Showing 450001 words to 453000 words out of 557259 words
pillow
"Anni" Ta kira sunanta kai tsaye tana jin wani jarumta yana shigarta. Kai kawai anni ta tada ta kalleta,don bazata iya tuna yaushe ta kira sunanta haka ba.
"Kunason nutsuwata da kwanciyar hankalina?" Ta tambayi anni still tana dubanta. Alhaji hamza dake tsaye daga bakin qofa anni ta kalla,sai ya gyada mata kai,tasan umarni yayi mata sai ta dawo da dubanta kan sabreen.
"Sosai sabreena.....sosai". Idanunta da takeji hatta su sun mata nauyi a jikinta ta lumshe sannan ta bude.
"Abu daya nakeso anni da zai bani wannan nutsuwar......abu guda daya take nake da buqata....." Ta fada tana daga yatsanta daya,idanunta nayin wani iri kaman wadda tasha abun maye ta maku.......
*_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_*
08187255862
π π π π π π π π
_Zafafabiyar_
ΜΆBΜΆOΜΆOΜΆK ΜΆ2
β±§Ιβ²Ιβ₯β³
ππΌππ 125
125
"Mene sabreen?" Anni ta sake tambaya tana zama gefanta,tana jin kamar an salube qashinta daga cikin tsokokin jikinta,tana fata ba abinda bazai yuwu bane sabreen xatayi magana akai.
"Anni ku kaini wajensa" Ta fada a taqaice hawaye suna cika fararen idanunta da tuni kalolinsu na fari da baqi ya jima da sauyawa daga idanunta.
Da hanzari anni ta kalleta,kai ta dan girgiza mata.
"Kiyi haquri ameenatu......ta yaya kina cikin irin wannan yanayin zaki tafi ki ganshi a yanayin da yake ciki?,ba abinda yafi buqata illa kiyi masa addu'a ki kuma kula da abinda yake cikinki......bazai taba iya mantawa ba muddin kika kasa riqe abinda yake cikinki kika kasa rainan masa su....."
"Bazan iya rainonsu ba anni muddin babu shi a kusa dani.......zan fara lissafin yankewar numfashi daga gangar jikina daga yanzu zuwa fitarsa na qarshe" Ta qarasa maganar hawayen da take tarewa suka gangaro saman kuncinta.
Wani abu ya ratsa anni da Alhaji hamza tun daga saman kansu zuwa tafin qarfinsu. Tsahon rayuwarsu zasu iya cewa basu taba ganin zazzafar soyayya irin wannan ba.....soyayya da qauna me wani irin zafi da radadi,soyayya da qauna ta gasken gaske......soyayya ta a mutu da kowanne motsi da yanayi na abokin soyayya ya tsayema dan uwansa a rai.
Rasa bakin magana anni tayi,ta daga kanta tana duban Alhaji hamza da shima ya gama sallamawa. Kai kawai ya jinjinawa anni sannan ya dubi sabreen.
"Indai don wannan ne ki kwanta kiyi baccinki sosai,daga gobe zuwa jibi in sha Allah zan siya mana tickets na fita taiwan......zakije ki ganshi....amma sai kinyimin alqawarin daga yanzu harmu tafi ba zaki sake damuwa ba......kuma zaki sakeyimin alqawarin idan munje ba zaki daga hankalinki ba.....ko a yaya kika sameshi zaki sawa zuciyarki nutsuwa da kwanciyar rai har ya samu lafiya kamar yadda muke kyautata zaton hakan". Kai ta shiga jijjigawa a jejjere.
"Nayi maka alqawari abba.....nayi maka in sha Allah". Kai ya gyada shima,wani irin tausayinta yana kamashi,ya yiwa anni alama da hannu sannan ya juya yana fita.
Saida anni ta tabbatar ta kwanta ta kuma nutsu,sannna ta saka mata karatun qur'ani qasa qasa kusa da ita,ta kira mata ma'u suka kwanta tare sannan ta fice.
