Showing 417001 words to 420000 words out of 557259 words
zama.
Tuni maamah ta yiwa kanta mazauni a executive suit,a nata zaton shine guri na qarshe da yafi kowanne tsari,batasan sam da VIP suit ba,wanda wada dama mazauni ne na fu'ad din shi kadai,saidai idan yaso wani ya shigo ya zauna.
A Aminitiy anni tayi zamanta,zaman jirgi ba baqonta bane,amna ma a nan ta zauna sai sabreen ta zauna kusa da ita suna taba hira abinsu,saidai komai ya tsaye mata a wuya,hatta ruwan da tasha.
Yana takowa ta tsakaninsu xai wuce VIP suit zazzafan aman ya taso mata,ta saka hannu da nufin tareshi ta miqe da saurin don wucewa lavatory.......saidai inaaa,wani karo da tayi da fu'ad din take aman ya qarasa fitowa ta kuma soma kwararashi tun daga qirjinsa saman lafiyayyar suit dinsa har saman qafafunsa. Ba wannan bane damuwarsa.......yadda take kakarin amai duk jikinta yana kyarma shi yafi daga hankalinta,ya bita da sauri a rude yana fadin.
"Subhanallah......ya salam......sannu.....am sorry" Kaman zai sake mata kuka. Yadda ya kanainaye abarsa su anni sai baya suka tsaya suns jera mata sannu tana ci gaba da yunquri kaman zata fidda kayan cikinta.
Kafin ta gama kanta ya fara sarawa da wani irin ciwo,zazzabi jikinta kuma ya sake ninkuwa akan nada.
Shi ya karbi ruwan daga hannun daya daga cikin crew din ya bata tasha saboda yadda take haki,ya saka hannu ya dagata suka wuce lavatory.
Da idanu take binsa kawai sanda yake qoqarin gyara mata jikinta ba tare da ya damu da qazantar data zuba masa a nasa jikin ba. Idanunta ta lumshe a hankali a kansa sanyi yana ratsa gabbanta. Ta dauka zaiyi mata fada,ko zai nuna fushi saman fuskarsa,ko yayita hargagi idan ta kama ya tureta ma,amma sai taga sabanin hakan. Gaba daya ya bata attention dinsa,tanaji anni na cewa amna ta biyosu ko xata tayashi da wani abun yace "no need.....zauna kawai".
Wani irin abu taji yana ratsata a kanshi,ta zuba masa ido sosai sanda yake goge mata saman qafafunta da takalminta daya dan baci,saita miqa hannu ta zaro napkins dake ajiye a lavatory din ta tsugunna a gabansa tana daidaita tsahonsu. A nutse ya dago suka hada idanu,fararen zagayyun idanuwansa sun qara haske wanda suke sauya launi nan da nan da wani abun ya taba zuciyarsa,sai ta langabe sannan a nutse ya dora napkin din saman qirjinsa tana cewa.
"Am sorry" Ta furta a hankali. Labbanta yabi da kallo yana jin suna qara burgeshi,murmushi ya subuce masa wanda ya sake qara fidda kyansa,hannuwansa duka ya saka ya daga kafadunta suka miqe tsaye,idanunta yake kalla
"Sorry for what?" Shima ya tambayeta muryarsa can qasan maqoshi. Idonta ta janye tana nuna qirjinsa da yatsarta,sai shima ya maida dubansa wajen. Murmushi ya kuma saki,ya kamata yana jinginata da jikin mirror din gurin,sannan yaja da baya ya soma balle button din suit din farkon,ya xareta ya ajiyeta a gefe,ya sake balle button din ta biyun itama ya ajiyeta a gefe,sai ga shirt din cikin ta ukun ta fito fes ba abinda ya tabata. Idonsa ya sake dagowa ya kalleta sannna ya daga mata kafadunsa gami da watsa hannuwa alamun ba abinda ya sameshi. Murmushi ta saki itama abinda ya kusa narkar dashi kenan,fararen jerarrun haqoranta sun fito reras tamkar adon lu'ulu'u,har qasan ranta taji dadi da dayar rigar bata baci ba,ya sunkuya a nutse ya zare takalman qafarsa sai socks kawai daya rage,sai ya miqa hannu ya kama hannuwanta,a hankali yace
"Kinga abinda nake gudu ko?,zazzabin nan ya dawo sosai".
