Showing 297001 words to 300000 words out of 557259 words

Chapter 100 - ๐ƒ๐”๐๐ˆ๐˜ATA BOOK1 AND 2 HAUSA NOVEL

HUGUMA   

03 Nov 2025

444

kwance ta koma tayi relaxing jikin kujerar tana duban maamah,sannan a nutse ta daga qafarta ta dora daya saman daya tana ci gaba da dubanta.

"Karki wahalar da kanki.....kada kuma ki wahalar da shari'a,kada kiyi kaman bakison kudi hajjiya......idan sun miki kadan kawai kice na qara miki,sai na qara mikin a wuce gurin.....fu'ad kawai nakeso,kudi ba matsalata bace sam sam". Sake tsare laila tayi da ido a karo na biyu tana karantar gaskiyar abinda take fada har zuciyarta. Qwaqwalwarta ta lula zuwa duniyar tunani duk da bata barta tayi nisan zango ba.

Akan me zata bari tayi asarar kudin da take gani a gabanta yanxu haka?,bayan tana da damar mallakarsu?. Tabbas akawai manufar turo laila da ubangiji yayi cikisu a daidai wannan lokacin da take neman dukka hanyar da zata cisge sabreen daga gidan fu'ad.....babu ko shakka laila itace macen daya dace ta maye mata gurbinta.

Duka ma a ture ta batun kudaden da zata mallaka......babban abun alfahari ne a yadda ubangiji ya yiwa yaronta kudi yabi sahun manyan masu kudin africa ma gaba daya......ace kuma yau shine yake auren diyar mutum kaman ambassador khaleed mustapha,wanda a muqamai dai na duniya tana jin ba wanda bai riqe ba,saidai kuma a lahira idan ana riqewa.

Lallai ne ita mariya sunanta yana dab da sake fantsama cikin bakunan al'umma.....qawaye dangi da 'yan uwa,tana dab da sake taka wani matsayi na zama cikin manyan matan da fu'ad har yanzu yaqi sakar mata jelar macijin tayi wasa da ita da kyau,....wannan shine mafarin da tauraruwarta ta gaza yin haske kaman yadda takeso. Sunanta takeso ya zama cikin jerin sahun sunayen mata masu aji da sukafi kowanne mata a africa da duniya ma wasa da kudi.....cikin jerin sunayen iyayen attajiran 'ya'ya da kowanne taro ake kwadayi da rububin gayyatarsu,saboda sun zama bangon sugar ko na zuma,masu yayyafin kudi in dollars not in naira......don tana jin zuwa yanzu a arxiqinsa ita kanta tafi qarfin yin kyauta da naira.

"Ki rubuta dukka adadin da kikeso" Ta tsinci muryar laila tana fadi,saita sauke idanunta akan abun rubutun da laila ta aje a tsakaninsu tana rutsata da idanu. Maida dubanta tayi kan fuskar laila,duk da alamu sun nuna tasan wani abu a kanta......amma ba zatayi saurin bada kai bori yahau ba haka da wuri gudun raini.

"Ba ta wannan nake ba.....kawai ina duba cewa mahaifinki babban mutum ne da yakai kowacce uwa taso hada jini dashi.....ko don saboda shi zan shige miki gaba har ki samu fu'ad.......amma samun muhammad ba abu bane me sauqi......da gareshi akwai wasu tsauraran matakai,kamar yadda nima daga wajena akwai wani mixani da nakeso duk matar da zai aura lallai saita cikemin su cif da cif......yanzu haka rashin cike wancan mizanin daga matarsa ta yanzu ya sanya take fuskantar barazanar gutsirewar aurenta daga yanxu zuwa kowanne lokaci"

"Daga yanzu zuwa kowanne lokaci?,ashe ma baki da guarantee......ashe baki da tabbas?" Laila ta fada da narkakkun idanunta dake nuna yadda suke da kyakkyawar alaqa da kayan maye


"Ai kawai kiban wannan kwangilar.......nan da jibi ko gata.....kwanaki uku idan sunyi yawa zata zama tarihi a rayuwarsa......shiga cikin mutane xai gagareta......bama ita kadsi ba,haka dukka wani dake da nasaba ko alaqa da ita" Tayi maganar da cikakken qwarin gwiwar daya sanya maamah tsayawa ta xubawa laila ido.