Tana jin fitar annin,saita runtse idonta tana jin wani rauni yana saukar mata,kuka takeso tayi wanda batasan iyakarsa ba,amma kuma sautin qur'anin da yake shiga kunnenta ya bata wata irin cikakkiyar nutsuwa,a hankali ta sake maida idanunta ta rufe,saita dinga jin kaman wani tabbaci take samu daga zuciyarta na samun nasara da sauqi a dukka al'amuranta,ta sake imani da wannan ayar da take cewa.
(Ku saurara,da ambaton Allah kadai zukata suke samun nutsuwa).
A dan gaggauce anni ta qarasa dakin Alhaji hamza,ta dubeshi,waya yakeyi yana daga tsaye a daren,batasan koda waye yake wayar ba duk da dare ya soma nisa,sai ta zauna tana jiransa ya kammala. Ba jimawa ya kammala din,ya dubeta yana aje wayar
"Na saka su dubamin tickets ne xuwa taiwan.....na gobe ko na jibi,ina zaton kuma sai jibi ma za'a samu".
"Amma abba.....kana ganin ya kamata mu dauketa mu kaita ta dinga ganinsa cikin engine da tashin hankali?kasan tabbas sai muhammadu yafi son rayuwar yaran nan da nashi rayuwar?,kasan sai yafi qaunar ta kula da kanta da lafiyarta akan tashi?." Dan murmushi ne ya subucewa abban,sai ya zauna gabanta yana dubanta.
"Ameenatu.....zuciya da ruhin soyayyarsu ba gama gari bace irin ta kowa.....karatun da na yiwa soyayyarsu shine.....suna sake qaunar juna da tsananin son kasancewa da junansu a sanda jarrabawa ko musiba ta samu daya daga cikin su,sunfi qaunar duk tsanani su kusanci juna akan suyi nesa da juna......sabreena ba zata taba samun nutsuwa ba.....ba zamu taba samun yadda mukeson gani ba muddin bamu sadata da barin ruhinta ba.....xakisha mamaki idan kikaga tafi nutsuwa a can fiye da anan din duk da unconscious yake?" Ya qarasa maganar da tambaya yana duban idanun anni. Shuru annin tayi tana juya maganar abban. Ta jima bataga soyayya me zafi jini da hanta da zuciya harma da b'argo irin tasu ba.
Kanta ta gyada a hankali bayan ta gama nazarin,ta kuma yarda da maganganun abban dari bisa dari don itama taga hakan.
"Allah yayi mana jagora,ya taqaita dukkan wahala da sharrin masu sharri"
"Allahumma ameen" Ya amsa mata yana miqewa.
_TAIWAN_
_TAIPEI_
*_Taiwan Taoyouan international airport_*
Yammaci ne sosai sanda suka sauka a taiwan,misalim qarfe hudu na yammaci,wanda yayi daidai da qarfe sha daya agogon nigeria.
Da yake tafiya ce bata shiri ba,cikin motocin da gwamnati ke ajiyewa saboda baqi da wadanda ke buqatan hayar da zaiyi driving da kansa,ya gama adadin kwanakin ka maida inda ka karbo ita suka karba.
Abdulgaffar ke driving din,yana yi yana duba map da address din da ya samu da zai sadashi kai tsaye da asibitin.
Duk yadda garin yakai ga kyau tsaruwa da daukan hankali ba wannan bane a gabanta,bama kasafai take iya fahimtar inda suke wucewar wa,burinta kawai.shine su isa asibitin,burinta kadai shine ta ganta a gabanshi,burinta ta ganshi a gabanta ta daina jin cewa yayi mata wannan nisan da kowacce rana zuciyarta da gangar jikinta suke jiye mata.
Tafiyar mintuna arba'in suka fada ainihin titin asibitin,ba wani wanda yake iya cewa da danuwansa komai. Saddiq musaddiq abba da anni......ballantana sabreen da take ganin kaman laqai laqai kawai abdulgaffar yakeyi bawai tuqi ba,kaman tafiyar kunkuru yakeyi,kamar ma bayason ya sadasu da asibitin.
Mintina sha biyar map ya nuna musu suna daidai asibitin,suna shiga titin shine gini na farko daga hannun dama.
Idonta ta daga a hankali tana kallon tsararre kuma ajiyayyen ginin asibitin,wanda ko ba'a gaya maka ba kasan cewa gurine me cike da tsari da tsananin kulawa,guri ne kuma da lafiya ke tsaye da qafafunta.
