA NAN
08103155915
π π π π π π π π
_Zafafabiyar_
ΜΆBΜΆOΜΆOΜΆK ΜΆ2
β±§Ιβ²Ιβ₯β³
ππΌππ 175
*_Domin qulla huldar kasuwanci damu,HUGUMA CLOSET.......,siya ko siyowa wani,reposting ko sari akan farashi me rahusa da babu irinsa,maza yi joining group namu don samun ingantattun kayan da babu ha'inci a ciki da izinin Allah_*
https://chat.whatsapp.com/FrqgC0YmUWP4FPmUzYuLJX
____________________________
*_PLEASE FOLLOW MY TIKTOK PAGE_*ππΎππΎππΎ
https://www.tiktok.com/@huguma.closet?_t=ZM-8y1pf9yfIVZ&_r=1
__________________________
175
A maimakon jirgi a babbar lafiyayyar mota suka taho zuwa makka. Wata irin tafiya ce ta iyali me dadin gaske,hirrraki da labarai duka sun cika motar dake dauke da JADDA FAMILY.
Saidai duk da hakan daga can seat din baya ita da fu'ad ne zaune,tadan dora kanta saman kafadarsa tana jin kasala da wani saqe saqe da cikinta yayi mata wanda batasan Meye dalili ba.
A fili kuwa hotunan graduation din take kalla daya bayan daya. Duk inda zata wuce fu'ad da yaran sai tayi zooming ta kallesu sosai,tana jin kaman ba yaranta ba,kaman wani imagination ne a cikin duniyar mafarki ma,har sai da fa'ad daketa sauraron shirmen yaran daga gaban motar yana murmushi kadan kadan ya ankara da ita.
"Kina mamaki ne?" Kai ta daga ta kalleshi sannan ta maida saman kafadarsa.
"Ina mamaki mana hamma......yau sabreen da kowa ke mata kallon KARUWA da yara irin wannan?,sabreen din da kowa ya gaza janta a jiki yaji meye damuwarta,meye kuma uzurinta yau ita keda yarannan?......sabreen din da tafi kowacce yarinya nutsuwa da hankali saboda ita din rainon ummee ce yau ta zama haka meye sila?,ba hujja ba dalili sai yanke hukunci babu bincike". Bata tsaya jin ta bakinsa ba ta dora.
"Alhaji ahmad me citta shine asalin sunan mahaifina,wanda ya shahara da sana'ar saida citta kanunfari da sauran kayan da suka danganci wannan da wasunsu ma daga qasar larabawa ake shigo musu dasu. Abbana ya auri ummeena ne a sanda yake da matan aure biyu da yara mata goma sha biyar,ummena ce ta uku,mace me tsananin haquri da kawaicin daya sanyata taci nasarar zama da sauran matan abbana,wanda cikin su take da babbar abokiyr adawa wato bibo,wadda ita ummee ke bi. Abban mu ya tsaya sosai a kanmu,shanmu cinmu tarbiyya da iliminmu,don har yanzu tasirin dagewarsa ce a jikina na ilimin dana samu daga private school daya sakamu me tsada,tun daga matakin free nursery har secondry,duk da cewa ina js 3 abbanmu ya koma ga Allah,ummenmu itace ta jajirce naci gaba da wannan makarantar har na shiga ss3 second semester,a lokacinne Allah yayi mata rasuwa,a lokacinne asirinmu ya tonu,maraici kuma ya afko.mana gadan gadan,ummenmu ba 'yar qasar nan bace,don haka bamu da kowa a kusa damu da zai tallafemu. Sh momma sunso tafiya damu amma kawu ya saka kuka,wai ya za'a tafi da zuri'ar ahmadu yana raye?,shi yayi alqawarin kula damu kaman yadda abbanmu ya kula da rayuwarsa. Abbanmu ne ya riqeshi bayan rasuwar iyayensu tun auren abban ma na fari,bai kuma qyale kawu ba sai daya aurar dashi ya hadashi da jari yana saka ran wasu halayensa da bayaso zuwa sannan kawun ya dainasu. Da wannan yaqinin suka barmu hannunsa,ashe kuma lokaci lokaci suna masa aike da sunanmu,amma ko labari bai taba bamu ba bare muga abinda suka kawo.