Daga jin alwashin dake fita daga bakin laila kadai ya isa ya gaya maka ita dinma wata akwai wani magana ta daban a kanta......itadin ma a shirye take

"Dole kema nayi takatsantsan dake.....aminta dake haka lokaci guda babban kuskure ne......amma dole na fara miki da karin maganar nan da hausawa ke fadin DUK WANDA YA RIGAKA KWANA DOLE YA RIGAKA TASHI.

Murmushi ta sake mata tana dubanta,ta sake yalwata fara'ar dake saman fuskarta tana kallonta.

"Wannan ba wani abu bane da zai zama matsala......na baki wuqa da nama.....idan akwai wani information da kike buqata dukka a shirye nake na baki shi". Kai laila ta jinjina tana sakin murmushi

" Zan iya gaya miki har fiye da abinda kika sani......ina da labarin abinda na tabbatar ke baki sanshi ba". Ta qarashe maganar tana bude handbag dinta qirar kamfanin Hermes ta zaro cheque.

Rubutu tayi samansa hankali kwance tayi kuma sign dinta,sannan ta miqawa maamah. Kudi ne a rubuce kamar yadda ta furta zata bayar da farko,maamah din bata gama wannan tunanin ba muryarta ta sake fargar da ita

"Wannan din somin tabi ne.....muddin kikayi nasarar zama surukata,zaki mallaki wata power ta fada a ji a manyan gurare da dama ta hannun mahaifina".

Komai ganinsa maaamah ta dinga yi kaman cikin mafarki,duk da ta tattara dukka mamakinta ta hadiye don ba buqatar laila ta karanci komai.

"Zamu iya ganawa dashi a yau?" Laila ta tambaya maamah tana jin kwadayin ganinsa a daren yau.

"Baki da matsala da wannan"

"Zamu wuce masauki yanzu haka don mu huta sosai,bayan magrib sai na dawo,hakan yayi?"

"Yayi" Maamah ta fada tana daga zaune har yanzu,don mamakin da taketa boyewa yaqi barin zuciyarta. A gabanta Laila ta miqe tana fita daga parlor din,maamah kuma ta rakata da idanu.

Tana fita daman jira takeyi,ta miqa hannu ta jawo cheque din tana dubawa

"Da gaske adadin ta rubuta,akwai genuine din signature nata da komai?" Sake jujjuyashi tayi a hannunta,sai kuma wani murmushi ya qwace mata.

"Lallai ni mariye me sa'a ce,ko rashin samun fu'ad a hannu akan lokaci na yarda lokaci kawai ne baiyi ba" Ta gayawa kanta da kanta tana gyara zamanta sosai tana jin kamar kanta zai fashe saboda wata izza da take saukar mata har tsakiyar ruhinta. Ta zubawa guri daya idanu murmushi na fita daga fuskarta lokaci bayan lokaci. Yau da wacce irin sa'a ta tashi?,wacce addu'a tayi yau?,babu....shine amsar data bawa kanta da kanta,don ko basmala cikakkiya bata jin tayi tun daga safe kawo yanzu.

A dan fusace ta juyo jin an murda qofar ana shigowa,saboda ita din bata sakarwa kowa da kowa shigo mata guri kai tsaye ba....ko waye kai saika nema izini ta kuma baka.

Idanu suka zubawa juna ita da hajja,saita janye cheque dinta tana lanqwasheshi ta daga pillow din kujerar gefanta ta saka a qasansa. Idanun hajja yana kai,abun kuma ya sake haifar mata da wani matsanancin bacin rai. Iya wannan abun da mariya takeyi kawai ya isa gaya mata komai daya faru ya faru ne bisa son ranta da kuma zabinta. Tunda suke da mariyan ba rufa rufa irin wannan tsakaninsu......tayi baqi ta kasa ganawa dasu a gabanta?,taga takarda duk da batasan ta mece ba amma mariyan ta jata ta boye?.

"Kinga surukarki ko?,diyar ambassador khaleed mustapha" . Maamah ta sake maimaita abinda tasan already hajjan ta jishi.

