Showing 447001 words to 450000 words out of 557259 words

Chapter 150 - πƒπ”ππˆπ˜ATA BOOK1 AND 2 HAUSA NOVEL

HUGUMA   

03 Nov 2025

551

dake hannunsa. Kamfanin jaridar yafi kowanne kamfani fidda adadin jaridu siyar dasu da cinikinsu,saboda yafi kowanne gidan jarida fidda labarai latest masu daukan hankali,labarai na gaske da suke daukan hankali tsakanin kwanaki da makonni.

Hannu ta saka ta karba tana dan mita,saboda a yanzun ba abinda tafi buqata irin ya barta ta zauna tayi nazarin hasarar data sake fada mata. Kudade masu ciwo ta biya don wanzuwar aikin,sai data siyar da bangles dinta na gold sannan ta biyashi kudin aikin.

Wareta tayi tana mita a ranta,saidai bata samu sukunin sauke mitar ba tafkeken hoton farko daya mamaye jaridar ya dauki hankalinta.

Hoto ne da alamu suke nuna daga cikin video aka ciroshi,fuskar hajja sosai ya fita,yayin da ita dake gefen hajjan kwata kwata fuskarta bata fita ba bata kuma nuna ba.

Bata sani ba.......ta gurin bugun jaridar aka samu akasi tayi damage?ko kuma ana sane aka lalata gurin?.

Kayan dake jikinta a jikin hoton tabi da kallo,sune dai......sune dai wadannan kayan data sanyasu a ranar da zasuje gidansu sabreen zuwa na farko......gabanta yayi wani mahaukacin faduwa sanda wani abu ya darsu a ranta.

"Na shiga uku?!,me zan gani wannan?" Ta tambayi kanta da kanta hannuwanta suka dauki rawa,da wani irin sauri ta maida dubanta saman manyan rubutun da suke saman newspaper din da aka yisu in bold style yadda zai dauki hankalin harda na nesa.

_CIKIN WADANDA AKE ZARGI KENAN DA SACE SHARARREN ATTAJIRIN KASUWAR GOLD DA DIAMOND KENAN MUHAMMAD JADDA_

Dukka hannunta suka dauki rawa,wata kidima ta saukar mata,ta dubeshi gumi yana sake tsatstsafo mata,yau itace buge cikin calendar da sunan wadda ake tuhuma da satar d'anta?,ba wanda zai aikata wannan sai yarinyar.....don kuwa ita daya take videos din ta tabbatar. Kamar wadda kuka zai qwacewa cikin rawar murya da qwacewa dukkan wani hanzari daga gareta tace.

"Yaushe aka buga wannan labarin?,har ina kuma labarin yakai?". Gyara tsaiwarsa yayi da fuskarsa da bata nuna wanzuwar imani a zuciyarsa ko kadan yace.

"Tun da sassafe....nima a teburin me shayi naga wani yana karantawa,sai naga kaman nasan fuskar,koda na duba sai naga fuskar hajja harira ce.....wannan ta kusa da ita dince dai ba'a gane fuskartata". Wata gauruwa ajiyar zuciya ta sake,tabbas zai wahala a gane fuskartata,amma ga wanda yayi mata farin sani hakan bazai bashi wahala ba sam.

Qarar wayarta ya sanyata zabura tana dubanta,don sam bata tsammanin kiran wayar kowa a irin wannan lokacin. Hannu ta sanya ta dauka tana duba me kiran,hajja harira ce,tayi kaman ba zata daga kiran ba amma sai taji tana buqatar sanin waye.

Karata tayi a kunnenta,tana shirin yin sallama sai sallamar tata ta maqale. Muryar hajja harira ce wadda ta fara da sauke mata zazzafan ashar.

"Ni zaki wulaqanta a duniya?,ni xaki toxarta mariya?,meye ban miki ba a rayuwa?,saboda kin asircemin yarinya na miki shuru?,an gaya miki shuruna yana nufin tsoro ne?,bakisan ja da baya ga rago ba tsoro bane shirin fada ne?,ni xaki buga a jarida akan abinda bani da masaniya?,ke bakisan kuskure bane tarar fada da wanda yasan sirrinka ba?,ganganci ne tarar rigima da wanda yasan waye kai ba?......to kin tara kin samu....mu zuba,dani dake shege ka fasa,hoto na gaba idan kika tashi tsirara zaki sakani......hukuma kuma ina nan ina dakon isowarta gidana,qarqari idan sun kamani su kulleni......idan kuma ya tabbata bani ke da hannu ba dole su sakeni". Daga haka hajja harira ta katse kiran.

