Showing 369001 words to 372000 words out of 557259 words
jadda din,amma a sannan idanunta basa ji basa gani,burinta kawai ta bata mata suna......ta tona mata asirin da shi kansa baisan dashi ba,ta saka masa shakka da kokwanto me yawa a kanta.
"Su waye kika aika cikin gidana har dakin matata!?" Ya sake mata wata tsawar da sai da taji 'yar qwarya qwaryar gudawa ta hadu a cikin ta ta cure lokaci guda,glass doors din dakin kaman zasu tsage saboda yadda suka amsa.
Tashin hankali......kada dai ace ta taka sahun barawo?,da yaushe kuma aka shiga gidan nasa?......wata shigar akayi bayan wadda mahaifiyarsa tasa ayi?.
Da sauri ta fara girgiza kai tana dubansa da sabbin hawaye,don gaba daya yatsunta bata jinsu a gangar jikinta.
"Ban sani ba wallahi.....bani bace.....saidai.....saidai....." B'am bakinta ya bame ya kuma kasa kama sunan maamah kaman yadda take da marmarin shaida masa ita ce. Tanason gaya masa mahaifiyarsa ce,ga sunan a bakinta amma ta kasa furtashi waje,ta dinga kokawa da harshenta amma kaman wadda gabbai ko rassan maganarta suka samu matsala.
"Saidai me?" Ya tambayeta yana tsareta da idanu yanason samun ragowar tabbacin da yakeson samu.
"Na gidan jaridan......nice" Maimakon wancan bayanin ta sake bashi yaqini akan wancan tana sunkuyar da kanta,baqinciki da bacin rai yana cika zuciyarta. Me ya sameta ta kasa gaya masa sirrin da baisan dashi ba?,idan ita yasa an mata irin wannan mummunan dukan ita kuma da take uwarsa tana son taga ya zaiyi da ita.
Idanu ya zuba mata,yana ji a jikinsa akwai saura......akwai abinda yayi saura.....akwai abinda jikinsa yake bashi game da ita wanda ya rage bata fada ba.
Saman qafafunta ya maida kallonsa bayan yaja kujerarsa nesa da ita. Ta sauqaqawa kanta wahala......don ba qaramin bugu yaso Jordan yayi mata ba da qattin qwanjinsa. Yaso ya rage mata adadin yawan haqoran dake a bakinta ko zasu zame mata tunasarwar shigarta hurumin muhammad fuad anan gaba,ya kuma zamewa 'yan baya izina. Qafar ta tasa tayi suntum cikin qaramin lokaci,alamun mummunan targade ko karaya sun samu wajen zama. Banda ita din mace ce baya jin iya wannan dukan ya wadatar dashi,amma duba jinsinta yakeyi.....idan yace zai zazzage dukka muguntarsa a kanta ba zata wanye lafiya ba. Ya maida kallonsa ga fuskarta da har ta suntume,kamatunta sun tasa sun soma hayewa saboda munin marin daya sauke mata,idanunta har sun fara yin ciki
"Zan baki dama ta qarshe da zaki fice daga rayuwata.....ki kuma sanyawa ranki baki taba sanin wata me suna sabreen ba.....fu'ad kuwa ki saka a ranki a saqe saqen mafarki kika taba saninsa.......saidai kafin sannan......na baki wata guda kacal kije kiyi jinyar qafafunki da fuskarki,zan sake waiwayarki......ba kuma waiwaye na arziqi ba. Sa'arki daya labaran ba inda suka fita.....yau da newspapers dinnan sun fita...." Sai ya kada kai daga hagu zuwa dama
"Ko buzunki ba za'a samu ba ina me tabbatar miki da wannan" Ya qarasa fada yana nunata da yatsa.
"Kije kiyi jinya kafin amsa tuhuma ta gaba......ruwanki ki gayawa babanki......ruwanki ki rufe bakinki wannan matsalarki ce......amma inaso ki rubuta ki ajiye.....idan ma kina da plan na guduwa wani guri da kike tunanin zaki samu tsaro to ki sani.......lahira ce kawai zaki tafi ki kubuta daga tuhumar muhammad jadda" Daga haka ya miqe tsam yana takawa yana barin dakin.
