Showing 177001 words to 180000 words out of 557259 words

Chapter 60 - πƒπ”ππˆπ˜ATA BOOK1 AND 2 HAUSA NOVEL

HUGUMA   

03 Nov 2025

494

kawun

"Haba rufa'i......Sabrina fa 'yarka ce halak malak...."

"Na sani rabi'u.....na sani,Kai dai kawai ka barni......na fika sanin wacece ita,wallahi duk taqadirancina ta dameni ta shanye yarinyar nan......yadda kasan me gani har hanji akan maza.....tana iya zuqe tattalin arizqin kowanne d'a namiji idan taso tana zaune daga gida.......ka bani shawara rabi'u,yau daya sai nakejin ina shakkar tunkararta". Shuru rabi'u yayi na wani dan lokaci sannan ya gyara zamansa

"To a zahirin gaskiya dai aurar da Sabrina ba wani abu bane mummuna,asalima yin hakan tamkar taimako ne ka baiwa rayuwarta.....kuma a addinance kai din uba ne a wajenta da zai iya zaba mata mijin aure,to abinda nake ganin yafi kawai ka tunkareta da zancan.....sannan kabi dukkan hanyoyi na hikima ka kwatanta mata aure shine babban rufin asirin mace".

Shuru kawu rufa'i yayi tamkar me shakka ko kokwanto akan shawarar rabi'u.

"Har yanzu rabi'u bakasan yarinyar nan ba,kafaffiya ce me shegen taurin kai da rashin tsoro,idan ta kafe akan abu babu wanda ya isa ya tanqwarata,bata tsoro shakka ko kuma shayi.....ba irin Sabrina bane ake zuwa musu da magana haka kai tsaye a hada da wa'azi da shawara ba kuma su dauka.......Sabrina rinduna ce da sai an fuskanceta da gayyar jama'a....amma dai kafin sannan zan gwada wannan din rabi'u "

"Zata aminta in sha Allah,kuma komai zaizo da sauqi"

"To Allah yasa" Kawu rufa'i ya furta ajiyar zuciya tana subuce masa. Shi kadai yasan kalar tashin hankalin da yake ciki,yayi nadamar sanin duk wani dan caca tun daga haihuwarsa kawo yau bare kuma har ta zame masa sana'a.

*****Shi daya ne tal tsaye cikin kitchen din,sanye da fararen tanks top da joggers masu taushi. Kunnensa daya yana maqale da earpiece yana amsa waya. Daga gefe guda kuma yana tsaye ne gaban wani qaramin cabinet yana ciro ganyen zaitun,ginseng wolfberry da zai dafa tea dinsa na musamman dasu,sannna ya jawo wai qaramin plate din daban ya zuba dabino teen da busashen inibi da ake kawo masa shi tun daga china bayan anyi packaging nasa a wata jar leda mai kauri.

Hankalinsa yayi nisa sosai wajen amsa wayar da dafa tea din,har baiji shigowar farouq ba,wanda ta qaraso dab dashi ya kumayi tsalle ya haye saman kitchen cabinet din kusa da plate din da fuad din ya zuba friut din,ya soma miqa hannu yana tsinta daya bayan daya yana jefawa a bakinsa gami da cilla qafafunsa yana duba wayarsa rabi da rabi,yayin da kuma lokaci bayan lokaci yakai kai dubansa ga fuad din.

Daidai sanda ya gama amsa wayar tea din nasa ya gama dahuwa,ya jawo kebantacciyar ma'ajiyar kyawawan kofunan shan shayi na tangaran.

"Nayi zaton baka shigo ba ai". Fuad dake zuba musu tea din ya furta ba tare daya kalli farouq ba.

"Na shigo tun dazu......na tsaya duba wasu baqi ne da abba yace na sauraresu don yayi nisa". Kai kawai ya jinjina,yayin da farouq ya maida dubansa kan cups din da fuad ke zuba tea din

"Amma dai bani ka zubawa ba ko?" Ya fada yana dan yamutsa fuska. Sai a sannan ya daga kai ya kalli farouq din.

"Ba dole bane sai ka sha......" Yayi maganar shima yana hayewa saman kitchen cabinet din tare dakai cup din bakinsa a nutse hankali kwance yana sipping.

Sosai farouq yake kallonsa kafin murmushi da yafi kama da dariya ya subuce masa

"Ina mamaki idan na ganka a kitchen......zai zamewa 'yan jarida babban labari idan sukasan muhammad jadda dinnan yana shiga kitchen da kanshi time to time"

"It's my hubby.........inason dafa tea dinnan da kaina.......na tabbatar bakasan amfanin wadannan ganyayyakin a jikinka ba da bazakayi wasa dasu ba". Yakai qarshen maganar yana sake maida cup din bakinsa.

