Showing 381001 words to 384000 words out of 557259 words
nan ya zame hannuwansa daga nata,yaja baya still idanunshi a kanta yana tunanin maamah na parlor din har yanzu ko tabar wajen.
Har takai qofar dakinta ta fasa shiga,ta samu kujera ta zube tana qoqarin qwato koda abu guda ne cikin tarin abubuwan da suke karakaina a kanta.
Da gaske bariki ne zalla za'a gwada mata?......ta samu nasarar mallakarsa ne?,yaushe ta ingizashi zuwa soyayyarta?,tayi imani a banza fu'ad bazaiso mace irinta ba......matar da karuwanci da bariki suka zama shaida kuma tambarinta na farko koda mutuwa tayi?.
Hannuwansa ya miqa mata bayan ya gama daidaita mode dinsa. Bata ko kalleshi ba bare yasa ran zata bashi hannun nata.
"Musunki da gardamarki zasu iya tunzurani na aikata abinda banyi niyya ba.....karki manta kawaici kawai nakeyi miki.....karki yadda kawaicina ya qare......kika bari hakan ta faru.....to tabbas ki rubuta ki ajjiye zan daukeki na kaiki wata duniya da ba wanda ya isa ya ganki sai muhammad fu'ad shi kadai". Fararen idanunta da suka sake glowing saboda siririn hawayen da yake a ciki ta watsa masa,kai tsaye ya saka hannu yana dafe qirjinsa hadi da lumshe idanunsa kafin ya sauke hannun nasa ya saka hannu ya kamo lallausan tafin hannunta yana sauko da ita.
"Kinci bashi da yawa na rashin kula da abubuwan da suka ratayi a kanki nawa......duk wani abu nawa daya kamata ace kinyi bakiyi ba ki rubuta ki ajiye ya shiga sahun bashi". Kasa musanta masa tayi sanda yake riqe da hannunta suna fita a kitchen din.
Hannun kujera ta koma ta zauna tana hade hannayenta a qirji zuciyarta tana mata wani irin zafi. Bata jin zata iya daukan wannan abun sam ba zata jura ba.....tana da shakka idan har zata iya barin sabreen a gefen danta har xuwa lokacin data tanadar mata.
Sanda ta daga idanun nata don sake duban kitchen din sai tayi kyakkyawan gani,yana riqe da hannunta gam da taketa qoqarin zamewa.
"Kina qarawa kanki laifi akan laifi......please ki hutar da kanki" Ya fada yana lumshe idonsa gami da jin yadda riqe hannunta kadai ke sakarwa jikinsa wadansu kaifafan makamai.
"Muhammadu" Ta kirashi da wani kaifi da yake nuna zallar bala'i da bacin rai da zuciyarta ke ciki,musamman data lura bai ankara da wanzuwarta a wajen ba.
_ayimin afuwa a karbi wannan ba yawa,mu hadu gobe in sha Allah_
*_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_*
08187255862
π π π π π π π π
_Zafafabiyar_
ΜΆBΜΆOΜΆOΜΆK ΜΆ2
β±§Ιβ²Ιβ₯β³
ππΌππ 93
93
Kiran data masan yaja hankalinsu shida sabreen din,idanunsu suka hadu karon farko ita da sabreen suka sakarwa juna wani kallon kallo kafin sabreen din ta janye idanunta salin alin tana kuma sulale hannuwanta daga cikin nasa. Ta kowanne fanni jikinta ya bata al'amura da dama akan matar daga kallon farko kawai,ta danne zuciyarta tadan ciji labbanta na qasa ta taka a hankali tana qarasawa gabanta.
Abinda bata taba kawowa zai faru ba,sabreen din ta zame a gabanta tana fadin.
"Barka da yamma". Ruwan mamaki ya gama kasheta,ta dauke idanunta daga kanta tana maidawa kan fuad din. Sam idonsa bai kansu,kamar ma bashi a wajen.
