Showing 57001 words to 60000 words out of 557259 words
wannan ajiyar,naji tana lissafin abinda zatayi dasu idan ta dawo” ya fada yana cusa hannunsa a aljihu yana laluben wayarsa. Fuskarta anni ta shafa tana fadin
“Idan har ba’a gansu haka zata haqura ai,tsautsayi da qaddara tana wuyan kowane bawa”.
Shuru sukayi dukkansu suna saurareb sautin din…..din,sautin dake gaya musu lallai kiran ya isa ga wayar anni dake tare da documents dinta da kuma sauran kudade masu kauri cikin jakar.
Kamar cikin mafarkinta ta dinga jin wani sauti mara qarfi yana ratsa kunnuwa zuwa kwanyarta.
Shuru tayi ba tare data motsa ba,daddan ring tone din mara hayaniya yana tasowa can qasa qasa,da alama akwai abinda ya sake rage kaifin sautin.
Sai data fahimci ba cikin bacci bane sannan ta qarasa bude fararen idanunta da suka qara girma saboda bacci. A hankali ta yamutsa fuskar tata sannan ta sanya hannunta ta maida lallausar sumarta me tsaho data rufe rabin fuskarta baya,ta juya daga rub da cikin da tayi zuwa rigingine sannan ta miqe ta zauna sosai tana wuwwurga idanunta zuwa kowanne sashe na dakin don gano ainihin ta inda sautin yake fita.
Ba kowa a dakin,don tuntuni su huda sun gama shiryawa sunyi abincin safe kaman yadda suka saba sun wuce makaranta,don ko idanunta bata iya budewa tace dai kawai su buda jakarta su dauki kudin makaranta su kuma ja mata qofan idan sun fita.
Fes dakin yake kamar kullum kamar kuma ko yaushe,sai ta saka hannunta ta tattare gashinta ta qulleshi tsakiyar kanta idanunta ta tsaiwa kan medium luggage din dake cike da tsarabar da aka kawo mata,wadda ko samun damar budeta batayi ba.
Tayi matuqar gajiya a jiyan,tana fita kusan kowacce rana.....amma bata yin awanni masu yawa kaman haka a wajen. Komai nata yana da lokaci tsari da kuma iyaka. Ta zube fararen qafafunta saman qaramin carfet data sanya musu daga gaban gadajen nasu saboda sanyin tile,ta jawo dankwali me santsi ta daura sannan ta miqe tana isa gaban luggage din.
Sai a sannan ta kuma gasgatawa daga cikin qaramar handbag dinta sautin ke fita,jakar ma da gaba daya ta mance da ita tun ranar data je musu siyayya ta dawo,ko tarkacen ciki bata kwashe ba. Hannu ta zura tana laluben meye yaketa qara din haka cikin jakar,sai kawai ta wuce gaban gadon ta zazzage jakar gaba daya saman gadon.
Kyakkyawar purse baquwa ta gani cikin jerin tarkacen dake cikin jakar wanda ta tabbatar duka nata ne. Onion color me ratsin maroon a jiki. Hannu ta miqa ta jawota,ta dagata a hannunta tana jujjuyata cikin mamakin a ina ta samo ta?,kuma ta waye?,tun yaushe take cikin kayan nata?. Kamar anason sanar mata da amsar duka tambayoyinta ne sai wannan siririn sautin da ya tasheta a bacci ya sake kadawa daga cikin jakar.
Kai tsaye ta zuge jakar,ba wani ba wata ta sani waya ce. Wayace qila da take da alaqa da mamallaki ko mamallakiyar jakar.
Wata siririyar Samsung ta gani,ta sanya hannu don cirota da gaggawa gudun kada kiran yanke,take sabbin dollar din dake maqale a zip na daban na jakar suka biyota suka fada saman cinyarta hade da qananun hotunan passport. Ba wannan bane a gabanta,don haka batabi ta kai ba ta fara duba sunan dake yawo saman screen din wayar
MUSADDIQU NA....shine full name din dake jikin number. Tadan tsaya tana sake duba sunan da kyau tare da bitar karantashi,sai kuma tadan tabe baki kadan sannan ta daga kiran ta Kara wayar a kunnenta
"Alhamdulillah.....an daga anni" Musaddiq ya fada yana sanya wayar a kunnensa.