"Inaso na koya......but bakina yanason dadi.....harshena ba irin naka bane" Yayi maganar yana nuna damuwa akan fuskarsa. Sake cire cup din yayi yana balla masa harara

"Ka zauna dadi ya kasheka......you know baka fini son girki me dadi ba......but lafiyanka a matsayinka na d'a namiji sama take da komai.....wait.....wai meyasa ma zan zauna inatayi maka wannan bayanin,do what you want,amma sanda kayi aure kada ka nemeni da shawaran komai". Murmushi ya sake kubcewa farouq,yana so yana kuma farinciki yaga ya sanya muhammad magana har haka,wannan dalilin ne ya sanya baya gajiya da tsokananshi,duk da ba kasafai yake biye masa ba.

"Kaine na hannun daman ango.....so that kai ya kamata na fara nema kuwa......"

"Baka da wani abu me muhimmanci ne da zaka fada?" Fuad din ya fadi yana kafe farouq da idanu. Dariya sosai farouq ya saki harda sunkuyawa kadan

"Da alama aljanar amaryarka ta iso,taji batun aure....."

"Farouq" Fuad yadan kirashi da husky voice dinsa.

"Times up" Farouq ya furta yana daga hannayensa sama

"I have something to talk about.......very serious" Farouq din ya fada yana gyaran murya kadan sannan ya maida fuskarsa serious,abinda ya sanya fuad shima ya bashi hankalinsa ganin ya koma umarul farouq dinsa na asali.

"Tun jiyan zuwa yau nake zuba ido da kunnen ka nemeni ko kayimin qarin bayani...."

"Akan me?" Fuad din ya tari numfashinsa.

"Akan yarinyar daka nema aurenta ta hannun kawunta a office dinka......kwata kwata ban fahimci meye shirinka ba......in fact ma duk wanda ya sanka dole abun ya sanyashi mamaki......how and when ka fara sassautawa ra'ayin riqau akan aure?,when kasan yarinyar har soyayyar da za'a iya aure ta shiga?,.....anya auren tsakani da Allah zakayi kuwa dude?"

Sassauta zamansa fuad din yakeyi,baisan murmushi ya subuce saman kyakkyawar fuskarsa ba. Murmushin da ya sanya farouq ya sanya masa qatuwar ayar tambaya ya sabbaba masa kafe fuad din sosai da ido.

Bayaso fu'ad din yaje ya aikata wani kuskure,yanason koma meye su bishi a sannu

"Banda kai dan rainin hankali ne dama ana auren wasa ne?.....da gaske aurena zaa daura mata,aure zan nema kaman yadda kuka nema kuke kuma neman naku....already ma gayawa wancan tsohon nata...two weeks ma nace masa badon ina nufin nan da 2weeks din nake buqata ba,zan daura mata igiyata kaman kowanne mutum......but....." Ya katse maganar yana durgowa daga saman cabinet din,sannan ya fara takawa zuwa bakin sink din kitchen din ya kunna tap yana wanke cup din. A mugun qagauce farouq yake kallonsa yana son jin qarshen labarin,ya sani tsaf zai iya qin qarasa masa ya barshi da guntuwar magana a ciki

"But what fu'ad......tell me mana?" Farouq ya furta cikin damuwa,danuwar data taba zuciyar fu'ad din har ya waiwayoshi bayan ya gama wanke cup din.

"I want her to lern the hard way.......she made a mistake data zabi taba kudin jadda company"



𝗗 𝗨 𝗑 π—œ 𝗬 𝗔 𝗧 𝗔

𝙃 𝙐 𝙂 𝙐 π™ˆ 𝘼

π™‹π˜Όπ™‚π™€ 96


Yayi maganar yana zube idanunsa akan farouq da mamaki ya fara saukar masa

"To learn what?fu'ad?......sai ka aureta ne sannan zata koya darasin rayuwa?". Wani dan qaramin murmushi ya saki,ya miqe tsaye sosai yana goye hannayensa har yanzu idanunsa akan farouq din

" Ba wata hanya me sauqi da zan sanyata ta barwa sauran mata masu irinta darasi sai ta wannan hanyar.....dole ta fuskanci hukunci.....dole ta gane yadda ta dauki kanta batakai can ba......dole ta karbi sakamakon mutanen data dinga sanyawa a masifa saboda rabasu da dukiyarsu data dinga yi ba dalili.....inason ta san meye rayuwa......tasan kokai waye kana da iya limit dinka a rayuwa.......abdus salam na tura mata amma tayi avoiding nasa........kaga inda tayi accepting dinsa da hukuncin zaizo da sauqi" Yakai qarshen zan can yana sakin hannayen nasa gami da juyawa yana nufar inda ya ajiye wayarsa.

