Showing 102001 words to 105000 words out of 557259 words
zama malamarta qarfi da yaji?.
"Kina mamaki ne mariya?" Ta tambayeta tana kallon hanya
"Ai duk wanda yayi bacci a wannan zamanin zaiga bacci.....ba yara na ba ba surukaina ba.....hatta da jikokina.....yara da manya dukka sai abinda hajja ta shimfida"........
Ji yayi tamkar an daka masa tsawa tsakiyar baccinsa ana kuma masa umarni da ya farka. A nutse ya farka saidai kuma yanajin wani irin sauti mara dadi yana amsa kuwwa cikin kunnuwansa tamkar dai a mafarki akayi masa tsawar. Idanunsa ya lumshe a hankali yana son tuna abinda ya faru din,amma kansa blank bai iya hasaso komai ba
"Hasbiyallahu la'ilaha illa huwhuw,alaihi tawakkaltu wa huwa rabbul arshil azeem" Ya furta a hankali bakinsa yana motsawa.
*D U N I Y A T A*
*_H U G U M A_*
PAGE 55
Tsam yayi da ransa yana jin yanayin jikinsa yana sauyawa daga ainihin yadda ya kwanta din a dazun. Numfashi ya aje a hankali ya yaye blanket din ya miqe,ya zauna sosai saman gadon. Duk da knocking din da akeyi din hakan bai hanashi hada hannuwansa guri guda yayi addua ba,ya shafa saman fuskarsa a nutse sannan ya zuro qafafunsa qasa ya miqe.
A nutse yake takowa zuwa ainihin falon nasa dake cike da nutsuwa,shuru tamkar ba cikin gidan yake ba,komai komai cikin matsananciyar tsafta a killace kamar yadd yakeso koda yaushe ya dinga ganin komai a hakan.
Yana ci gaba da jin jikinsa da wata 'yar maqalalliyar kasala har ya isa qofar falon,ya murza key ya bude qofar amma bai murza handle ba,ya barta a haka yana komawa da baya hadi da bada umarnin a shigo.
Tun bai zauna ba ta sako qafafunta falon,dauke da wani kyakkyawan kwando me qananun tayoyi,yana da mariqi tamkar na luggage ko trolley da zaka iya rageshi ko ka qarashi sannan ka jashi yadda kakeso.
Da sallama a bakinta da qanqanuwar nutsuwar nan da take samar da ita a gabansa.
"Wa'alaikumussalam" Ya amsa yana zama saman daya daga cikin qawatattun sofas din da suka yiwa falon qawanya masu tsananin taushi da kyau na gaske,yasa hannunsa yana lalubem remote na A.c din falon don ya rageta. Shi din ba kasafai ya fiya son ac ba ko ya qureta har haka ba,wannan din sai oga farouq,a nan ma zaka iya jin kansa dashi.