Shuru tayi tana sauraren motsin dake fita daga daya bangaren,kafin daga bisani sallamarsa ta maye gurbin shurun. Muryarsa a nutse dake dauke da kamala yayi cikakkiyar sallama data sanyata motsa bakinta da tata siriryar muryar tana amsa sallamar.
"Barka da warhaka" Ya fada a nutse.
"Yauwa.....barka" Itama ta amsa masa a taqaice
"Don Allah idan ba zaki damu ba zan iya tambayarki wayar nan ta waye?" Banbarakwai taji tambayar tazo mata,har sai data sake duba sunan dake jikin wayar,amma yanayin yadda muryarsa ke nuna kamalarsa da nutsuwarsa ya sanya tayi gyaran murya daban
"Kaman sunan me kiran dana gani akan wayar yana da alaqa me qarfi ko kuma mafi kusanci dame wayar ko?". Murmushi ya saki,yadda tayi maganar cikin fasahar harshe da tsari sai yaji ya burgeshi,hakanan kuma a karon farko ya gano muryar,yakuma dago ko wacece
"Hakane ranki ya dade.....idan na canka dai dai.....kamar mutuniyar kirkin nan kuma baiwar Allahn nan data ceci rayuwar mahaifiyarmu ko?" Dan jim tayi tana son gano ma'anar zancansa,don tuni rayuwarta taci gaba daga inda ta tsaya,tuni ta shiga wani babin kuma na daban,ta manta abinda ya faru dazu jiya bare shekaran jiya.
Haka policy na rayuwarta yake. Ba kasafai take bawa komai gurbi cikin rayuwarta ba bare ta hadu da traffic akan dukka plans nata da kuma tunaninta ba.
"Dattijuwa me asthma a masallacin HGMS store?"
"Oops....." Ta furta a hankali,yanayin daya sanya musaddiq sakin murmushi don ya fahimci abun ya kwanta mata
"Kayi haquri don Allah,ka kuma nawa mama haquri,na hada da purse dinta ne a cikin kayana bisa rashin sani,bansan ma da ita din ba sai yau da aka kira"
"No....karki damu......mune ma muke fata Allah yasa bamu takuraki ba....."
"Zaku iya karbanta a jambulo third gate.....link 5" Abinda ta furta kenan ta yanke wayar,daidai sanda anni ta miqa hannu da zummar karbar wayar su gaisa.
"Ya ka katse wayarwayar inaso mu gaisa nayi mata godiya da ban gajiya"
"Daga canne anni ta yanke......" Ya bawa anni amsa yana duban wayar tare da mamakin yadda take magana da bada amsa haka cikin taqaice komai
"Babu matsala.....amma zanso sake ganinta ko magana da ita......zanso nayi mata godiya sosai,dukan wanda yayi saving rayuwarka ai baka da sama dashi.....mutum ne me matuqar kima da martaba cikin rayuwarka.....har yanzu ina iya jin sanda ta rungumeni sosai a jikinta kamar ta sanni......sai na dinga jin kamar amna ke riqr dani......ta damu sosai kamar mahaifiyarta ce a cikin halin" Ta qarasa maganar tana duban fuskar musaddiq,fuskarta kuma na nuna abubuwa da dama da zuciyartata taji. Zamanshi sosai ya gyara yana murmushi.
