Showing 174001 words to 177000 words out of 557259 words

Chapter 59 - πƒπ”ππˆπ˜ATA BOOK1 AND 2 HAUSA NOVEL

HUGUMA   

03 Nov 2025

522

sanyaye.

"To mun gode fa" Hajja ta fadi tana bin bayan maamah da tuni ta fice.

Zumbur ta miqe tabi bayansu tana leqensu ta tsakanin labule,salati da sallallami kawai takeyi zuciyarta na wani irin bugawa. Tunda take a rayuwarta bata taba ganin baragurbin iyaye ba irinsu,shin anya ma da gaske kuwa suke?.

Tsaf nutsuwarta ta dauke,tana jin ba zata iya zama haka ba tare data labartawa kowa wannan zancan ba. Balaraba bata nan tun dazun ta fita.....bata jin kuma zata samu cikakken hadin kan yin magana da daada,don tasan ba kasafai ta fiya shiga shirgunan da ba nata ba,ballantana ma kuma lamarinsu Sabrina din.

Wuf ta fito ta kuma fada dakin daada hankalinta a kansu sanda suke cire takalmansu suna shiga parlor dinsu Sabreen.

"Lafiyarki meye haka bibo?" Daada dake zaune tana gyaran zogale cikin rumfarta ta fada idanunta akan bibo.

"Muhammadur rasulillahi daada.....zo kijimin wata lalacewa....zo kiji wata almara,wai zuwa akayi neman auren yarinyar nan Sabrina?". Tayi zancan tana zama d'aid'ai a gaban daadan.

"Wa'alaikumussalam" Sabreen ta fada a hankali tana daga idanuwanta zuwa ga bakin qofar falon nasu.

Idanu ta zube musu sanda suke shigowa cikin falon,haka kawai taji gabanta yana faduwa akan baqin fuskar da batasan su waye ba. Sai ta samu kanta da miqewa tsaye tana fadin.

"Sannunku da zuwa"

"Yauwa sannu 'yar nan" Maamah ta furta cikin murmushi yayin da hajja ke qarewa sabreen din kallo wadda ke sanye cikin soft Egyptian bubu me mayafi,amma madadin mayafin sai ta sanyawa kanta hula wadda santsin gashinta ya hanawa hular zama daidai,kaman ma ta mata kadan sakamakon nannadadden gashin data daure a qeyarta.

A nutse ta taka zuwa ga fridge dinsu tana lalubar musu ruwa,yayin da su kuma suka dinga bin dakin da kallo suna ganin zallar banbanci tsakanin falon da sauran falukan gidan,wanda hakan ya sake jaddada musu zarginsu.

A hankali idanun maamah ya fada kan babban hotonsu guda daya dake kafe a falon. Sabreen a tsaye huda a zaune a gabanta,nadra da haneefa suna zaune daga dama da hagunta. Idanu ta tsura musu tana kallon yadda suke kamanceceniya da juna,tana mamakin kuma yadda sam sunan yaran bai fito cikin bincikensu ba.

Gabansu ta ajiye ruwan sannan ta koma da baya ta zauna a nutse tana kallonsu.

"Barka da warhaka" Ta fadi tana qoqarin karantarsu,don ta fahimci akwai wani kallo na daban qasan idanunsu da sukeyi mata ita da falon.

"Yauwa sannunki 'yammata.....ya kike ya garin?" Hajja ta fada da murmushi

"Alhamdulillah.....wa kuke nema?" Ta tambayesu kai tsaye,don itadai tasan dukan wanda yake alaqa ko mu'amala da ummensu na kusa kona nesa ya jima da sanin rasuwarta,tun suna zuwa wadanda basu sani ba daga baya har labarin ya game ko ina,kuma an jima sosai da sunan anzo wajenta.

"Ke muke nema wajenki mukazo" Hajja ta sake fadi har yanzu tana murmushi

"Ni kuma?" Ta tambayesu a mamakance

"Eh ke" Hajjan ta jaddada mata

"To gani,Allah yasa lafiya"

"Lafiya qalau sai alkhairi......yaronmu mukazo nemawa yardarki ki zame masa matar aure" . Tamkar tana karanta tatsuniyoyin gizo da qoqi haka taji zuwan zancen kunnenta,daga inda take zaune ta daga idanu tana kallonsu,kalmar aure tana maimaituwa a kunnenta.

"Aure kuma?,bam fahimta ba,ya sanni ne?,idan ya sanni munyi jarjejeniyar aure dashi?"

