Showing 555001 words to 557259 words out of 557259 words

Chapter 186 - πƒπ”ππˆπ˜ATA BOOK1 AND 2 HAUSA NOVEL

HUGUMA   

03 Nov 2025

3535

dake da shekaru biyar neman ummenta takeyi bare sauran da suke da hankali.

Ya kasa gayawa kowa abinda ya faru,yadai ce musu tana masallacine kawai. Sannu a hankali hankalin anni yakai kai,saboda yaran da suka matsa da qorafin taje ta dade a masallacin.

Zaman jiransa sukayi har yaran sukayi bacci bai shigo ba,yana can yana dubata a ciki da wajen masallacin. Bai shigo ba sai daya baza masu duba masa ita,wai ko madeena ta koma daya daga cikin gidajensa?,saidai acan dinma duka daya ne bata koma ba ba wanda yaga gilmawarta.

Nigeria ya karkata kiran nasa,tsakanin abuja lagos da kano,can dimma duka daya,don bata je musu ba.

"Innalillahi wa inna ilahi raji'un" Kawai shine abinda ya dinga maimaitawa,a rayuwarsa wannan shine ainihin color din tashin hankali tsurarsa daya taba gani ido bibbiyu.

Yana kallon wayarsa na ruri da numbers na anni da maamah,kowacce kiranta yana katsewa na 'yar uwarta yake fadowa,amma ya gaza daga koda yatsansa ne bare ya amsa musu.

A jikinsa yake jin bazai iya komawa masauki ba,idan ya koma da anni da maamah da dukka yaran me zaice musu?,sai kawai ya wuce bandaki ya sake alwalarsa ya dawo gaban ka'aba yayi salla raka'a biyu ya sake istigfari sannan ya zauna ya durqushe yana roqon Allah cikin qanqan da kai da neman afuwarsa da agajinsa.



*_NACE BA......._*🧏🏽🧏🏽

*_Hajjaju a ina kike siyan turare?....._*

*_NACE A INA KIKE SIYAN TURARE?_*

*_Ga wani fa........TASTED AND TRUSTED ne.......mun gwada munga ingancinsa_*

*_Da yardar Allah saikin godemin_*

*_KUNSAN DUK INDA QAMSHI YAKE ZAKA SAMENI A GURIN,MAGANAR GASKIYA KENAN AHTO_*πŸ˜‚πŸ˜‚

Golden oud
Hawi
Sandal balls
Sandal flakes
Cotton bakhoor
Kabbasine mix
Khumra(alba,alsuma,ebony,monarch,musk)
Deep crush (luxury khumra).
Signature oil
Kuleccham
Kabbasine spray

*_YA SUBHANALLAH.....hajiyata dukka wadannan zaki samesu a_*

*_PRIME SCENTS(the scents of royalty_*

*KE DAGA JIN SUNAN KINSAN ZA'A ZUBDA QAMSHI ME AJI DA DAUKAN HANKALI*

*SUNA NAN A*

*_No 3,kabiru sani lawan street,farawa layout,Maiduguri road kano_*

*BA'A KANO KIKE BA?*

*_karki damu,tuntubeta ta nan,TABBAS kayanki zasu iskeki a duk inda kike cikin aminci da yardar Allah,NA BAKI TABBACIN HAKA_*

*DANNA RUBUTUNNAN DON YIN MAGANA DA ITA KAI TSAYE*πŸ‘‡πŸΎπŸ‘‡πŸΎ
wa.me/+2348103155915

KO KI KIRATA TA NAN

08103155915𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓 𝐀
_Zafafabiyar_

ΜΆBΜΆOΜΆOΜΆK ΜΆ2

β±§Ι„β‚²Ι„β‚₯β‚³

π™‹π˜Όπ™‚π™€ 177



*_Domin qulla huldar kasuwanci damu,HUGUMA CLOSET.......,siya ko siyowa wani,reposting ko sari akan farashi me rahusa da babu irinsa,maza yi joining group namu don samun ingantattun kayan da babu ha'inci a ciki da izinin Allah_*
https://chat.whatsapp.com/FrqgC0YmUWP4FPmUzYuLJX
_________________________
*_PLEASE FOLLOW MY TIKTOK PAGE_*

https://www.tiktok.com/@huguma.closet?_t=ZM-8y1pf9yfIVZ&_r=1




177


Baisan adadin lokutan daya kwashe a wajen ba,baisan mutun dari nawa ne suka zauna suka kuma tashi ba a wajen. Har zuwa sanda ya soma jin wani siririn sautin kuka daga gabansa.

Guri ne da mutane masu damuwa da buqatu kala kala ke zuwa,don haka baiko dago ba yaci gaba da abinda yakeyi,saidai kukan dayaci gaba da tashi ya fusgi hankalinsa don sautin Sabreen yake ji sosai.

