Showing 525001 words to 528000 words out of 557259 words
da sauran.
Ta bangaren maamah kuwa.....tun ranar daya kai mata yaran suka kasa bacewa daga idanu da kunnenta. Cikin awanni ashirin da hudu na yininta kowanne awa bata rufewa ba tare data tunasu ba. Sannu sannu sai takejin kamar tanason ta sake ganin yaran,kaman tana kewarsu,idan tana dakin bata da aiki sai kallon muhallin da ya kwantar dasu a waccan ranar. Wani abu takejin kamar yana shirin kamata me kama da hauka hauka akan yaran,tana yawan jin irin kukan da sukayi a waccar ranar,tana yawan jin muryoyinsu kaman suna wajen.
Daga qarshe dai ta fahimci son ganinsu takeyi,saita ta rasa kuma yadda zata fahimtar dasu saratu tanason ta sake ganin yaran,don iyasu kadai kawai takeson gani banda mahaifiyar tasu.
A hankali sabreen din cikin salo da hikima ta soma gyaran jikinta ta hannun dattijuwar matar nan da tasan jiya tasan yau kuma har gobe ake tafiya da ita wato Bgawos kitchen and aphrodisiac. Ingantattun kayan gyara natural na matan da suka jima a duniya kusan shekaru hamsin.08127084190/08104553105(tasan sirrin gyara sosai,gyara irin na dauri na tsaffin mata bana zamani ba,bana gama garin masu magungunan matan yanzu ba,bama gyaran kadai ba,hadda duk wani nau'in abinciccika,na biki ne suna taron sauka walima da sauransu,ko kuma kawai akwai ranar da zaki tashi bakya sha'awar shiga kitchen?,kinaso kuma abincin gidan ki ya zama ready a tsaftace kaman ke kika shiga kitchen din kikayi da kanki?,karki tsallake wannan).
A jikinta kawai taji canji me matuqar yawa,ta sake jinta tana sake kintsuwa tako ina. Har ta soma gyaran jiki ta watsar,don ta tsorata sosai ranar da fu'ad ya rutsata,da qyar tasha,amma daga qarshe ya gaya mata yana lissafe da satittikan da suka rage.
Tunani ta shiga sosai na yadda zata kubce masa,tanaso ta sake warkewa sosai,uwa uba kuma sunyi hira da fannah,har suka gangaro kan tsarin iyali.
"Muddin period dinki ya dawo to duk sanda kuka kasance tare xaki iya daukan wani cikin" Idanu sabreen ta waro waje.
"Ciki fannah......" Ta danyi dariya.
"Satinsu fauzan nawa?" Dariya fannah tayi.
"Shi ba ruwansa da satin yaranki nawa......indai har period ya dawo daidai shikenan magana ya qare"
"Fannan BB...." Sabreen ta fada tana cin serious.
"Adda sabreen" Ta amsa mata tana dariya qasa qasa.
"Kibar zancan nan tukunna......me zaki bani na gyara tsarabar bare bari" Gyara zama fannah tayi.
"Kamar kuwa kinsan mu bare bari ba wasa bane" Sai suka saki dariya a tare.
"Bari na gutsira miki kadan.....ki samu 'ya'yan habbatussauda da dabino ki dinga ki tsaga dabinon ki cire qwallon ki zuba yayan habba din ki dinga taunawa kullum safe da dare". Da daya da daya ta dinga bata sirrikan da na barebari ne,ita kanta ta qaru ta kuma sallama (sai damu wallahiππ₯±).
A tsorace take har zuwa sanda suka cika sati shida,ganin sun tsallake ranar baice mata komai ba,don washegari qaramar tafiya ta kamashi zuwa branch dinsa na lagos,don haka kawai tayi amfanin da wannan damar ta tayar da yawon arba'in.
Dabara tayi,ta kira anni tace mata tana son zuwa din,amma bata samu hamman ba,tunda tasan wani lokaci idan tafiya me muhimmanci wadda take ta gaggawa irin haka ta taso masa yakan saka layinsa a flight mode ne
"Yana da kyau ai,ko don a sake ganin 'yan uwa,zan gaya masa da kaina" .
