Showing 141001 words to 144000 words out of 557259 words

Chapter 48 - πƒπ”ππˆπ˜ATA BOOK1 AND 2 HAUSA NOVEL

HUGUMA   

03 Nov 2025

465

kai hannunsa saman dan qaramin table din da aka zube masa sabbin newspaper din bayan an kwashe na jiya.

"Lafiya alhamdulillah sir"

"Ma sha Allah" Ya furta yana bude page din farko na jaridar ba tare daya tsaya karanta bangonta dake dauke da title na labaran ciki ba.

Labarin farko suka wafci idanunsa. Ya sake dawowa da baya bayan ya karanta layin farko da akayi da manya manyan zane. Bai tsaya bata lokaci ba ya koma bangon don sake duba title din da ya tsallakeshi a dazu. Tabbas duka abu guda suke nunawa cikin harshen turanci

*_GAGARUMAR SATA.....AN WAWASHE KOMAI DAGA ASUSUN JADDA DIAMONDCHORE RESOURCES/AKWAI YIWUWAR DURQUSHEWAR COMPANY DIN NAN DA WANI DAN LOKACI_*.

Jaridar ya juya tamkar ma ya manta wanne gidan jarida ne suka kafe labarin. Sai ya maidata ya ajiye yana dauko newspaper ta gaba.

Ita dinma kaman wancan,bangon farko abinda yake rubuce kenan a jiki,ya sake juyawa shima ya duba gidan jaridar sai ya maidata itama din ya ajiye,ya sake daukan ta uku.

To ita dinma babu wani canji,duka dai labari guda daya ne,abinda ya bashi tabbaci da yaqinin wannan shine labari na farko da zaiyi trending kenan yau a duniya kasuwanci.

Idanu kawai yaci gaba da zubawa rubutun kamar wanda kwanyarsa ta kasa gano komai,ya daga idanunsa a nutse da suka fara sauya launi ya kalli ameh daketa goge dining din da kyau don kawar da qura datti ko maiqo komai qanqantarsa daga muhallin cin abincin boss din nasa da ya sani da tsananin tsafta da rashin son qura ko datti komai qanqantarsa

"Ameh......dauki waya ka kira sassan saddiq.....i wanna see him yanzu yanzu".

"Yes sir" Ameh ya amsa masa yana sakin komai,sannan ya gangara a hankali yana nufar inda wayar take girke.

Daidai sanda ameh ya gama shaidawa saddiq saqon fuad farouq yayi knocking daga can first door sannan ya turota a hankali ya shigo. Yana sanye da kayan motsa jiki da alama fitowarsa kenan daga dakin motsa jiki na gidan,wanda dama kusan kullum shine qarshen shiga,fuad kuma na farko,saddiq da musaddiq ke binsa daga baya.

Dauke yake da jaridu har guda uku a hannunsa,kallo daya fuad yayi masa ya karanci shima labarin ya gani kuma shi ya shigo dashi. Fuskarsa a dinke ba walwala ya samu kujerar dake fuskantar fuad din,wannan ya sanya me sunan malam ficewa ba tare daya gabatar da abinda ya kawoshi ba,hakanan ameh shima ya wuce ta kitchen ya bulla ta baya yabar sassan.

"Tun jiya naketa qoqarin ganinka.....duk da dare yayi sanda kuka dawo nayita nemanka ban samu ganinka ba........yanzu da safe kuma sai naga wannan" Ya fadi yana zube masa jaridun hannunsa. Binsu yayi da kallo sannan ya maida dubansa kan fuskar farouq

"Nima haka na tashi na gansu farouq"

"How comes fuad?" Ya furta tsananin bacin rai yana cin zuciyarsa. Kanshi ya motsa kawai yana girgizashi kadan