Karo na farko data soma yarda da gaske ko a qasashen waje akwai rayuwar masu hannu da shuni akwai ta tsaka tsaki akwai ta talaka. Tun kafin sukai ga shiga asibitin checking nasu da akeyi kadai ya isa ya tabbatar maka akwai tsaro sosai cikin asibitin. Checking da ya sanya ta dinga jin kaman wani salo ne na hanata isa garesa.....kafin yafi tsaye mata a rai sama da zaman da sukayi cikin jirgin kafin isowarsu taiwan.
A muhallin da aka tanada saboda ajiyar motoci abdulgaffar ya tsaida motar sannan ya kasheta. Ta daga idanunta tana jira taji wani a cikinsu ya bude motar da zummar fita amma bataga kowa ya motsa ba. A nutse Alhaji hamza kibiya ya fiddo wayarsa sannan yayi kira,kiran da duka duka bai wuce minti daya ba
"Muns parking lot" Abinda ya fada kenan ya yanke kiran yana dubansu.
"Muje ko.....ga Jordan nan zuwa". Kiran sunan Jordan kadai ya sanya jikinta ya fara rawa,a kasalance ta sanya qafafunta waje tana ambatar sunan Allah bayan musaddiq ya bude mata murfin motar,sai taji jikinta kamar yayi nauyi ta dafa murfin tana fitowa.
Komawa gefenta anni tayi tana saka hannuwanta cikin nata,ta daga kai suka hada ido da anni.
"Karki manta alqawarinmu,kada ki sabashi......be strong please ameenatu......na sani ke din jaruma ce" Kai ta gyadawa anni,bawai don a yau tana jin wannan jarumtar ba,ta dade da sani da kuma fahimtar indai akan fu'ad dinne bata da wani sauran jarumta daya rage,ita din raguwa ce ta qarshen qarshe.
A hankali suka fara takawa suna dosar main entrance na asibitin,wanda basuyi taku goma cikakke ba saiga Jordan din,sukayi kacibus dashi a hallway din yana fitowa daga elevator.
Kallo kawai sabreen take qarewa Jordan,abinda bata taba yi ba,saidai koda bata taba qare masa kallo ba amma ta sani yana da qiba da kuma tsaho gami da murdewar jiki,amma a yanzun abinda idanunta suke iya gane mata shine zubewar da yayi. Ya rame sosai duk da har yanzu wannan kuzarin yana tattare dashi,abinda ya sanya dukka gwiwoyinta yin bala'e'en sanyi tana jin tabbas ko meye ya faru da hammanta ba qaramin abu bane,abun har ya taba jordan har haka?.
"Welcome madam" Ya fadi mata yana tsaye daga gefanta cikin tsananin girmamawa tausasawa da kuma kulawa. Bata iya amsa masa ba,sai idanunta data zare daga kansa gudun kada taje ta rasa ragowar qwarin gwiwar data rage mata.
Musaddiq da abba da jordan su suka fara wucewa saman,kafin su kuma su kuma da saddiq su kira wani elevator din suka shiga suka bi bayansu.
Farouq ne mutum na farko data fara hangowa yana fitowa daga wani balcony na daban bayan doguwar hanyar da kebantattun amenities suke. Faduwar gabanta ya sake tsananta saboda ganin irin zubewar da jordan yayi akan fuskar farouq. Ta kasa dauke idanunta a kanshi,kaman yadda ta lura shima din ita yake kallo. Suna takawa zuwa inda yake shima yana matsowa garesu,har suka riski juna a hanya.
"Adda......haka kika koma?" Farouq ya fadi a raunane yana jin wani irin tausayinta yana ratsashi. Karo na farko da yaji yarda dari bisa dari yau yayi ido da ido da salon soyayyar da yakeji a ransa a baya cewa babu irinta a duniyar zahiri......saidai a duniyar litattafai da kuma fina finai.
Kanta ta dauke tana qoqarin hadiye wani abu daya tsaya mata a wuya.....tambayarsa kulawa ce ta kawota.....amma da zaiyi mata wani abu da yafi wannan tambayar faranta mata rai. Ya sauketa da labarin halin da hamma fu'ad yake ciki.....ya gaya mata yanayinsa shi zaifi komai mata dadi.
