Showing 135001 words to 138000 words out of 557259 words
wani irin jan aji da kamewar da bai taba gani a wajen matan titi ba sai a kanta,amma ba komai,yaci alwashin a yau dinnan sai ya banbance mata aya da tsakuwa,dukka wannan jan ajin garawar da wahalar dashi data dinga yi sai ya fansheshi a yau.
Tana gaba yana bayanta kamar ma ba tare suke ba har suka wuce ciki. Bata sake gasgata da gaske yayi booking ba......da gaske lamarin namiji abune me bada mamaki da daure kai ba sai da suka shiga babban dakin daya kama musu,wanda duk kwana daya a yadda ta gani cikin jadawalinsu naira dubu tari takwas da hamsinne. Komai an jere na kayan abinci,isowarsu kawai ake jira. Ya fada saman lafiyayyen gadon da yafi kama da gadon da ake shirin cin amarci a kai yana dubanta qasa qasa.
"Komai da kike buqata akwai an tanadeshi.....amma inajin sai kinyimin alfarma na matse baccin nan ko na awa daya ne cakal.....kiji dadinki yadda kikeso.....idanma akwai wani abu da kike da buqata ga waya can ki musu magana zasu kawo miki" Yayi maganar muryarsa tana maye ita kanta,da alama baccin yayi mugun cin qarfinsa.
Sanda ya miqe yana shirin sabule wandonsa da riga sai ta kau da kanta tana jin yadda zuciyarta tayi wani irin bugawa. Irin wadannan abubuwan take gudu shi yasa bata taba yarda ta biyo kowa wani kebantaccen waje ba,sai gashi haka kawai jib ya takura mata sai tabi mutum biyu don samun cikar aikinsu.
Yif taji ya koma ya fada saman gadon,koda ta maida dubanta sai taga bai iya cire komai a jikin nasa ba,kawai kokawar banza ya gama yi ya koma ya fadi cikin bacci.
Minti goma qwarara ta bashi sannan ta taka ta isa gabansa. Yayi sadidan a baccinsa,taja da baya a hankali tana jin faduwar gaba tace
"JIB yayi bacci"
"Good" Ya fada yana jawo dukka kayan aikinsa.
"Stay tuned.....minti talatin ya wadatar......ki kula da duk abinda zanyi requesting"
"Okay" Ta fada tana jin sanyin jiki da faduwar gaban da batasan dalilinsu ba.
Ganin mintuna arba'in suna niyyar shudewa ba wani labarin nasara,ga mikail yana motsawa lokaci bayan lokaci ya sanyata magantuwa
"Jib.....ya ake ciki?"
"Wannan aikin yayi tsauri da yawa adda.....akwai tsauraran matakai da shinguna masu zafi a kai,yanxun haka abinda na soma fahimta kamar wani abu ya fara alerting nasu anason musu kutse cikin asusun nasu" Ya fadi shi kansa kamar yanajin qarfin gwiwarsa yana son sarewa. Duk inda ya zaci zai samu nasarar balla account din nasu da dukkan hanyoyi da dabaru amma sai yaga abun kamar ya wuce nan.
Daidai lokacin da yake tsaka da meeting da investors din da suka jima suna da shaawar sanya hannun jarinsu a kamfaninsa na jadda diamondchore resources da yake a lagos da kano.....da kuma sabon kamfanin da yakeson yabude din a yanzu na jewelry da sauran dangin kayan ado da qawa na mata.
Daga saman system dinsa wani abu ya fara harbawa. Alamace da take nuna masa DANGER. Sosai ya zubawa alamar idanu,sannan da hanzari ya jawo system din gabansa ya soma bibiyar abun
"What?,scammers?" Ya furta qasan ransa,sai ya kalli baqin nasa yana miqewa tsaye gami da daukan wayarsa
"Excuse me" Yana daga musu hannu tare da takawa a hankali yana matsawa nesa dasu. Sadiq dake can nesa dashi ya kira
"Call the security team na kamfani......ka gaya musu akwai alamun shirin yin kutse su kula".
"Done" Ya fada kaman yadda ya saba gaya masa. Juyawa yayi yana komawa wajen baqinsa,ya koma mazauninsa ya zauna yana jawo system din gabansa.
Hankalinsa ya raba biyu,yana saurarensu yana kuma duba yadda suke samun progress na sake kutsa musu. Alama ta qarshe daya gani ta sanyashi lumshe idanunsa hadi da ture system din gefe kadan ya maida dukka hankalinsa dari bisa dari akan baqinsa.
"Done adda!......done,millions of naira sunyo dropping" JIB ya fadi da wani irin sautin farinciki,yana jin sukuni yana ratsashi na samun cikar mafarkin mutanen da suke rayuwa ruhinsu a jikkunansu.