"Kwantar da hankalinki,baki sanshi ba bai sanki ba.....hasalima mu muka shirya abun". Idanunta ta sake azawa sosai a kansu tana musu kallon masu tabin qwaqwalwa a wannan karon,kamar wasu qananun yara?,hadin aure kaman wasan 'yar tsana?.

" Eh.....zakiji abun wani iri ko?...."

"Da zaki daure ki tafi bayaninki kai tsaye da sai nafi fahimta" Ta furta a gajiye da zamansu a wajen,don bata fatan su huda su dawo su samesu cikin falon.

"Dalla dalla zan miki yanzu yammata......auren KWANGILA ne,shi mukeso kiyi da d'anmu..... Wanda dukanmu mu dake zamu amfana gaba daya,zaku fimu samun moriyar abun ma,don ke da kanki zaki yanks adadin kudin da kikeso kafin aikin da kuma bayan aikin......ga mahaifiyar yaron da kanta zata tsara miki yadda takeso abun ya kasance".

Da wani irin madaukakin mamaki ta maida idanunta kan fuskar maamah,uwa kuma?,uwa da nemawa d'anta auren kwangila?,wacce irin uwa ce wannan?.

Mutuwa tayi murus a zaune sanda maamah ke karanto mata qudirinta,har ta kammala ta kasa janye idanunta a kansu.

"Muddin komai ya tafi yadda nakeso......zaki zama wata abun kwatance cikin ahalinku......hakanan zaki gane a baya wahala kawai kikeyi.....zakiyi arziqin da me kamoki cikin danginki sai yayi da gaske,zaki samu kudin da rayuwar wadannan zata zama rayuwa mafi gata" Maamah tayi zancan idonta akan sabreen hannunta kuma yana nuni da hotonsu dake bango tanason ganin reaction din sabreen akan hoton.....don ta fuskanci wani abu kadan daga gareta.

"Basu da alaqa da dukka wani aiki ko kwangila......ki sauke hannunki daga saman hotonsu" Sabreen ta furta da wani irin emotion idanunta itama tsaye cikin na maamah.

Wani shu'umin murmushi maamah din ta saki,sai ta sauke hannunta a hankali,ta samo abinda takeson samowar,kuma tabbas lallai komai zaizo da sauqi.

"Aure na gaske ko na wasa,na kwangila ko wanda bana kwangila ba baya cikin tsarina hajiya,bama wannan deal din ba.....koma meye a yanxu bani da sha'awarsa......bana buqatar komai bana buqatar kowa!" Tayi zancan da wani fushi fushi da kuma dakewar zuciya.

"Koda wannan shine aiki na qarshe da zakiyi sai kin mana wannan yarinya......ina me baki shawarar ki kwantar da hankalinki kibi kawai......cikin sati daya ko biyu ma zuwa wata daya idan buqata ta biya kina iya tafiyarki.....kada ki yarda akan wannan ki jefa rayuwarki cikin hadari".

"Bazanyi ba" Ta furta idanunta a lumshe kuma a nutse,saidai kuma batasan me yasa zuciyarta take wani irin tsananin bugu ba. Bawai barazanarsu bace ta tsoratata kota dameta ba,don ba kalar barazanar da bata gani ba,to wadannan su ko nasu qalubalen yasha banban da sauran?.

"Zata iya yiwuwa" Zuciyarta ta gaya mata kafin muryar maamah ta sauke a kunnenta.

"Kwana daya kacal kike dashi kan bayyanar yardarki......idan kika haura haka kuwa.....zamu tilastaki ki yarda koda baki so ba" Ta qarasa maganar tana matsawa gabanta ta ajiye kudi masu yawa da rubutacciyar number wayarta,sannan suka juya suna fita daga dakin salin alin. Dole ta bude idonta ta rakasu da kallo,ta rasa abinda take ji a qasan ranta,tsoro ko fargaba?,wanda dukkansu bata sansu ba,ko kuma shakka ce ko kokwanto?.

Suna shirin sanya takalmansu su huda suka shigo,kallon kallon sukayi a junansu su hudan na mamakin ganin fitowar baqi daga dakinsu,abinda suka manta rabon dasu gani,ganin yadda baqin ke kallonsu sai suka gaidasu,suka amsa kuwa cikin fara'a,su suka wuce suma suka fada dakin.

"Ban taba zato ku tunanin yarinyar nan zata watsar da damar samun kudade masu kauri irin haka ba" Hajja ta fada sanda driver ke tuqasu don maidasu gida.