"Hamma barka da warhaka". Ta fada cikin shagwabarta da marairaitar nan tata data zama a halittarta. Labbansa ya motsa kadan da wani yanayi da yafi kama da murmushi
"Habibtyn hamma" Ya furta a nutse kaman yadda tsoron qarewar haruffan bakinsa. Sunan daya kiratan dashi ya sanyata ta sake rakwarkwabewa. Ta tabe fuska tana kallonsa
"....hamma na dauka ka daina yayi na......BB farouq yacemin ka samo wadda ta sace zuciyarka.....tunda ta sace zuciyarka wai kuma tayi snatching naka a wajen kowa....she owns you ita kadai". Qaramin murmushi ya sake subuce masa wanda yafi na baya. Rigimar amna yawa ne da ita,har yau bata girma baisan kuma sanda zata girma din ba,yafi tunanin aure ne kawai zai kawo mata wannan hankalin da girman. Gefe daya farouq,shikam a duniya yanaso yaga ya tubura amna din,wani lokacin yana yi ne kaman hankalinsu daya,abinda kuma bazai taba zama hakan ba
"Zo nan" Ya fada yana yafitota da hannu gami da nuna mata gefansa. Sai ta tako din a hankali ita da kwandon nata har ta iso gabansa ta zame ta zauna sosai
"Baki gaya masa tare zaku zabi mata da hamma ba?,baki gaya masa sai wadda kikace tayi kinaso sannan hamma ya aura ba?" Yayi mata tambayar yana kallon qwayoyin idanunta abinda ya qara mata karsashi da qwarin gwiwa. Murmushi ya subuce mata data tuna da wannan
"Na gaya masa hamma sai ya tabe baki,kasan me yace?" Kai ya girgiza yana qara girmama quruciyar amna din,tabbas auta ba wasa ba,ko yaya sai wannan quruciyar ta tabashi
"Wai ita soyayya ba ruwanta da jiran lokaci ko dacewa,sace zuciya takeyi ko an shirya ko ba'a shirya ba....." Ta qarasa maganar daidai sanda farouq din yayi knocking hadi da turo qofar yashigo gaba daya,don yaji muryarta alamun suna zaune daga falonne.
Tsaf kalaman nata da suka fito daga bakin farouq din duka zauna masa akai,sai ya daga kai yana dubansa sanda yake takowa falon. Ya bude baki zai fara mata tsiyan nashi fu'ad din ya tari numfashinsa
"Kai kakeso ka lalatamin kunnuwan qanwa?.....kai kake karanta mata yadda soyayya take ko?".
Wani dariya ya saki yana saka hannu ya dauki green apple guda daya cikin apple din dake ajiye cikin wani dan kwando nan saman fridge din dake kusa dashi yana takowa falon
"Har yanzu kallon jaririya kuke mata ba?.....zakusha mamaki sanda ta kawo wani tace itace shi takeso,aure takeso kuyi mata".
"Hamma....." Ta fada idanunta suna yin rau rau tana duban fu'ad. Hannu ya daga mata alamun tayi shuru kada tace komai,sai ya maida dubansa ga farouq din
"To sai me?,idan ta fada dinma ai daidai ne". Yana zama a gefansa yace
"Ni zanfi kowa murna da hakan ai......tashi ki bamu waje" Farouq din ya fada yana komawa serious dinsa. Duk sanda yayi irin hakan ta tabbatar Lokacin wasa ya fita kenan,don haka bata musa ba ta tsugunna tana rage plates da bowls din da tasan fu'ad ya gama amfani dasu saboda ta sanshi bai fiya son tarkace a waje ba,yanzun saisu sanyashi fasa cin abincin gaba daya.
Spoon ya dauka kawai ya saka a plate din fu'ad din bayan fitar amna,wannan din ba wata sabuwar dabi'a bace,kusan sun saba cin abinci kwano daya,tun daga wancan lokacin da suke fafutukar rayuwa da samarwa kawunansu 'yanci,har zuwa yanzun da suka zama cikakkun mutane kuma 'yantattun 'ya'ya.
A nutse suke cin abincin kuma ci gaba da tattaunawa akan tafiyar tasa. Har suka kammala basu tashi a gun ba,sai da kiran anni ya shigo masa waya.
"Ka shiga wajen maamah kuwa?" Tambayar data fara yi masa kenan
"Zan shiga dai anni....."
"Kome kake ka barshi,ka shiga ka gaidata tasan da dawowarka"
"In sha Allah anni" Ya fada a nutse,sai ta katse wayar shima ya sanya hannu yana sauka daga bangaren kiran gami da fidda siririyar iska daga hancinsa.
Miqewa farouq yayi abinda ya sanya fu'ad din daga kai daga zaune ya kalleshi. Kafin yakai ga tambayar shi ya rigashi magana
"Na jima ban shiga abuja ba,ina jin gobe ko jibi zan shiga din......."