" Ba matsala......zai"
"Da matsala mana......bakisan yanzun nan sai na rasa nutsuwata ba saboda wannan zazzabin?" Ya tambayeta da dukka idanuwansa a kanta suna kuma karanta gaskiyar abinda yake fadi daga qasan zuciyarsa ne. Wani abu na daban takeji,wai yau ita ake damuwa da ciwonta?,matar da saidai ta damu da ciwon wasu amma nata ciwon dai damuwar qannenta ne kurum?.
A nutse ya riqe mata hannu suna takowa har xuwa bakin wani dan box,yasa hannu ya danna ya budeshi,saiga loafers masu kyau ya ciro ya saka a qafarsa sannan ya kalleta
*_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_*
08187255862
π π π π π π π π
_Zafafabiyar_
ΜΆBΜΆOΜΆOΜΆK ΜΆ2
β±§Ιβ²Ιβ₯β³
ππΌππ 110
110
"Zan iya daukarki mu qarasa?" Kai ta girgiza masa da sauri,sai ya dauke kai bai sake cewa komai ba.
Qafafunta takejin kamar ba zasu iya daukarta ba sanda daya daga cikin crew din ke gyaran wajen aman haka taja jiki tana komawa gurin ta. Xarginta yana sake qarfi da kowanne motsi na yarinyar,amma jikinta da zuciyarta sunqi aminta da cewa coki zai iya kasancewa a jikinta. Ita ta kawo yarinyar rayuwarsa kuma har yanxu bata manta da fafatawar da akayi dashi kafin ya karbeta ba......to mene haka yayi sautin sauya masa ra'ayi game da yarinyar idan ba sihiri bane?. Wannan abun yafi qarfin bariki......ta samu kalar kulawa da damuwar da ko amernatun bata sameta ba. Har yanzunda take zaune idanunta suna iya gane mata yadda hankalinsa yayi mugun tashi da aman da takeyi din,baya jin kunyar kowa dake tsaye a wajen,kamarma ya manta da wanxuwar kowa a wajen saishi da ita kawai....dole ta lalubo musabbabin ciwon nan da dukka iyawarta,musaddiq ne kawai kuma zatabi ta kanshi ta samu information din da takeso hankali kwance.
Tayita zuba idanu ta gansu ta inda su anni ko maamah suke amma sai tsintar kanta tayi a VIP suit. Ta yita maimaita sunan bayan ganin wajen,wajen yaci sunansa dari bisa dari,zama rantse da Allah ba cikin jirgi kake ba,don ko windows sai ka danne wani abu sannan zai yaye maka su. Akwai mini bed da sofas masu tsananin kyau da taushi a gurin,tamkar kana cikin wani qawataccen madaidaicin parlor maras tarkace da hayaniya,harda office area da aka yiwa gurin daya ajiye tarkacen kayan aikinsa kamansu system dinsa da wasu documents nashi.
Gadon yaso tayi kwanciyarta amma taqi,sai ya ajiyeta saman recliner,ya jawo foot setter din dake qasanta ya dora mata qafanta akai sannan ya lullubeta da wani sky blue din blanket sannan ya juya a hankali yana fita a wajen ta wata qaramar qofa.
