Showing 453001 words to 456000 words out of 557259 words

Chapter 152 - πƒπ”ππˆπ˜ATA BOOK1 AND 2 HAUSA NOVEL

HUGUMA   

03 Nov 2025

407

ke kurdawa ta kowanne lungu na zuciyarta. Kewarsa me matuqar qarfi ta taso ta lullube zuciyarta ta sakata jin wani rauni na mamayarta,take idanunta suka cika da hawayen da bata da ikon tsaidasu.

Hannunsa daya ya miqa mata yana ware mata su alamun marabtarta yakeyi,cikin wani irin zaquwa da dokin isowarta gareshi,batayi wata wata ba ta soma takawa da sassarfa zuwa inda yake tana jin kaman lokacin isarta inda yake ma ya mata yawa.....inama zaiyiwu ta zama walqiya cikin qiftawar idanu ta samu isa gareshi.

Jikinsa ta fada gaba daya kuka yana qwace mata,tsam ya riqeta cikin jikin nasa yana mata kyakkyawan masauki zuciyarsa na tsananta bugu cike da wani bahagon so,idanunsa suka dinga lumshewa da kansu,dumin jikinta yana ratsa qashinsa bargo harda jinin dake harbawa kowanne sashe na jikinta. Hannunsa daya ya sanya ya riqo fuskarta,idanunta yake son kallo,qwayoyin idanun nan nata da yayi matuqar kewa yakeson gani.

Bata hanashi ba,ta daga oily eyes dinta masu sheqi da suka jiqe da hawaye tana kallonsa. Nutsewa idanunsu sukayi cikin na juna,wani irin feeling ke ratsa kowannensu wanda yafi qarfin baki ya bayyanashi. Wani deep connection ya qullu a tsakaninsu,magana ce tsakanin zuciya da zuciya kawai wadda tafi qarfin baki ya bayyanata. Idan ya motsa labbansa sai yaji sun masa nauyi.....sai yaji kaman sunyi kadan su isar da saqon da zuciyarsa keson fadi

"Sabrrrr" Ya samu ya fusgi kalman da qyar zuciyarsa naci gaba da bugawa. Itama kaman zai bace mata takeji daga qiftawa qwaya daya tak da zata yiwa idanunta,don haka ta motsa labbanta ba tare da amsar NA'AM din da takeson furtawa ta fita a bakinta ba.

"Love is in the eyes.....eyes don't lie.....sabrrrr.....kalli idona.....me kika gani?" Ya motsa labbansa ya fada da wata irin narkakkiyar murya irin wadda soyayya ta yiwa lahani.

Inda yasan yadda qwayoyin idanunsa suke narka mata bargo da bai buqaci ta kallesu har haka ba....saidai kuma kallon nasu wani abune na musamman cikin ruhi da zuciyarta. Ci gaba tayi da kallon idanun nasa.....taga abubuwa masu tarin yawa.....taga abubuwa masu yawan da sai da taji kaman zata zauce,duka ita daya?,duk ita daya muhammad fu'ad kewa wannan zazzafan son?.

Hannu ya kama ya riqe kumatunta yana aza shimfidadden murmushi kan fuskarsa.

"You're a thousand miles away.......but no one else is closer to my heart than you are" Ya qarasa fada yana kama fuskarta sosai gami da hade goshinsu guri daya.

Musayar numfashi suka fara yi a tsakaninsu,kowanne yana shaqar numfashin da dan uwansa ya fesar,hakan na sake qara musu wani qaqqarfan alaqa tsakaninsu data tsananta bugun zuciyarsu duka su biyun.

"Zan iya mutuwa.......Allah zan iya mutuwa idan ka sake matsawa daga gareni irin wannan matsawar da kayi.......zaka iya rasani......ka rasa kuma babies dinmu gaba daya" Ta qarashe maganar tana sakar masa kukan da ya koma zuwa na shagwaba kuma a wannan lokacin.

