Showing 186001 words to 189000 words out of 557259 words

Chapter 63 - πƒπ”ππˆπ˜ATA BOOK1 AND 2 HAUSA NOVEL

HUGUMA   

03 Nov 2025

470

ne haka na alawa da biscuit masu tsada kuma?,ko kantin siyayya zai bude ai sai haka ko?......hadiyya tsame hannunki ki leqa ki ganemin". Zubda ruwan kurkurar bakinta daada tayi,a karon farko tayi magana

"Ke kin fiya ci da zuci wallahi.....wai shinma a kanki kayan zasu zauna?,koma meye ai zaiyi bayani ko?,tunda shima kinsan bakinsa baya shuru".

"Adai dubo din daada abun ya fara wuce lissafi". Ko kafin hadiyya ta fita ta dawo kwalayen sun sake yawa,sai gata tana zare mayafinta

"Aida saura bibo.....shikam yana can yanata bawa yara umarnin aci gaba da shigo dasu". Wannan karon har daada tsaiwa sukayi suna kallon ikon Allah,zuwa wani lokaci da faffadan tsakar gidan nasu yayi hani'an da kaya,muryar nan tasa dake iya tada mutum a barci ta karade tsakar gidan,ta kuma ratsa har kunnuwan Sabreen da haneefa dake riqe da hannun juna a daki.

"Me bacci ya tashi......wanda kuma idonsa yake biyu ya bani hankalinsa ta nan......me aiki ya ajiye aikinsa saina kammala bayani na" Ya qarashe maganar yana saba babbbar rigarsa gami da jawo botikin fenti ya haye sama yana harde qafarsa daya kan daya.

"Lallai ba'a daya a dangi.... Kuma gado ba karambani ba......yau ta tabbata cikin diyoyin dan uwana akwai wadda tayo gadon arziqi irin namu.....ta fita zakka diyar albarka haihuwar asuba" Yayi zancan yana dukan tafin qafarsa daya dora saman gwiwarsa.

Harara bibo ta galla masa tana jan qaramin tsaki

"Kai ka fiya sarqa zance,ba yadda za'a yi kayi magana miqaqqiya......akan meye kake magana?akan kuma wace?" Tayi zancan gabanta yana faduwa,saboda tsoron kada zuwan matan nan a wancan kwanakin yana da alaqa da wannan uban kayan da kwatankwacinsu basu taba shigowa cikin gidan ba.

"Akan waye kuwa nake magana idan ba'a kan Sabrina ba?......akwai wata me qashin arziqinne sama da ita cikin gidan nan?". Sosai takeso ta rufe kawu da balain yadda yake ware 'ya'yansu,yana abu kamar su ba haifarsu sukayi ba,to amma kuma tana buqatar taji kan zancen sosai.

"Sabrina kamar yaya?"

"Sabrina?" Huda itama dake daki ta maimaita sunan tana maida idanunta akan fuskar Sabreen din data tabbatar itama taji sautin futar sunanta daga tsakar gidan nasu da yake tamkar sansanin yaqi wasu lokutan.

Wuf tayi zata miqe,Sabreen tasan fita zatayi taji ba'asin sunanta da aka kama,don haka ta jawota ta zaunar da ita tana girgiza mata kai idanunta cikin nata.

"Sabreen fa......cikin ikon Allah yau na bada aurenta ga hamshaqin attajirin nan da basai ba gaya miki sunansa ba.....zaki gani cikin IV" Baki duka suka saki suna dubansa,banda daada data nufi dakinta tana cewa

"Allah ya tabbatar da alkhairi"

"Ameen hauwa'u....ke da yake baki iya doguwar magana ba" Fara takawa yayi yana nufar dakinsu Sabreen din yana cewa

"Bari naje na fito" Yayi maganarsa gaba gadi yana dosar dakin.



Page 100


Yau din da cikakkiyar sallama ya shiga falon,wanda duba daya Sabreen tayi masa qirjinta taji yayi wani mummunan faduwa. Ta dauke idonta a kansa tana amsa sallamar ta dubi huda.

"Ki wuce ciki ku zauna keda su nadra.....kada ki bari haneefa ta fito" A sanyaye huda din ta miqe,tana jin kamar ta zauna taji da meye kawun yazo dashi. Abune me wahala ya shigo dakinsu da alkhairi,koda yaushe idan kaga ya shigo akwai wani tashin hankalin da yake tafe dashi.