"Let her fu'ad......"

"Am sorry bro....Definitely sai na nuna mata kuskurenta......na dauki wannan alwashin" Ya sake fada yana bude wayarsa.

Shuru farouq din yayi yana wani gajeran tunani.....yafi kowa sanin waye fu'ad.....yafi kowa sanin halin tsaiwarsa da kafiyarsa akan komai ma.....idan yace zaiyi ba gudu ba ja da baya

"Amma ta yaya zaka tunkari su abba da wannan maganar?".

" Kaman yadda kowanne me neman aure yake sanar da iyayensa mana......akwai wani abu sabo ne a ciki?" Yayi zancan kanshi tsaye hankalinsa kuma kwance ba wani haufi.

Duk da yasan waye fu'ad amma wannan karon mamaki yake sake bashi,yayi tsai da ranshi yana kallonsa kamar yadda shima shi yake kallo.

"Da wani abu?" Fu'ad ya furta yana dage dukka girarsa biyun. Kai farouq kawai ya girgiza,yama rasa me zaiyi?,murmushi ko takaici?.

"Idan naji wani abu daban daga wajen anni ko abba tabbas kaine" Fu'ad ya fadi ba tare daya kalli farouq ba daya sauko daga saman cabinet din shima.

Harara ya watsawa fu'ad din kaman zai idanunsa zaso fado

"Saika hanani fada din" Daga haka ya soma tattaki zai fice daga kitchen din

"Karka damu,koda ka fada din ai ba wani abun bane.....zan koya mata tarbiyya ne na kuma koya mata wadatar zuci da kame kai daga dukiyar al'umma......kaga ko ba komai zan samu ladanta ko?"

"Kai ka sani" Farouq ya fada yana qarasa fita a kitchen din,yanayin yadda yayi magana kuma ya sanya fu'ad sakin wani lallausan murmushi.

*****Tamkar tsakanin hajja da maamah din babu wani me sauran abun fada sanda driver ke wulwula saura dasu cikin baqar range Rover din mallakin maamah.

Ba wanda yace komai din har zuwa sanda maamah ta gaji da shurun ta gyara zamanta.

"Amma hajja abun yazomin a bazata,ya kuma dauren kai matuqa". Juyawa gefanta hajja tayi tana duban maamah data tsinke mata zaren nata lissafin da take hadawa tare da qoqarin ganin amsar lissafin ya fito daidai.

" A yadda bayaninta ya nuna......zata iya aikata komai muddin akan kudi ne.....hakanan kudin sune abu mafi daraja cikin idanunta......ya akayi ta wofantar da buqatarmu ta watsa mana qasa a ido?......duk da cewa ido ba mudu ba ai yasan kima.....duk wanda ya kallemu zai shaida irin daula da ni'imar da muke ciki". Wata ajiyar zuciya hajjan ta saki itama,ta zubawa waje daya idanu kafin tace

"Ni kaina abun ya dauren kai,kuma iyakar tunani na bamu shiga mata da wani abu da ba daidai ba" Tayi maganar cikin 'yar damuwa. A wannan gabar ita kanta nasara take buqatar a samu.....nasara takeso tazo musu......yarinyar zata zame mata tamkar wani tsani me tsananin sauqin da zai ciccibata ya zuwa matakin tata nasarar.

"Ba wani abun damuwa bane ba hajja......ita iya nata hasashen ta dojewa buqatarmu.....kina tunanin zan barta?" Ta jefawa hajja tambayar.

Duk yadda hajja ta saka idanunta cikin na maamah din don hango plan dinta akan yarinyar ta gaza ganowa,don haka ta dora da tambayar

"Wanne mataki kenan zaki dauka?".

"Matakin da shine mafi dacewa da ita,ki zuba idanu kawai ki jira cikar kwanaki ukun dana bata.....da kanta zata budi baki tace ta amince" Ta furta sanda motar ke tsayawa a farfajiyar gidanta,don haka ta saka hannu da kanta ta bude murfin tana fita hajja ta mara mata baya zuciyarta cike da wasiwasi.