"Musaddiq ne kenan shima????". Kai da maamah kr girgizawa ya hana hajja qarasawa.

" Fu'ad dai,d'ana fu'ad ". Da wani mahaukacin mamaki hajja ke bin maamah dake doka murmushi da kallo

"Kinga Kalar surukan da ake fatan samu......wadanda za'a ciccibi juna....ba wadanda suke hangen turmusheka kai da mafarkinka ba.....maciya amana masu fatan kayi gyangadi su kafta maka sara.......zan shiga ciki in huta,ina da baqi anjima......idan kin gama ki rufe gurin.....karki damu kanki da lamarin laila......dama haka rayuwa take.....ka riqe dan wasu kaima a riqe naka,duniyar juyawa take haka da sauri........su madeena sun isheki zama.....ni kuma laila kadai ta isheni" Tana qarasa maganarta ta fara takawa zata fice54


_Daga nana aisha RA tace,manzan Allah S A W yace: "anayin wanka akan abubuwa guda biyar,janaba....da wankan juma'a...da idan anyi qaho,da wankan mamaci(mutum ya yiwa gawa wanka)_




"Mariya!" Hajja da zuwa lokacin ta kasa riqe kanta ta kirata a hautsine

"Koda wasa......koda tsautsayi kada kiyi tunanin cutar da laila......karki manta dukka sirrikanki a nan suke" Tayi maganar tana nuna mata tafin hannunta.

Murmushi ta kuma sakar mata sannan ta juyo sosai tana amsata.

"Wadannan sirrikan da kike da ganin sun isa abun tunqaho.....nabar miki su halak malak kiyi yadda kikeso dasu.....laila kuwa a yanzu mallakina ce,baki da hurumi a kanta,idan kuma kina ganin zaki iya to bismilla,ga fili ga me doki,kinsan dakin dana sanya aka sauketa ai" Ta furta tana nuna mata hanya,sannan ta juya hankalinta kwance tana fita daga dakin.


โ˜…k'arfe biyar da rabi yammacin ranar jerin luxury cars dinsa sukayi matsugunni a babban sashen ajiyar motoci na mansion House din nasa. Wani baqon abu daya kwana biyu baiyi ba,wato dawowa gida a lokaci irin wannan. Dawowarsa da wuri shine qarfe takwas zuwa tara na dare,wanda ita kanta matar gidan batasan lokutan dawowarsa ba.

Kaman ko yaushe daga farfajiyar gidan ya tsaida kowa ya kuma sallami kowa,wanda kusan quarters ne guda daga can wani sashe daban na gidan da yawancinsu suke da nasu apartment din,ba lallai ma ka fahimci da wasu dake rayuwa cikin gidan bayan ainihin masu gidan saboda nisan tazarar dake a tsakaninsu.

A hankali yake takawa zuwa ciki suna magana da farouq qasa qasa.

"Na fita daga company,kuma ina tunanin sai gobe zan sak shiga......wani irin headache ne yake matsamin tun jiya......but daga dazun zuwa yanzu kaman ya qaru"

"Dude.....kana over work fa?,Allow your self downtime......kana da aure amma a suna kawai......kasan benefit na aure kuwa da ba zasu qirgu ba?....Emotional support and mental health duka zaka samesu if ka bawa matarka damar shiga rayuwarka"....


" Hey.....zaka fara ko?,waye ya gaya maka kowacce mace ake bawa dama ta shiga rayuwarka?,wasu matan poison ne fiye da yadda kake kimantawa,they are wicked" Ya fadi yana hadiye wani yawu lokacin da madaurin tunaninsa ya warware yana koma masa can shekarun baya.....sanda maamah ta zama silar rasa lafiyar mahaifinsu duk da kasancewarsa mutum ke kazar kazar,ta kuma zama silar barinsa sararin da suke kai yanxu suke rayuwa akai wato DUNIYA. Daidai sanda ta sauka daga saman high chair din data zauna a akai cikin kitchen din suna taba hira da ma'u,wadda take hada qullin wainar shinkafa zata soya musu

"Bari na dauko na dawo" Tace da ma'u din tana gyara yafen qaramin Chantilly veil din data lullube sassalkan gashinta. Furucin nasa ya sanyata tsaiwa cak sanda muryarsa ta kaiwa kunnuwanta saqon da yake isarwa farouq,sai taja da baya tayi tsaye jikin qofar yana jiran wucewarsa don ta wuce itama zuwa dakin.