"Nayi alqawari DUNIYATA.....nayi alqawari bazan qara ba,i promise" Fuskarta ta qwace ta cusata cikin qirjinsa tana shaqar wannan tattausan qamshin nasa da tayi matuqar kewa kamar zata zauce.

"I pray to god that you will stay permanently in my life".

"I pray too my world" Ya fada yana kissing tsakiyar kanta. Qanqameshi tayi da kyau don sake bawa kanta tabbacin reality ne bawai mafarki ba. Kalmar "wash Allah na" Daya fada ita ta sakata saurin sakinsa tana kallon fuskarta.

Idanunan dai nashi ya zuba mata murmushi na fita a fuskarsa,sai ta tabe baki kaman zata saki kuka. Da sauri ya mata nuni da hannunsa,ta waiwaya a hankali zuwa sashen da yake nuna mata din.

Miqewa tayi ta zauna da sauri saidai ya hanata hakan,ya jawota jikinsa ya maidata sosai yadda zaici gaba da jin qamshinta da duminta.

"A nan suka harbeka?" Ta tambayeshi a sanyaye da wani irin emotion na bacin rai saman fuskarta. Girarsa kawai ya dage mata yana dubanta har yanzu fuskarsa da murmushi duk da yadda yadan fada kadan.

"Allah ya isar mana....Allah ya saka mana"

"Very soon duniyata......mu ajiye wannan maganar yanzun......i need you duniyata.....kaman dazu naji kince babies instead of baby right?" Ya tambaya yana tsareta da idanunsa. Tsam tayi tana dubansa,sai kuma ta saka tafukan hannayenta duka biyun ta lullube fuskarta dasu.

"Yes......twins n....." Bata qarasa fada ba taji yana lalube rigarta,saidai jikin ba qwari kwata kwata da alama don haka ya ajiye hannun nasa yana maida numfashi. Koda ta kalleshi kwantaccen hawaye ta gani saman idanunsa,batasan me yasa akan duk abinda ya shafeta ba shi rago ne na gasken gaske.

"Please sabrrrr......ki dagamin rigar na gani,haka Allah ke sona?" Yadda yayi maganar da gaske abun ya taba ranshi,ba zata iya hanashi ba,don haka ba musu ta miqe ta yaye abayan jikinta,tayi qasa da under wear dinta take farar fatar cikinta ta fito. Jawo qugunta yayi sosai,a hankali ya aza labbansa saman mararta.

Har tsakiyar kwanyarta taji wani yaarrrrr,wani abu ya tsarga mata ya saukar mata da wani irin yanayi a sassan jikinta. Lips dinsa nakan marartata ya daga idanunsa ya kalli yanayin fuskarta,kunya ta sakata runtse idanunta sai ya aje mata tattausan kiss sannan ya janye bakinsa ba tare daya saki rigar ba. Batasan me ya karanta ba,amma ya kusa mintina biyu bakinsa yana motsi kafin ya matsa kusa ya tofa mata abinda ya karanta din,ya sake kai hannunsa ya aza akai ya sake karanta wasu addu'o'in sannan ya sake mata rigar.

Still hankalinta yana kan hannunsa,tayi taku biyu zuwa wajen ya sake jawota jikinsa

"I really missed you......kiban koda 10minutes naji duminki......ban taba zaton zan sake rayuwa ba......dazu na tashi daga suman da nayi duniyata" Yayi maganar yana aza kansa saman kafadarta,yana jin ya samu wani peace daya dauke masa duk wani abu da yakeji a jikinsa da zuciyarsa.

Idanunta sukayi rau rau da hawaye

"Ko waye wannan bazan taba yafe masa ba.....ko wayeshi" Ta fada muryarta tana rawa. Ya buda baki zaiyi magana muryar farouq ta ratso dakin,yadan bude qofar kadan amma fuskarsa da idanunsa sun basu baya.