*SU SAKE DAWO MUKU DA WASU SABBIN LABARAI*
*_BAYAN WASAN DA AKA BUGA GA WANI SABON WASAN_*
*_MIQAQQIYAR TAFIYAR NISHADI_*
*_KAFATAWA DA ZAFAFAN MUHAWARA_*
*_LABARAI MASU DAURE KAI DA SANYA NISHADI A CIKIN ZUKATAN MASU KARATU_*
*ZAFAFA BIYAR*
*_MASUBURBUDAR LABARAI MASU CIKE DA HIKIMA DA DEBE KEWA DA WASA TUNANI TARE DA TSUMA ME KARATU DA TSUMAMMIYA KUMA TSAFTATACCIYAR SOYAYYA_*
*Hanzarta shiga ayarin ZAFAFA FAMILY(WATO IYALAN ZAFAFA DA BASA GAJIYA DA KASANCEWA DA SU*
_TA HANYAR SHIGA RUKUNIN MASU SIYAN LITATTAFANSU KAMAR HAKA_
_QIRJIN ME HANKALI Miss xoxo_
_K'ALBIM Mamuhghee_
_AJIYA A DUHU Billynabdul_
_DUNIYATA Huguma_
_Dukka qunshin litattafan daga farko har qarshensu_
*hudu 2k*
*uku 1500*
*Biyu 1k*
*Daya 500*
_YADDA ZAKU BIYA IDAN KATI NE:_
*09032345899 KATIN MTN, IDAN AN TURA SHEDAR MA NUMBER ZAA TURAWA*
*IDAN BANKI NE A TURA SHEDA ZUWA GA*
*09033181070*
*BANK NAME/SUNAN BANKI: ACCESS BANK*
*ACCOUNT NUMBER/LAMBAR ASUSUN BANKI: 0022419171*
*ACOUNT NAME/SUNAN DA KE ASUSUN BANKI:MARYAM SANI GUMMI*
*AL'UMMAR MAQWAFCIYAR QASATA NIJER KUWA*🇳🇪🇳🇪
89825722
Nousaiba lawali maradi
1000cf
*_Madalla da masoyan ZAFAFA BIYAR_*
*_MADALLA DA KASANCEWARKU TARE DASU_*🥰🥰
*D U N I Y A T A*
*_H U G U M A_*
*Arewabooks:@Huguma*
PAGE 33
"Ni kaina anni ina iya hango sanda taketa masifa da fada da gaske wai mun banzatar da rayuwarki,bamusan illa da kaifin ciwon ba......amma fa anni kaman ina zaton.....anya bata da ciwon itama ko wani nata?" Yayi tambayar yana duban anni kamar annin tasan zahirin maganar.
Cikin isa izza da jin cewa takai kowanne qololuwar mataki na rayuwa ta ratsa babban falo kuma na farko na gidan,ta ratse dukkan wasu hadimai da kuma masu aiki na farkon gidan,falon farko har ta dangane da falo na biyu.
Kowanne taku idan tayi idanunta suna sauke zazzafan kallo ne akan kowanne alatu da kuma jayan jin dadi na rayuwa dake kowanne muhalli na falon. Kowanne abu da idanunta zaya sauka akai tana debe kallonta ne daga kanshi cikin jin wani irin zafi da quna gami da radadi idan ta tuna cewa MUHAMMAD FU'AD ne ya yishi tare da gumin dan uwansa MUSADDIQ.
Da wannan tunanin ta tsaya tsakiyar falo na biyu hannayenta riqe da qugunta tamkar qaramar yarinyar da take ganiyar fitsara da kuma jin cewa tana daidai da kowa.
Ko ita dinma a yanzun kusan hakan take. Tsaiwarta a falon qiris ya rage dukkan wani ganuwar haquri nata kawaici da yakana da takeyi su qare,haquri da kawaicin da take ganin tunda tazo duniya bata taba yiwa wata halitta irinta ba
"Amina nakeson nayi magana da ita" Ta fadi kanta tsaye sanda daya daga cikin hadiman dake da alhakin kula da wannan sashen ta qaraso.
"Eyeee?" Me aikin ta tambaya cike da mamakin yadda ta kirayi sunan dattijuwar data zame musu baya goya marayi haka gatsal,babu sayawa ko qanqani,duk kuwa da cewa zasuyi sa'annin juna,amma a garesu kiran ainihin sunanta wani baqon abune da yake jimawa bai faru ba
"Nace AMINA nake buqatar gani.....uwar farouqu da saddiqu" Ta maimaita a wannan karon da madaukakiyar muryar data sanya hadimar maida hankalinta ta hanyar dubanta da kyau,sai kuma taja baya kadan tana cewa
"Inji wa zaa ce mata?" Ta tambayeta tana sake kallonta sosai
"Kice mata uwar Muhammadu da musaddiqu" Sunayen data furta din ya saka hadimar sake dubanta da kyau,saidai bata ce komai ba don bata da hurumin cewa komai din,ta taka a hankali ta kama stairs tana hawa a hankali don isar da saqonta ga anni.