"Let's try not to judge people and instead understand their perspectives".

"Am not judging fa......dude ba zaka gane bane,na iso gida.....i need to rest.....call you later"

"Okay byee" Farouq ya fada yana sauke wayar iska ya furzar daga bakinsa yana duban file din dake gabansa cikin katafaren kamfanin sarrafa kayan abincinsu dake sharada industrial area. Yanaji a ransa zai sake rage kwanakin tafiyar nan tasu ko wataqila hakan zai kawo kasuncin da yake fata tsakaninsa da ita. Yasha attempting saka amna cikin abun,yasan zatayi aiki sosai.....saidai kuma amna din quruciya tayi mata yawa,baisan ya zata dauki abun ba,uwa uba yana buqatar yayi komai cikin sirri.

Shurun da taji cikin parlor din ya sanyata tunanin ya wuce,ta sauke siririyar ajiyar zuciya,kunnuwanta na maimaita mata da meye da meye ya fada akan mata?. Siririn tsaki ta saki zuciyarta na siffantashi da jerantashi cikin sahun mazan da sam bausan mutuncin diya mace ba....suke mata kallon kuma wata halitta da bata da wata daraja kwata kwata.

Siririn tsakin daya sanyashi daga kansa a hankali daga rufe bottle na ruwan da ya tsaya ya bude yasha saboda yadda maqoshinsa ya bushe,yana ji kamar bazai iya qarasawa saman ba.

Guri daya idanunsu suka hadu,ya kafeta da qwayar idanunsa da sukayi wani laushi tubus saboda yadda ciwon kan ke sara masa lungu da saqo na cikin kansa. A hankali ta zare nata idanun daga kanshi,sannan ta koma da baya zuwa kitchen din ba tare data qara koda second uku a wajen ba.

Kansa shima ya dauke yana ajiye robar,sannan ya soma takawa a nutse yana wucewa ciki kafin ya haura zuwa saman. Tun daga wancan ranar bai qara ganin gilmawarta ba cikin gidan,wasu lokutan ma sai yaje gaida anni ta tambayeshi iyali take fado masa a rai. Wani irin mummuna fito na fito yayi da kansa akan damuwa da abinda tayi masa a ranar din,yana ganin bai cancanci ya sanya damuwarta a ransa har haka ba.....sai ya sake qarawa kansa wani busy din akan wanda yake ciki,yana saka ran wannan ya zama silar mancewarsa da komai,wanda yawan ayyukan da suka zarta qa'ida din daya azawa kansa yake kyautata zaton shine silar wannan ciwon kan da ya fara fama dashi.

A gajiye da wani irin bacin rai da baisan meye dalilin faruwarsa ba daga shigowarsa gidan ya dinga zare suit din jikinsa yana zubarwa,duk da cewa ba al'adarsa bace hakan.

Bathroom ya wuce kai tsaye,ya hada ruwa me dumi da zai dace da yanayin sassanyar iskar dake kadawa,wanda asalinta hadarine daya hado,bai saukar da ruwan ba,amma ya canza kala zuwa ruwan toka,ya kuma bada iska me sanyin dadi dake busawa da qamshin qasa,yanayin da yake bada tabbacin anyi ruwa a wani gurin kusa da kano.

Mintuna kusan arbain ya fito daure da towel,gargasar jikinsa dama sumar kansa duka sun jiqe da ruwa. Faffadan qirjinsa dake lullube da gargasa ya fara gogewa da towel din yana isa gaban madubi,daidai sanda yaga wayarsa na haske. Kaman ya share saboda bayason doguwar magana,amma koda ya duba yaga maamah ce sai ya zamana bashi da wani zabi daya wuce ya daga kiran.

Sai daya zauna saman bean bag chair din dake ajiye a gefe sannna ya daga hade da sallama.