"Safe journey" Fu'ad din ya fada a taqaice yana miqewa shima. Siririyar dariya farouq din ya saki yana tsare fu'ad din da ido wanda alamu ke nuna yana Neman hanyan wucewa ne daga wajen
"Kar muyi haka dakai.....karka canza kuma daga yadda na sanka......ko da da sau daya baka taba yimin kara ka rakani wajen fannah ba.....kayimin alqawari next time idan na tashi zuwa tare zamuje......."
"Yanzun daga daukomin dogon sharhin nan farouq.....cewa nayi bazani ba?.....kawai dai kasan ba abu bane me sauqi gajimare ya gama yawo dani na sake komawa wani tsakanin kwana daya ko biyu kawai......infact ma kasan yanzun shirye shiryen dake gabanmu ai.......ba cikakken lokacin batawa a irin wadannan abubuwan.....but duk da haka bazan karya alqawari ba.....if zaka iya jirana na kammala sai muje din". Dariya ce taso qwacewa farouq din amma ya maze,ya san dama zaa rina,kuma wannan dogon bayanin da yakeyi duka yana neman hanyar guduwa yaqi zuwa ne.
Bai taba ganin mutumin da soyayya bata taba burgeshi ko d'ad'ashi da qasa ba ko yaya takai ga bawa jama'a sha'awa ba irin fu'ad din. Bawai ya tsani mata bane......aah......amma yadda yake nesa qwarai da al'amuransu kai tsaye idan kace bai jituwa da shirginsu bakayi laifi ba.
"Kanka tsaye kacemin yanzun ma ba zakaje ba.....kacemin ka shirya nunawa fannah iyakata....ni din ba kowan kowa bane a wajenka" Ya fadi yana hade rai sosai idonsa akan fuskarsa. Kallon idanun farouq din yayi,bai wani damu ba yasan halin kayansa sarai,yasan ya fada ne don ya motsashi,don haka ya daga kafadunsa
"Ka fada soyayya ne at wrong time......har yanzun kana da sauran lokaci da ya kamata ace kana gina kanka ne bawai soyayya ba......ita soyayya idan lokacinta yayi zata kawo kanta da kanta"
"Kaiii.....inaaa......a wannan lokacin da mutum ke bacci da qyar?,am against you fa har abada indai ta nan wajen ne.....kaidai da waccan aljanar tayi maka shigar sauri zamu ci gaba da nema maka magani......" Bai qarasa ba yaji saukar spoon a kafadarsa,ya goce spoon din ya fadi qasan marbles,sai ya soma sauka daga dining area din yana dariya abinsa gami da cewa
"Tafiya abuja dole ce......zan siya ticket harda kai......alfarma daya zan maka zan daga zuwa next week cikin weekends din" Yana kaiwa nan ya fice abinsa daga parlor din.
Kai kawai ya girgiza yana murmushi qasan zuciyarsa. Bazaice ko sau daya ga sanda suka taba samun sabani da farouq ba ko wani ya bata ran dan uwansa. Wani hadi ne daga buwayi gagara misali,idan kaga musaddiq da Sadiq zakayi tunanin sune uwayensu daya,kaman yadda da yawa ake tunanin shi da farouq din twins brothers ne da suke da kamanni daban daban.
Baiyi mamakin jin ba ruwan zafi a toilet kaman yadda ya saba samu koda yaushe ba,don dukka ma'aikatansa da sauran masu masa hidiman sassansa ya basu hutu na satittikan tafiyarsa south Korea,don haka ya kunna heater ya dawo cikin bedroom din sannan ya wuce kai tsaye yana fita daga ciki.
Qofa ce qwaya daya tak wadda batakai duka sauran doors din falon fadi ba,ya budeta ta hanyar key din dake maqale a jiki ya turata a hankali ya shiga.