"Kaima bakaga yadda ka koma ba BB?" Ta qarashe tambayar tana kallon fuskarsa kai tsaye muryarta tana rawa,tana fatan ganin wani mode da zai bata haske akan yanayin da fu'ad din yake ciki.
Wani busashen murmushi yayi yana kada kansa,sannan ya maida dubansa gasu anni.
"Sannu da zuwa abba.....anni sannu da zuwa".
"Muje farouq ciki....muje dakin" Anni data kasa haquri ta fada tana yin gaba sabreen kuwa ta sanya qafafunta ta rufa mata baya kai tsaye xuwa dakin da sukaga farouq din ya fito.
*_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_*
08187255862
π π π π π π π π
_Zafafabiyar_
ΜΆBΜΆOΜΆOΜΆK ΜΆ2
β±§Ιβ²Ιβ₯β³
ππΌππ 126
*_Bgawo's KITCHEN AND APHRODISIAC_*
*_WATA KILLATACCIYAR MASARAUTA CE,WADDA KE QUNSHE DA DUKKAN NAU'IKAN ABINDA KUKESO_*
*_GIRKE GIRKE NA ZAMANI_*
*_KAYAN MAQULASHE DA NAU'IKAN DRINKS KALA KALA_*
*_INGANTATTUN TSUMAMMUN MAGUNGUNAN GYARAN MUTUNCIN 'YA MACE......GYARA IRIN NA IYAYE DA KAKANNI DA INGANTATTUN MAGUNGUNAN DA BABU DUNGUSHE KO KOKWANTO A KANSU_*
*_KALAR MAGUNGUNAN DA SAO WAJEN IYAYENMU NA DAURI.....INGANTATTUN SAUWOYI DA SAQE SAQI DA AKA SARRAFASU ZUWA MAGANIN GYARAN DIYA MACE_*
*_BIKI KUKE DASHI KO SUNA?_*
*_SAUKAR KARATUN QUR'ANI?_*
*_KO KUMA WALIMAR AURE QARIN MATSAYI A GURIN AIKI KO KUMA WANI QWAR QWARYAN TARO?_*
*_KO YAU DIN BAKIJIN SHIGA KITCHEN?,TSAFTATACCE KUMA INGANTACCEN ABINCI KIKE BUQATA A CIKIN WARMERS DINKI KO FOOD FLASK?_*
*_HAIHUWA KIKAYI?_*
*_KO GYARA ZAKIYI KAWAI A MATSAYINKI MA CIKAKKIYAR MACE?_*
*_BGAWO'S KITCHEN SHINE MUHALLIN DAYA DACE DA DUKKA WADANNAN BUQATUN NAKU_*
_Maza garzaya ki tuntubesu ta wannan number wayar_
08104553105
08127084190
*_zaki godemin qwarai da haduwa da BGAWO'S KITCHEN_*
*_BGAWO'S KITCHEN_*
*MATATTARAR BIYAN BUQATUNKU*
126
Daga balcony din ma'aikatan lafiyar wajen suka tsaidasu,kowanne aka bashi riga da hula ya sanya,sannan suka musanya takalman qafarsu zuwa wasu ajiyayyun tsaftatattun fararen Crocs da suke wajen.
Lafiyayyen parlor ne wanda aka tsarashi cikin wani irin yanayi da zai bawa me jinya dama wanda ake jinyar yanayi me kyau,bisa wadatacciyar iska da haske,irin iskar dake fitowa daga tsirran da aka wadata bayan dakunan dasu,wanda kana iya hangen komai tarwai ta gilasan da dakunan ke dashi daga gaba.
Sam parlor din baiyi kama da asibiti ba,an saka sofas set guda,tv plasma freezer da side tables da babba guda daya,curtains da komai na parlor din fari ne qal tamkar hannu baya tabawa saboda tsananin kula da tsafta,hakanan qamshi ne me kwantar da hankali kawai yake fita.
"Akwai likita a ciki a tare dashi,bibbiyu bibbiyu nake ganin ya kamata a shiga......" Farouq ya fada yana rarraba idanunshi tsananin fuskokinsu.