A hankali ya matsa zuwa gaba,ya kuma daidaita zamansa daidai da inda ta zauna. Jin mutum kusa da ita sosai ya sakata daga kanta,idanunsu suka gauraya dana juna,take kowannensu wani qaqqarfan abu dake riqe da zuciyarsa akan dan uwansa ya motsa.

Fatali tayi da abun,ta kuma yi zumbur ta miqe kamar wadda cinnaka ya cijeta,saidai ko gama daidaita batayi saman qafafunta ba shima ya miqe,hakan ya sanyata ta fara hanzarin barin wajen,don tabbas inda tasan zai fito da tsakiyar dare irin haka ita ba zata fito ba.

"Sabreen" Ya dinga kiranta da tausashiyar murya sanda suka fita a haramin gudun kada ya janyo hankalin jama'a kansu.

Kaman ba zata amsa masa ba........amma wata raunanniyar zuciyar ta gaza jure jin yadda yake jera kiran sunanta da wata irin sassarfa wadda tafi qarfin tata tafiyar,saboda qoqarin tsere masa da takeyi sai data hada da gudu gudu.

"Ki dakata sabreen".

" Bana buqatarka" Maganar data cake masa a tsakiyar qirjinsa kenan. Bazai iya jure jin sake fitar wata magana haka daga bakinta ba,don haka yayi taku uku qwarara sai gashi a gabanta,baiyi wata wata ba kuma ya dagata cak kaman yadda ya saba yi mata. Ya raina jawota da hannu daya ko dagata kaman yarinya qarama,saita fara wuntsila qafafunta tana magana cikin kuka.

"Ka saukeni......bana buqatarka,kace ka daina sona fa.....kai kacemin na tafi.....na tafi kenan bazan dawo ba,kuma nima na daina son......." Ai bai iya bari ta qarasa ba ya manne bakinsa da nata,wanda cikin second kadan qafafunsa suka soma qoqarin kayar dasu saboda wasu irin taurari da suka soma kewaya jininsa.

Sauketa yayi ya hadeta da bangon wani gini dake kusa dasu,ya sake lalubar bakinta ya shigar dashi gaba cikin nasa yana aike mata da wani irin zuzzurfan kiss.

Hawaye kawai takeyi,ta kasa hanashi,ta kuma kasa tsaidashi,kaman yadda zafin maganganunsa suka kasa cirewa daga kanta.

Sai daya galabaitar da ita gaba daya,ya kuma zare duk wani tasirin fushi da yake iya hanga sannan ya zare kansa daga gareta. Hannunta yaja ya zaunar saman wata concrete chair dake wajen shi da ita duka suna sauke numfashi kaman wadanda sukayi tsere.

A madadin ya zauna,sai ya zame yana tsaiwa saman gwiwoyinsa. Hannunta ya kamo ya sanya tsakiyar nasa hannun.

"Sabrrr" Ya kirata da wani irin taushi daya sanya taji wani sanyi ya sauka tun daga tsakiyar kanta har tafin qafarta.

"Sabrrr" Ya sake kiranta wannan karon saita lumshe masa kyawawan idanunta kawai da suka sanyashi yaji kaman ya hadiyeta ya huta

"Ki amsamin don Allah.......kice na'am hamma idan baso kike na zauce miki ba".

" Hamma" Ta furta tana ware idanunta da suka wani zuge saman fuskarsa. Sosai yaji abun ya sokeshi,me ya shigeshi ne haka jiya?.


"Please forgive me my world......forgive me.....am mad duniyata.......i hurt your feelings......ki yafemin......bazai sake faruwa ba,ke na batawa amma ni na karbi hukuncin,'ya'yanki da iyayenki da qannenki dukka sun zuba mini ido ja fiddo musu madame dinsu......in fact ni kaina zuciyata da kanta fushi take dani,don na haramta mata ganinki.....na haramta mata kasancewa dake". Yayi dukka maganar yana dora hannuwanta saitin zuciyarsa dake fama gudu.

Hannunsa guda daya ya zame a nata,ya danganashi da saitin ka'aba sannan ya fara magana.

"Ni muhammad fu'ad......daga rana irin ta yau nayi alqawarin bazai sake bari hawayen bacin raina ya zuba a idanun ameenatu na ba.....idan har kuma hakan.......".

Da wani irin sauri ta zame daga inda take zaune tana riqe dukka hannayensa biyun tana girgiza masa da sauri.