"Na fiki mamaki hajja,anya bayanan da muka samu a kanta babu na bogi?"



*D U N I Y A T A*

*_H U G U M A_*

PAGE 94


"Nima na fara wannan shakkar,saidai kuma na yarda da aikin hidima.....ya iya aiki fiye da zatonki,wannan ya sanya bamu rabu ba tsahon shekaru" Kai maamah ke jinjinawa

"Ta yaro kyau take bata qarko.....a wannan karon zata fahimci duk wanda ya rigaka kwana sai ya rigaka tashi".

**Duk wata jijiya dake harba jini a jikinsa kyarma take,kaman yadda ya jiqe jalab da gumi a sanda yake zaune saman kujerar cikin shaddarsa dataji aiki,kadan daga shigar yiwa talauci jan kunne daya fara yi a kwanakin kenan a cewarsa.

Zaman MUHAMMAD JADDA a gabansa a yanzu sai yakeji kadan yake da banbacin zaman mala'ikan mutuwa a gabansa. Ya tsinewa Mikhail dake zaune a qasa da mato yafi sau shurin masaki,hatta da wanda ya shirya cacar ya tsine masa a ransa har baisan adadi ba.

Wallahi inda yasan akwai wani daya jibanci muhammad jadda ma sam da baiyi kuskuren hada caca dashi ba ballantana akai ga karbar dukiyarsa,bai sani ba.....qaddara kuma ta rigayi fata.

"Dukka wannan abubuwan daka lissafo malam rufa'i matsalarku ce.......abinda nakeson tambayarka shine.......nawa ta raba ta baka kayan ta qwamushe kudade daga account na kamfani na?" . Gigicewa ya sakejin yayi da saukar tambayar da baiyi zatonta ba ballantana tsammani.

"Sabrina?" Sunan da yazo masa a cikin zuciyarsa kenan,saidai abinda bai sani ba ya zarce har zuwa saman harshensa sautin sunan kuma ya bayyana a kunnen fuad da Mikhail dake zaune a wajen.

"Yes" Fuad ya furta yana yin relaxing bayansa a jikin kujerar yana kuma qarewa kawu rufa'i kallo tare da karantar duk wani motsi nasa.

Salati kawun ya dinga debowa a tsakanin rude,daga sama zuwa qasa,daga qasa zuwa sama. Wani irin tashin hankali yakeji yana saukar masa,wacce irin masifa ce Sabrina din keson jefasu?.

"Wannan yarinya anyi 'yar Allah bani......yallabai....wallahi wallahi bansan da komai ba.....gagararriya ce dama ta fitinemu,tunda uwarta ta sanya qafa tabar duniya shikenan yarinyar ta zama kangararriya........wannan aikin nata na kwashe kudaden akawunt na al'umma dama na jima inajin qishi qishin dinsa......batun zamowarta karuwa kuwa na jima da sani......"

"Dakata" Ya tsaida kawun ranshi yana tsananin baci. Dukka komai ma akan yarinyar gaskiya ne kenan?,komai da komai ya gama samun tabbatattun shaidu da hujja.......a nata tunanin har takai riqar da zata shiga gonarsa?,idan har ta saba shiga shirgin wadannan tarkacen maza.....tana tunanin muhammad jadda zai tabu?.

"Ba kowanne namiji take saurara ba......tana da girman kai da izza......sai namijin da taso tayi alaqa dashi.....koshi dinma yana gwaruwa kafin ya samu ta fara saurarensa......amma ni yallabai,ba abinda ya taba faruwa tsakanina da ita duk da naso hakan ya faru,amma aurenta naso yi,saidai kwata kwata aure baya gabanta,shine cikin jerin sahun lissafin abu na qarshe da take tunanin wataqil watan watarana idan tana raye zatayi,hasalima zancan aure dana fara mata dashi ya kawo rashin samun cikakkiyar fahimtar juna a tsakaninmu.....hakanan da sunan FATEEMA NA SANTA". ya tuna maganarsu da Ya'aqoub kenan a jiya bayan ya sanya an kawo masa shi a wani kebantaccen guri.

Tashi yayi ya zauna sosai yana harde yatsunsa cikin juna gami da zube idanunsa akan kawun idanunsa a samansa,fuskar nan shimfide da wani lafiyayyen fushi daya cakuda da izza da kuma miskilanci. Yanaso ya tuna hukunci guda daya mafi tsaurin da zai musu......yanason ya musu hukuncin da zasuji a jikin su,saidai kuma yanaso hukuncinta yafi zama mafi tsaurin da ba zata sake gigin maimaita kusakuren data aiwatar a baya ba.