Numfashi taja sosai tana saukewa,tana yawo da qwayar idanunta cikin wajen. Wani nutsatsen guri ne da yaci sunan VIP suit din,daga ita saishi a wajen,guri ne da idan kana nan bazakasan meye yake faruwa cikin jirgin bama. Tabbas duniya girma gareta kuma fadi gareta,sannan ta sake yarda ta sallama kuma rayuwa mataki!mataki ce. Daga shigarta family din jadda taga abubuwa masu yawan gaske da idan a baya akace mata akwaisu a duniya hankalinta bazai dauka ba,da gaske ne kudi ba wasa bane.....arziqi kuma ba qarya bane......kudi nada wani irin power......suna mallakawa mutum girma da fadin ikon da baisan iyakarsu ba. Wani lokacin idan ta kalleshi sai ta dinga jin yafi qarfinta nesa ba kusa ba......ya kuma tserewa ajinta.....wani lokacin saita dinga jin kokwanto da shakkar sake masa dukka gaba daya.....kada a gaba ya samu dukkan komai ya kuma zame ya barta tunda tabbas ita ba ajinsa bace,saidai kuma wucewar kowacce daqiqa da second yana sake bata dukkan wani dalili na soyayyar gaskiya a aikace ba wai a baki ba. Maida idonta tayi ta rufe tanajin yadda zazzabin ke ratsa qasusuwanta,gefe guda kuma tana jin irin tababar da akeyi tsakanin bangarorin zuciyarta dukka akan MUHAMMAD FU'AD JADDA.
Motsinsa taji kafin taji sautin nutsatstsiyar muryar nan tasa da sautari takan mata gizo.
"I'd appreciate it if everyone could stay where they are,am looking for some peace and quite,i need some time to myself.......madam bata da lafiya" Yayi maganar cikin dakiya da miskilancin nan nasa.
"Okay sir" Crew din data kawo masa abubuwan daya buqata ta fadi tana juyawa bayan ta ajjiye masa. Idanunsa ya daga ya mayar kan farouq daya tsayar daga qofa ba tare da ya barshi ya qaraso ba.
"Karkace komai.....wannan saqok ba da crew dinka kawai kake ba.....ni akewa jirwaye da kaman wanka.....aini kaina yanzu nasan kafi qarfina.......system zaka bani zan rage wani aiki kafin mu qarasa dubai......acan zamuyi layover". Hannu ya miqa cikin shariya ya jawota ya miqa masa yana kafeshi da idanu,dole dariya ta qwacewa farouq ya amsa yana komawa.
"Wallahi duk kaci bashi saina rama"
"Can maka" Ya fada yana takowa ciki,sai tayi saurin lumshe idanunta don kada ya kamata tana qare masa kallo. Rigar ta zauna masa sosai ta fidda muscle dinsa dake boye a rigar,hakanan ta sake haskashi qwarai,dram dinsa da farouq sai data sakata murmusawa duk da yadda takejin zazzabin na rarakarta. Shikam yayi sa'a daya samu amini kaman farouq a sanda yake cikin yanayi na tsanani......ita ta rasa kaman farouq din,ta kuma rasa abbanta da ummienta,su huda kadai suka rage mata,take taji wata kewarsu tana kamata.
Tayi nisa a tunaninta ta jishi cikin jikinta.
"Oya.....get up" Ya fada yana dan dagota. Mug din hannunsa ta kalla,ita yanzu ba zata iya sawa cikinta komai ba,saita langabe masa tana girgixa kai.
"Bazan iya sha ba"
"Even a little?" Ya tambayeta tana dage mata girarsa dake da cikakken eyebrows,kai ta daga masa a hankali tace.
"Zansha idan na huta.....I'm feeling nauseated" Hannunsa yasa a tausashe ya shafi gefan fuskarta,sannan ya jawo wani qaramin ottoman sofa ya zauna a kai.
Haka kawai ya sakata a gaba,yana kurbar tea din yana qare mata kallo kaman wanda ya samu mirror,blanket dinta taja zata rufe fuskarta ya saka hannu daya ya riqeshi gam.
"Ki barni mana na kalla......wannan face din kawai nake kalla naji nutsuwa ta saukarmin" Ya fada a karye kaman wani maraya,har sai da taji tausayinsa ya tsarga mata.
Hakan bai isheshi ba,koda ya kammaka sai tsintarsa tayi cikin blanket din,ya haye recliner din abinsa yana cusa kansa a cikin blanket din
"Wannan ta miki fadi,bari na cike miki space din daya rage" Ya fada yana shigewa abinsa ya kamota cikin jikinsa sosai.
