Showing 531001 words to 534000 words out of 557259 words

Chapter 178 - 𝐃𝐔𝐍𝐈𝐘ATA BOOK1 AND 2 HAUSA NOVEL

HUGUMA   

03 Nov 2025

471

ya dauke idonsa daga inda take a tsaye ya maida idanun kan screen din yana taba Bluetooth din kunnensa

"Am hearing you" Daya fada shi ya alamta mata cewa waya yake amsawa.

Duk da haka bata fasa sallama ba don tasan ita din me laifi ce,ta taka a nutse tana shiga ciki idanunta nakan wani irin gado dake wani shiyya daban na parlor din. Kaman gado kama lilo haka aka tsarashi,amma idan kakalli cikinsa sosai zaka fahimci gado ne na 'ya'yan gata wanda aka yi masa lafiyayyar shimfida me tsananin taushi.

Gaban gadon ta tsaya tana qare musu kallo,sai wani tausayinsu taji yana ratsata. Kayan jikinsu na dazun yanzun ba sune a jikinsu ba,an canza musu su zuwa kayan bacci masu taushi na jarirai farare qal dukka iri daya,hatta da socks na qafansu dana hannunsu,sai suka sakeyi mata kyau,taga kaman sun qara girma akan girman su na dazu.

Kewarsu takeji sosai,don haka ta miqa hannu don fara daukan almustapha.

A qirjinta ta sakashi,ta rungumeshi sosai tana shafa kan fawwaz. Ta jima a haka kafin ta sanya fawad a kafada daya,fawwaz a daya kafadar,ta fara takawa a hankali tana sauka dasu. Sai data kwantar dasu sannan ta dawo ta dauki fauzan.

"Kinci darajar ma'aiki daya hana raba uwa da d'anta......banda hakan da daga yau ba zaki sake dora hannunki kan yara na ba" Maganar daya fada kenan wadda ta sanyata tsayawa cak. Batayi tunanin ya gama wayar da yakeyi ba,a sanyaye ta juyo zuciyarta na bugawa,saidai kafin ta gama ajiye kallonta a kansa tuni har ya wuce dakinsa abinsa.

Jikinta a mace ta gama shirin kwanciya tana juya maganarsa a ranta. Tayi fakare tana jira taji ko zataji shigowarsa?,don ko dakin bata kulle ba,hakanan su fauzan duka akan gadajensu ta kwantar dasu,saidai harta gama zaman jiransa bacci yayi awon gaba da ita.

Koda ta tashi har an gama sallar asuba. A gajiye ta miqe tana duba ko ina na dakin,ba alamun ya kwana a dakin,a haka taja jiki zuwa toilet tayi wanka sannan ta hada da alwala ta dawo ta bada farali.

Shiryawa tayi cikin sassauqar doguwar riga data mata kyau ta fidda quruciyarta. Qarfe bakwai da ashirin ta wuce zuwa kitchen da nufin shirya masa breakfast,don bata da scheduled dinsa na satin gaba daya,amna ta tabbatar dole zai buqaci breakfast din.

Kafin ta kammala har ma'u ta gyara su fauzan gaba dayansu,sai ta shiga wuce daki kawai ta gyara jikinta.

Kwalliya tayi sosai data dace da safiyar,ta wadata jikinta da sassanyan qamshin nan da tasan yana masifar so. Bata ma dauki su fauzan ba kai tsaye ta wuce zuwa samanshi.

Koda ta samu daman shiga parlor din bata wani ji motsinsa ba,don haka ta wuce zuwa master bedroom dinsa. Tun a nan ta fahimci tuni ya fita,don ga alamu nan sun nuna,comb dinsa da towel dinsa,da qaramin cup da yasha ruwan dumi duka saman mirror. Zama tayi gefan gadon tana maida numfashi,hakan yana nufin yayi fushi sosai da ita kenan?.

Wayarta ta bude ta soma kiran numbers dinsa,saidai kowacce gaya mata akeyi a kashe take,dole ta haqura da neman nasa ta sauko qasa saboda kukansu fawwaz da yayi mata maraaba.

Tana shayar da yaran amma duka hankalinta yana kan tunaninsa da tunanin abinda ya faru. Duk hankalinta a jagule yake gaba daya,ta dinga gwada kiran number dinsa amma bata shiga,tun tana sanya rai harta haqura ta daina neman nasa,sai gajeran saqo data tura masa,wanda shima har magariba tayi bata samu amsa ba.