Har yakai qofa sai ya dakata,ya juyo ya watsa mata wani kallo sannan yace.
"Daga yau.....na yanke duk wata alaqa tsakaninki da maamah......idan kuma baki yarda ba ko kina doubting akai......ki sake koda kiran layin wayarta ne.....koda sau daya ne" Ya furta yana daga doguwar yatsarshi dan manuni,sannna ya sanya qafa ya fice abinsa.
Tunda tazo duniya ba'a taba gwada mata azaba irin wannan ba......tunda uwarta ta haifeta bata taba ganin qasqancin d'a namiji ba irin na jadda. Inda wanine yau yayi mata wannan abun ta tabbatar bazaisha ba a hannun daddynta dama ita kanta. To amma.muhammad jadda fa?,ta sani farin sani cewa wutsiyar raqumi tayi nesa da qasa. Alfarmarsa ta wuce duk yadda ake tunani,duk arziqi da alfarmar ubanta da take taqama dasu bai wuce yaron jadda ba. Ta sake tsinkewa da lamarinsa sanda daddynta da kansa yake bata labarin yadda fu'ad din ya soke masa wata kwangilar millions of naira,wanda gwamnatin tarayya taso bashi amma jaddan ya fahimci cin hanci da rashin kyan aikin yayi yawa. Ya fusata a sannan baisan waye jaddan ba,ya kuma bazama da zummar a nemo masa wayeshi a hada musu zama....saidai randa ya soma yi masa ganin farko ya kuma zauna dashi da qyar ya qwaci kujerarsa ta ambassador. Har qasa yakai yana hurwa da neman ya rufa masa asiri,ya barshi ne bisa sharadin komai zai dinga tafiya bisa adalci da amana,ya kuma tsaya da iya muqami da dukiyar da Allah ya bashi. Tun daga ranar suka yiwa juna farin sani,labarin da daddyn nata kuma ya bata ya sanya mata tsananin son mallakar fu'ad din. Tanason namiji me qarfin izza da mulki gami da iko takowacce fuska,a duk inda ya tsaya yayi magana za'a dakata a saurareshi,a duk inda yayi umarni dole za'a bi.....to amma sai gashi dare daya komi ya watse komi ya wargaje mata daga hannunta.
"Zan iya barinsa kuwa?" Ta tambayi kanta sanda wata zuciyar ta fara mata saqa da mugun zare.....zuciyar ta fara ayyana mata daukan BAQAR FANSA da kowanne irin hukunci daya kamata ta zartar kawai a kansa.
_uhmmmm,nidai nace wanda baiji bari ba yaji hoho_
Ido farouq ya zuba masa sanda yake dawowa wajen. Sai a sannna hankalinsa ya kawo abinda fu'ad din yayi masa. Cikin dakewa da kuma basarwa yace yana zama.
"Sarkin noma.....na dawo" Sarai yasan magana ya gaya masa,amma ganin ma ya zaro wayarsa ya soma lalubar wata number sai kawai ya qyaleshi da duk abinda zaice dashi,illa dai yace masa.
"Ina fatan baka rabata da numfashinta ba"
"Ta samu wannan tsiran saboda batayi musu ko gardama ba" Yana kaiwa nan ya saka wayar a kunnensa yana magana da daya bangren.
Ya kusa mintuna talatin yana amsa wayar kafin daga qarshe ya rufe da
"Aikinka na kyau CP.....good job,akwai zuwaira......akwai harira ko something hajja......yes......yes" Daga haka sukayi sallama.
Zazzafar numfashi ya sauke yana aje wayara a gabansa gami da watsa idanunsa saman glowing beach din da ruwansa ya fara komawa sea of stars,hakanan yashin dake kwance a wajen ya soma glowing sosai kaman an warwatsa taurari a qasan wajen.
"Wai wanne irin kame kake ne dude?.....har mutum nawa zaka saka a kulle maka?". Idanunsa da suka masa nauyi saboda tunanin daya cika zuciyarsa ya janye ya maida kan farouq,ya kafeshi da idanu sosai saboda tunaninsa ba'a wajen yake ba. Gaba daya tunaninsa ya ta'allaqa a kanta,yana jin a yadda yanayin wajen ya masa kyau da dadi kamata yayi ace tana tare dashi yanzu haka a gefansa,ya shaqi daddadan qamshin jikinta.....lallausar fatar nan tata me wani irin dumi me bawa zuciya da gangar jiki nutsuwa.