"Kada kayi haka......kowanne zaman aure dauke yake da qalubale.....komai dadi kuma wataran sai an bata ran juna......nima ina bata maka rai fa hamma......sau nawa ma......amma saika dinga yi kaman ma ban bata maka ba......kawai abu daya ne banaso ka sake fada don Allah". Ta fadi hawaye yana silmiyo mata,da alama maganan ita daya tayi mata ciwo fiye da sauran komai. Kafin ma yaji abinda zata ce din ya dora kanta saman qirjinsa yana lallashinta

"Mene ne?,me na fada sabrrrr?".

" Kada ka sake cewa zaka iya rayuwa babu ni......don wallahi ni bazan iya rayuwar da babu kai a cikinta ba". Wani abu me nauyi yaji ya sake sauka saman zuciyarsa game da ita,ya runtse idonsa sannan ya budesu.

"Sabrrr" Ya sake kiranta a tausashe.

"Na'amm hamma"

"Adda na" Ya sake kiranta yana jin kaman ya maida agogo baya ya shafe abinda yayi mata.

"Muffin" Ta motsa labbansa tana kiransa da sunan da yafison ji a bakinta sama da kowanne suna

"Wallahi Allah mugun maqaryacine ni indai akan wannan ne......zan iya rayuwa babu ke?,ko na daina sonki?,babbar qarya ce wallahi wallahi da babu ta biyunta a duniya".

Sam sam ta mance da mode dinta sai wata irin dariya data kwashe da ita. Yayi matuqar bata dariya yadda ya taqarqare yake siffanta kansa da siffar da tasan yafi tsana guda uku a rayuwarsa. QARYA YAUDARA DA HA'INCI.

"Mijina ba maqaryaci bane......ban taba ganin mutum me gaskiya irinsa ba........a shekara goma sha shida ban taba tuna wata tana daya batamin rai ba koda sau daya kuwa.....don me bazan masa shaida ta cikakken adali ba?,tabbas dana zama cikakkiyar butulu kuwa idan na tuhumeshi akan wannan laifin qwaya daya". Dagata yayi cikin jin alfahari da ita,ya kalli fuskarta sosai ya sumbaci goshinta.

"Allah yasa ke matatace har a aljannah".

"Haka nake fata ka zama mijina har aljanna.......amma akwai albishi daya" Ta fada tana murmushi.

"Wanne kenan?" Ya fada yana dubanta cikin zaquwa.

"Allah karimi ne me karamcin da babu irinsa kaf a halittun duniya.......Allah me boye baiwarsa ne ga bayinsa duk yadda yaso yayi hakanne zai faru.......bayan na fito sanda gari ya waye jiri ya daukeni,daga haram suka kaini asibiti don na huta,sunyimin gwaji abun mamaki sun tarar da cikin da ake rigima a kansa a jikina......kasan watansa nawa hamma?" Ta qarasa fada a mugun sanyaye tana aza hannunsa saman cikinta. Kai ya girgiza yana jinsa kaman a duniyar mafarki.

"Wata uku hamma amma dukanmu bamu sani ba.....dama haka yana faruwa?" Wani irin rauni ya kamashi,ya daga tafin hannunta ya sanya saman bakinta wai yana qoqarin controlling farincikinsa kada murna tasa ya furta abinda bai dace ya fada ba.

Sai bayan wasu wasu sakanni ya iya magana da muryarsa me rawa.

"Yana iya faruwa saboda haka Allah yaso ya kasance.......astgafirullah......Allah ka yafemin bisa gaggawa da shishshigin da na yiwa lamarinka......tashi na maidaki cikin ahalinki don basu da wata madadinki" Ya fada yana dagata zuwa jikinsa gaba daya.

"Da alama su suka sanya sabrrrr dina me ma'anar sunan haquri ta zama mafadaciyar qarfi da yaji?" Kunya ta kamata,ta shige jikinsa sosai yana boye fuskarta,ga kunyar albishir din da takeson yi masa.

"Hamma two embrayos........ina fata su zama dukka baby girls,abinda na zauna na yita roqa maka kenan......sunan waye da waye zaka saka?".

" Sunan maamah.......da kuma nagartacciyar surukar data haifamin wannan DUNIYAR TAWA" Ya qarasa fada yana matse hancinta me kyau. Dariya ta saki har fararen haqoranta suna bayyana,tana wassafa kuma irin soyayyar da yarinyar me sunan umminta zata samu daga gareta.

"Godiya ga Allah daya bani DUNIYATA na haqiqa......ya fiddani daga wancan DUNIYAR me cike da rudani" Tayi maganar ne a zuci batasan ta fito ba har sai da suka hada idanu ya kashe mata ido daya,kunya ta sakata cusa kanta cikin qirjinsa tana boye fuskarta gami da shaqo tattausan qamshin nan nasa daya mata wani irin dadi kaman bata taba jin qamshin ba sai ranar,da alama za'a fafata kenan,da alama kuma wannan cikin meson zuminci da babansa ne,don dama tanata mamakin yadda cikin watannin ta sake zama very addicted da lamarin.