Wani tashin hankalin na daban maamah taji yana sauko mata,har numfashinta taji kaman yanason riqewa. Sam ba wani motsi data sakeyi akan hajja harira saboda dalilai.guda biyu. Dalilim farko ita daya ce mutum guda daya data mallaki sirrikanta ciki da bai,birnannun sirrikan da babu wanda ya sansu,babu wanda yasan da zamansu sai ita din tak!. Dalili na biyu laila dake hannunta,tasan wannan kadai ya isa ya zame mata daukan fansa game da cin amanar da hajja taso tayi mata,to amma ko a yanzu ikirari da kurarin da hajja tayi mata bazaiyiwu ta barta ba,don haka ta share gumin fuskarta ta soma tura mata gajeran saqo.

_"kiyi komai harira,bazan hanaki ba,amma kada ki manta a hannu kike,laila tana gaidaki da kyau da kyau,tace kuma na gaya miki ki kula,ki kuma kula da kanki"_

Kamar jira shigar saqon yakeyi wani kiran ya sake shigo mata. Baquwar number ce da haka kawai ta sanya gabanta faduwa,ta dinga bin number da kallo tana raba daya biyu. Special number ce,simple da bata cika tarkacen lambobi da yawa ba,ta jima tana kallonta kafin daga bisani dab da xata tsinke ta daga.

Karo na farko da muryarta kawai ta saukar mata da wani mummunan faduwar gaba da bata taba jin irinsa ba.

"Ina fatan saqona ya riskeki zuwa yanzu?,idan ma bai iskeki ba to na tabbatar yana dab da iskeki......somin tabi ne kenan wannan din.....iname sake aike miki da gargadi.....ki nemo min mijina kuma uban 'ya'yana a duk inda kika kaishi.....ba sassauci ba daga qafa.....idan nar yakai awa saba'in da hudu.......abinda zai faru na gaba yafi qarfin wannan......yanzun ba irin wancan lokacin bane.....lokacin da zaki zubdasu ki watsar dasu a duk inda kikaga dama,yanzun rayuwarsu gewaye take da masoyansu......rayuwarsu gewaye take da rayukan dake buqatar su,suke da muhimmanci a wajensu.....suke muradi da mararin ci gaba da wanzuwa tare dasu,da dadi ko ba dadi.....da dukiya ko babu,da lafiya ko babu,saboda su din akeso.......zallar su din ba abinda ke tattare dasu na ni'ima ba".

Har sai da maamah taji numfashinta ya sarqe guri daya da zafafan maganganun data soka mata,to amma zuwa yanzun ko taqi ko taso tana ji a jikinta itace a hannu,duk da tana ji nadan lokaci ne hakan zata kasance,sai maganan harira da suka gama yanzu ta dawo mata.

_"Kuskure ne tarar fada da wanda yasan sirrinka.....yasan waye kai ciki da bai"_ tabbas a dazun kawai.harira ta bata wani darasi daua kamata ace kanta ya kawo mata,amma ko banza a yanzun ma ta zamu wani ajiyayyen darasi da zai zame mata makamin yaqi tsakanin ita hariran da sabreen.

"Sabreena......ki saurareni kiji.....kuskure kikeso ki aikata wanda zaki dana sani daga baya.....ta yaya zan zama silar batan yaro na kamar a film ko a rubutaccen wasan kwaikwayo?" Wani numfashi sabreen ta sauke sannan tace.

"Komai da kika taba aikatawa a kansu a baya din ai hankali bazai dauka ba......hakanan idan ka saurari labaran ba abinda zai hana kace cikin litattsfan labarai ne ba cikin rayuwarmu ta zahiri ba....."

"Ba maganar baya akr ba......maganar yanzu akeyi sabreen" Maamah ta fada karon farko tana sassauta muryarta gudun ballewar sabreen din.