"Rufa'i kake ko?" Ya jefa masa tambayar yana furzar da iska me zafi daga bakinsa.

"Na'am yallabai.....labbaika" .

"Inason kai da d'iyarka ku hadamin kudina nan da awa ashirin da hudu,ficika a ciki banaso tayi ciwo,naira biyar idan babu a ciki zata iya zame muku matsala..... Muddin kuwa ba haka ba......" Kawai sai ya girgiza kai ba tare daya qarasa fadin abinda zai fada din ba,ya maida bayansa ga kujerar yana jawo wayarsa ya fara latsawa hadi da bawa banza ajiyarsu shida Mikhail din.

Yadda cikin kawo ya karta ya bada wani sauti zata zaci zai tsinke da gudawa ne,cikin kwanakin yaci kudin da baisan iya adadinsu ba,wanda maidasu a yanzun wani gagarumin tashin hankalinne da baisan ta ina zai tarosa ba. Uwa uba sabreen.....yarinyar dake da matsiyacin taurin kai da daukar kasadar da yasan ko sama da qasa zasu hade ba zata fidda abinda ya shiga hannunta ba.

"Tana da taurin kai da kasada......wonderful" Ya qarasa maganar yana maida idanunsa saman fuskar kawu rufa'i ba tare daya motsa daga yadda yake a zaune ba.

"To me zai hana ku bani aurenta a madadin kudin da kuka cimin kai da ita?". Tsananin mamaki da rudu ya sanya kawu rufa'i rikitowa daga saman kujerar sai gashi ya zube a qasa a gaban muhammad fu'ad

" Wallahi tallahi yallabai mun baka.....na yarda munci sadakinta harma da sauran kudin hidimar aurenta....."

"Oh.....da kana tunanin wani kudin daban zan lissafa na baku?" Fu'ad ya fada very calm yana dage dukka girarsa idanunsa akan kawun.

"Inaaa yallabai.....wane mutum?,wane aikinsa?" Ya fada yana jijjiga kai da kalar mamakin daya kasa sakinsa.

"Oya.....kaje ka shaida mata ka bada aurenta nan da sati biyu kacal masu zuwa"

"An gama ranka ya dade" Kawu rufa'i ya miqa kaman babbar rigar jikinsa zata tadeshi ya fadi ya durfafi qofa,jordan ya bude masa ya fice babu ko waiwaye bare ya tuna da Mikhail daya bari a ciki.

πŸ”…Idanun bibo akan su maamah har suka fice daga gidan,saita dawo a gaggauce ta sake zama gefan daada

"Kin gansu can daada......don girman Allah daada ki dubamin zancan nan fa?". A karo na biyu daadan ta sake dubam bibo bayan ta dauke kai daga farantin zogalenta

"To wai ke meye naki a ciki bibo?". Kaman ta harari dadar sai kuma ta daure

" Haba mana daada,don ke yaro daya Allah ya baki yana can saudiyya baisan me ake ciki a qasar nan ba?,fisabilillahi ace duk kamammun 'ya'yanmu a rasa wanda zaa zo neman aure cikinsu sai wannan tambadaddiyar?"

"Duk tambadar tata kin gaya musu,kuma sunce sunji sun gani,ke meye yayi miki saura a ciki?" Daada ta sake jefawa bibo tambayar. Bata da amsa amma kuma bata gamsu har yanzu da cewa ta zuba idanu wannan abun ya tabbata ba. Iya leqen da tayi qofar gida taga motar da sukazo a cikinta ya sake dasa mata kwadayin duk yadda zatayi ta tabbatar likita hadiyya ce ta shiga wannan ahalin,saita miqe ta fita da sassarfa zuwa dakin Sabrin.

Duk su huda sun wuce ciki sunata qoqarin sauya uniform dinsu zuwa kayan gida,su kuma killace sauran. Tana nan zaune inda suka barta ta kasa koda motsawa wanda ita kanta batasan dalilin mutuwar jikinta da fargabarta ba.

Ciki ciki ta amsa sallamar bibo din,don duk sanda ta ganta a dakin ba wani ba wata,ba tantama ba alkhairi bane ya kawota.