Magariba ta wuce,isha'i ta shigo itama ta wuce,shuru ba shi ba wayarsa ba dalilinsa. A haka ta samu su fauzan dukkaninsu sukayi bacci,don dama idan sun jima sukai bayan ishai'i,idan kuma suka kwanta matuqar sun tashi to yunwa ko qishirwa ya tashesu,basa farkawa yawanci da safen ma,sai sukai bakwai da rabi har takwas suna bacci abinsu.

Baccinsu ya sake sakata ta dan qar samun nutsuwa. Wannan karon koda ta kirashi wayar yana shiga,amma haka ta qaraci b'urarinta ta katse bai amsa ba.

Dole ta ajiye komai gefe,ta qarfafa jikinta ta shiga wanka. Saidai duk wata laka ta jikinta an zare mata ita. Batajin sam sam zata iya ci gaba da karbar wannan hukuncin nasa,batasan haka ya iya hukuncin 'yar shariya me ciwo ba sai yanzu. Zaifi mata sauqi ya kulata,yayi mata fada ma,idan ta kama ma ya zaneta ko ya zageta zaifi sauqi.

To yau kam ma duk wani shirinta bata samu ganin shigowars gidan bama kwata kwata. Har sha daya na dare idanunta biyu,batasan kuka ta fara yi ba saida taji damshi saman fuskar fawwaz dake shan mama wanda ya tashi a sannan,daga qarshe ma tana tsaka da bawa fauzan mama bacci yayi gaba da ita,wanda a sannan sha biyu saura na dare.

Washegari taga alamun gidan ya kaana,saidai duk saurint na ta sameshi bata iskeshi ba. Wunin ranar gaba daya dauriyarta a ya qare,wuni tayi a daki ma'au nata cigiyarsu,don batason ta fito ma'u taga canji a fuskarta ta zargi wani abu.

Ranar ta rantse ba zatayi bacci ba sai taga shigowarsa,koda zata kwana ne a zaune,don haka koda goma na dare yayi ta tabbatar yaran sunyi bacci,goma da rabi ta sauya kayan bacci.

Lafiyayyun kayan barci ne masu wani irin sulbi da yauqi,wadanda ta siya a HUGUMA CLOSET da sukazo kai tsaye daga Dubai. Suna da wani irin bin jiki da daukan hankali,lingerie ne sosai na isassun mata.

Curling iron ta saka ta zauna ta yiwa gashinta wani irin nannadewa kaman macaroni,sannna ta tattarashi zuwa left side na kafadarta gaba dayanshi. Daga daya side din tadan tareshi da mabanbanta shapes na hair clips. Tattausan lips nata ta wadata da lips gloss daya qara masa kyau da sheqi,ta wadata kowanne part na jikinta da kalar turaren da musamman aka yishi saboda gurin,wannan turarrukan ta sansu da amfaninsu ne a wajen mummy sultana mummyn twins BATOUL DA BENAZEER(Gudun k'addara).

K'awace ta mummy safuura,ranar da suka isa abuja tazo mata a gaggauce da nata twins din din batoul da benazeer,wadanda aketa shirye shiryen bikinsu dukka su biyun,duk da bikin saura watanni shida,amma tsananin gata idan kaga yadda aketa shiri saika dauja gobe ne ko jibi.

Ita kanta ko yaya ta motsa qamshin jikinta burgeta yakeyi,ta tsaya gaban madubi taga yadda ta ajiye wani sassanyan kyau,ta gamsu da kanta da kanta,don haka saita tofe su fauzan da addu'a ta kuma wuce zuwa parlor na biyu.

Ba sabonta bane kallo,amma yau da kanta ta kunna Tv din,ta kuma kamo tashar tumbin giwa ind suke wani hausa series.

Rabi da rabin hankalinta yana kan wayarta,batasan adadin saqonnin data aike masa a kwanaki ukunnan ba,amma ko qwaya daya tal bata samu amsarsa ba. A baya ta shiga tsanani na rayuwa da barazana kala kala,amma bata taba jin tsananin da yakai mata wannan wahala ba. Bata taba jin nutsuwa da lafiyar zuciyarta tana mata barazana ba irin na wanann lokacin. A wannan lokacinne take tabbatar da ma'anar TASHIN HANKALI da kuma rashin sukuni da gasken gaske.

Ba fahimta take cancan ba,saita yanke kiran fannah kawai suyi hira.

A qalla sun kusa awa daya da fannah din,har sai da taji farouq ya iso kusa sosai,tana jinsa yana saka fannah din dariyar da bata shirya ba,dole ta yanke kiran. A gogo ta kalla,taji kewar nata mijin yana saukar mata,banda wannan matsalar data faru a tsakaninsu da tuni zuwa yanzun shima yana tare da ita,ta sauke idanunta tare da ajiyar zuciya zuwa saman Tv din,daidai sannan ya murxa handle din qofar parlor din ya shigo da sallama muryarsa can qasa,yanajin kowacce gaba ta jikinsa a mugun jigace.