"A lot of things farouq......bansan ma ta inda komai ya fara ba......na kuma rasa ta inda zan kamoshi......inajin kamar ana warwaremin tunani na ne......da farko wawashe asusun kamfani ta sigar da ba wanda zai iya yinta sai na kusa ko wanda yasan sirrin asusun......ina cikin aikin kamo zaren kuma sai ga wannan......wannan fantsamar labaran tabbas shiryayyen abune koda kwashe kudin ba shiryayye bane.......zakafi kowa fahimtar anyi ne don a yiwa kamfanin illa......ta yaya babban kamfani kamar namu da yake da hannuwan jarin manyan 'yan kasuwar duniya ace saboda tsananin rashin tsaro har za'a iya kutsa kai ciki a debe kudin mutane?......wanne tabbacin tsaro muke dashi da zamu baiwa dukkanin wanda yake da buqatar kasuwanci damu?,wannan shine tuhumar da xamu fara fuskanta daga wajen al'umma......waye ya fidda labarin cikin qasa da awanni uku,har ya zamana labarin da kowanne shafin jarida suka maida bangon labarinsu?". Kai farouq ke gyadawa cikin zuzzurfan nazari,ya daga Idanunsa ya sake duban fu'ad

"Shi kansa kwashe kudin nan baka tunanin aike ne?,ture ne?,kuma suna da alaqa da wanda ya fidda labarin?". Mintuna kusan uku fu'ad din baice komai ba,kansa yana sake qullewa,sanda ya bude baki zaiyi maganar sadiq ya shigo sanye da jallabiyya hannunsa riqe da system.

Kallo daya dukansu sadiq din yayi musu ya fahimci sunga komai,tun da sassafe kiraye kirayen wayoyi suka tasheshi,kusan fitar labarin su suka hanashi fita motsa jiki tun daga sallar asuba daya koma. Yana tunanin ta yadda zai iya sanarwa da fu'ad din abun,amma kuma yasan zai wahala awannin safiya su wuce bai sani ba tunda shi din ma'abocin bin shafukan jarida ne.

"I hope abba baiji komai ba ko bare anni?" Fu'ad yayi tambayar tsananin fuskar farouq da sadiq. Junansu suka kalla kafin farouq ya amsa

"Zai wahala abba bai sani ba,tunda kasan yana bibiye da kafafen yada labarai,annin dai ita zaka zatarwa haka" Kai ya girgiza yana yin qasa da kan nashi,yasa hannunsa yadan shafi qasan wuyansa.

"Yanzu mene abunyi?" Farouq ya tambayeshi yana kallonsa.

"Dole komai ya kasance cikin hikima da kuma tsanaki,hakanan for now dole mu zama cikin takatsantsan da sanya ido akan kowa,faruwar wannan kadai ya sake gayamin tabbas akwai wasu qofofi dana bari a bude......akwai wasu bayanai namu tabbas da suke fita.....akwai wanda kuma yake dauka yakai din......sadiq " Fu'ad ya fadi yana dubansa

"Na'am hamma"

"Inaso kabar kowa a haka,kada ka sake amsa waya ko maganan kowa.....amma ka shiryamin meeting na sirri,koda me sunan malam banason yasan da zaman.....ka tsara awannin da zamu zauna din zuwa tashi,zai fara daga goma na safe har sai sanda na buqaci tashi......general meeting nake buqata"

"Okay hamma" Ya fadi yana sauke system din saman cinyarsa cikin qoqarin duba schedule dinsa na yau yayi cancelling wasu ya kuma gyara time na wasu koda akwai yiwuwar zai iya gabatar dasu.

Sun jima da farouq a wajen suna tattaunawa kafin farouq din ya miqe ya wuce nasa sassan da zummar shiryawa,don yanason ya bishi zuwa kamfanin.

Sai qarfe tara saura suka fito,kaman ko yaushe ya taka zuwa sassan anni. Kowacce safiya takan zauna a parlor har sai taga ficewar kowa zuwa wajen sana'arshi. Yau dinma tana zaune cikin riga da zani na lallausar atamfar super exclusive me ruwan sararin samaniya da ratsin ruwan ganye. Ta lullube jikinta da tattausan mayafi dan turkey daya dace da atamfar,dukka hannayenta siraran awarwaro ne masu daukan idanu da suka dace da fatarta da batayi komai na darajar kulawa nutsuwa da kwanciyar hankalin da take ciki.