Hankali kwance tahau shirinta,so samu ma ta wuce mali wajen mommanta,to amma mali din tasan tayi nisa ta tsallake zuwa can,don haka kawai saita shirya zuwa abuja gidan yayan ummeenta da bai jima da dawowa Nigeria ba,ta shirya su fauzan duka da masu aikinta,ta siya musu ticket suka wuce abinsu.
Sanda anni ta gaya masa harda 'yar mitarsa,yana tunanin cikin kano ne zasuyi ziyaransu gidan kawu rufai da gidansu da sauran wajen 'yan uwa su dawo gida su kwana.
"Anni kina ganin ba zata debowa yaran nan iska ba?,40 days fa kawai sukayi,nima kwana uku kawai zanyi fa na dawo,meye na fitan?" Ya kasa boyewa sai daya furta.
"Banda abinka fu'ad ai sada zumunci ne,kuma a al'ada ai dama ana yin wannan zagayen,kaman ba gajiya ne da kuma nunawa dangi lafiya kuke ne" Shuru ya danyi,dondai anni ce,yana kuma kunyar jayayya da ita.
"Shikenan,Allah ya kiyaye hanya"
"Ameen ameen" Anni ta amsashi suka dan sake tattaunawa sannan suka shiga wani maganan na daban.
_Yawon arba'in ko?....hmmmmππ......._
_get ready muna pages din qarshe ne fa in sha Allah_π₯°π₯°π₯°
β
Kwanansa uku a lagos,kwanan sabreen biyu a Abuja ya dawo kano. Har ya iso gidan baiyi wani tunanin abuja ta tafi ba,sai bayan ya shigo ne yadda gidan yayi masa shuru da yawa ya sakashi ya fara kokwanto. Tun a parlor na biyu ya soma da duba kitchen. Ba alamun dazu ko jiya anyi amfani dashi,kai tsaye kawai ya wuce bedroom dinta.
Yadda yaga komai a killace ya bashi amsar cewa ba mutum a gidan,mamaki ya sanyashi zama gefan gadon nata,yana kallon inda aka shirya qananun gado saboda su fauzan idan a dakin zasu kwana.
Sai lokacin yayi noticing wani abu,tunda ya tafi shi yake kiranta,idan ya kunna wayar yana tunanin zai samu saqonta ko miscal dinta sai ya tarar wayam,idan kuma ya tashi kiran nata sai ya kira sau nawa ana gaya masa isn't reachable,sai daga baya ya sameta. Jiyama kwata kwata basuyi waya ba,don ya shiga cikin qaguwar kammala aikin daya kaishi ya juyo gida.
Ya manta rabon da yayi nesa da ita har haka.....bare su yaran da dama bai taba nesa dasu ba sai a wannan karon.
Koda ya ciro wayarsa sai ya rasa waye zai kira?. Anni dai ya tabbatar bada cikakken saninta akan baisan nesa zasuyi ba akayi tafiyar ba........ita kuma sabreen ya kirata yace mata me?.
Wani mummunan baci yaji ranshi ya soma yi,zuciyarsa ta soma tafasa sosai,sai kawai ya fara maimaita
"A'uzubillahi minashshaidanir rajeem.....innalillahi wa'inna ilaihi raji'un". A hankali a hankali yaji zuciyarsa tana yin sanyi,gefe guda kuma yana tunawa kansa maganganun malamai da yawa da kuma abbansa,hadisin manzan Allah S A W da yake gayawa maza su waye mata?.....karkatacciyar halitta da aka halicceta da qashi mafi karkacewa na haqarqari,da wannan ya danne zuciyarsa badon ranshi ya daina baci ba.
Samansa ya haura yayi wanka,ya dawo ya shirya cikin shigar wani tattausan yadi ruwan sararin samaniya,kawai sai ya dauki key da wayarsa ya fice a gidan,duk da cewa yunwa yakeji.