"Kai....ya salam......your temperature is too high" Ya fada yana matseta a jikinsa sosai. Ita kanta ta sani,qaruwa kawai zazzabin yake,sai kawai tayi luf a jikinsa shi kuma yayi mata masauki me kyau. Shuru ne ya ratsa tsakaninsu,kowanne yana sauraren bugun zuciyar dan uwansa,suna jin sanda jirgin ya soma motsawa,bayan wasu mintuna kuma ya cira yana lulawa sararin samaniya dasu.
β
a awannin da sukayi suna tafiya cikin sararin samaniya duka bacci tayi sosai,duk da irin zazzabin dake a jikinta bai kuma sauka ba. Tafiyar awanni biyar suka sauka a dubai Abu Dhabi.
Movenpick hotel and apartments nan farouq ya kama musu,5star hotel ne dake da tsada saboda kusancinsa da burj alkhalifa. Ya zabar musu shi saboda yafi kusa da American hospital.
Kafin su qarasa ma tuni yayi booking Dr din da zata dubata,don ya tabbatar fu'ad bazai yarda mo giyar wake yasha namiji ya taba sabreen ba.
Cikin mintuna kadan ya kammala dubata,akwai test da taso ayi amma fu'ad din yace suna kan hanya,awanni kadan zasu wuce madina,a can za'ayi mata general checkup gaba daya,ta bata kawai taimakon da zazzabin zai sauka.
Ruwa ta saka mata wanda zai suake zafin zazzabin,ya kuma bata qwarin jiki,wannan ya sabbaba ba mata wani sabon baccin bayan wanda tayi.
Kwata kwata hankalinta yaqi kwanciya kaman yadda bataso fu'ad din yace abar test din ba,zataso taji mene ne?,wanne irin lalura ce wannan tun daga wata uwa duniya har nan gurin?.
"Wanne irin abune da zai sanya ka hana a gwadata aga abinda yake damunta?,idan akayi maya treatment da ka fa?" Maamah data kasa hadiye abinda yake cin ranta ta fada tana duban fu'ad.
Duba daya anni tayi mata ta maida dubanta ga plate din abincinta da yake dukkaninsu suna kan dining table. Maganin shege karen maguzawa,ta fahimci duk wata alqibla ta maamah.......tana kuma karance da dukmotsina,wannan dalilin shi ya sanya duk sujjadarta idan ta aza goshinta a qasa saita yiwa Allah magiyar ya sanya rabo ne a jikin sabreen din,wala'alla wannan ya zamewa mariya ishara a rayuwarta.
"Ni banason wannan tangal tangal din da rayuwa,karo na gaba dole a gwadata asan me yake damunta,ayita zauje da ciwo ba'asan wanne iri bane?".
"Na alkhairi ne" Shine abinda anni taso fadi,saidai kuma ta duba cewa da d'anta take magana.....bari ta barta da pain din rashin sanin taqameme din ciwon sabreen din,sai hasashe sai zargi da zato da zai hana zuciyarta nutsuwa guri guda.
Shurun da akayi mata ya sake qonata sosai,taso tayita jan maganan ne amma ba wanda ya tayata a cikinsu,dole ta qunshe maganarta,daga qarshe ma abincjn qin ciyuwa mata yayi,saita koma daki ta kasa zama.
"Ko na sakashi ya kawomin ita da xummar zan kula da ita zuwa safiya?,ta nan wataqila na fahimci komai?" Ta shawarci kanta da kanta,saidai ita kanta tasan wannan shawarar bame bullewa bace,don bataga ta inda zai aminta ya bata sabreen ba,mutumin da bai jima da dawo da ita cikinsu ba.
Wayarta ta dauka ta djnga laluben da wanda zata zanta,sam sam bataso rabuwarsu da hajja a irin wannnan lokacin ba bayan muradanta basu kammala cika ba. Number bokanta ta shiga hasashen inama akwaita?,inama yana riqe waya?,saidai nan ma ba wani mafita dole Takoma ta zauna tana tunanin zai wahala ta zauna a makka ko!madina harsu gama kwanakinsu,tanajin zata saka ya sanya a maidata gida ne,idan yaso su sa taho daga baya,kafin su iso djn kuma ta gama nata shirin......sai fashewar bomb dinπ₯.