"Barka da yamma" Ya dora da fada yana lumshe idanunsa saboda yadda kansa yake sarawa.

"Barka kadai......kana office ne?,inason ganinka idan kun tashi,akwai muhimmiyar magana da zamuyi da kai,sannan akwai baqi da sukeson ganinka" Ta fada kanta tsaye. Yatsun hannunsa da baya riqe da wayar ya cusa cikin sumarsa,yanajin yadda ta jero buqatunta kai tsaye ba tare da neman jin uzuri ba.....ya ya wuni?,akwai damuwa?,yana da lafiya ko babu?. Baisan sai yaushe wannan dabi'ar tata na damuwarta itace kadai damuwa zata sauya ba.....baisan sai yaushe zata damu da damuwar wani ba ta aje tata damuwar da son kan a gefe ba.

"Bana company na dawo gida....."

"Okay,to ya za'a yi kenan?,don duk yadda za'ayi inason ganinka lallai lallai a yau din,ko meye kakeyi ka katseshi kazo ka sameni" Ta sake fadi da dukka sautin da zai gaya masa da gaske take.

Jaririyar ajiyar zuciya ya sauke yana cire yatsunsa daga sumar tasa

"Ciwon kai nake maamah.......amma zansha magani na kwanta zuwa anjima zan shigo" Ya fada da raunanniyar murya,yana jin har qasan ransa ya rasa wani part me girma a rayuwarsa,yanajin ya rasa wani abu me matuqar muhimmanci a rayuwarsa. Duk da yana da anni,yana da farouq,yana da saddiq da musaddiq,amma lokuta da dama yana jin kamar shi kadai ne.....yanajin kamar shi kadai yake rayuwa a duniyar,wani irin maraici da kadaici yana mamayarsa.

"Allah ya kaimu,kada kayi dare da yawa Allah ya sawwaqe" Ta hade maganar duka lokaci guda.

Ya jima idanunsa saman wayar yana kallonta,zuciyarsa na tuna masa abubuwa da dama ciki harda abbansu. Tun asali shike damuwa kuma shike kasa bacci idan dayansu baida lafiya,koda ciwon baikai ya kawo ba. Tun da can ita din bame damuwa da lamuransu bace,tafi damuwa da duk hanyar da zata maida taro ta koma sisi.

Sai daya bushe tas bai sani ba kafin ya miqe yana isa ga walk-in closet dinsa,boxer kawai ya zura bayan ya mulke jikinsa da cream dinsa,ya kuma shafe jikinsa da turarukansa,sai ya koma gefen gado ya zauna bayan ya balli wasu tabs na saukar da ciwon kai ya sha,ya dauki remote guda uku,daya ya zuge duka labulayen dakin dashi,daya ya kashe hasken duka fitilun dakin banda ta gefen gadon,dayan kuma ya saisaita sanyin ac din yadda zai daidai da yanayin da yake ciki.

Cikin duvet ya shiga ya duqunqune yana lumshe idanunsa gami da sauke nannauyan numfashi,ya lumshe idanunsa yana son fatattakar kowanne tunani da lissafe lissafe ko zai samu brain dinsa tadan huce.

Ana kiraye kirayen sallar magariba ya farka daga gajeran baccin daya daukeshi,yaji dadi sosai a jikinsa,sai ya wuce toilet yayi tsarki ya daura alwala. Masallaci ya wuce kai tsaye,akayi magariba da ishai duka dashi,sannan ya dawo ya shirya cikin tattausar exclusive Morocco ta maza me zuwa hade da wandonta. Kalar royal blue ce,sai akayi mata ado da gold zare daga wuyanta hannu aljihu qasan wandon da tsagar gefe da gefe na rigar. Wata zagayyar hula ya dora saman kansa ruwan gold din,wanda yawanci yankin larabawa su sukafi ta'ammali da ita,take farin bafullatanin nan muhammadu jikan jadda ya fito da wani irin kyau da zai wahala ka kalleshi sau daya ka kauda idanu
(Niko nace uhmmmm,kaman kuwa yasan zance akazo yi gurinsa๐Ÿ˜‚).

Clogs ya sanya gold color,ya feshe jikinsa da mayen turarensan nan

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login