"Turqashi.....ni zaki saka cikin kokwanto?" Ta ayyana a ranta. Cikin kwanakinsu dashi a saudiyya ta dinga jeranta masa huduba da qorafin rashin kirkin matarsa da fatan samun wata kafa da zata sake nesantata daga rayuwarsa.......a yanzun kuma sai ga yarinyar da take complain a kanta zube a gabanta tana kwasan gaisuwa.
"Ta yaro kyau take bata qarko......idan kinsan wata bakisan wata ba yarinya".
"Lafiya qalau......sai yau kika iya tunawa da wanzuwata?" Tayi maganar tanason tabbatar da maganarta ta farko a zuciyar fu'ad da ya fara wucewa zuwa dakinsu.
"Aah fa.....wannan d'iyar tamu sai kin mata uzuri.......tunda mukazo Maldives ba lafiya.....yanzun haka jinya take" Muryar anni ta ratsa plan din maamah din ta kuma wargazashi,sannan ta saukar mata wani irin gigitaccen yanayi daya hautsina kwanyar maman.
"Bata da lafiya?,me kuma ya sameta?" Tayi subul da bakan jefa tambayar dake yawo tsakanin zuciya da harshenta.
"Tashi daga tsugonan nan karki wahala da yawa.......jeki watsa ruwa ki huta,Allah yayi albarka" Anni ya fadi tana taya sabreen ta miqe. Ko waiwayen maamah din sabreen bata sake yi ba......zubewarta a gabanta yana da nasaba da musaddiq.......mutum ne cikakke d'aya da d'aya,wanda ke tsananin ganin kimarta da kuma mutuncinta......idan har zata iya wuce mahaifiyarsa saboda wani abu daban da tsakaninsu ne kawai.....to tabbas bata mutunta mutuntawar da yake mata ba. Ya girmeta amma baya iya gaidata a tsaye ba tare daya duqa mata ba.....dame zata biyashi.
Yadda maamah tabi sabreen da kallo zuciyarta na wani irin duka ya sanya anni sakin gyaran murya. Dawo da dubanta tayi kan annin ita kuma ta basar tana cewa
"Dazun kina tambayar me ya sameta.....lalurarmu ca ta mata......matar aure ai ba'a rabata da qananun lalurori" Anni ta fada tana ajjiye diffuser din da dama ita ta fito da ita ba tare data sake kallon fuskan maamah ba.
Wani dummm taji kunnuwanta har qwaqwalwarta sunayi. Maganan anni maimakon bata haske sai duhu ma data sake sanyata a ciki. Lalura ta mata ciki ko bari?,wanne anni ke nufi a ciki?. Tsaye tayi a wajen kamar sakarya,kafin wani lokaci falon ya sake zama sai ita daya a ciki.
A daren tayi nadamar da batasan adadinta ba na tsananta bincike har kunnuwanta sukaji mata maganar da ta gaza samun amsarta. Magana me harshe damo mafi rudani data taba ji. Idan tace a daren tayi bacci to tabbas me karatu ma yasan tayi qarya,ta qulla ta kuma kwance har batasan adadin sau nawa ba. Tayi rantsuwa ta kuma lashi takobin muddin ciki ne da yarinyar......muddin tayi kuskuren samun juna biyu da muhammadun lallai saita sakata cikin nadama da dana sanin da babu ranar fitarta. Daga qarshe ta yanke shawarar sanya idanu a dukka motsinsu don tasan wanne mizani zata dora mataki na gaba
β
Jiyan tunda wuri ta gama shirinta ta kwanta abinta,don haka daga maamah har d'an nata babu wanda yaga gilmawarta sam. Cikin rashin sani maamah din ta tsareshi wajenta da hirarrakinta marasa armashi,a nata tunanin Daki daya suke kwana,duk da tana kokwanton hakan a ranta,amma zargin cikin da takeson tabbatarwa ya kasa bata nutsuwa ko tabbacin taren suke ko ba tare ba.