"Duk wanda ya taba kiranta da karuwa......duk wanda ya taba yi mata sharri ko qazafin zina ko neman maza......bazan qyale kowa ba farouq". Kallonshi sosai farouq yakeyi yana kallon yadda idanunsa suka jirkice da wani irin giyar soyayya me qarfin gaske. Ya karanci wani muguwar kwankwada fu'ad ya yiwa giyar soyayyar sabreen din,ta kuma bugar dashi fiye da yadda ya kamata.
"To amma ai sai ka hada da kanka da kanka a kullewar ko?" Ya fada yana dage masa girarsa duka biyun sama. Kallon days jefeshi dashi ya tabbatar masa b'arna fu'ad zai masa,ya sanshi yasan abinda zai iya aikatawa,don haka yaja kujerarsa baya da sauri yana dariya. Qwafa yaja yana gyada kai,baisan abinda yakeji ba tabbas farouq da bai qara masa ciwo akan ciwo ba.
Barinsa yayi yaci dariyarsa me isarsa kafin ya kira sunansa.
"Yes sir" Ya amsa masa har yanzun lamarin fu'ad da gaske yana bashi dariya. Yana sassauta masa ne kadai saboda yasan bashi da wani gurin samun sassaucin sai wajensa.
Sai daya ware idanunsa a kansa sosai sannan ya tashi ya zauna yana dubansa.
"Me yasa soyayya take haka ne?" Yayi tambayar sounding serious......saidai kuma abun ya bawa farouq dariya amma ya danneta.
"Me tayi maka kuma?" Ya tambayeshi yana matse dariyarsa da kyau. Kasa magana yayi don baisan ma yadda zai kwatanta masa ba,sai kawai ya dora hannunsa akan qirjinsa da yakeji zuciyarsa na azalzalarsa akanta. Ya dauki wasu sakanni kafin ya iya buda bakinsa a hankali da wani irin calmness.
"Bansan adadin Lokacin da na dauka ina sonta ba......amma inaji a jikina ba sai bayan abun nan ya faru ba na fara sonta.....kaman wani dadadden so ne daya saba dashi.....na taso dashi,aka kuma haifeni dashi". Sosai maganganunsa ke ratsa farouq......da gaske ne fu'ad din yana sawun mutanen da suke iya boye so ba ko su daukeshi da sauqi ba.
*_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_*
08187255862
π π π π π π π π
_Zafafabiyar_
ΜΆBΜΆOΜΆOΜΆK ΜΆ2
β±§Ιβ²Ιβ₯β³
ππΌππ 88
88
"Kayi qoqarin koya mata yadda zata soka........ta fahimceka.......tasan ainihin waye kai da kuma rayuwarka,daga nan komai zaizo da sauqi......zan baka kowanne kalan goyon baya da kakeso.....nayi maka alqawari......amma nima kayimin uzuri daya alfarma daya" Ya fada yana kama hannun fu'ad din.
"Fadi muji dude" Ya fada yana sake jin qaunar farouq da kimarsa tana ratsashi.
"Duk sanda naga taka kalar haukan soyayyar ka yiwa Allah karka hanani inyi dariya......i swear wallahi kai babanmu ne ta nan.....nayi imani da gaske irinku masu shuru shurun nan kunfi kowa zurmawa da iya rikita mata". Danawa bayan hannun farouq dake cikin nasa duka yayi yana zame hannunsa sannna ya miqe.
"Ka lallabani farouq......kasan Allah zan daga aurenka?".
"Iyeeee.....eh ai kayi haka mana,tunda kai ka samu kanka ka zazzage lalurarka ta shekara da shekaru...."
"Idan bata haukatani ba farouq kai zaka haukatani" Kawai yace dashi yana yin gaba abinsa. Da sauri farouq din ya tashi yabi bayansa,don yasan tsaf zai iya tafiya ya barshi a wajen. Tuni suka gaya masa an biya kudin komai da komai tun kafin suzo ma,harda qarin wasu kudin spare da yayi ragowa idan suna buqatar qarin wani abun.