Sulalewa tayi ta zauna saman sofa din,koda farouq yace ta fara shiga batajin zata iya hakan,gwara a cikinsu wasu su fara shiga din,yanayin fuskar kowannensu shine zai bata qwarin gwiwar shiga ko akasin hakan.
Kaman anni zatayi magana sai kuma ta fasa,ita da abban sukayi gaba farouq yana musu jagora suka buda qofar suka shige.
Zaman jiran fitowarsu annin ba wani abu bane me sauqi a wajenta,sai ta jita tamkar tana zaman jiran isowar layin mutuwa kanta,kanta a qasa ta saka hannuwanta dukka biyun ta dafe kanta tana jin yadda zuciyarta ke harbawa kaman zata fado qasa. Wani motsi takeji mararta tanayi,baqon abune da bata taba jinsa ba sai a ranar kamar ana d'allinta da yatsa.
"Hasbiyallahu la'ilaha illa huwa,alaihi tawakkaltu wa huwa rabbul arshil azeem" Ta dinga maimaitawa labbanta kadai ke motsawa. Da yatsunta ta dinga irga kowanne wucewae second,tanajin kaman suna wucewa da kowanne dama na rayuwarta,tana jin kamar suna wucewa ne da farincikin rayuwarta gaba daya.
Sai da su abba suka kwashe mintuna kusan goma harda doriya kafin taji fitowarsu. Duk yadda taso daga kai ta kalli reaction na fuskarsu ta gaza yin hakan,ta kasa koda motsawa,tana jin tsoron abinda zata daga ta gani tattare dasu. Saidai takum tafiyarsu su biyun bata tsinci komai a ciki ba,karsashi ko akasin hakan,wanda hakan ya sake sanyata a taraddadi me yawa da kokwanto.
"Ni zan shiga" Ta fada da wani irin fusgar kalma cikin ba zata a sanda saddiq da musaddiq ke takawa zuwa qofar dakin.
Miqewa tayi ta zauna sosai tana dubansu sanda suka dakata daga shigar da juyyayyun idanunta,tana jin kamar kafin su shiga su fito zata iya rasa numfashinta da rayuwarta gaba daya,koma meye gwara ta shiga ta gani ta kuma fuskanceshi da.dukkan iyawarta,da wannan qudurin ta taho,ba kuma zata iya canzashi ba.
Da baya suka dawo,ba wanda ya musanta mata ko yace wani abu,saita miqe a hankali tana jin kamar qafafunta ba zasu dauketa ba ta doshi dakin.
Ta kusa sakkani talatin riqe da handle din ta kasa murzawa,har sai da muryar farouq dake bayanta ta dawo da ita daidai
"Are you okay?" Ya tambayeta yana leqen fuskarta. Kai ta gyada masa.
"Ko na bude miki?" Ya sake tambaya cikin kulawa saita girgixa kanta ta kuma tattara gaba daya qarfin daya rage mata ta murda qofar tana shiga.
Jijiyoyin jikinta ne taji tamkar suna tsinkewa,numfashinta kamar an musanya mata da wani abun daban me tauri bawai lallausan iskar da kowanne me rai yake shaqa ba. Ta dinga ganin idanunta kaman gizo suke mata,ba ainihin abinda zata gani bane take gani......gani take zolayarta kawai idanun nata sukeyi saboda abinda take kwana ta tashi da fatarsa kenan.....abinda take kwana ta tashi tana mafarki da burin ya kasance kenan.
Yana zaune saman gadon da aka tallafo bayansa aka dago kan gadon sosai yadda zaiji dadin zama. Jikinsa sanye da rigar asibitin ruwan sararin samaniya me haske sosai. Lallausan blanket ne lullube da qafafunsa zuwa qugunsa.
Fararen idanunsa tarr bisa fuskarta,idanun da suka dan rusuna kamar wanda bacci yake cike a idanun nasa. Kallon kallo ya wanzu a tsakaninsu,zukatan kowannensu yana bugawa da sauri da wani irin doki da zumudin ganin daya bangaren zuciyar tasa.
Wasu irin abubuwa ya dinga sakar mata suna ratsa sassan jikinta......wani irin shauqi mahaukaciyar soyayya da zazzafar qauna