Kafin anni ta furta nata hasashen knocking dinta ya dakatar da firar tasu. Firace da yawancin lokuta musaddiq din yakan qaraso har quryar bedroom din anni ya tayata don debe mata kewa lokaci lokaci da hanata zaman kadaici. Duk da cewa gidan cike yake da hadimai wadanda suka aiki qarqashinta ta kowanne fanni da take da buqata na rayuwa. Hatta hirar akwai masu tayata cikin masu aikin,wadanda aikinsu kenan,gwanaye ne wajen iya hira da mutum,debe masa kewa da sanyashi nishadi......musamman FU'AD ya daukesu aiki saboda haka kawai,amma ko kusa ko alama hira dasu bai kama qafan hira da yaranta ababen soyuwarta ba.
"Waye?" Musaddiq ya riga anni tambaya
"Badawiyya ce"
"Bismillah qaraso" Anni ta bata umarni tana gyara zamanta saman lallausan abun sallarta.
A nutse kuma cikin girmamawa ta qaraso cikin dakin. Ta tako a hankali zuwa gaban annin ta tsugunna
"Baquwa kikayi anni" Ta fadi kanta a qasa
"Baquwa kuma?,daga ina?" Tayi tambayar cikin dan mamaki,saboda yau din ba ranar ganin baqi bane,tana cikin ranakun hutunta,sannan tun bayan dawowarta ma daga asibiti fu'ad ya hana kowa ganinta,yace saita murmure ta huta tukunna.
"Ban dai kai ga gane fuskarta ba.....tadai ambaci asalin sunanki,tace kuma a gaya miki babar fu'ad da musaddiq.......kuma...." Tadan fadi tana daga kai kadan ta dubi fuskar musaddiq da ya tattara dukka hankalinsa akan waya,har sai da yaji sunansa ya fito cikin zancan
".....suna dan yanayi da yallabai musaddiq kadan". Dukkaninsu daga ita har musaddiq din kowannensu ya fahimci wace......kowannensu ya gane wace take nemanta.
Fuska annin tadan saka kadan tana murmushi
" Banda abun badawiyya,ai ba baquwa bace 'yar gida ce itama.....ki gaya mata ta hauro.....ta qaraso zuwa falon sama".
"To anni" Ta amsawa anni din a ladabce tana miqewa don isar da umarninta,saidai kuma a can qasan tata zuciyar mamaki ne kwance. Mamakin yadda annin ta bada umarnin qarasowar matar zuwa falonta na qarshe wanda daga shi sai dakunan baccinta.....matar da sam bataga ruwa ko alamun kirki a tattare da ita ba,tun daga yanayin kallonta har zuwa lafuzzan bakinta,to amma menene ALAQARSU DA YALLABAI FU'AD DA KUMA MUSADDIQU?,tambayar da bata da amsarta kenan daidai sanda ra qaraso falon.
Tana nan a tsaye inda ta barta,kamar dazun ba abinda ya sauya daga yanayin tsaiwarta a cikin falon,zuwaira na daga gefanta bayan tayi amfani da sakannin hawan badawiyya sama da saukowarta ta sake yiwa zuciya da ruhinta wani karatu da sake dorata akan wani bigiren.
"Tace ki qaraso saman" Badawiyya ta furta a ladabce kaman yadda tsarin aikinsu yake cikin gidan girmamawa ga duk wani baqo da zai sanya qafafunsa cikin gidan alhaji hamza kibiya,walau me dogon zangon zama,ko kuma me gajeriyar baquntar da bata wuce awanni zuwa mintuna
Kai ta jinjina,eh yana da kyau hakan,ko ba komai a karon farko idanunta zasu ganeta komai da kyau......idanunta zasu gane mata yadda akayi amfani da kudi da jini da kuma quruciyar d'iyanta don shimfida kyakkyawan rayuwa ga wasu.
Cikin jin isa taqama gami da izza take taka kowanne step na stairs din,idanunta na sake qididdige mata adadin dukiyar da aka narkar wajen ginin gidan tare da qawatashi da kayan alatu dana alfarma na kecewa sa'a. Irin alatun da ita shine nata mafarkin,irin qawar da shine burinta DUNIYARTA. Yau ga komai a kusa......komai a dab da ita da sunan mallakinta.....amma wani taqi da kuma taku kadan sun hanata isa ga wannan bigiren. Iya lallausan carpet din da aka mamaye ilahirin stairs din dashi aka lullube tsadajje marbles din dake shimfide don kada anni taji sanyi cikin jiki da qashinta......duba daya zakayi masa kasan asalin tsadar da yake dashi. Wani abu ya dinga taruwar mata yana tsaya mata a wuya,wutar bacin rai taba taso mata kamar ta hallakata.