Dakin yana da dan duhu don haka ya laluba makunni ya kunna fitila take haske ya gauraye dakin
*D U N I Y A T A*
*_H U G U M A_*
PAGE 56
A yadda qofar dakin take daga waje,ba zakayi tsammanin taras da yalwataccen daki me wani irin tsari da kyau ba kaman haka. Ci gaba yayi da kunna kowacce fitila ta cikin dakin,kama daga ta bango zuwa kyawawan table lamps masu wani irin kyau me daukan hankali. Wani irin guri aka tsaga daga sashen nasa da yayi Linkin da ainihin farfajiyar gidan bangaren da duk yawan taro ko hayaniyar jama'a da gidan zaya tara zaiyi wuya ka iya jinta muddin kana wajen. An qawatashi da wasu irin shelves da drawers masu mugun kyau da daukan hankali da aka tsara takardu documents zuwa litattafai nau'i daban daban daga yarukan duniya daban daban da yake iya fahimta yake kuma iya magana da wasunsu.
Ragowar bangunan kuma manyan frames ne masu asalin kyau da tsada na qasar turkey da dubai da aka kashewa kudade masu ciwo aka tsara sunayen Allah da ayoyin qur'ani masu girma da wani irin ruwan gold daya sake baiwa frame din kima kyau da daraja. Akwai kyakkyawan table din daya zama cikon ado wa home office din nashi da yake hade da kujerarsa,sai kuma wasu cushions da aka zuba gajajjeru da ba zasu bata tsarin wajen ba,daura dasu kadan kuma wani board ne dake dauke da rubuce rubuce barkatai da baya rasa alaqa da tsare tsare na abubuwan da ya sanya a gaba zaiyi.
Komai na room din neutral color ne kaman yadda dayan bedroom dinshi yake,abinda zai bayyana maka kenan normally bayason kaloli masu hayaniya can can can.
Da gaske a yanzun target dinsa shine bude kamfanin......babban burin da a yanzun bashi da wani sauran abu daya rage masa kamar shi,saidai abune daya tabbatar yana buqatar qarin jajircewarsa da kuma aiwatar da komai cikin sirri har sai an kai gabar da ya kamata komai din ya bayyana.
Ba alaman qura ko datti ko qwalli daya,don duk wanda ke aiki dashi yasan tsarinsa da kuma dokarsa. Waje ne da ba wanda yake bari ya shigar masa sai family dinsa,anni farouq amna saddiq sai musaddiq......sai kuma amintaccensa mutum guda daya me sunan malam.
Ya bude lockers da yawa,ya kuma jona abubuwa da yawa kafin ya daidaita komai ya juya yana fita a dakin da zummar zuwa sanda zai dawo komai ya zama normal,don yau din aiki yakeson yi sosai kafin ranar Monday ya isa kamfani ya duba yadda ya barsu.
Fes ya fito a shirye,sanye da lallausan yadin filtex fari qal mai qarancin nauyin da har kana iya hangen farar vest din jikinsa data lafe takuma saje da yadin sosai saboda tsananin haskenta. Sassanyan qamshin nan nasa dake da daukan hankali yake fitarwa sannu a hankali,fuskarsa tayi fresh cikin yanayin da zai nuna maka cikakkiyar nutsuwar zuciya da ruhi da yake da ita. Sabanin wasu lokutan,yanzun kanshi saye yake da hular data dace da yadin jikin nasa,sai half covers din daya sakaye doguwan qafansa a ciki.
Komai rashin nisan waje bazai taba iya taka qafarsa ba tare da ya sanar da anni ba,yanzunma sassanta ya bulla,yana tafe yana amsa waya har ya cimma sassan nata.
Bai iya ci gaba da amsa wayar ba sanda qafafunsa suka shiga ainihin falon,sai ya zare wayar daga kunnensa sakamakon sautin karatun qur'ani dake fita daga speakers din dake daura da qatuwar plasma din dake girke saman mulmulallen tv stand din.