Da kansa yake driving,kanshi cunkushe da tunanin ina zata je?,ina zataje da har bai sani ba?,ya miqa hannunsa ya dauki wayarsa da daya hannun dayan kuma yana riqe da steering ya soma kiran anni.
Bugu uku annin ta dauka,yana iya jin maganarta da su nadra,yaran da qiri qiri tace nata ne.....bama tun ya zu ba,tun a baya inda tasan dasu da tuni sun jima da zama a hannunta,dole kowa dake da kwadayin daukarsu ya haqura yabar mata su.
"Barka da dare anni" Ya furta muryarsa ba wani karsashi yana rage gudun motar.
"Barka kade me babban suna,abban abbobinsa" Ta fada da dan tsokana kadan a muryarta. Duk yadda yakejin muryarsa a jagule saida sabon sunan data sanya masa ya sakashi sakin murmushi.
"Mun yini lafiya?"
"Alhamdulillah.....ka dawo ne?". Sai daya hadiye wani abu sannan ya amsa mata.
" Na dawo dazun,bai wuce awa daya ba".
"To ma sha Allah,Allah ya bada abinda akaje nema da nasara me yawa"
"Ameen ya hayyu ya qayyumu" Sai kuma ya danyi shuru.
"Da wani abune?" Ta tambayeshi,kaman yadda ta saba da saurin gano damuwarsa tun baikai ga furtata ba.
"Cewa nayi anni......wanne waje ne su fauxan suka je?" Banbarakwai anni taji maganar
"Abuja mana.....ina cewa kun fara magana dama tun kafin ka tafi?". Kai ya girgiza a hankali,ya fahimci inda maganar yanzun ta dosa. Idan ya cewa anni baisani ba hakan bai dace ba,zai zamana kaman ya nunawa anni wani laifi nata da wala'alla zai saka annin jin wani iri a kanta,don haka sai kawai yace.
"Ba komai anni......na dauka sun canza booking ne"
"Aah abujanne dai,gidan uncle mubarak ko".
"Ba matsala.......sai na shigo".
"To Allah ya kawoka lafiya" Har zai yanke kiran ta rigashi.
"Me kaci daka dawo?" Tayi tambayar ne don bata gamsu da yanayin muryarsa ba,kuma wani tunani ne yazo kanta a sannan.
"Ba komai anni....amma zanci".
" Ka qaraso ga favourite dinka anyi".
"In sha Allah,godiya nake" Ya fadi yana yanke kiran.
Cilla wayar yayi seat me zaman banza yana jin wani bacin rai yana taso masa. Duk wani dalili na kiranta yakejin babu shi yanzu a tattare dashi. Gudun na meye?,kaman wadda yake sarar naman jikinta?,ko soyayyar daya bata ne ta mata yawa takeson ta fara karya alqawarinsu,ta kuma fara wahal dashi kaman yadda sauran mata sukeyi a sanda suka samu soyayyar d'a namiji yadda sukeso?. Shikam yana jin bazai dauki irin wannan ba,ya tsare mata dukkan komai,itama ya kamata ta tsare masa.
_hausawa sukace zo mu zauna zo mu saba,ran maza ya baci_
_wanne hukunci kuke ganin ya kamata jadda ya yiwa sabreen?_ππ164
Karya kan motar tasa yayi zuwa unguwar tasu,yana jin ya kamata ya duba maamah,duk da ko bayan ya tafi kullum sai ya kira yaji ya suka kwana,ya kuma suka tashi.
Tun daga gate masu aikin gidan suke gaidashi,har zuwa sanda ya isa qofar parlor din. Takalmansa ya cire,sam bashi da wannan dabi'ar na shiga guri da takalmi,duk da girman daraja da matsayin da Allah ya bashi,ya sanya kansa a parlor din a nutse bakinsa dauke da sallama,duk kuwa da yadda zuciyarsa ke a matuqar b'ace.