Sai da badawiyya ta fice daga dakin sannan anni ta janye idanunta ta maida kan musaddiq. Suna hada idanu sai ya janye dubansa daga kan annin ya mayar ga wayarsa. Ta tabbatar yaji komai kuma shima ya fahimci wacece tazo din. A karon farko kenan data fara tsomai qafafunta cikin gidan tun bayan data sake bayyana cikin rayuwarsu karo na biyu.
Yanayin yadda ya share din kamar baisan meke wanzuwa ba yadan sanyata murmusawa. A sannu a sannu hali da dabi'ar dan uwansa tana masa naso cikin jiki. Saidai bata da tabbas din shima dama yana da dabi'ar ne ta iya shariya dayin kamar baiga abu ba?,ko kuwa kuma daga bayane zama da madaukin kanwa ya sanyashi koya?.
"Musaddiq" Ta kira sunansa kai tsaye
"Na'am anni,akwai wani abu da kike buqata ne?" Yayi tambayar badon haka bakinsa yakeso ya fadi ba. Kai ta girgiza har yanzu tana duban fuskarsa. Cikin ranta tana jin inama wannan dukka tarin kulawar,.....wannan nuna damuwar da bata muhimmancin zasu rabata ko yaya yake da matar da suke kira MAAMA?. Saidai ta sani,TUN RAN GINI tun ran zane.....bakin alqalami kuma ya riga ya bushe......dawo dashi bisa zarafin aiki da damshinsa don gamsar da buqata kuwa aiki ne ba na yanzu yanzu yau ko gobe ba
"Ba buqatar komai......amma bakaji wadda tazo bane?" Ta sake tambayarsa
"Naji anni.....maama ce" Ya amsa mata kai tsaye. Kai ta sake jinjinawa,ta buda baki zata sake magana amma ya rigata
"Maama ce.....kuma bani da tabbacin alkhairi ya kawota" Ya sake fadi idanunsa na nuna akwai wani abu daya taba zuciyarsa. Fuska annin ta sauya tana rage adadin saketa da tayi a baya tadan tsuketa kadan
"Wato kaima kanason bin sahun dan uwanka kenan musaddiq?" Ta Tambayeshi cikin tsuke fuska. Kai ya jinjina sannan yakai hannunsa ya ture hularsa baya yana shafar sumarshi
"Ba haka bane anni.....akwai wasu abubuwa da wasu lokuta suke iya tasowa dan adam a matsayinsa na dan adam din,duk kuma yadda mutum yaso ya ture ya goge ko ya shafesu ba zasu taba barin zuciya da ruhi su huta ba".
" Ya isheni......tashi muje" Ta fada tana yunqurawa sannan ta miqe tsaye tana gyara lullubinta.
Tana sanya qafarta cikin falon qofar bedroom din anni dake falon ya bude. Anni ce a gaba musaddiq da ya bude mata qofar yana daga bayanta.
Kyakkyawan kallo ta sauke musu a sanda take tsaye tsakiyar falon tana kallon yadda dukiya ke magana da kanta cikin falon. A iya rayuwar da tayi.....a iye shige shige gami da fadin tashin da tayi cikin duniya tasan abu me daraja......tasan abu me tsada kamar yadda tasan abu me aji,don haka bata buqatar batawa kanta lokaci wajen sake nanatawa kanta a nan dukiyar da yaronta ya mallaka take tafiya,da gaske ne.....ba sharri bane.....hakanan ba cikin labarai na qanzon kurege bane.
Sanda suke takowa zuwa falon yana biye da anni saita gaza dauke idanunta a kansu. A hankali taji tashin hankalinta yana sake qaruwa. Kana musu duban farko a yadda suka fito shi da anni din baka isa duk masifarka kace ba diyan cikinka bane. Musaddiq ne.....musaddiq din da tun farar safiyar jiya bata sake sanyashi a idanunta ba bayan zaman