*D U N I Y A T A*
*_H U G U M A_*
Page 73
"Zan iya tafiya?" Shine abu na farko data tambayeshi ba tare da tabi takan adadin kudin da suka samu cira ba
"Yes adda.... Zaki samu me napep a corner farko na street din yana jiranki gudun samun delay". Katse kiran kawai tayi,ta miqe tana daukar jakarta ta jefa wayar hannunta da sauri tana dan duban yadda mikail yaketa motsawa,alamar koda kowanne lokaci yana iya farkawa,saita wuce kai tsaye ta bude qofar ta fice.
Sai data tsaya da lobby din ta daidaita nutsuwarta da kyau gudun zama suspect a idanun security na hotel din,sannan ta fara takawa a nutse tana qarasa ficewa.
Hankalinsa a tashe yake dawowa wajen fuad din,yama gaza kiransa a waya kaman yadda shi ya kirashi a daxun.
Ta bayansa ya qaraso,yadan rusuna don sanar dashi halin da ake ciki
"Na sani.....jeka jirani mu qarasa mu wuce gida" Ya dakatar dashi ba tare da ya barshi yace komai ba. Da dan mamaki sadiq yake dubansa ganinsa zaune hankali kwance. Duk da yasan yafi gaban hakan amma wannan din ba qaramin abu bane da ya kamata ya ganshi haka a zaune calmly ba yana tattaunawa da investors,to amma bashi da sauran zabi illa juyawa ya tafi din kamar yadda ya buqata.
Tana tafe a hanya tunane tunane cinkus cikin kanta da qwaqwalwarta. Haka kawai taji ta kasa isa gida,sai kawai ta bawa me napep din umarnin suna da wajen da take so ya kaita.
Guri ne very quite,ba cikar jamaa,kuma kowa sabgan gabanshi yakeyi. Hakanan gurin yana da yalwa da fadin da zaka zauna a guri wani ma da yake nemanka bai ganka ba. Order din lemo da ruwa kawai tayi don batajin zata iya cin komai. Batasan me yasa ba.....ba yaune karon farko da haka ta fara faruwa ba amma wannan din yanason tsaye mata gami da sanyayar mata da jiki.
"Eh ba shine na farko ba......amma kuma yafi kowanne nauyi da girma......baki taba samun kudade masu tsananin kauri da yawan wadannan ba,sannan kamar an shiga lalitar wadanda baki taba koda magana dasu ba.....kaman akwai nasu haqqin a ciki". Wani sashe na zuciyarta ya fara tunasar da ita. Wanda qarar ring na wayarta ya katse mata tunanin.
Sunan titi data gani shi ya dauke hankalinta daga dukkan tunanin komai,ba jinkiri ta daga wayar suka fara magana
"Da sauqi.....amma sumanta biyu yau"
"Komai ya qare in sha Allah" Ta bawa titi amsa a taqaice saita katse kiran. Dukka karsashinta taso dawo dashi,ta fara lalubar wata number da jib ya bata.
Ayyuka biyu tayi a wajen da suka qara kashe mata kusan awa daya da rabi. Ta tura dukkan abinda mutumin ya buqata don yiwa titi aishatu da dan rakiya daya visa na fita qasar india da ita da komai da komai da zaa buqata na asibiti lafiyarta da sauransu wanda ya lashe maquden kudin da suka ninka kudin da akayi hasashen zaa kashe din. Abu na biyu kuma ta zauna ta datse ta share ta kuma sake toshe kowacce hanya ko kafa da zata sake sadata da mikail.....sai data tabbatar ta sanya kowanne shinge da zai nesantata dashi nisa na har abada sannan ta tattare komai nata tana fita daga wajen.
_hmmm,anya kuwa kayan Muhammed fuad jadda zasu tabu 'yammata?,to muje zuwa dai muga yadda wasan zai kaya FUAD dinne keda nasara?,ko SABREEN?_
Karo na farko a rayuwarta da taji shigowar sabreen cikin gidan dama dakin gaba daya amma ta shareta kamar ma bataji ba. Tayi lakur saman gadon tana ci gaba da kwanciyarta.
Hirarsu da hameed yau ta dasa mata abubuwa da yawa cikin zuciyarta dangane da yayartata. Tayi amanna ta kuma yarda hameed mutumin kirki ne na qwarai,daga yadda yake yawan mata nasiha da wa'azin ta kare mutuncinta......ta guji yawace yawace da yawan fita barkatai.....don duk yarinyar data fiya fice fice,qafafunta basa zaman gidan tabbas akwai ayar tambaya a kanta ko taqi ko taso,alamar kamewa ga mace shine ta lazimci zaman gida.