Muryarsa ta sanyata daga kanta da sauri daga karbar madarar da saratu take bata. Idanunta ta kafe a kansa kafin ta maida dubansa zuwa ga bayansa kaman me neman wani abu. Ita shima yake kallo,yana mamakin yadda taketa kallon bayansa din,kwanyarsa nason lalubo masa dalilin kallon.
Bugun zuciyarta yadan qaru,sai taji zuciyarta tana dan washewa daga sanda yayi sallama a parlor din. Can qasan ranta ta samu kanta da fatan Allah yasa tare yake da yaran,Allah yasa tare suke,saidai duk walwalar da taji ta sauko mata sai taji tana komawa sanda ya qarasa shigowa falon,ta kuma fahimci shi kadai ne.
"Kawo na qarasa bata" Fu'ad yace da saratu sanda ta gama gaidashi yaja kujera ya zauna daura da maamah din. Amsa masa tayi cikin girmamawa,ta miqa masa hade da dan qaramin towel sannan ta miqe tana basu guri.
Duk sanda ya miqa madarar bakinta sai yaga ta kafeshi da wani irin kallo,ya kasa gane abinda yasa take binsa da kallon,saidai yasan cewa lallai akwai wani abun a qasa.
Wani irin boundaries takeji tsakaninta dashi,zamansa kusa da ita yana shayar da ita madarar sai taji kamar ana sauyata ana kuma sauya jiki da zuciyarta. Fuskokin yaran guda uku take gani a tasa fuskar,tanaso tace masa ina suke?,tanaso tace masa ina ya barsu?,tanaso tace masa yaje ya dauko mata su amma kuma ba halin hakan,ba kuma bakin hakan a tare da ita.
"Akwai wani abu da kike buqata?" Ya tambayeta ganin yadda kallon yaqi qarewa yana kallon hannuwanta. Kai ta girgiza masa a hankali,amma still bata daina kallonsa ba.
"Zaki iya rubutu?" Ya tambayeta bayan ya gama kallon hannunta guda daya wanda tun wancan ranar yaci gaba da motsi. Kai ta daga masa a hankali tana jin zuciyarta tana tsinkewa. Kowa da yake tare da ita ya gaza gano mata hanyar fadin abinda yake bakinta amma gashi daga zuwansa har ya gano hakan.
Tana ji yana kiran saratu,sannan ya sakata taje ta dauko memo da sticky notes a ajjiye mata koda yaushe a kusa da ita.
Sanda ta kawo din sai ya ciri sticky notes din guda daya da a biro ya dora saman cinyarta
"Write it down" Ya fada a nutse yana kallonta. Gabanta ne ya fadi,jikinta kuma dukka yayi sanyi tana jin wani yanayi daya haifar mata da fara rawa da jikinta yayi. Sauke biron tayi tana jin ba zata iya rubuta komai ba. Tana jin kunyar tambayarsa yaran duk kuwa da yadda take bala'in son ganinsu......ba abinda ya dawo mata a lokacin sai gamuwarsu ta qarshe,daya ajjiye mata abun rubutu kaman haka,yace kuma ta rubuta dukka adadin abinda takeso zai bata don ta rabu da rayuwarsu har abada,kenan hakan yana nufin inda ta rubuta din sun rabu?,inda ta rubuta din da yanzu ko dan tsako bata dashi wanda zai zauna haka a gabanta ya damu da damuwarta?. Ga dukiyar ga komai tana gani......amma kuma bata wani jin d'andanonta sam a tattare da ita.
Lumshe idanunta kawai tayi tana maida bayanta jikin kujera ta jingina,yadan tsaya yana kallonta saiya kalli saratu.
"Idan bacci takeji a maidata daki a gyara mata gun kwanciya.....ni zan wuce,sai da safe idan Allah ya kaimu"
"To ranka ya dade....Allah ya tashemu lafiya".
Kai tsaye gidan anni ya wuce,ya sameta da 'yan matanta guda biyun,nadra da haneefa. Abinci sukeci,kai tsaye nadra ta shirya masa nasa abincin sannan sukayi qoqarin tashi su basu waje shida anni.