"Da da da yanzun duka daya ne......ba wani abu da zai canzaki......ko a yanzun akwai wani abu da kikeson cimmawa shi ya sanyaki tsaiwa kina bayanin nan,bawai don kinga ya dace kiyi ba,ba kjma wai don kin damu da batan dama faruwar komai ba......kawai abjnda nake buqata daga gareki shine......ki sakarmin mijina.....ki fice a rayuwata.....kije kiyi taki rayuwar duk yadda kk so kika kuma tsara"

"Bani da masaniyar komai sabreen,karki manta mana.....nifa uwa ce"

"Ni kuma me shirin zama uwar,uwarma kuwa ta gaske ba MUNA UWA BA,uwar data shirya tsaf don bawa rayuwar yaranta kariya.....wadanda zasu zo dama wadanda basu taho ba.....kariya daga dukkan wani kalar farmaki daga miyagu da mafarautan mutane,irin kariyar da sunanta zai tumbatsa da tambarin SADAUKARWA.....sadaukarwa mafi girma kuwa cikin rayuwar 'ya'ya akan iyayensu.....irin sadaukarwar dake sanya kowanne yaro cikin alfahari da kasancewar iyayensa su suka haifeshi". Wani irin nannauyan abu kalamanta suka sauke mata......ta kuma isar mata da saqonni masu yawan gaske da.maganganunta masu harshen damo.

"Ki huta lafiya" Magananta ta qarshe kenan da ita tana yanke kiran.

Mayar da dubanta tayi kan huda dake zaune a gabanta. Tun dazu da abba yazo asibitin yace bai gamsu suci gaba da zama ba,Dr mubeena ta sallameta bisa alqawarin zata dinga zuwa ganinta kullum don samun cikakken kulawa fiye da asibitinma.


*_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_*
08187255862


𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓 𝐀
_Zafafabiyar_

ΜΆBΜΆOΜΆOΜΆK ΜΆ2

β±§Ι„β‚²Ι„β‚₯β‚³

π™‹π˜Όπ™‚π™€ 124



124


"Zaku wuce kaman yadda ani ta buqata.....komai bazai fasa faruwa ba huda....komai kuma bazai sauya ba sai abinda qaddararmu ta tanadar mana". Hawaye sosai huda keyi,duk da yadda take qoqarin riqe kanta daga aikata hakan a gaban sabreen.

"Zamu tafi adda da ciwo da firgici.....zamu tafi ba tare da taqamaimen masaniya akan ina hamma yake ba......yadda ya kula da lamarinmu muma ba zamuyi qasa a gwiwa ba wajen addu'ar bayyanarsa........da kuma tonuwar asirin duk wanda keda hannu wajen kitsa komai da zai illata rayuwar kamilin mutum me taimako irin hamma fu'ad".

Ba qaramin jarumta sabreen din ta nuna ba a sanda suke sallama dasu nadra din da yammacin ranar,sai takejin kaman zata sake tabbatuwa cikin kadaici,ta dinga jin kamar ita daya ta rage a duniyar zata ci gaba kuma da rayuwa ne ita kadai.


*11:30 pm*


A hankali ta farka daga wani nannauyan bacci daya saceta saman abun sallah bayan ta kammala sallar nafilfilu da dukka addu'o'inta,ta kuma cika da sallar nan me matuqar fa'ida da kuma alfanu wato sallar wuturi.

Hijabin da dardumar dukka suna jikinta,alqur'aninta yana ajiye a gefe yayin da tasbahar hannunta ta sulale ta fadi a qasa ba tare data sani ba. Ta qarasa bude idanunta da fadin

"Alhamdulillahi ala kulli hal" Cikin kowanne lokaci idan ta bude ido tsammani takeyi zata ga komai ya wuce tamkar cikin duhun mafarki ne da hasken rayuwa da idanu biyu ya ratsata,saidai duk sanda zata farka din tana samun komai a inda ta barshi,komai yana nan yadda yake.

Fitsari ne ya cika mata mararta,ta sanya hannu ta zare hijabin jikinta idanunta yana sauka saman tray din dake table din gefanta. Komai an shiryashi akai,tasan kuma wannan aikin ma'u ne bisa umarnin anni.