Idanunsa da sukayi laushi qwarai su ya fara zube mata,tayi masa wani irin fitinannen kyau,ya sauke dubansa kan gashinta da yasa kwalliya da wani irin salo,salon da hatta yanayin zamanta saman kujera yau din na musamman ne.....

Cikin wani irin hanzari ya dauke kanshi daga dubanta sanda ta daga risunannun idanunta zuwa kanshi. Yadda ya dauke kan baima ko nuna ya ganta ba ya mata wani irin ciwo,duk da haka ta daure tace masa.

"Sannu da zuwa".

"Yauwa " Ya amsa still ba tare daya kalli sashenta yana takawa zuwa hallway din.

Idanunsa ya lumshe,yana jin wani abu yana harbawa zuwa kowanne sashe na jikinsa. Ta masa kyau iyaka,ta fusgi hankalinsa qwarai,saidai har yanzu yana jin tasirin fushinnan da yakeyi da ita. Ta dauka masa yara sun fita daga gidan daya killacesu ba tare da yasan adadin nisan da zatayi ba,ta dauka masa yara ba wasu cikakkun masu tsaronsu......uwa uba ta taba masa martabar igiyar aurensa......tayi nisan da bai kamata ace ta yishi ba tare da muharraminta ba.....ba kuma tare da izininshi ba.

Idan har ya sake mata haka da yawa gaba yana da guarantee din me zaya faru?. Iyali suke tarawa shida ita,fata yake kuma su gina iyalin da kowa zasu zame masa abun alfahari. Babban abun dake mintsinar zuciyarsa shine......tsoronsa daya karanta cikin idanunta tun wancan ranar,to meye yake mata a shimfidarsu da zai sanyata gudunsa har irin haka?.

Ya sani......duk duniya ita zata fadi wayeshi a wannan fannin.......tafi kowa alfahari dashi........wani irin yanayine da take ji dashi cikin rayuwar aurensu,amma dare daya saita nema sauya hali?.

Alqawari ne ya yiwa kansa tun first night nasu......bazai sake kasancewa da ita ba ta wani yanayi na daban har sai da shauqinta da cikakkiyar amincewarta,koda kuwa son kusancinsa da ita zai masa mene ne.......bare a yanzun da yake cikin fushi da ita.......banda wannan kallon daya mata na yanzu da yake shirin wargaza masa lissafin da baiyi niyyar wareshi a nan kusa ba.

Dakinta ya wuce kai tsaye,kaman yadda ya saba shiga ya gansu suna bacci batasan ma shigar tasa ba bare fitowarsa. Ya qarasa gaban gadon,ya riqe yatsun yaran idanunsa a kansu. Wani sanyi yaji zuciyarsa tana yi.......da gaske da ake cewa yara sanyin idaniyar iyayensu ne.

Yana iya jinta sanda ta tura qofar dakin ta shigo yana tsaka da musu addu'a,bai waiwayo ba,bai kuma tsaya da abinda yake ba har ya gama tofesu da addu'ar sannan ya juya a hankali da zummar fita a dakin.

Dab da zai isa bakin qofar tasha gabansa,ta shiga ta tsakanin hannayensa ta tsaya a tsakiyarsa tana lalubar qwayar idanunsa ta saka nata a ciki.

Narkakkun idanun nan nata da suke kasheshi......narkakkaun idanun nan nata da suke zare masa dukka wata laka tasa,su kuma kashe wutar fushi dake ruruwa a zuciyarsa,idanun da har yau wani haske da qyalli suke kasa kaman ranar farko daya fara ganinsu.

"Zan wuce a gajiye nake.....bacci nakeji". Ya fada da wata maqalalliyar murya daga can qasan maqoshinsa,muryar da takeso lallai saita tona asirin dake danqare a zuciyarsa da gangar jikinsa.

Qwalla sosai ta cika fararen idanunta,ta koma masa kaman wata yar shekara goma saboda yadda ta maqale.kafada.

"Zakaje ka kwanta kayi bacci ko?,sabreen ita kuma ta mutu?". Sai kawai ta fashe masa da kuka.

Cije labbansa yayi,yana jin yadda kukanta ke huda masa sassan jiki yanason kassarashi da kassara qarfin qwanjinsa dana zuciyarsa. Ya dake sasai yana fadin.

"Nifa ba kuka na tambaya ba,hanya nakeso a bani......zancan sabreen ta mutu kuma ai bai taso ba.....ki bani hanya please" Ya fada a dake yana basarwa,yana fata ta matsa ta bashi hanyar kafin ya qarasa karyewa daga hawayen dake fita a fuskarta.