*_Tammat bi hamdillah_*


*_Alhamdulillah alhamdulillah,Allahumma lakal hamdu fil ula wal Aakhira_*

*_lallai a rayuwa komai yayi farko yana da qarshe,doguwar tafiya me cike da tarin qalubale masu dadi da sauqi dalilin SUPPORT NA MASOYA_*


*_sau tari wata rayuwa na zame maka mabudin alkhairan da bakayi zato baπŸ₯°_*

*_sau tari wasu dalilan ma zame maka falala me tarin yawa cikin hikimar gwani na gwanaye wajen iya tsara rayuwa da dukkan hukuncinsa da iyawarsa_*


*_wata DOGUWAR TAFIYA da inajin bamu taba irinta baπŸ˜„,wadda a zahiri bazai yuwi nayi shuru ban yaba muku ba ku kanku_*

*_kunyi yawan da bansan wasu bama a cikinku......masoyan da suka dora dambar bibiyar SAFIYYA HUGUMA badon tafi kowa ba.....ba kuma don tafi kowa iyawa ba,sai don saboda soyayya da qauna data zama SILA_*


*_INA MUKU FATAN ALKHAIRI DA DUKKA FURUCIN BAKINA......INA FATAN ALLAH YA SAKE SADAMU A TAFIYA ME DADI IRIN WANNAN CIKIN QOSHIN LAFIYA AMINCI QAUNAR JUNA DA SUPPORTING JUNA_*

*_ALKHAIRIN ALLAH YAKAI MUKU A DUK INDA KUKE AREWABOOKS FOLLOWERS_*

*_ALKHAIRIN ALLAH YAKAI MUKU 'YAN WHATSAPP.....INA FATAN ALLAH YA AMINTAR DA KOWANNENKU YA YALWATA ARZIQINSA DON ALFARMAR SHUGANA S A W_*

*_NAJI DADIN WANNAN TAFIYA MATUQA,NA SAMU SUPPORT DA SHINE QASHIN BAYAN NASARATA A WANNAN TAFIYA DAGA GURIN MABANBANTAN MUTANE,UBANGIJIN AL'ARSHI YA DAFA MANA GABA DAYA_*

*_AMANA/GASKIYA/ADALCI/DATTAKO/KAWAICI SUNE TUSHEN KOWACCE NASARA_*

*Darasin DUNIYATA*

*_KOWACCE RAYUWA AKWAI NATA KALAR QALUBALEN,BA KOWANNE MUTUM BANE ZAKA GANI CIKIN INUWAR DUKIYA KA DAUKA SHIKAM BAIDA MATSALA BA,BA KOWANNE MUTUM ZAKA HANGA KA DAUKA YA SAMU DUKKAN WATA WATA NI'IMA TA RAYUWA BA_*

*_KAYI RAYUWA IYA MATSAYINKA......KADA KAYI MIQAR DA ZATA WUCE TSAHONKA,DUK GAGGAWARKA RABONKA SHINE NAKA,BA ZAKA TABA CIN RABON WANI BA_*

*_BAWA BAI ISA YA YIWA KANSA ARZIQI BA,SAI ABINDA BUWAYI GAGARA MISALI YA HUKUNTA MAKA_*

*_KE UWA!.....BAKI DA KAMAR 'YA'YANKI.....SUNE RAYUWARKI.....KIYI AURE AMMA KARKI YADDA KI FIFITA KOMAI NAKI SAMA DA TARBIYYARSU DA KUMA RAYUWARSU_*

*_AIKATA ALKHAIRI KA WUCE ABINKA KA BARSHI AGUN,ZAI CIMMAKA WATAN WATARANA.....KAMAN YADDA IN KAYI SHARRI HAKA WATARAN ZAI DAWO MAKA_*


_Kusakurai da aka samu a ciki da abinda bai kammalu ba ayimin haquri,na rubutu matuqa har naji rubutu ya ginsheniπŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚_

_wanda na batawa ya yafen,na yafi kowa,kuskuren ciki ubangiji yayi afuwa,ya tattaramu a ladan,ya bamu ikon daukan me kyau a labarin mu watsar da shirme_


Every conclusion sparks a new inception
Nothing lasts forever
Every dawn has a dusk
Ending are part of beginnings in sha Allah

_subhanakallahumma wabi hamdika ashahadu an la'ilaha illa anta,astagfiruka wa'a tubu ilaika_

_Allahumma salli wa sallim ana nabiyyurrahmati_ S A W

08187255862

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login