β
Karo na kusan barkatai ya qara daga fuskar wayarsa ya kalla yana hadiye wani abu me tauri a maqoshinsa. Kwanaki kusan takwas kenan rabon daya sanyata a Idaninshi,tun ranar da sukeja Vaadhoo Island shi da farouq bata sake bari yaga face dinta ba.
Da farko yayi tunanin zai jure,kwana daya biyu uku hudu ana biyar din yaji bazai iya ba,yakai bango kaman numfashinsa na shirin masa qaura. Ba ganin face dinta ba kuma jin muryarta?. Koda ya shiga dakin da nufin gaida anni tanajin alamunsa take shigewa duvet ta kwanta abinta. Ya fuskanci kaman tana garkuwa ne da anni wadda ba lallai ta fahimci abinda yake faruwa. Yana jin nauyin anni yana jin kunyarta,amma ta fara kaishi bangon da yakejin yana dab da ajiye kunyar a gefe.
Wayar amna ya soma kira yana sanyata ta bata wayar. A kunnensa yakejin sanda amna take bata wayar amma saita karba ta kife taci gaba da sabgarta. Idan ya kira amna ta wayar anni tana bashi tabbacin wayar na hannunta,sai mintuna suyita tafiya babu ko motsinta bare tarinta. Da yaga haka saiya koma kiran annin yasa a bata,still dai haka take masa,kwanaki uku kenan yau tana masa haka,adadin kwanakin da lissafinsa yake gaya masa jibi ne yarjejeniyarsu da anni na zuwa daukota daga macca.
Bazai iya jure wannan ba......da kansa ya sanya order din wayoyi har guda biyu aka kawo mata,Falcon supernova iPhone 6 pink diamond edition irin wayar dake hannunshi kenan. Sai iphone 4s elite gold. Dukkaninsu wayoyi ne masu tsananin tsada da ba kowa yasan da zamansu ba,saboda ba kowa keda qarfin tattalin arziqin mallakarsu ba. An qera jikinsu ne da diamond da kuma gold masu tsananin daraja.
Yana jin cewa idan ya bata wayar ya zamana tana da tata mallakin kanta dole idan ya kira ta daga din.
Har ya gama shirin kwanciya tun goma na dare amma kewar nan da yakeji ta hanashi kwanciyar,ya tashi ya sanya pyjamas dinsa light blue da suka amsheshi sosai ya sanya flipp flops dinsa ya kwashi wayoyin ya wuce dakin anni.
Tana zaune abinta qasan carpet dauke da littafin hadisinta da yafi mata dadi akan komai a yanzun. Tayi kyau kaman wata 'yar baby cikin milk color din Indonesian hijab me haske sosai daya fidda fuskarta.
Tunda taji sallamarsa wani abu ya tsarga mata,ya shammaceta sosai,yau ko qamshin turaren nan nasa da takeji bata jishi ba.
"Barka da dare anni...." Ya fada cikin girmamawa yana zama saman sofa din dake opposite dinta,kansa tsaye yau duka idanunsa suna kanta. Ji yakeyi kaman yayi shekara takwas ne bai ganta ba bawai kwana takwas ba. A yau din har anni ta ankar da hakan,tadan dauke kai kaman bata gani ba cikin jin nauyi tace.
"Barka kade me babban suna.....mun yini lpy?"
"Alhamdulillah" Ya amsa mata yana maida dubansa ga amna data tsugunna tana gaidashi.
"Lovey dovey.....barka da dare"
"Barka kadai hamma". Sak tayi,bata da niyyar magana kowacce iri ta hadasu,amma gaisuwar anni data amna ta daureta,dole ta gyara zamanta daidai sannan tace
"Barka da dare,ina yini?" Kowanne gaba ta jikinsa sai data amsa sautinta,bai taba sanin yayi masifar kewar muryarta kawai bama sai yanzu,amma duk da haka ya dake yana hade fuska.
"Bazan amsa ba.......sau nawa ina kira a wayar amna nace ta baki?.....sau nawa ina kiran wayar anni a baki saiki ajemin waya.....saboda kin rainani?". Dukka duf dakin yayi,nauyi ya kama anni da kunya......yayin da sabreen din wata masifaffiyar kunya nauyin anni da fargabar kada ya ballo magana gaban annin ya kamashi. Amna kanta sak tayi,saita miqe kawai ta fara lalubar hanyar fita kada ayi fadan soyayya a gabanta,duk abinta itama wani lokaci tana kunyar annin.