"Su musaddiq kuwa zasu samu yin dubiyar nan?,ko kuma su koma kawai sa dawo?". Sassanyan numfashi ya aje kafin ya motsa labbansa.

"Bansan me yasa baka da imani ba farouq....aidai ka tausayamin ko?.....na yafe dubiyar,kaima ka bisu kuje ku huta......thanks so much dude". Baki kawai farouq ya sake,ya dauka fu'ad din zai tuna dasu anni a wajen ya sakaya zancansa?.

" Dama shi dan adam butulu ne ai,na maka welcome to the world ai ko?,alright.....but kasan hannunka yadda yake......yana buqatan a kula dashi.....still itama me jinyar taka ba'a dade da sallamarta daga asibiti ba.....banajin she can take good care of you".

"I can BB.....i can wallahi" Sabreen ta samu kanta da fadin haka ba tare da wani kunya ko d'arr ba.



*_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_*
08187255862


𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓 𝐀
_Zafafabiyar_

ΜΆBΜΆOΜΆOΜΆK ΜΆ2

β±§Ι„β‚²Ι„β‚₯β‚³

π™‹π˜Όπ™‚π™€ 127


*_Bgawo's KITCHEN AND APHRODISIAC_*


*_WATA KILLATACCIYAR MASARAUTA CE,WADDA KE QUNSHE DA DUKKAN NAU'IKAN ABINDA KUKESO_*


*_GIRKE GIRKE NA ZAMANI_*

*_KAYAN MAQULASHE DA NAU'IKAN DRINKS KALA KALA_*

*_INGANTATTUN TSUMAMMUN MAGUNGUNAN GYARAN MUTUNCIN 'YA MACE......GYARA IRIN NA IYAYE DA KAKANNI DA INGANTATTUN MAGUNGUNAN DA BABU DUNGUSHE KO KOKWANTO A KANSU_*

*_KALAR MAGUNGUNAN DA SAO WAJEN IYAYENMU NA DAURI.....INGANTATTUN SAUWOYI DA SAQE SAQI DA AKA SARRAFASU ZUWA MAGANIN GYARAN DIYA MACE_*

*_BIKI KUKE DASHI KO SUNA?_*

*_SAUKAR KARATUN QUR'ANI?_*

*_KO KUMA WALIMAR AURE QARIN MATSAYI A GURIN AIKI KO KUMA WANI QWAR QWARYAN TARO?_*

*_KO YAU DIN BAKIJIN SHIGA KITCHEN?,TSAFTATACCE KUMA INGANTACCEN ABINCI KIKE BUQATA A CIKIN WARMERS DINKI KO FOOD FLASK?_*

*_HAIHUWA KIKAYI?_*

*_KO GYARA ZAKIYI KAWAI A MATSAYINKI MA CIKAKKIYAR MACE?_*

*_BGAWO'S KITCHEN SHINE MUHALLIN DAYA DACE DA DUKKA WADANNAN BUQATUN NAKU_*

_Maza garzaya ki tuntubesu ta wannan number wayar_

08104553105
08127084190

*_zaki godemin qwarai da haduwa da BGAWO'S KITCHEN_*


*_BGAWO'S KITCHEN_*
*MATATTARAR BIYAN BUQATUNKU*


127



"Pay no attention to him,brush him off" Fu'ad ya fadi yana lalubenta,abinda ya dameshi kawai shine yaga abinda ya sameta don yaji farouq yace bata da cikakken lafiya.

Fes farouq yaji abinda dukkaninsu suka fada,ya jijjiga kai yana mamaki

"Fu'ad......farouq ne fa?,lafiyanka nake magana kana gwaleni?". Hannun sabreen ya kama ba tare daya waiwaya sashen da farouq ke tsaye ba,a yanzun baya buqatar kusanci da kowa idan ba ita ba.....idanma akace wani zaya zauna dashi a dakin ai yana ganin an gama zaluntarsa. Yasan tsiyar farouq tsaf zaice shine zai zauna dashi saboda mugunta,yadda ta gayawa farouq kai tsaye zata iya kulawa dashi ya matuqar burgeshi,don haka ya qara encouraging nata.