Kamar kullum kuma kaman ko yaushe ya duqa gabanta suna gaisawa. Yau din bata ja zance dashi ba saboda ta karanci kaman gaggawar fitar sukeyi.

"Muhammadu" Ta kirashi sanda suka gama sallama ya juya zasu fice


*D U N I Y A T A*

*_H U G U M A_*

PAGE 77


A nutse ya waiwayo sannan ya amsa

"Na'am anni......akwai wani abunne?". Kai ta girgiza tana jin tausayinsa hakanan yana tsarga mata. Tasan cewa akwai abubuwa da yawa da suke damunshi cikin zuciya,amma shi din wani irin mutum ne me masufar zurfin ciki. Zai wahala kaji ya b'ara ko kaji kukanshi.

"Kaman akwai wani abu ko?" Ta jefa tambayar gareshi don batason fitowa kai tsaye ta Qureshi da tambayoyinta

"Ba komai anni" Ya fada cikin bata tabbaci,don yayi imani ya nuna mata akwai damuwar,to yinin yau gaba daya haka zasu barta cikin rashin sukuni.

Kai ta gyada ba don ta yarda ba,sai don tasan koma meye idan ya dace ta sanin shine mutum na farko da zai fara gaya mata

"Ubangiji ya kauda dukkan abunqi,Allah yayi jagora"

"Ameen ya hayyu ya qayyumu anni,na gode" Daga haka ya juya yana fita. Har cikin ransa yakeji irin wannan addu'o'in nata,duk kuwa da cewa bawai shi daya takewa adduar ba kowannensu ne,amma yakanji a ransa kamar tasa ta dabance.

Bai shiga mota daga parking lot na gidan ba,sai yace su fiddo motocin su sameshi waje. Ya soma takawa a nutse suna jerawa shida farouq suna tattaunawa kadan kadan har suka fito a gidan.

Sanda suka doshi gidan nasu yayi tsammanin farouq zai dakata daga yi masa rakiya amma sai yaga yaci gaba da binsa har suka isa bakin gate. Sun gaisa da malam saidu cikin girmamawa sannan suka kutsa kai ciki,guards dinsa guda biyu dake biye dashi suka dakata suna jiran fitowarsa.

Tunda ta wayi gari ta kasa tabuka komai,tana kwance kawai a daki tana kwancewa da saqawa bayan doguwar wayar da sukayi da hajja harira. Anya kuwa nasarar da take sanya ran samunta zata cimmata?,zata ma iya haqurin kwana ukun da bokan ya deba mata kuwa ba tare data koma ta sanar dashi komai ba?.

Maida tunaninta tayi tana sarrafa shawarar da hajja hariran ta bata. Bata jin cewa shawarar zatayi aiki har ta lanqwaso mata me babban suna yadda takeso?.....anya bazai zama doguwar hanya me wahala ba?.

"Waye ne?" Tayi tambayar cikin izza sanda taji an nace da knocking mata qofar bedroom

"Nice hajiya.....yallabai ne yazo" Me aikin ta furta a qasqance

"Yallabai?,fu'ad kenan?" Ta tambaya a mamakance tana duba lokaci

"Eh shine" Ta sake amsawa a ladabce. Cike da mamaki ta kalli agogo. Wannan ba shine lokacin da suma saba shigowa gareta ba,me ya kawoshi yau da safe?,ko dukka cikin dabaru da salon son kauce mata ne?.

"Ina zuwa" Ta amsa mata sannan ta fara yunqurin saukowa daga saman gadon.

Tun daga nesa ta zuba idanunta a kansu,hira suke qasa qasa da wani irin kusanci da emotion da zaka tsammaci su din tagwaye ne da ska rayu qarqashin mahaifa guda daya. Bata ga wani banbanci ba ko kadan tsakanin danta muhammad jadda mamallakin kamfanin haqa da sarrafa diamond ba.....da kuma farouq hamza kibiya me kamfanin saida tsabar abinci da taki ba!.