"Yar arziqi......yarinyar kirki,haihuwar albarka,kedai Allah yayi miki albarka,farar haihuwa,ubangiji ya jiqan mahaifinki da mahaifiyarki,ba abinda zamuce da haihuwar diya irinki sai sambarka,kin zame mana marufar asiri,kin zama kuma silar kawo mana hamshaqin attajiri cikin salsalarmu" . Dukka yayi maganar ne yana kallonta,bakinsa cike fal da fara'a.

Wani irin duba take masa,don gaba daya bata fahimci inda maganar sa ta dosa ba.

"Nasan ba zaki fahimci komai ba,amma yanzu zan miki bayani......ungo wannan" Yayi maganar yana ajiye damin sabbbin 'yan dubu dubi din a hannun kujerar da take kai

"Duba tsakar gida daga nan idan zaki iya hangowa....goro alewa da biscuit din na aurenki......wannan kuma" Yayi maganar yana nuna kudin dake kusa da ita.

"Ki cire million biyar kudin aurenki kenan,sauran kuma kyauta suka baki tukuicin auren dansu da zaki yi,kome kike buqata kuma ki samu takardar kiyi list......karki cuci kanki idan da hali ki siyo full scape masu yawa ki raba dare kina lissafawa ba abinda zaifi qarfinsu don akwai.abun fiye da tunaninki".

Cikin kanta da zuciyarta taji tana tantama,anya mafarkin yin arziqi bai soma haukata kawu rufai ba?. Kaman yaji me take tunanin,cikin murmushi yace mata

"Kina kallona kamar na tabu ko?,to wallahi koke na gaya miki wanda ya biya sadakin aurenki saikin zabure.......da farko dai kuma a taqaice na bada aurenki ga Muhammad jadda......mamallakin jadda diamond chores resources LTD....ga sadakinki nan......sati biyu masu zuwa zasu zo da waliyyansa da naki a tara shaidu kowa ya shaida".

Wani wawan duba take masa a kaikaice kamar taga wani tuburarren mahaukaci,yayin da gagarumar jayayya da yaqi ya barke tsakanin bangarori biyu na zuciyarta.

Sashen farko ya cika da fargaba da kuma zulumin komai fa kawu yana iya yi indai akan kudi ne.......kada ya zamana zancansa gaskiya ne.......yayin da wani sashen na zuciyarta kuma kewa abun kallon zancan shifcin gizo ne kawai. Ta yaya zai bada aurenta haka?,sai kace wata diyar 'yartsanar roba ko abun wasan yara?,a haka ake bada aure bada masaniyar kowa ba sai tasa masaniyar shi kadai?. Sam sam kanta ma bazai dauki wannan shirin film din na kawu ba,saidai batasan me yasa takejin muguwar faduwar gaba da wani irin tashin hankali dake cakude da fushi ba,ta zuba masa idanu yayin daya ci gaba da zuba mata bayanan da sam ita bama fahimtar me yake fada takeyi ba. Abu na qarshe data fahimta shine,wayarsa daya ciro yana cewa

"Kawunki na senegal abdulk'adir ya bani damar karba.....yace kuma idan na shigo na hadaku kuyi magana".

"Uncle abdulk'adir?......tashin hankali!" Maganar tayita qasan zuciyarta zuciyartata na wani irin bugu mara misali.

Uncle abdulk'adir.....zazzafan mutum me tsananin tsauri da kafiya......me zafin zuciya da kafewa kai da fata wajen gaskiya.....mutumin da ako da yaushe take kaucewa haduwarsu......mutumin da ko yaushe take qaranta yin waya dashi,mutumin da har yanzu bata yarda yasan ainihin number wayarta ba gudun bin diddigi tsanani takura da kuma sanya idanu......yau shine kawu rufai ke ambata a gabanta?. Da gaske bakin alqalami ya riga ya bushe tunda har sunan kawu abdulk'adir ya fito cikin batun!!!!.

"Kinga ban sameshi ba,dama dazun yacemin yau jumaa sai yammaci yake fita a masallaci.....qila ya kashe wayar da zai shiga,amma ba matsala anjima saina dawo na hadaku".

Batasan takai hannu ta watso kudin qasa daga hannun kujerar ba saida taga kawu na binsu yana tarosu.