A yau din ayoyi qwalli biyu da hadisai guda biyu suma daya karanto mata sunja hankalinta. Itakam hameed yayi mata,a yanzu dukka burinta shine tayi aure......tayi aure ta matsa daga rayuwar da take sake Fahimtar yaa sabreen din tana yi.....ta auri hameed tayi nesa daga cakwakiyar gidansu.....baqaqen maganganu zallar gori da habaice habaice. Ta tabbatar zata samu irin rayuwar da takeso daga wajen hameed,zai killaceta kaman yadda yake fadi din.
Tayi mamaki sosai da taga qofar tasu a bude,sanda ta shiga kuma falon sai ta tabbatar akwai wani a ciki,sai ta aje jakar hannunta ta kutsa uwar dakin.
Gaban gadon hudan ta qarasa tana kiran sunanta. Da farki sai tayi banza kamar bataji ba,har sai data saka hannu ta yaye bargon da take ciki
"Lafiya huda?" Ta tambayeta tana qoqarin son ganin fuskarta
"Lafiya qalau" Ta samu kanta da bata amsa kai tsaye. Wani irin mamaki yaso kasheta a tsaye,amma sai ta cinye wannan. Hudan a yanzun ta fara zama budurwa,shekara sha biyar ta fara hawa bigiren kaiwa yammatanci,tabbas zata iya faskantar canje canjen halaitada dabi'u a tattare da ita kaman yadda ta tabaji mamanta ta fadi a sanda take cika tata shekara sha biyar din,wanda a yanzun shekara biyar daidai kenan
"Idan har lafiya lau huda me zai hanaki zuwa makaranta kuma uhmmm?". Kamar ta bude bakinta ta gaya mata aure takeso,kamar ta bude baki tace ta bawa hameed ita,kamar tace mata ta gaji da ganinta kullum tana fita babu sahihin inda take zuwa,ba makaranta ba ba kasuwa ba,amma sai tace
"Gajiya nayi,amma zani gobe"
"Gajiya?" Ta maimaita qasan ranta,amma a sarari sai tace
"Allah ya kaimu" Ta juya zuwa sashen kayan sawarta tana fidda kayan jikinta don sauyawa da wasu. Can qasan ranta zuciyarta ta kasa samun nutsuwa,sake gaya mata takeyi
"AKWAI MATSALA.....DOLE KI NINKA SANYA IDANUNKI" da wannan tunanin ta kammala canza kayan sannan ta juya ta koma falon don duba me dame akayi da bata nan.
Da kallo ta bita har ta fice,sai taja qaramin tsaki qasan ranta zuciya da shaidan suna ayyana mata ko dame dame ma tayi sanda ta fitan?,caraf kuma wani sashe na zuciyartata ya kwabeta
*D U N I Y A TA*
*_H U G U M A_*
PAGE 74
Kaman kowanne lokaci ya bawa kowa daman yayi order na abinda yakeso qarqashin kulawar sadiq da shike handling kusan komai.
Shi daya ya ware kansa a wani table da corner na daban,ya fidda system dinsa da ya sanya sadiq dauko masa ita. Ranshi a tsananin bace yake,amma kuma yana da wani irin abu,ya iya boye fushinsa idan yaso,ya iya kuma danne abinda yake damunsa,dole da rayuwa sun sanyashi iya controlling anger dinsa.
Yana da matuqar sani da zafi gami da kaifi ta bangaren computer.....ya koma da baya daga baya cikin karatunsa,ya zabi computer science ya kashe lokaci akai har sai daya zama qwararre kuma cikakke akan fannin,saidai ba kasafai ayyuka da cushewar abubuwa ke bashi daman practicing karatun nasa ba,amma komai nasa zaka sameshi a tsare da burbushi da alamu dake nuna yasan kan computer sarai.
A nutse ya soma bin komai daki dai cikin matuqar qwarewa tare da sanin makamar komai. Ba jimawa musaddiq ya iso wajen,sai yayi masa alama yayi joining sadiq kawai. Juyawa yayi yana matsawa daga wajen don tunda ya ganshi a hakan ya bawa system nutsuwarshi yasan akwai abinda yakeyi me amfani.
Ya samu sadiq din yana waya wanda ya kasa jurewa ya kira security team din da kansa. Ranshi a bace shima yake wayar,duk da abincinsa dake ajiye gabansa baiko bi ta kansa ba. Dan zuba masa ido musaddiq yayi kafin ya zauna,jikinsa kuma yana bashi lallai akwai wani abu. Jawo tray din yayi yana bude komai tare da warware spoon da fork din dake nade cikin tissue,ya sanya musu cikin abincin ya saita musu komai saidai still hankalinsa yana kan saddiq din.
Kusan mintuna goma sha biyar da isowarsa kafin ya kammala wayar,ya kasheta ya ajiye yana jan tsaki.