Hatta da dakin suna dawowa annin ta saka aka shiryashi yadda ya dace saboda jin dadinta.

Qafarta tadan riqe saboda yanayin zaman da tayi a wajen na wani lokaci,ta miqe a hankali tana nufar toilet. Ba jimawa ta fito daure da sabuwar alwala,tun daga sanda ta fahimci muhimmancinta ta daina zama babu ita,musamman ita din da tasan akwai mutum irin maamah dake gefe tana farautar rayuwarsu ta kowanne fanni. (Koda baka da masaniyar takun saqa tsakaninka da wani wanda kake kyautata zaton yana 'yan biye biyen shirkarsa,ka tabbatar baka zama ba tare da alwala ba,koba komai ita din haske ce a gareka,ga kuma kariya da zata baka daga dukkan sharrin me sharri).

Wani sauqi sassauci da kuma rangwame take ji duk sanda ta tuna ta sakarwa maamah wani tsoro da firgici,don tana zaune ta shiga shafukan sada zumunta,kai tsaye ta dinga cin karo da labarin yanata trending,ga 'yan qarawa miya maggi da gishiri sunata qawata topic din da kalar qarairayinsu. Har ta gama shawagin ta sauka labarinne ta kowanne handle na bloggers da gidan jaridu mujallu harma da celebrities.

Har zata koma ta zauna taji qishirwa sosai ya kamata. Koda ta duba tray din ba zam zam ma'u ta saka mata ba,ruwan gora ne,tana kyautata zaton kuma batasan ba kowanne ruwa take iya sha din ba sai zam zam shi yasa,don haka sai kawai ta maida hijab dinta ta zura flipp flops dinta ta nufi qofar.

Sanda take takawa zuwa parlor din sai ta dinga jin wata kakkaurar murya tana magana,kaman tasan muryar,kafin ta qarasa tunaninta kuwa tuni ta fusgo mata cewa muryar abdulgaffar ce.

Sunan fu'ad da taji an ambata ya sanya gabanta wani mummunar faduwa,qafafunta suka fara slow suka gaza ci gaba da tafiya da ita,sai kuma suka tsaidata cak qirjinta kaman zai fito waje.

"Mun samu nasarar gano inda yake.......farouq da pilot dinsa sun fitar dashi daga qasar.......suna taipei capital na taiwan,asibitin taipei wellness hospital and resort,mun samu magana da farouq,saidai na lokaci kadanne ya datse kiran,alamu sun nuna bayason kowa yaji.....kuma haka mukayi dashi,ya bani information dinne nima na through waya ba,yace idan zaiyiwu kada kowa ya sani sai abba" Muryar anni rawa takeyi sosai,yayin da sabreen taji wani murdewa da mararta tayi,tanaso taji ya fu'ad yake......tanaso taji halin da yake ciki,muddin ta bayyana ba zasu fadi komai a gabanta ba ta sani.....muddin sukaji motsinta kuma nan ma ba qarasa maganar zasuyi ba bare tasan me ake ciki,don haka salin alin ta sulale tayi zaman dirshan a nan tana dafe hannuwanta jikin wata kujera qwaya daya da aka ajiye a wajen.

"Me ya samesu abdulgaffar.....kada kace zaka boyemin komai" Shuru abdulgaffar yayi yana sadda kansa qasa,har sai da abba ya qagu shima yace

"Zauna ameena.....kaima zauna abdulgaffar....." Dukkansu suka zauna sannan abban yace.

"Dani da ameena bana jin muna cikin mutanen da zaka boye mana komai,shi kansa farouq din nasan bazai taba lissafamu a ciki ba,koda zaice kada a fada din zai fada ne saboda matarsa......tana cikin lalurar da ba komai dama ya kamata a gaya mata ba".

"Ba gatan da zakuyimin abba sama daku gayamin halin da hamma yake ciki" Sabreen da jikinta ya soma daukan wani yanayi ta fada cikin zuciyarta,tana jin kamar ta jawo abdulgaffar ya gaya mata komai da gaggawa.