....... Tom ko bayan mutuwar abba kowacce mace ita ta koma hidimar kanta da kanta,to yanzun da bamu da uwa sai ya zamana ba wanda ya damu damu,ba wanda yake dubamu,ba wanda yake damuwa da munci bamu ci ba,munsha ko bamu sha ba,mun tashi lafiya?,waye baida lafiyar?,dukka ba wanda ya saka hakan a tsarinsa. Da farko na dauka abun na wasa ne,na dauka zasuji qanmu,saina fara nema mana abinci daga dakunansu kafin na fahimci ba wanda zai iya cida mu,don da zagi nake fita a dakin da qyama da tsangwama,daga bisani dole na koma roqarwa su huda a maqota,donni ban damu naci ba,muddin sukaci shikenan tawa me sauqi ce,zan iya kwana uku ma banci komai ba,saidai nasha baqin ruwa na kwanta. Sannu a hankali suma maqotan suka fara hanani,sai ya zamana mun qarasa galabaicewa,ciwon yunwa yanason kama huda da haneefa da bata gama sanin ma me ake ba idan yunwar taji ba. Ba wanka ba wanki don ba wanda zai bamu sabulu,saidai da yake ummenmu ta saba mana da tsafta hakanan mukeyi da zallar ruwa.
Maqociyarmu kuma qawa ga bibo ita ta fara bani shawara.
"Kina da kyau sosai sabreen,kaf gidanku ba yaro me kyanki.....me zai hana ki tallata hajar jikinki?,wallahi abinci ma saikun bawa wani" A ranar hankalina yayi mugun tashi,mukayi uwaka ubaka da ita,kaf kimarta ta zube a ido na,ita kuma ta kamani tamin shegen duka akan na mata sata kuma na mata rashin kunya. Ba wanda ya damu yaji ba'asi saboda basa sonmu bamu da gata,saima tayata da bibo tayi,haka nayi kwana uku kwance ina zazzabi ba magani a dole na warke. Sanda naga yunwa na neman rayuwarmu saina fara da tambayar alhaji baqo,aboki na kusa ga mahaifinmu wanda nake kyautata zaton zai iya taimaka mana" Shuru tayi tana hadiyar wani abu me ciwo.
"Saidai abun mamaki abinda kuma ko yau na tuna yakemin ciwo,ya nemi yaci amanar amintaka,ya nemi na bashi mutuncina yaci gaba da ciyar damu duka. A nan ne naci masa mutunci saboda mamakin daya bani,kamar yadda mukayi da waccar matar shima duka yayimin ya hadamin da sharri,abu na farko daya fara qeqasarmin da zuciya,na fahimci kaman ba wanda zaiji tausayinmu a unguwar,binda yasa na kasa mantawa ko yafewa,na koma na kunna masa gobara a dakinsa data jaza masa asara me yawa,ya gano nice,yace zai kaini ga 'yan sanda,na gaya masa ina da shaidar cewa muddin ya aikata haka ni kuma nizan babbake gidansa duka da 'ya'yansa da matansa,abinda ya sakashi haqura kenan,tun daga ranar idan na ganshi sai tsaki habaici da tsartar da yawu,sai duka ya tsargi kansa yana tsoro kada na tona masa asiri,sai ya koma kaman sirikina. Daga nan saina fara yawon nema mana abinci,duk da ba cikin kyakkyawar kama nake ba,amma duk wanda ya ganni ringidi ringidi zai jani ya kaini gun cin abinci a zubamin,saina juyewa su huda a leda,sukance ki cinye,indai kin bamu hadin kai lallai abinci saikin ture. Mutun na farko daya fara nunan me hakan yake nufi na samu na gudu ina zaginsa,akayi na biyu na uku na hudu na biyar shida har goma,duk wanda yaga bazai samu abinda yakeso ba saiya qwace abincinsa. Maza da yawa haka muka dinga yi,abinda ya sake dasamin duniya ba imani.....babu me taimako don Allah sai don wani abu na daban,dana fahimci haka saina fara tunanin ta yadda zan amfana da kudadensu ba tare da mutuncina ya tabu ba.
.....salis shine mutum na farko dana fara gwada hakan a kansa,na saka masa maganin bacci a lemo,na kuma debi kudade masu yawa na gudu. Wannan kudin su suka fara canza rayuwata,na siya mana abinci me yawa,suturu da komai na fara kwalliya muka fita daga qazanta.
Da bincike salis yasa aka samoni,aka kamani,kamun da dashi bibo tayi amfani ta fara bugamin tambari da batamin suna,tunda tana baqinciki kwana biyu muna cikin abinci da duk kayan wadata na rayuwa,saita saka idon lallai sai tasan inda na samo,saiga case din salis.
Sanda ake tuhumata na kasa bada amsa,na tsinci dai wata murya tana cewa.
"Ku saketa fa,nine shaida bata da laifi,ya cinye kudinsa ne kawai zai laqabawa wata" Wani matashin dan sanda ne ya fadi haka. Wannan shine jib,silar haduwarmu kenan,mayen computer na gaske da salis da yake kawunsa yaqi taimaka masa da registration a shekarar qarshe da yake ciki saboda rashin kirki,wannan ya sanyashi rasa damar karatunsa,da cuku cuku ya samu aikin dan sanda da qaramin albashin da bai wuce ladan ganin ido