"Yaushe mukayi dakai zaka aurar dani ga wani da bansan waye ba?,saboda son dukiyarka da kwadayin abun duniyarka kawu?......" Saita saki wani murmushi daya sanya hankalin kawu ya tashi

"Bari na baka shawara......tunda wurwuri.....tun komai da duminsa kaje ka warware abun nan.....wallahi wallahi wallahi ba wanda ya isa ya auraminshi ko wayeshi kuwa,bansan da wannan zancan ba haihata haihata,ba kuma abinda ya shafeni bane"

"Za kuwa kiyi kaffara aminatu......" Muryar kawu ta isa kunnenta sanda take yunqurin shigewa daki abinta don batason taci gaba da zama awajen.

Yadda yayi furucin da wani qwarin gwiwa ya sakata waiwayowa. Yana tsaye kawun riqe da kudaden

"Zakiyi kaffara.... Don baki da kudin da zaki iya biyan me jadda kudaden kamfaninsa da kika sace......hakanan bani da kudin da zan biyashi kudinsa da na ci a caca cikin rashin sani......ke din fansar kudadensa ce......cikin dattako da kuma alfarma irin tasu duk da haka suka sake biyan wasu kudaden saboda aurenki.......kin shirya yaqi da fito na fito da mamallakin diamond gold da azurfa?".

Qafafunta taji suna yunqurin kayar da ita,maganganun kawun suna mata girma akai dama sassan jikinta tamkar bata da jarumta da qwarin gwiwar iya dauke dukkan bayanansa.

π™ˆπ™ͺ𝙝𝙖𝙒𝙒𝙖𝙙 𝙛π™ͺ'𝙖𝙙


Idanunsa zube cikin na farouq sanda yake masa bayanin yadda komai ya kasance. Yayi relaxing sosai abinsa,yayin da ya miqe dogayen qafafunsa saman table din glass dake gabansa yana sipping ruwan wolf berries da wasu daga cikin 'ya'yansa cikin qaramin cup na glass.

A nutse ya ajiye cup din,me sunan malam ya dauka yana ficewa dashi daidai sanda farouq ya kammala duka bayaninsa. Yatsunsa ya sarqafe waje guda idonsa akan farouq

"Duka wannan hidimar wa ya aikeka tsarata?.....bakasan already ta debi kudin aurenta ba?". Qaramar harara farouq din ya watsa masa yana dora qafarsa shima daya saman daya

" Duka wannan kai ka sani......abu daya nake da matsaya akai......daga gidan dattako muka fito....so dole neman aurenmu da kuma matayenmu susha banban da na kowa......that's all" Kai fuad yake jinjinawa da wani qaramin kwantaccen murmushi can qasan fuskarsa.

"Tunda kuka sake basu dukiyata dole na tsaurara matakan tsaro.......kuma tamkar kun sake lafta musu bashi ne.....don already na sallamesu,nace su lissafa cikin abinda suka dauka su zare kudin komai da komai". Girgiza kai farouq yayi,wai me yake damun fuad ne akan wannan batun?. Duka duka abinda aka basun ma baikai koda kaso daya cikin goman abinda yake fiddawa kusan kullum ana rabarwa mabuqata ba. Gyara zamansa yayi ya sako masa zancan da yafi damunsa tunda suka dawo din......ya kuma tsaye masa a rai.

"Abu mafi muhimmanci da kuma ban mamaki ma.....kai da maamah ashe gida daya.....kuma yarinya daya kuke nema". A nutse ya daga idanunsan nan da wani lokaci suke fita gada gada,wani lokaci kuma su kasance lumsassu kamar wanda bacci ya kama ya zubawa farouq su

"Ba wadannan idanun nace ka watsamin ba......na gaya maka wani abune da yaban mamaki". Dan murmushi yaja kadan,idan bai manta ba farouq ya taba gaya masa bai fiyason ya watsa masa idanunsa ba,don wani lokaci suna masa wani iri da dan sakashi jin kamar ba me babban sunansa ba.

"Maamah tana da nata plan din......kamar yadda nima nake da nawa plan din......so an samu haduwar target duka akan abu daya". Zuba masa ido farouq yayi yana jin zuciyarsa na sake cika da shakkar halin matar,duk kuwa da cewa mahaifiya take a wajen dan uwan nasa kuma rabin jikinsa. Saidai duk inda akaje aka dawo shi din me qoqarin saita fuad ne,musamman akan mahaifiyar daya fahimci shi da ita duka zukatansu sunyi nisa akan abinda suka saka a gaba.