"Haka ne,sun hari boss ne,a sannan yana tsaye suna magana da jordan,ya kauce basu sameshi ba,yana daga kai kuma ya hangi wanda yayo harbin,baice da kowa komai ba ya soma dosar inda yake hangoshin,daga can sama ne wani guri da ba kasafai aka fiya amfani da wajen bama,ganin ya hangoshi kuma ya nufeshi sai ya sake yin harbin a jere har sau biyu don kada ya samu isa gareshi,to amma kuma baiyi nasara ba,don harbin daya ne ya sameshi a damtsansa,dayan ya sake wuceshi,harbin bai hanashi qoqarin cimma mutumin ba,ganin yana dososhi da gaske kuma dab yake da riskarsa,jordan da farouq na biye dashi a baya sai ya fara hade kayansa zai gudu. Har yayi taku biyu ana ukun ya damqeshi yanason cire hular fuskar daya saka ya rufe idonsa,juyowar da zaiyi kawai sai ya shaqa masa wani abu a handkerchief din hannunsa yana qoqarin zamewa ya gudu,saidai kafin abinda ya shaqa masan ya kama jininsa su jordan sun qaraso,qarasowar tasu kuma yayi daidai da zubewarsa a wajen,basusan waye da waye a wajen yake tare dasu ba,basusan kuma waye ya aikoshi ba,wannan ya sanya kawai suka yanke shawarar komawa dashi su fitar dashi daga qasar,shi kuma mutumin sun sakashi hannun hukuma,He's unconscious har yanzu,wannan dalilin ya hana oga farouq bayyana ko bayyana komai".

"Innalillahi wa inna ilaihi rajiun" Shine kawai abinda anni ke maimaitawa. Komai jinsa sabreen tayi kaman tana saman gajimare ko iska yake faruwa,ta dinga kokawa da numfashinta tanason kamoshi ta kuma kama ayoyin Allah da zasu taimaketa,saidai ta gaza hakan har sai da sautin muryar anni ya bayyana.

"Innalillahi wa inna ilaihi rajiun!!!" Tabi bayan ta anni tana maimaitawa,saidai tata da wata madaukakiyar murya ce data fusgo sautinta da qyar daga maqoshinta,sautin kuma ya iske anni dake zaune tana maimaitata. Cak anni ta dakata tanaso taji sautin daga inda yake fitowa,jin daga inda sautin yake ya sakata waiwayawa tana duban fuskar abba wanda shima ita din yake kalla.

"Innalillahi wa inna ilaihi rajiun!!!!" Kalmar data sake maimaitawa da wani irin gunjin kuka shiya ankarar da anni daga inda sautin yake fitowa.

Da wani gudu anni ta miqe tana nufar wajen hankalinta yana tashi,bai kamata sabreen taji wannan mummunan labarin ba,bai kamata ba,labarin da aketa boyonshi ta yaya ta jishi?".

A zaune ta sameta tanata maimaitawa,wasu irin hawaye sun wanke fuskarta,jikinta kawai rawa yakeyi,durqusawa tayi a gabanta tana kamata yayin da Alhaji hamza ke tsaye a kansu shima yana tayata maimaitawa.

"Me kika fito yi sabreen?,me yasa kika fito?" Anni ta maimaita a gigice tana riqeta cikin tsananin tsoron abinda zai iya faruwa da ita. Numfashinta yana wani iri,ta tabbatar kuma tana da asthma ne irin nata,tana tsoron kada ta sarqeta cikin wannan daren.

Zuciyarta taketa qoqarin bawa dakiya da juriya.......tanata qoqarin maido wannan qwarin gwiwar juriya da jarumtartata,tanason dawo da old version of sabreen dinta. A yanzu bata da wani buri daya wuce ta bude idonta taga fu'ad din,ko a yaya yake......ko a wanne irin yanayi yake sai yafi mata nutsuwa akan zamanta a nan.

"Ruwa zan sha anni" Ta fada muryarta tana rarrabuwa.

Da kansa Alhaji hamza ya koma ya dauko mata ruwan,ya miqawa anni ta bude ta bata sannan yace.

"Maidata daki ameena,muje na bude miki qofa". Riqeta anni tayi har yanzu suna maimaita hasbunallahu wani'imal wakeel tare.

Saman gadonta ta ajiyeta tana jingina mata

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login