_Wato dai da gaske kai ragon namiji ne indai akan sabreen ne?,zamu gani,zaka iya daurewa?😂😂_167



"Hamma" Ta sake kiransa muryarta a karye da sautin kuka.

"Am really sorry hamma......Allah bazan sake ba" Tun daga tsakiyar kansa har tafin qafarsa yaji kiran sunanshi da tayi,zuciyarsa tayi sanyi amma tana gaya masa ba yanzun ba......da sauran karatun.

"Naji na haqura.....matsa na wuce" Ya sake fadi yana kuma tsare gida. Fararen idanunta da suka dan surka kadan saboda kuka ta daga ta kalleshi,shima idanunsa suna kanta,amma koda ta kalleshin sai ya dauke kansa,saboda tsigar jikinsa ya da yaji gaba daya ta tashi.

"Hamma baka haqura ba....."

"Goyaki kikeso nayi?,shi zai tabbatar miki na haqura ko kuwa yaya?". Yadda yayi maganar da wani basarwa sai ya karya mata gwiwa,gaba daya sai taji kaman ya tozartata da yadda yake qoqarin tankwabe rarrashin da take masa.

"Bani hanya please" Ya sake fada yana kuma hade gira.

A hankali ta janye jikinta ta bashi waje,ya taka hankali kwance kaman wani abu be tsikareshi ba ya fice a dakin.

Sulalewa tayi a wajen,sai wani sabon kukan ya tsinke mata. Tsoro taji yana shigarta,tsoron kada ya zamana fu'ad ya fara juyawa daga muhammad din data sani......zuwan mazajen yau da mata ke complain a kansu. Idan haka ta kasance a kanta bata jin zatakai labari.....don ta ta'allaqa dukka burinta da fatanta a kansa,ta karkatar da akalar rayuwarta a kansa,ta saka buri me yawa kuma akan nasa.

Tas taci kukanta ta godewa Allah,sannan ta miqe tana qarfafawa kanta gwiwa. Ta shirya abincin duka cikin wani kwando na daban ta haura masa sama dashi. Ba kowa a parlor din,tafi sanya ran wanka ya shiga,don haka ta jera komai tsaf saman dining ta wuce bedroom dinsa.

Kai tsaye ta murza handle na toilet din ta shige abinta gaba gadi. Cikin Jacuzzi ta hangoshi,ya sakarwa kansa ruwa wanda yake wanka duk kumfar daya sabawa jikinsa. Idanunta ta Maida ga bathtub din data cika masa d ruwa da kuma sassanyan turaren wanka,ba alamar ya taba ruwan ma bare akai maganar yayi wanka dashi,saita hadiye abinda ya taso mata ta nufi jazucci din kai tsaye.

Zuge qofar tayi,ta taka a nutse tana shigewa ciki. Ya ganta sarai amma bai waiwaya ba,yaso ace sanda bai shiga azumin fushi da ita ba ta kawo kanta a irin wannan lokacin,lallai da ya samu ganima.

Yana jinta ta gama tsokane tsokanenta bai nuna yasan tana ciki ba,ya gama ya nannade jikinsa da towel ya fito. Tana tsaye a nan kamar wata hoto har yabar toilet din,ranta taji ya soma baci,to amma ya zatayi?,duk ita ta jawo,ta tabbatar fushinsa lallai ba abu bane me dadi,tunda ya gwada mata ta gani.

Ko data zuba masa abinci ma cewa yayi ya qoshi baya buqata,ta san halinsa koda yana buqatar abincin ma ba lallai yaci,zaice bazaici abinci bane late,don haka ta shiga kitchen ta hada masa fruit salad me kyau da nau'un fruit din da basu da matsala ga lafiya da dare,a cisu kuma a kwanta.

"Ajiye a nan xanci" Ya fada kawai yana duba wasu file. Ajiye masan tayi,ta kuma sauka qasa tayi shirin bacci.

Still cikin wasu red night gown ta shirya,ta saki gashinta kafadunta yanzun bayan ta tajeshi daga curling nashi da tayi a dazu.

Sanda take kawo yaran zuwa gadonsa dake gefan dakin,yana kwance cikin duvet a qudundune amma tun shigowar farko sassanyan qamshinta ya ruskeshi har inda yake din.

Wata wawiyar ajiyar zuciya ya sauke yana runtse idonsa,bai taba kawowa zai iya jure wadannan kwanakin ba.......bai taba zaton yana da haquri a kanta har haka ba sai yanxu.

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login