"Ashe sun tafi.......lalatattu mutanen banza da wofi,haka ake zuwa neman aure?,mata ma da zuwa neman auren idan banda lalacewa?" Saita soma sakin kuka tana matse hawaye

"Allah sarki rayuwa......Allah ya jiqan alhaji da rahama,mutuwa me tonon silili,banda baka wai yau shine har wasu matan ke takowa gidansa da sunan nemawa diyarsu auren dansu?,yaron da ba'asan asalinsa ba?".

Idanunta sabreen ta lumshe sannan ta budesu lokaci guda,tana jin muryar bibo har tsakiyar kanta ne

"Don Allah ki fita.....banason hayaniya" Tayi zancan a nutse tana yamutsa fuska.

Haba bibo ta kama,yarinyar dake da wannan halin tun yanzu inaga ta shiga gidan arziqi har haka?,tabbas ba shakka sai inda qarfinta ya qare

"Wato abun arziqi ma bai karbi kare ba ko?,don inason kare haqqin zaman tare?,a gidan waye ya shigo miki bandani?,to kuwa muddin na haifu ga cikin sahura da labaran bazan sake shiga shirginki ba"

"Da dai yafi miki" Sabreen din ta furta qasa qasa tana jan qaramin tsaki sanda bibo ke fita a dakin gwiwa ba qwari. Taso taji sauran bayani daga bakin sabreen din yadda suka dade a dakin,taso kuma taji meye matsayar yarinyar akan mutanen.


𝗗 𝗨 𝗑 π—œ 𝗬 𝗔 𝗧 𝗔

𝙃 𝙐 𝙂 𝙐 π™ˆ 𝘼

π™‹π˜Όπ™‚π™€ 95


Wani zuzzurfan numfashi sabreen ta sauke,tana jin yanayinta gaba daya yana sauyawa. Tun daga tunaninta bugun zuciyarta dama komai nata. Zuwan mutanen ya kasa barin zuciyarta da idanunta har ma da kwanyarta.

"A ina suka sanni?,su waye su din ma tukunna?" Wadannan sune tambayoyi masu ban tsoro da kuma qara sanya mata firgici. Qasan ranta kuma zuwa yanzu takejin ya kamata tayi qaura daga ainihin inda aka Santa,ta koma wani bigire na daban wanda ba kowa yasanta a wajen ba don sake lullube kamanninta dama komai nata,tare da sake bad da sahu da dukkan wata alama da zata alamtawa masu farautarta inda take.

Saidai kuma......wani hanzari ba gudu ba,har yanzu tana tattalin MUTUNCI,har yanzu kuma tana matuqar girmama kalmar MUTUNCIN MACE.....kalmar da tayi imani tayi adabo da ita daga idanun mutane da yawa.

******Dukkaninsu shuru sukayi kai kace ruwa ya cisu. Ba abinda kawu rufai yakeyi sai sharce zufa tare da mutsu mutsu kamar wanda wani abu yake cizo. Gefe guda mutumin dake kusa dashi ya sake sauke zuzzurfar ajiyar zuciya,ya kuma miqe ya zauna sosai yana tura hularsa baya.

"Rufa'i.......baka da wata mafita akan buqatar muhammad jadda......"

"Ina naga mafita rabi'u?.....aini godewa Allah kawai nakeyi nake kuma sakeyi.....don na tabbatar inda wa'adin biyan kudinsa ya sanya mana da mun bushe.....wallahi bani kadai ba ba kuma Sabrina ba......dukkan danginmu qwanmu da kwarkwatarmu......waye zai iya fada dame kudi?,wa ya isa yaja dame kudi?,wahala ma kenan rabi'u" . Kai babban aminin kawu rufa'i yake jinjinawa,banbancin ra'ayi wajen sana'a shi ya kawo nisan alaqa kadan tsakaninsa da rabi'u din. Sam rabi'u baya hanyar caca ballantana yayita,suna kuma yawan samun sabani da kawu rufa'i akan hakan,wannan ya sanya indai kaga kawu rufa'i yayi shawara da rabi'u to babban al'amarine dake neman nutsuwa da hankali irin wannan.

"Yanzu abinda kawai yake damuna rabi'u......yarinyar nan Sabrina,bansan ta yaya zan bullo mata da batun maganar na bada aurenta ba......yarinyar ta fita zakka a cikin dangi kamar wadda akayi tsugunnon haihuwarta tsakanin fukafukan shaidan....."

"A'uzubillahi" Rabi'u yayi saurin fada yana dakatar da

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login