"Kada kayi mummunan zato ko zargi akan yarinyar daka zaba don ta cikashe maka rabin addini da rayuwarka.....hakanan kada ka dora zargi akan mahaifiyar da tayi silar shigowarka duniya".

Wani murmushi ya saki yana sauke qafafunsa qasa,sannan ya miqe ya zauna sosai yana duban farouq

"BB farouq.....har yanzu sai nake ganin kamar baka gama sanin waye Muhammad fuad jadda ba.....any way......komai ina sane dashi,zan kuma ji dashi daidai da yadda ya dace...."

"But....."

"But what?" Ya katsi numfashin farouq.

"Don't make....."

"Ba abinda zai faru dude" Ya sake fadi kawai yana miqewa daga zaman alamun yakai qarshen maganarsa dama hukuncinsa.

Yaji wani irin abu tun daga saman kansa har tafin qafarsa a sanda ya kammala bincikensa kan wacce maamah keson hadasu. Kenan ba wani guri daya kuskure wajen fahimtar hatsarin yarinyar?,zallar rashin tarbiyyarta?,qwarewa wajen iya taku tare da buga kowanne irin wasa da qwaqwale zuciya dama dukiyoyin jama'a?. Kenan ya tabbata itama jan wuya ce tunda ga hadin gwiwa nan ya tabbata tsakaninta da maamah?. Abu daya ne tak! Da baikai ga ganowa ba.....hakanan duk wasu 'yan bincikensa suma basu kai ga ganowar ba shine.....KAN WACCE IRIN KWNGILA SUKA GINA ALAQAR?......MEYE LULLUBE QARQASHIN BATA AURENSHI?. Shidai yasan tasa agenda din.....TO MECECE TASU?.

"zaki gane baki da wayo.....i will teach you a lesson........ You'll learn through experience" Yayi zancan yana fitar da wani siririn murmushi.

Cikin ranshi yake tsara wanne hanya zaibi don ya fara gwada mata nashi salon izzar?,tasa isar?....da kuma qarfin ikonsa tun daga yanzu?". Dakatawa yayi daga tafiyar da yakeyi,yadan waiwaya kadan sashen da farouq yake

"Kace ba?,kunkai sadaki ko?" Ya yiwa farouq tambayar data dan sashi maida hankalinsa akanshi

"Yes.....haka na bawa abba shawara kuma hakan akayi".

"Good boy" Ya fada yana dan murmushi

"Ka gaya musu.....cinta shanta dama fitarta dukka yanzu suna qarqashina......kada ta sake fita muddin ba da sanina ba".

" What kind of madness......"

"Tell them ko ni na kirashi da kaina....you know ina da number wayarsa ko?".

"Oh sheet" Farouq ya fada yana kama goshinsa.

"Wai meye damuwanka?......bakason komai.....but kana bibiyan komai why?" Juyowa yayi sosai yana duban farouq din,wannan karon murmushinsa yadan bayyana

"Wickedness" Ya amsa masa a taqaice.

"Bai kamata a dinga qyale irinta ba haka suna ci gaba da abinda sukaga dama......punishing nasu ya kamata ayi ta hanyar da zasu ji har cikin tsoka da jinin jikinsu"

Balcony dinsa ya isa kai tsaye hannayensa zube a aljihun wandonsa,yana bin dukka tsirran dake shuke daga gaban wajen da ido. Haka kawai yakejin interest dinsa yana qaruwa akan ya hora yarinyar. Abinda ya karanta maza sun badasu da har ta raina ajawalinsu haka da yawa,so dole ta fahimci nata kuskuren.


*_SABREEN_*


Jadda wani dadadden suna ne daya jima yana shiga kunnenta lokaci bayan lokaci,saidai ta tantance wayeshi yadda ya kamata abune da bazata iya ba. Tun daga fitar sunan daga bakin kawun har zuwa shudewar daqiqa sittin kallon kawu din kawai takeyi,kafin daga bisani qarar wayarsa ta katse wa kowa saqar da yakeyi cikin zuciyarsa.

Sau da dama bayyanar number farouq cikin wayarsa wani abune dake zame masa kama da ZAK'I DA MADAC'I,daidai ga gaurayar farinciki da kuma dimuwa a lokaci guda a kuma muhalli guda.

"Ga iyalin gidannan.....bismillahir rahmanir rahim" Ya ambata kafin daga wayar kaman yadda amininsa ya bashi shawarar yi domin amintar da kunnensa daga jin abinda zai dinga daga masa hankali har a samu a qare maganar auren.