Duk da akwai cook dinsu ta musamman dake zuwa musu girki tun a wancan gidan,amma sai ta kasa kwanciya bayan gari ya fara haske. Daga amna har anni da bacci ya dauke saman abun sallah tana tsaka da karatun qur'ani basusan da fitar ba.
Haka kawai takejin bai kamata ace ita da amna duka suna kwance ba har sai sun jira cook tazo. Ta san ba wani qwarewa tayi da kalolin girke girke irin nasu na masu hannu da shuni ba,amma ko yaya tana da rawar da zata taka,tana kuma da gudunmawar da zata bayar,zata kuma iya dafawa aci ba qorafi ko mummunan rashin dadi.
Shuru parlor din nasu,kowacce qofar daki kuma a rufe,haka ta ratsa a nutse har ta isa kitchen din. Bata da tabbacin ya tashi,amma still sai taqi fidda hijabin nata,don ma qarami ne bazai hanata kowanne aiki ba,ta fara duba freezer da ma'ajiyar abincin tana tunanin me dame zata fara aiwatarwa kafin matar ta iso?.
Tunda ta idar da sallah tana saman abun sallar,bawai kuma zikiri ko karatun qur'ani takeyi ba.....aah babu ko guda daya. Ta zauna ne kawai tana gadin lokaci,ta zauna ke kawai tana sanya kunne da idanu akan kowanne motsi da zata iya jiyowa daga parlor din.
Tunda yayi sallar asuba shi dinma bai koma ba,wani irin bacci ne mara dadi kwata kwata ya daukeshi. Zuwa lokacin yana jin kamar haqurinsa yana dab da qarewa,cikin sati hudu anci sati uku.....baisan wanne haqurin zaici gaba dayi ba sama da wannan. A jiyan sanda ya baro wajen maamah yayi zaton daya koma dakinsa zai samu anni ta turo ta,ya fuskanci anni ma kaman tana bayanta ne,banda haka yaci ace an duba lamarinsa an bashi matarsa. Farouq kadai yasan zai iya masa wannan aikin,saidai kuma shaqiyancin farouq din kawai yasan ya isheshi kafin ya samu yayi masa abinda yakeso din.
Kayan jikinsa ya canza zuwa kayan motsa jiki da suka fitar da murdaddiyar surar nan tasa da ginannen jikinsa. Kwana biyun da bai motsa jiki ba sai yake jin jikinsa kaman yana masa ciwo,ya sanya rufaffun takalma a qafarsa ya kashe wayoyinsa ya ajiye ya fito.
Already ya samu gym nan kusa dasu,ba wani nisa ne tsakaninsu ba,don a qasa ya qarasa da sassarfa. Awa guda kacal ya gama ya kammala ya fito,suka jero shida jordan suna magaganu jifa jifa akan abinda ya shafesu.
A nutse ya buda qofar parlor din yana takawa a hankali,idanunshi still akan qofar dakin anni. Idanun nasa ya janye yana lumshesu,yana jin inama zaya samu daman da zai qarasa gareta. Wata kewarta ke ratsashi....kewarta ba kuma iya kewar fuskarta kawai ba......dumin jikinta.....qamshinta.....da tausasan labbanta.....harda tsiwar nan tata da wani lokaci take maidata qanqanuwar yarinya ba tare data san da hakan ba.
Har zai wuce dakinsa yaji yana buqatar ruwa,tunda baishan ruwa yawanci bayan kammala motsa jiki sai bugun zuciyarsa ya daidaita.
A nutse yake takawa xuwa kitchen din,cikin jikinsa da zuciyarsa sai ya dinga jin kaman akwai wani abu me muhimmanci a wajen,kaman yana qara kusanci da wani bangare na musamman daya tsage daga zuciyarsa.