β
β
_WASHEGARI_
*_GAMO DA KATAR_*
_Prince muhammad bin abdul'azeez airport (madina)_
A tausashe yake riqr da tafin hannunta sanda suke saukowa daga cikin jirgin har suka kammala saukowar. Batasan kallonta yake ba sai daya matsa hannunta,tadan daga kanta ta dubi idanunsa. Haka kawai takejin wani farinciki yana shigarta duk da rashin dadin da jikinta da takeji.......farincikin sauka a birnin madina......birnin da ba birni kamarsa,wanda yake qunshe da baiwawwaki masu tarin ni'imomi da falala.
Saukarta a garin kadai ya tuna mata labarin madeena da ummensu tasha basu.
"Gari ne dake da wani irin nutsuwa a cikinsa,kana sauka zakasan yasha banban da duk wani guri da kuka taba zuwa a duniya".
Ta sake samun tabbaci yanzu haka,ta kuma sake gamsuwa da hakan dari bisa dari.
" Zuciyata tanata rayamin baby zaki haifomin sabrrrrr......ki daure ki cikamin wannan mafarkin nawa......ni kuma zan fansar miki da ko mene na mallaka a rayuwata" Ya qarasa maganar yana kallon gabansa sanda suke dab da isa arrival hall. Idonta ta zare a kansa,ta jima bataga wani mutum me jarabar son yara ba irinsa,batasan me zata ce masa ba,don haka ta zabi yin shuru.
"Zaki bani baby my world?" Ya sake tambaya yana dan matsa hannunta kadan na tare daya kalleta ba. Shuru ta sake yi sai shima bai qara tambaya ba har suka qarasa gurin.
Hannu taga yadan daga,saita maida dubanta ta gurin. Saddiq ya hango,sanye da baqar jallabiyya ta maza da baqin hiram. Quruciyarsa da kyansan nan da suka gada daga gurin anni ya sake fita sosai.
Kaman giftawar walqiya,kaman kuma cikin majigi idanunta ya subuce zuwa gefansa. Farar matashiya ce,sanye da baqar abaya itama,hannunta dauke da welcome board dake dauke da sunan ADDA SABREEN AHMAD. Ta kasa ganin fuskar matashiyar don ta kare fuskartata da board din. Jinin jikinta taji ya harba da gaske da wani irin gudu,saita soma leqawa ta hagu da dama tanason ta tabbatar abinda take zargi ne ko kuwa kawai hasashe ne irin na zuciya?.
Ta leqa ta sake leqawa amma bataga fuskar ba,sai kawai ta maida dubanta ga fu'ad don ta tambayeshi yana ganin abinda take gani kuwa?. Gani tayi hankalinsa baya wajen,don haka ta sake maida dubanta gurin,saidai kuma a yanzu alluna uku take gani maimakon daya,kuma kowanne dauke da sunanta,hakanan kowanne me riqe dashi ba'a iya ganin fuskarta.
Cak ta tsaya tana qare musu kallo,tana jin bugun zuciyarta yana qaruwa. Bataso ya zamanto gizo idanunta suke mata,ta laluba kuma ya zamana ba abinda take muradi ba,bataso ta saka rai akan abinda daga qarshe zai zamanto ba haka yake ba,ta daga yatsunta tana sake irga allon daya bayan daya,a hankali ta samu bakinta da furta.
"Huda.....nadra.....haneefa" Murmushi me sauti ya subuce masa ganin yadda ta fadi sunansu a jere a yadda suke. Sautin murmushinsa ya tabbatar mata yana ankare da komai,ya latsa wayarsa ya aike saqo a gaggauce ga saddiq wani irin ruhin soyayya da 'yan uwantaka yana ratsashi. Yaso musaddiq tamkar haka a duniya......a sanda ya