"Kuyi zamanku" Fu'ad ya fadi yana ganin fuskar haneefa kamar sabreen ce a wajen saboda kamannin da suke da ita.
Sosai yayi qoqarin share damuwarsa ta hanyar sakewa yayi hira da anni,saidai suna tsaka da hirar kiran sabreen ya shigo wayar annin.
Bai sake cewa komai ba yaci gaba da cin abincinsa,saidai kuma yana iya dauko sound dinta ta cikin wayar. Abinda ya sake quleshi yadda yaji tana hira hankalinta kwance,suka gama maganganun da zasuyi da anni su haneefa suka karba suma suka dora.
"Lafiya dai ko Muhammadu?" Anni tace dame babban suna wanda har ya kammala cin abinda zai iya ci ya miqe. Murmushi ya qirqira.
"Ba komai anni......" Bata gamsu ba sam sam,saidai daga kiran da sabreen tayi kawai taga fuskarsa ta sake canzawa,amma kuma bataso ta zama me yawan sanya kai akan mu'amalolin gidajensu. Koda matsala ce tafison su koyi kasheta da kansu da kansu,hakan zai koya musu jarumta da kuma dabarun xama da juna da kuma sake samun shaquewa sosai da juna.
Ya yiwa anni sallama ya fito zuwa parking lot na gidan farouq ya shigo shida fannah. Fanna ta gaidashi ta wuce ciki,shi kuma farouq din yayi tsaye daga wajen motar fu'ad na daga ciki ya zuro qafafunsa waje.
"Inata tunanin kiranka ai" Fu'ad ya fadi yana dan shafa sumarsa,don duk yadda yakeso yayi avoiding damuwar amma har yanzu yana jinta cikin kansa.
"Lafiya kake dude?" Farouq ya tambayi fu'ad din. Kaman zaice wani abu sai kawai ya basar,yanason koma meye ya ganar da ita kurenta da kansa,basai wani ya ji ba.
"Share kawai......hannu nakeso ka sakamin a nan" Ya qarashe maganar yana miqaqa farouq din. Karbar takardar yayi yana dubawa.
Takardar mallakar wani tafkeken fili ne me fadin qafa da tsaho me yawan gaske. Daga kai tukunna farouq yayi ya kalleshi.
"Wanne company ne haka zai sake lashe girman filin nan?" Murmushi fu'ad ya saki a gajiye.
"Ba wani company.........mafarkina nakeso na cika na gina mana gida guda daya amma me gidaje sassa daban daban a ciki,wanda zai qunshi duk wani jinin jadda......ina mana sha'awar mu rayu tare yadda yaranmu zasu tashi da zumunci fiye da namu in sha Allah". Kai farouq ya jijjiga,sai ya maida file din ya rufe.
"Wannan burina ne.....ni na tanadar mana wannan filin,bazan kuma bari ka rigani ba......kayi haquri ayi amfani da nawa" Kai fu'ad ya girgiza yana dage glass din motarsa
"Is too late dude........saidai ka dauki wani abun daban........amma wannan kam na riga na gama dashi,already ma yau nayi requesting ma wani company daga china zasu zo su fidda komai yadda nakeso ya kasance......idan ka saka hannun ka ajjiye documents din a hannunka,saida safe" Ya fada duka a dunqule yana jan murfin motar ya rufe abinsa sannan ya tashi motar da gudu yana fita a gidan.
Da kallo farouq ya bishi har ga bace masa,sai kawai ya jinjina kai yana maida dubansa ga file din,sannan ya fara takawa yana wucewa cikin gidan.
Ko sanda yaje lagos baiyi baccin wahalar da yayi ba a daren. Lagos yasan baqon guri yake,gurin da ba iyalin nashi,amma anan gurin a yanzun yasan cikin gidanshi yake,saidai ya kasance shi daya,don haka tunda asuba ya lalubi pilot nashi yace ya nema musu izinin tashi zuwa abuja a