Idanu ya zuba mata sosai sanda yake hangota,kaman shigen jiya saidai yau tana maqale da farin mayafi,tana tsaye gaban tarin Irish potatoes din da take barewa a nutse da peeler. Idanunshi ya lumshe yana kuma budesu duka lokaci guda,yana jin wani abu yana taso masa. Tun daga waccan ranar.....tun daga kuma wancan lokacin zuciyarsa bata sake samun nutsuwa ba,yana jinsa kaman bashi bane,yana jin kamar an sauyashi ne da wani mutum na daban ba muhammad jadda ba. Ta hana zuciyarsa hutawa tun daga wancan lokacin,ta kuma hana masa damar sanin WACECE ITA?. A jikinsa yake jin akwai wani daban tattare da ita.....akwai wani boyayyen labari a bayan wannan matsiwaciyar fuskar.
Kaman jiya dai,yau kam baisan me ya dauke hankalinta har haka ba,gwara jiyan akwai earpiece a kunnenta,wanda sai bayan ya zare yaji abinda take saurara din. Takawa yakeyi a hankali har ya isa bayanta.
"Salam alaikum" Ya fada yana harde hannunsa a qirji qamshin turarenta me wani irin sanyi yana buso masa. Wani irin faduwa gabanta yayi,ta tsorata ainun da jin muryarsa dab da ita,amma sai ta dake taqi waiwayowa,ta motsa labbanta muryarta can qasa ta amsa
"Wa'alaikumussalam" Ba tare data waiwayo ba tana ci gaba da bare dankalin. Shuru ya ratsa tsakaninsu,ya fahimci ba zata juyo bane don haka ya taka yana zagayawa ta gabanta a nutse ya tsaya a gaban nata,tazarar inches kadan tsakaninsu.
Hannu ya miqa kawai ya zare peeler din daga hannnunta,ya kuma miqa daya hannun ya zare irish din da take barewa. Fararen idanunta ta daga da zummar masa tsiwar tata,saidai cikin sa'a caraf suka shige tsakiyar nasa idanun. Da sauri ta kauda qwayar idanunta gefe,duk wani rashin kunya data tanadi yi masa ya soma zurarewa gefe.
"Duk karatun da kukeyi har yanzu baki koyi gaida miji ba?" Ya tambayeta calmly da wani irin sassanyan sauti. Gaza dubansa tayi saboda yadda kwarjininsa yake neman cika kitchen din gaba daya. Wadannan muscles din nasa ba qaramin tsoratata suke ba,har bata qaunar ya sanya qananun kaya. Ita daya tasan me takeji idan ta gansu,ita daya tasan irin qwarin da suke dashi,saita zabi matsawa daga wajen ko zata samu daman shaqar iska me kyau wadda bata gauraya da dumin numfashinsa ba da kuma na turarensa daya qara sanyi saboda cakuduwa sa gumin jikinsa da yayi.
Da qafa kawai ya tokareta,sannan ya daga nashi fararen idanun ya watsa mata,tayi zaton zai janyesu daga kanta don haka bata janye nata ba,idanunta suka sauka a hankali saman redlips dinsa masu tudu da wani irin shape,quarter million din dake zagaye da habarsa zuwa zaman labban nasa ya sake zamewa labban nashi wani ado na daban. Haka kawai tsigar jikinta taji ta tashi,abinda bata taba ji ba tsahon ganinta da duk wani d'a namiji. Qoqarin janye idanunta tayi,da qyar ta samu nasarar yin hakan kowanne sashe na jikinta taji yana daukan sanyi,rudewa taji tana shirin yi kaman barawon daya shiga tuhuma a hannun hukuma.
Wani siririn murmushi daga can qasan zuciyarsa ya qwace masa
"Dama bakisan ni naga dama nake qyaleki ba yarinya" Ya fada can qasan ransa,amma a sarari sai ya juya gefansa saman cabinet din,ya ajiye peeler din da Irish din,ya sanya hannuwansa ya zagayesu ta mazaunanta yana jawota jikinsa da dan zafi zafi,abinda ya bata daman zubewa a qirjinsa kafin ta daga kai tana neman qwacewa.
"Stop ita DUNIYATA" Ya fada softly idanunsa a kulle yana yadda fatar singalilin hannun ta ke gogar nashi tana tayar masa da tsigar jiki.