"Take what he says with a grain of salt,dont let him get to you" Ya fadi yana sake juya hannuwanta yana dubawa.

Salin alin farouq yaja qofan yana wucewa,saidai a ransa ya ayyana dashi fu'ad din yaci tuwo,zaisan kuma miya yasha


"What's wrong with you my world?" Ya tambayeta yana tallafo fuskarta,yaga alamun bata fahimta ba sai ya canza salon tambayar.

"Farouq.....yace baki da lafiya.....da gaske ne?" Murmushi ta sakar masa,ta miqa hannunta a nutse tana kama habarsa me cike da kwantaccen gashi.

"Kana tunanin zan iya lafiyayyar rayuwa sanda ake shaidamin muffin dina yayi batan dabo cikin DUNIYARSA?" Tambayar ta sanya murmushi kubce masa shima,ya girgiza kai yana kallon zara zaran eyelashes dinta.

"Wannan ciwon nayi.....amma daga yau na warke in sha Allah". Knocking na qofar da akayi shi ya katse musu wannan daddadan tattaunawar,ya kalleta yana dan hade rai da alamun gajiya da rashin jin dadi a fuskarsa.

"Inda zai yiwu.....zan sanya a sauyamin dakin da babu wanda ya sanshi bare a dameni" Idanu ta waro waje tana miqewa a nutse.

"Da BB yace na hure maka kunne....kuma daka cika me butulci".

"Kibar ganin farouq haka duniyata....zai iyayin abinda yafi nawa"

"Qarya kakemin......kunyarka tafi tawa yin qaranci" Muryar farouq din ta ratsa dakin sanda sabreen ta bude musu,itadai sai tayi baya tana boye fuskarta. Da idanu kawai ya bita yana sake ganin ta canza masa,ko takan tsiyar da farouq keyi masa da raddin da yake maida masa baibi bama sam sam.

Likitansa ne ya shigo a bayan farouq din,sai fu'ad ya kimtsa yanayin fuskarsa ta hanyar rage fara'arsa yana duban sabreen.

"Ki shiga toilet ki gyara lullubin kanki sosai.....banaso ko gashi daya ya fito" Ya qarasa fada yana maida dubansa ga likitan wanda dauke idanunsa kenan daga kan sabreen din.

Fuska a hade fu'ad din ya kalli farouq sanda likitan ke buda qirjinsa yana auna gudun zuciyarsa.

"Ka gaya masa,He should look down when she's around,matar aure ce".

"Tashin hankali" Farouq ya fadi,yasan ba qaramin daru za'a sha ba.....kowa ma sai ya shiga uku muddin duniyarsa tazo......wannan ya sanya yaso ya boye har sai ya fara samun lafiya da kuma sauran dalilai na tsaro da sukeso su gama binciken duk wanda keda hannu a cikin attack din ba tare da kowa ya ankare ba. Yasan da biyu ya fadi ragowan maganan da turancin englishi,dole yasan likitan zai fahimci wani abu.

Sanda ta dawo daga toilet din gyaran mayafin kujera farouq yaja mata yace

"Zauna a nan" Ya fada yana ajiyeta kusa dashi. Likitan yaci gaba da duk wani dube dubensa,ya kammala yayi rubuce rubuce ya ajiye file din ya fita farouq ya bishi.

Idanunta still akan hannun,har yanxu tana jin ciwon kaman cikin jikinta,yanzu kenan ida harbin ya subuce ya sameshi a inda ba'aso yanzun da wani zancan daban kenan akeyi?.

"Subhanallah" Ta samu kanta da furtawa tana dauke idanunta sai caraf suka fada cikin nasa. Abinda bata sani ba kallonta yakeyi da duk wani motsi nata. Ya miqa mata hannu yana daga kwance rigingine. Kafadarta ta noqe tana dubansa a shagwabe.