"What's going on?" Musaddiq ya jefa masa tambayar yana dage giranshi. Cup din daya zuba musu ruwa ya jawo yana kurba
"Scammers......hackers.....me ma zance ne musaddiq?". Idanu musaddiq ya waro waje yana kallon sadiq
"A'ina?Meye ya faru?"
"Sun diba maquden kudade daga cikin asusun company dazu........security team dinmu sun kasa aiwatar da komai......hamma fu'ad kuma baisan wanne matsaya ya dauka ba.....duk da nasan bazai qyale ba amma sai naga kaman ya dauki abun da sanya.....ina dai kyautata zaton yanzun yakebin kadin abun kamar ba kudi masu yawa aka diba ba" Saddiq yayi maganar yana maida hankalinsa ga fu'ad dake dan nesa dasu wanda baya iya ganinsa sosai da sosai
"Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un" Musaddiq ya soma maimaitawa yana rasa abun fadi kwata kwata.
Sannu a hankali ya soma bude idanunsa har ya gama budesu gaba daya
"Wayyo......." Ya furta yana miqewa sosai saman gadon yana jin yadda kanshi da idanunsa sukayi fresh. Komai ya sakeshi kenan,babu wani sauran burbushin giyar a tattare dashi,komai kuma zai tafi daidai yadda ya dace.
Idanunsa ya fara wurgawa cikin dakin bai ganta ba,sai ya barwa ranshi tana toilet ne tana shiryawa,don haka ya jawo wayarsa yana yana duba time
"Kai!" Ya fada a mamakance ganin irin baccin da yayi na kusan awa uku maimakon awa daya kacal kaman yadda yace zaiyi. Jikinsa ya danyi sanyi ganin yadda baccin yayi tsaho,zuciyarsa ta raya masa yarinyar nada wani irin aji da wahalar samu tamkar tarwada cikin ruwa,anya zata zauna duka wadannan awannin tana jira?.
"Da kuwa na tafka babbar asara" Ya furta a sarari gabanshi yana faduwa,sai ya jiye wayar ya miqe da hanzari ya nufi toilet din.
Duka bandakin ya duba ba ita ba alamar ta,sai ya fito ya soma duba dakin har zuwa balcony dake gaban dakin,lobby da sauran gurare,hakanan ya dawo zuciyarsa na harbawa da tsananin baqincikin kufcewar wannan damar a garesa
"Wai me yasa ma nasha barasa duk da sunan farinciki?,wannan tsinannen baccin......" Ya katse zancan bayan ya zauna gefan gadon yana dafe kansa da hannayensa bibbiyu.
Yadan jima a haka yana karatun asarar da yayi,da kuma wassafa yaushe zai sake samun irin wannan damar?.
Tsaki yaja sanda yaji wayarsa tana qara. Ya waiwaya yana duban me kiran,john ne chief of security team.
"Ubanshi zan masa......ya barni naji da asarar da nayi" Ya fada a sarari yana rejecting kiran.
Sake kira yayi bayan sakanni biyar kacal,hakan ya sake qufular dashi,don daga yanzu har wayewar gari har kwana uku bayajin zai huce daga asarar da ta sameshi.
Sake rejecting yayi,bai haqura ba ya sake kiransa a karo na uku. Wannan karon da niyyar cuccusa masa ashar ya dauki wayar,tunda a tsakaninsu kar tasan kar ne,saidai yana dagawa ya jefeshi da tambayar data sanya ya shiga tunani
"Kana tare da wayarka kuwa?,kasan me yake faruwa?,bakasan anyi kutse account din kamfani ba?". Dif wuta ta dauke masa,sai kuma ya bude bakinsa
" Kai john banason iskanci.....ka sanni na sanka,idan giyarka ka shawo ka daina gigin kirana ka bari ta sakeka tukunna,wayata tana hannuna......kuma ba wani abu daya faru,na sani fa ka dade kana harin muqamina,to qaryarka tasha qarya......in kanaso sai ka jira sai sanda matsayina ya qara daukaka a jadda company sai ka shiga takarar neman tsohon matsayi na" Daga haka ya katse kiran yana mitar shi baisan abinda yake damunsa ba zai qara masa damuwa.
Yankewa yayi kawai ya kirata ya lallasheta ya kuma sake shawo kanta,tunda kudin kwana biyu ma ya biya,ya samu ko wuni dayan gobe tayi masa tunda ya tabbatar ba zata taba dawowa a yau ba.
Saqon da idanunsa suka gane masa daga banking da kamfanin nasu ke ta'ammali dashi ya kusa sanya gudawa da fitsari duka yanke masa lokaci guda. Yayi wani mugun gigicewa sanda ya shiga saqon idanunsa suka haska masa adadin kudaden da aka zare daga asusun.
Wani irin abu yaji yana tsirga masa