Meye ribar suna da yayi?,meye amfanin salon banbancin kasuwanci tsakaninsu muddin a idanu zaka dinga hangar yanayin sukunin rayuwa iri daya tsakaninsu?. Kamata yayi ace ana hangen tazara tsakaninsu,kwatankwacin tazarar dake tsakanin bawa da uban gidansa.

Wani irin abu yayi mata tsaye a wuya,amma dole ta saita yanayin fuskarta sanda ta isa gabansu

"Wato farouq kayi wuyar gani,har gwara sadiq ya fika kirki anfi ganinka" Dukkaninsu ba wanda zancanta ya kwantawa,saidai kawai sun bita da irin yanayin da tazo musu dashi. Wannan faran faran sa sabuwar maraba da iyalan Alhaji hamza kibiya sabuwa a idanunsu da basu taba ganinta ba.....koda kuwa sanda ta dawo ta iske iyalinta cikin kyakkyawan rayuwa qarqashin jagorancinsu da tallafawar rayuwarsu.

"Wanne irin aiki ne ya riqeku jiyan kaida dan uwanka kuka saka halartar kira na?" Tayi masa tambayar daketa cin ranta,don har xuwa lokacin bata gamsu wai aiki ne ya riqeshi ba

Yana murza yatsun hannunsa idanunsa samansu,zuciyarsa na wani irin motsa cikin yanayi maras dadi. Koda yaushe maganarta babu komai ciki sai zallar son kanta a ciki......ba wani sauti alama ko yanayi na kulawa ko nuna damuwa......ba wannan shaquwar da maganadisu dake tsakanin uwa da danta da har zata iya karantar yanayin damuwa walwala ko farinciki da yake ciki,abinda dukka ta rasasu anni kuma ta haye kansu ta zauna sosai.

"Yanayi ne na aiki da zai iya rutsawa dakai ako wanne yanayi ko lokaci" Ya amsa mata a taqaice don bawa kansa kariya .

"Yau kuma fa?" Ta sake fadi tana tsareshi da dukka idanunta

"In sha Allah" Kawai ya fada shima nan a taqaice.

Duka duka zaman bai wuce na mintuna goma zuwa sha biyar ba suka wuce. Mintuna goman da suke da matuqar tsada da daraja a wajensa......don ita din itace.....yana jin ya wajaba ko yaya ya bata wadannan mintunan don tserewa tuhumar ubangiji.

Fadin ma yanayin daya kwana a cikinsa a wannan ranar dare har ya zuwa safiya bata baki ne. Duk sanda ya waiwaya ya sake duba wayarsa sai ya dinga jin abun kamar mafarki......kaman baccin daya kwanta shi yakeyi,kaman har yanzu idan ya farka zai samu komai ba gaske bane.

Daga sallar magariba har ishai saida safe ya hada da asuba ya ramasu. Gaba daya ya wani firgice ya fita hayyacinsa a tsakanin. Ba abinda yake iya tunawa sai wanene Muhammed jadda da kuma irin hukuncin da zai iya dauka a kansa.

Duk yadda yaso ma ya yiwa kansa hasashen ta inda zai fara kare kansa a gaban mutumin da a fagen aikinsa baida maraba da zakin daya fito farauta sai yaga sam zantukan daya tsara ko kadan basu hau kan saiti ba,basu kuma dace da hankali ba. Tsananin tsoron da firgicin ya sanyashi kashe wayoyinsa gaba daya,saishi kadai cikin dakin tamkar tsohon mahaukaci.

Ba abinda kunnuwansa ke gaya masa sai sautin sallamar talauci cikin rayuwarsa,an debi kudin da ya tabbatar baida abun biya koda kuwa zai saida komai daya mallaka shi da danginsa su koma yawo tsirara.

Taku biyu yayi don shiga toilet ya rage gudawar da yake fama da ita tun faruwar abun idanunsa suka fada kan dan kunnen.

Gabansa yayi wani mummunar faduwa sanda kwanyarsa ta haska masa wani abu lokaci guda tamkar haskawar walqiya cikin duhun dare.