"Kasan wadanne irin wahalallun kwanaki na dinga yi cikin duniya kuwa?" Idanunta suna tara hawaye har batason tuna wannan kwanakin.

"Inda nine inajin da tuni fargaba ya kasheni.......kinsan adadin son da nake miki kuwa?" Kallonsa take har bata qiftawa,tanason gwada ma'aunin sonsa a zuciyarta da yadda yake iqirarin nashi yafi nata.

"Kina tantama ko?" Ya tambayeta da murmushi,kafin wani ya sake cewa komai a cikinsu an sake shigowa.

Anni ce da musaddiq saddiq abba da farouq gaba daya,kunya ta lullubeta,tayi qasa da kanta tana niyyar tashi a wajen anni tace

"Yi zamanki" Suka koma saman ragowar sofas din dake dakin suka zauna. Duk budurinnan gogan idanunsa yana kanta bai iya dauke idanunsa ba sam sam.

Sabuwar gaisuwa da jaje suka sake yiwa juna,dakin yayi shuru sanda farouq yake bada labarin yadda abun ya kasance.

"Kaman gawa mukazo dashi abba......dazu da safe ya farka......amma ko jiya da daddare bayan an gama wasu test likitan ya sake jaddada mana abinda suka shaqa masan guba ce me qarfi....kuma idan ya wuce yau bai farka ba ICU zasu maidashi.....cikin hukuncin Allah sai gashi ya farka da yake yaji a jikinsa duniyarsa tana hanyar zuwa gareshi". Kunya sosai ta sake kama sabreen,tayi qas da kanta tana jan mayafinta. Abba da annin duka dariya kawai sukayi,saddiq ya bude abincin da sukayi takeaway da complete set da plate da spoons ya soma zubawa kowa ma'u tana tayashi.


*_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_*
08187255862


𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓 𝐀
_Zafafabiyar_

ΜΆBΜΆOΜΆOΜΆK ΜΆ2

β±§Ι„β‚²Ι„β‚₯β‚³

π™‹π˜Όπ™‚π™€ 128


*_Bgawo's KITCHEN AND APHRODISIAC_*


*_WATA KILLATACCIYAR MASARAUTA CE,WADDA KE QUNSHE DA DUKKAN NAU'IKAN ABINDA KUKESO_*


*_GIRKE GIRKE NA ZAMANI_*

*_KAYAN MAQULASHE DA NAU'IKAN DRINKS KALA KALA_*

*_INGANTATTUN TSUMAMMUN MAGUNGUNAN GYARAN MUTUNCIN 'YA MACE......GYARA IRIN NA IYAYE DA KAKANNI DA INGANTATTUN MAGUNGUNAN DA BABU DUNGUSHE KO KOKWANTO A KANSU_*

*_KALAR MAGUNGUNAN DA SAO WAJEN IYAYENMU NA DAURI.....INGANTATTUN SAUWOYI DA SAQE SAQI DA AKA SARRAFASU ZUWA MAGANIN GYARAN DIYA MACE_*

*_BIKI KUKE DASHI KO SUNA?_*

*_SAUKAR KARATUN QUR'ANI?_*

*_KO KUMA WALIMAR AURE QARIN MATSAYI A GURIN AIKI KO KUMA WANI QWAR QWARYAN TARO?_*

*_KO YAU DIN BAKIJIN SHIGA KITCHEN?,TSAFTATACCE KUMA INGANTACCEN ABINCI KIKE BUQATA A CIKIN WARMERS DINKI KO FOOD FLASK?_*

*_HAIHUWA KIKAYI?_*

*_KO GYARA ZAKIYI KAWAI A MATSAYINKI MA CIKAKKIYAR MACE?_*

*_BGAWO'S KITCHEN SHINE MUHALLIN DAYA DACE DA DUKKA WADANNAN BUQATUN NAKU_*

_Maza garzaya ki tuntubesu ta wannan number wayar_

08104553105
08127084190

*_zaki godemin qwarai da haduwa da BGAWO'S KITCHEN_*


*_BGAWO'S KITCHEN_*
*MATATTARAR BIYAN BUQATUNKU*

___________________________


128



ma'u tana tayashi. Parlor abba ya fita don amsa waya,sai sukaci gaba da tattaunawa a tsakaninsu.