"Anni" Ya kira annin kai tsaye yana maida dubansa sashenta.
"Muhammadu" Ta fada cikin jin nauyi itama.
"Ta rainani anni.....a qasana take amma tana iya aje waya idan na kirata".
"Baki kyauta ba takwara....bakisan aljannar mace tana qarqashin qafar mijinta ba?.....kada ki sake kinji ko?". Qasa tayi da kanta zuciyarta na karyewa tare da tarin haushinsa. Tun ranar da taga fareeda kwance a jikinsa ta tsani ganinsa ta kuma tsani ganin fareedan itama. Dama can sun shirya abunsu ne shi yasa da suka gama yawace yawacensu ya kori Jordan ya kaisu can saboda suna da agenda din haduwa......sannan daga qarshe saboda zalunci yazo yayi mata mummunan fyade irin wannan......ya karbi abinda sam ba nasa bane.
"In sha Allah anni......kayi haquri". Ta fada a sanyaye ba tare data kalleshi ba. Wani abu ya hadiye a wuyansa,shi ba haka yaso abun ya tsaya ba,ba haka yakeso ba.....sam bai gamsu ba. Yana tsaka da wannan tunanin yaga ta ajiye littafin ta miqe tana cewa
" Zan dauko ruwa kitchen " Tayi maganar ba tare da yasan dawa take ba.....izinin wa take nema?,saidai kawai ya tsinci anni tana cewa.
"To ba laifi" Sai ta taka a sannu ta fice. Yadan bita da kallo kafin ya dauke kanshi,shi ya sani ba wani ruwa da zata sha,kawai ta aikata hakanne don kada ta zauna inda yake.
Kwata kwata zaman dakin sai ya yaji ya gundureshi. Ya miqawa amna kwalayen wayar wadda shigowarta kenan yana cewa.
"Ki ajiye mata idan ta shigo ta zaba" Sannan ya miqe yana cewa anni.
"Jibi zanje na taho da maamah daga saudiyya.....kwana biyu kawai zan dawo in sha Allah"
"Ma sha Allah,hakan yana da kyau,Allah yayi albarka,banda banbancin fitowar visa ma ai da tuni.muna nan a tare,Allah ya kaika lafiya" Amsawa yayi da ameen yana fita a dakin gami dayi mata sai da safe.
Guri kawai ta samu tayi zamanta cikin kitchen din,zaman nan din ya fiye mata zama a dakin,qarfin halinsa kawai take gani,ga mari ga tsinka jaka?,ko kunyar annin bayaji kansa tsaye yake kai mata qararta?.
Sam sam yaji ya gagara wucewa dakinsa kaman yadda yayi niyyar yi,duk da yau din ransa yadan baci da ita. Sauya akalarsa yayi zuwa kitchen din,yanason ya tabbatar tana can din ko kuwa?,me ma takeyi?.
Idanunsa ya zube a kanta,tana gaban sink ta kunna famfo kawai ta tara hannuwanta kaman me lissafin adadin digon ruwan daya fado hannunta.
A hankali yake takawa don bayason ta jishi,ya samu nasarar isa dab da ita kuwa kafin mayataccen turarensa ya shaida mata isowarsa. Ta motsa da hanzari da nufin waiwayowa,saidai kuma ya rigata da hanzari da kuma zafin nama yayi mata kyakkyawan masauki cikin qirjinsa. Ta baya ya rungumeta tsam,zuqar farko da ya yiwa jikinta daddadan turarenta ya ratsa qofofin hancinsa ya kuma tayar masa da duk wani ajiyayyen tsumi dake jikinsa. Numfashinta ya kusa daukewa saboda yanayin jikinsa da taji ya fara canzawa,maimakon ya barta ta zame yadda take ta qoqarin yi sai ma ya sake manneta da jikinsa yana zura fuskarsa tsakanin wuyanta,ya kuma tura daya hannun nasa ta saman rigarta yana qoqarin kaiwa ga wancan wajen.
Hannunsa take