Sai daya zauna sosai sannan ya daga kiran,ya bada kunnensa yana sauraren bayanin da farouq ke masa,wanda duka bayanin yana yinsa ne yadda kawun zai fahimta.....ya kuma gwammace ya dinga isar da saqon fuad ne gudun kada ya bayyana halinsa.....ko aljanar daya sake haqiqancewa akwaita ta sanyashi yin wani baqon halin da mutuncinsu zai zube idanun surukai,duk kuwa da cewa shima dama a karan kanshi dan kai tsaye ne,dan gaba gadi.Page 101


"To.....to in sha Allahu ranka ya dade.....godiya muke qwarai da gaske....Allah ya qara arziqi" Yayi zancan yan a kashe wayar,sannan ya maida dubansa ga sabreen da tuntuni baqinciki ya qarasa kasheta a wajen,ta kuma koma ta zauna tun kan ya gama wayar,badon bata gaji da zamanta a wajen bane.....aah....don tana da sauran abun gayawa kawun,saidai kafin ta fara nata jawabin shidin ya rigata

"Saqo ne daga mijinki......yana me umartarki daki lazimci zama a gida......yace a gaya miki baya buqatar daga yau har zuwa randa zaa tara shaidu a shaida daurin aurenki ki sake leqawa ko ina.....amma dan uwansa yace idan kina da buqatar fita ki sanarmin a kawo mota da masu tsaron lafiyarki......zasu kaiki duk inda kikeso a qasar nan ko a wata qasarma idan kina buqatar haka" Yayi bayanin fuskarsa wasai farinciki yana nuna kansa muraran a fuskar tasa.

Idanunta ta lumshe tana son tilastawa kanta fahimtar ma abinda kawun yake cewa. Shigar maganar kunnenta daidai take da wasan kwaikwayon yara.

"Miji?,ita sabreen?,mijin kuma yana iqirarin hanata fita saida izininsa?,wai shin yaushe ma akayi daren har garin zai waye?,yaushe ta yarda da wannan wasan kwaikwayon nasu da har zai tunanin ta amsa sunan MATARSA?. Shi a matsayin wa da zai tilasta ta aureshi?".

"Ko baka qarasa bayanin komai ba tsaf na fuskanci dalilin da ya sanya ka bada amanna qulla auren nan......kawu......har yanzu ba'a haifi me arziqin da zan aureshi don dukiyarsa ba koda ina da manufar yin aure......ballantana sam sam aure shine abu na qarshe cikin jerin lissafin wajibai na rayuwata.......kawu......ka rubuta ka kuma ajiye,wannan abu tamkar sabreen bata taba sanin ya wanzu ba......ba wani qato daya isa ya hanani fita a sanda naso a kuma duk lokacin dana ga dama.....ruwanka kawu ka maida musu dukiyarsa ruwanka ka riqe......abu daya na sani....kudin dani sabreen na taba na tafi dasu ta hanyar da nake ganin tayimin daidai.....kuma yayi adabo dasu har abada saidai ya sake sabon zubi da lale" Daga haka ta miqe tana yunqurin shigewa daki tana jin kwanyarta kaman zata birkice.

Me yasa qaddarorin qulluwar aure suke ta yawo a kanta cikin qasa da sati daya kacal?. Ta gama laluben hanyar gamawa da issue din wadancan matan?,yanzu kuma sai ga wannan?.

"Idan dai har kina ganin zaki iya ja dame jadda ga fili game doki nan" Abu daya da kawu yace da ita kenan ya miqe yana ficewa abinsa yana barin sabbin kudaden dake a mazaunin sadakinta yashe a qasa.

ᎷᏬᎻᎯᎷᎷᎯᎠ ᎰᏬ'ᎯᎠ

"Hamma?......hamma?" Ya jiyo muryar amna dake cike da shagwaba tana kiransa da alama nemansa takeyi. Wata iska ya zuqa me yawa yana dauke dubansa daga saman furannin da yake kalla cikin balcony dinsa tun dazun,ya juya a nutse yana fadin

"Am here lovy dovy". Dan murmushi ta saki tana qanqame paper din hannunta da wani tsadajjen biro me garai garai,ta taka a hankali ta isa balcony din inda yayi tsaye goye da hannayensa a qirji yana jiran isowarta.

"Hamma wajenka nazo" Tayi maganar hannunta boye a

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login