Zukata sunyi sanyi sun kuma samu nutsuwa daidai gwargwado,sauran abinda ke cikinsu bashi da yawa,godiya kawai sukema Allah daya tsallakar dasu daga fuskantar wannan bala'in.

Idanunsa yake saukewa a kansu,kowa cikin walwala yake da farincikin samun kubutarsa.....kowa kuma a cikinsu soyayya da qauna ce irin ta fil'azal tsakaninsu,amma abu guda dake taba zuciyarsa shine sam ba MAAMAH ba dalilinta. Maman daya kamata itace a gaba kafin kowa?,maman daya dace a bisa mizani na hankali dacewa da kamata ace itace damuwarta ta dara ta kowa.....ta d'ara ta babarsa anni.....ta d'ara ta 'yan uwansa,ta kuma d'ara ta matarsa......saidai sabanin hakan maamah din itace halittar da tafi kowacce halitta rashin damuwa da yanayin nasa,sai ya maida idonsa ya rufe yana jin wannan zafin har tsakiyar zuciyarsa.

Saddiq ya gama da kowa farouq ya dubi musaddi

"Zubawa dude ka bashi ko kadanne ko zai karba". Harara fu'ad ya zubawa farouq,yaso ace su anni basu wajen da ya bashi amsa daidai dashi. Idanunsa ya juya a hankali inda sabreen ke zaune tana juya zoben dake yatsanta,don ita ba kowanne abinci take iya ci ba.

"Ke ba zakici abincin ba?" Ya fadi da wata murya can qasa yana mata kallon qurilla. Sau daya ta dago kai ta kalleshi ta mayar qasa tana ci gaba da juya zoben hannun nata.

"Na qoshi". Motsawa yayi kadan yana son gyara zamanshi.

"Zubo kizo nan" Ya sake fada ba tare daya dubi inda anni take ba.

"Yauwa....gwara ka tilastata taci,ko ba yawa aizai zauna,ta yaya kina da lalura amma cin abinci ya zama yaqi ameenatu?". Idanunsa ya sake maidawa kanta,sunan ameenatu yana masa dadi sosai,idan ya kalli fuskarta yakuma ambaci sunan sai yaji tayi bala'in dacewa da sunan,musamman idan ya tuna tarihin asalin me sunan.

A kunyace ta miqe,ta zuba komai dan kadan kadan sannan ta dawo.

"Zauna a nan" Ya nuna mata gefansa. Dan satar kallon anni tayi kafin ta zauna din tana bada tazara kadan tsakaninsu sannan ta ajiye plate din a tsakiyarsu.

Spoon ta zura masa a ciki ta kalleshi,sai ya langabe kai yana bata fuska.

"Bazan iya ci ba.....aikinsan bani da lafiya ko?" Sai kuma yayi qasa qasa da muryarsa yana satar kallon farouq.

"Idan kuma so kike farouq yayi mana dariya ya yadda da gaske ba zaki iya bani kulawa ba to".

"Anni muffin.....anni a gurin"

"Kada ki damu,ita hirartama take dasu saddiq,ita kanta zatafison taga kina kula dani......oya bani abinci" Ya fada yana lumshe idanu saboda yadda yakejin wani yanayi yana ratsashi.

A d'arare ta debo abincin ta taho dashi bakinsa,sai ya kauda kai yana kallonta.

"Eat first" Ya fadi yana tsareta da ido. Fuska ta bata,batasan ta shagwabe masa ba tace

"Hamma.....bazan iya ci ba".

"Zaki iya.....zakici in sha Allah,kada

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login