Karatu ne cikin muryar babban malaminsa sheik abdurrahman assudais,qira'ar dake balain kashe masa jiki tare da saukar masa da nutsuwa koda yana cikin bacin rai. Falon anni na dabanne,badai ka shigo ka samu ana kallace kallace marasa ma'ana ba bare akai ga batun jin kida ko waqa,kusan duka haka ta azasu akai,suma kuma haka suka taso.
Lokaci irin wannan magariba ke kan hanyar qarasowa,zaka sameta zaune cikin kamala tana wani abun da zaya amfani lahirarta,imma girkin abba ita da amna,ko ka sameta da carbi,ko tana sauraren wani karatun addinin.
Yanzunma suna tare da amna din,wanda daga gefan amnan kadan wata baquwar matashiyar ce da zata girmewa amna din da aqalla shekaru biyu ko uku.
Yana shigowa ta sanya remote tayi qasa da karatun sosai tana murmushi. Ya qaraso a nutse ya zauna daga gefanta yana tanqwashe qafafunsa tamkar ba wanda yayi shirin fita ba,sai kuwa ta tareshi
"A'ah miqe....ai sai ayi magariba kana zaune a nan.....kaje ka dawo.....don abincin dare ma yau banda kai a gidan nan" Girarsa duka biyun ya daga alamun mamaki,yanayin daya qarawa fuskarsa wani irin kyau,ya kuma fusgi hankalin matashiyar qwarai da gaske
"Anni yau din nayi wani laifi ne....?" Ya fada calmly idonsa akan annin. Kai ta girgiza
"Ko kadan......kawai nasan idan kayi dinner a daya gidan naku hakan zai farantawa maamah sosai,zai kuma sake bada fahimtar juna da shaquwa a tsakaninku". Tayi maganar cikin kwantar dakai itama tare da fatan kaishi zuwa ga abinda takeso din.
Kansa yadan motsa kadan,har yanxu anni kaman bata fahimci daga ina ainihin tushen matsalarsu ya fara ba?,har yanzu kuma kamar annin bata fahimci menene yake riqe da matsalar tare da sake wanzar da ita ba?,wanne fahimtar juna da shaquwa a yanzun ake nema tsakaninsu ne?.
"Saika dawo......kace ina gaidata" Ta fada tana daukan remote zata qara volume,abinda ke alamta masa ta gama fadin bayaninta kuma batason yayi sharhin komai akai
"Hamma....." Amna ta kirayi sunansa tana murmushi idonta a kansa.
"Lovy dovy" Ya fada yana xuba hannunsa a aljihun rigarsa yana jin karsashinsa da duk wani walwalarsa yana ja baya tamkar wanda aka tura gidan kaso.
Murmushi tayi,tsokanarsa takeso tayi amma kwarjinin nan nasa ya taso ya danneta
"In fada hamma?" Tayi masa tambayar tana dubansa
"Say it amna....." Ya maida mata cikin caring din daya kusa sanya matashiyar narkewa. Bata taba zato koda a mafarki yana da wannan siffar ta kulawa haka ba......bata taba hasashen akwai dabi'a ta sauqin kai a tattare dashi har haka ba
"Muhammadu.......yi tafiyarka......ku wuce ciki keda unaisa ku wankemin bottles dinnan,suna kitchen basu da yawa".
Duk da yaso ya wuce din kamar yadda anni tace amma dole sai daya dan tsaya a farfajiyar gidan suka gaisa da ma'aikatan gidan,sannan kuma me sunan malam yayi masa tattaki suka fice daga gidan bayan ya shaidawa security dinsa ba nisa zaiyi ba baya buqatarsu.
Yana takawa a nutse yana sake fuskantar gidan wani yanayi yana riskarsa,abubuwa masu tarin yawa da suka saba dawo masa a duk lokacin da zai gifta ko ya shiga gidan.....al'amura masu nauyin dake iya motsa zukata qwarai da gaske. Wannan