Tsugunnawa yayi ya dauki dan kunnen.....sai yanzu ma ta dawo kwanyarsa,sai yanzu tunaninsa ya soma haska masa wani abu

"Fateema?" Ta maimaita ainihin sunan da shine nasa STAMP din data bashi.

Komawa yayi ya zauna saman kujerar dake daura da qofar bandakin yanason tuna yininsu na jiyan a tare.

Yayi dukkan wani flash back daga qwaqwalwarsa zuwa zuciyarsa da kuma idanunsa,ba wani motsi nata guda daya daya bashi alamun rashin gaskiya a tattare da ita

"To amma me yasa na farka na nemeta na rasa?" Ya jefawa kansa tambayar data sanyashi miqewa ba shiri,ya jawo wayarsa da baiyi shirin kunnuwa ba ya kunnata,cikin ransa yana jin gamsuwar tabbas ita ta aikata ko kuma tana da hannu wajen afkuwar komai.

Sanda wayar ta daidaita sai ya fara yunqurin kiranta,saidai a duk sanda zai kirata din sai computer ta datse kiran ba tare da an masa bayanin komai daga danganci network ne babu a area din da take?,ko kuma wayarce dungurun gum a kashe?.

Ci gaba yayi da gwada kiran babu qaqqautawa,har sai daya sare,energy dinsa yayi qasa,ya tabbatar bazai cimmata a waya ba.

"Sai kayi tattaki ka sameta a inda take" Wannan shawarar ta sakashi zabura ya miqe,ya zura takalman qafarsa a gaggauce,saidai yana daukan key din motarsa komai ya tsaya masa cak

"A ina take?,a ina kuma zaka sameta din?" Zuciyarsa ta jefa masa tambayar data kusa tsaida numfashinsa

"Na shiga uku" Ya fada yana jin dukka jikinsa yana rawa

"Bansanta ba,bansan komai a kanta ba" Ya fadawa kansa da kansa idanunsa suna tara hawayen da babu makawa sai da suka yiwa kansu qofa

"Garin ya akayi haka?" Ya sake tuhumar kansa da kansa,abinda ya sanyashi sulalewa ya zauna a wajen.

Yafi qarfin awa biyu zaune ya kasa hasalawa kansa komai,kafin daga baya wata zuciyar ta bashi wata guntuwar shawarar data dan bashi nutsuwa kadan,har ya iya miqewa ya gyara rigar jikinsa ya maida hularsa ya lalubi qofar fita.

Dukkan wani muhalli da yasan sun taba haduwa,cin abinci,shan ice cream,shopping da sauransu ba wanda baije ba. Saidai duk inda yaje din dogon bayani ne maras fa'ida ko kuma alfanu,domin ba wanda ya ganeta. Abinda bai sani ba shine......ita din tamkar tarwada take a cikin ruwa......tana da matuqar santsi da idan taje waje zai wahala ka sake samunta a nan... Muddin taje waje dakai sau daya ta kansile wajen kwata kwata cikin jadawalin rayuwarta,ba guri bane da take mu'amalantarsa ba a koda yaushe ballanta fuskarta ta zama sanniya a wajen mutanen dake yawan xiyartar wajen ko kuma ma'aikatansu ba.

Tun yana zagayawa da qarfin gwiwarsa har ya sare. Zuwa sannan yanajin zai haukace ne idan bai gayawa kowa halin da yake ciki ba,don haka yana isa Bristol baiko koma dakinsa ba ya kira mato a waya.

Tazarar minti ashirin kacal ya iso,ya shigo dakin yana cewa

"Kai matsala ne dakai,wani lokacin sai ayita faman kiranka baka dagawa,tun jiya nake danna maka kira kaqi dagawa......gobe ne za'a zauna cacar nan fa......"

"Shut up mato!" Ya dakawa mato din tsawa,don maganarsa a sannan daidai take da yana buga masa abu me qara a kunne.

"Lafiya uban gidana?,me kuma ya faru?"

"Mato na hadu da 'yar damfara......na hadu da

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login