"When.....sai yaushe zaki fahimci cewa KECE DUNIYATA?" Ya qarasa maganar yana ware idanunshi gaba daya akan fuskarta. Wannan karon kasa jure kallonsa tayi,saita runtse idonta tana hade rai sosai.
"Banaso kana tabamin jiki.....bana so"
"Am addicted to you.......tabaki shine favourite thing a rayuwata gaba daya" Ya maida mata amsa kai tsaye yana me bata tabbaci ya kuma sake matso da ita sosai yana mannata da jikinsa.
Gigicewa tayi sanda taji ta saki ajiyar zuciya tare da tashi ajiyar zuciyar,kunya da wani irin takaici ya lullubeta,abinda taji haduwar jikinsu ya saukar mata ba zata iya shanyeshi ba idan bata bawa zuciyarta daman numfasawa ba......to amma kuma ta dauka a boye ta saki nata ajiyar zuciyar. Fitar sautin ajiyar zuciyar tata ya sakashi ware dukkanin idanunsa a kanta yana dubanta,duba ne na qurilla da son gane meye ya taba wannan zuciyar?.
A gaggauce gama shiryawa tsaf cikin Holland vlisco me asalin tsadar,an xuba mata dinkin manyan mata na buba,ta kuma cika wuyanta da hannunta da kayan ado na gold. Macace me son izza da alfahari,wadda idan tazo guri so samu kowa ya dusashe a gurin sai iya tauraruwarta kadai. Ta tsaya gaban madubi ta tabbatar komai yayi a shigarta sannan ta juya ta dauki wayarta tana nufin fita a dakin. So take ta kasa ta tsare......so take komai zai dinga wakana cikin gidan ya dinga kasancewa saman idonta,bataso tsakanin sabreen ko fu'ad wani yayi wani motsi da zai zarta ganinta da idanunta,wannan karon salon da zata bullo musu dashi na dabanne,har sai ta samu tabbatuwar nasara a gareta. Tanaso da iya dressing dinta kawai ameentu ta fahimci wutsiyar raqumi tayi nesa da qasa,ameenatu ta sake tabbatarwa da kanta cewa ita din fa itace mahaifiya ga muhammad jadda.......ba wata mace a duniya ta biyunta.
Cikin takun isa take fita parlor din tana qarewa ko ina na parlor din kallo. Siyan gida a qasashen waje musamman gidaje irin wadannan ba abu bane da za'ayi maganan qananun kudade ba. Abinda ta lura dashi wasa wasa ameenatu ta maida mata yaro saniyar tatsa kenan,taja wata irin qwafa tana samun sofa guda daya ta hakimce a kanta.
Daga inda take ta sanya remote ta kunna tv,tayi sa'a tashar farko ta kamota a inda suke gabatar da abincij breakfast na yaren mutanen qasar china.
Minti uku kacal taji tunaninta ya koma ga kitchen din gidan,tanaso ta tantance dame dame ya jibge musu suke ci?,wanne irin gadara kuma ake gwadawa a wajen?,don haka ta miqe tsam tana maida flats shoe dinta tana nufar kitchen din.
Yau kam sai data shigo sosai sannan idanunta ya sauka a kansu. Mugun gigicewa tayi fiye da jiyan,saboda yanayin data gansu a yau din yafi na jiyan munin gani.
"Na shiga uku ni mariya!" Ta fada muryarta na rawa tana yunqurin juyawa,wanda saurin da take ta matsa a wajen santsin gurin ya debeta ta kusa zamewa,cikin taimakon Allah ta kama murfin freezer ta riqe tana tsaiwa saman qafafunta.
*_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_*
08187255862
π π π π π π π π
_Zafafabiyar_
ΜΆBΜΆOΜΆOΜΆK ΜΆ2
β±§Ιβ²Ιβ₯β³
ππΌππ 94
94
Daga shi har sabreen din sai a lokacin suka dawo hayyacinsu. Ita ta fara zamewa ta tsakiya tana raba jikinta da nashi haushi yana