Sun samu zuwaira ta kammala komai,ta cika table da kalolin abinci iri iri na alfarma,wanda duka cikin izzar maamah dince. Ba'a abinci kala daya a gidan,bata yarda wannan ba,daga breakfast lunch har zuwa dinner ana mata varieties of food ne taci wanda ranta ke ra'ayi tabar sauran.

Daki na musamman da aka kebe ta sanya aka shigar da hajja don ta huce gajiya kafin itama ta watsa ruwa ta sauya wasu kayan ta fito. Kamanninta da musaddiq suna fitowa sosai sanda take fitowa daga dakinta sanye da wata bubu gown me tsananin laushi.

"Yau nake sake ganin kamanninki da musaddiq fa...." Hajja ta fada tana murza awarwaro hannunta.

Murmushi kadan ta saki tana jan daya daga cikin Kujerun dining din ta hau ta zauna

"Tun duniya na kwance akance kamannina da musaddiq yafi yawa......shi wancan babanshi ya dauko.....ni kuwa ba?" Maamah ta hade zancan duka tana qoqarin daukan cup da zuwaira ta fara zuba musu lemo

"Uhmmm" Hajja ta fada tana kallon maamah,can qasan ranta tana jin wani abu.....tana kwatanta irin izza gadara da mulkin da maamah din zata zuba a duk sanda haqarta ya cimma ruwa
"Waya sani ma ko ta rufe idanu ta manta dake ta canza qawaye?" Wani sashe na zuciyarta ya jefo mata wannan tunanin.

"Ni kuma bari zanyi hakan ta faru?" Ta bawa kanta da kanta amsa

"Kinsan wani tunani da nayi" Maamah ta sake fada tana juya cokalin cikin abincin bayan barin zuwaira waje. Zuwairan da a yanzu tsananin kishi da tsanar hajja ke ruruwa qasan ranta,ganin farat daya hajjan ta rushe gwamnatinta,gwamantin da da ita aka fara fafutuka aka kuma dasa harsashin gininta.

"Zanyi magana da fu'ad a yau ko gobe.....zan sanar masa ya fara shirin aurensa nan kusa". Kallo hajja ta bita dashi

"Da wuri haka?,har yanzu bamu samu tabbacin amincewar yarinyar ba". Wani murmushi maamah ta saki tana saka lomar abinci na farko a bakinta.

"Sabrin qaramar alhaki ce a wajena.....bata isa ta tsallakewa tarko na ba......amincewar fu'ad tafi zama abu me wahala a gareni akan amincewar sabreen.....na rantse miki da Allah.....muna nan zaune dake zata kira da kanta ta furta ta amince". Maganganun maamah din a yanzu daure kan hajja sukeyi. A kafe yarinyar take,ba wata alama ta amincewa a tattare da ita har suka baro gidan,to wanne abune haka zai sakata sauya ra'ayi da gaggawa?.

"Indai kina da wannan tabbacin to tabbas tsarinki yayi". Hajja ta bata qwarin gwiwa,daga wannan kuma sai suka zarce da wata hirar ta daban.

******A hankali suke takowa ta tsakanin kyawawan shuke shuken da aka qawata kusan kowanne sashe na gidan. Baqin wando ne a jikinsa wanda bai qarasa idon sawunsa ba da kadan,sai shirt itama baqa me gajeran hannu,hakan ya bayyana murdadden damtsensa,kalar rigar kuma daya kasance baqa ta haska farara lafiyayyar fatarsa dake sulbi tamkar ta mace. Kadan kadan iska ke wasa da sumarsa daga hagu zuwa dama,wani lokaci yasa hannu yadan shafeta kadan. Ko daga ina kake muddin a daura dasu kake to tabbas hancinka zai iya dauko maka lallausan qamshinsa daya zauna sosai a jikinsa,ya kuma kama komai da yake mu'amala dashi,kama da wayarsa keys dinsa briefcase da sauransu.

Shi da farouq ne bayan fitowarsu daga ainihin parlor din abba wato alhaji hamza kibiya. Karo na farko kaf tsahon rayuwarsa daya gabatar da wata d'iya mace a matsayin macen da yakeso ya aura. Har a sanda suke takawa yanayin anni ya kasa barin idanunsa,can qasan zuciyarsa sai yakeji anya ya kyautawa wadannan dattawan guda biyu da suka karbi lamarin auren hannu bibbiyu da zallar farinciki?.

"Alhamdulillah.....alhamdulillah,Allah na gode maka daka gwadamin wannan ranar da raina da lafiyata.....wacce me sa'ar ce?,a ina take?,ya kuma sunanta?" Anni da qananun hawaye suma maqalewa ta fada tana kallonsa.

Sunkuyar da kansa yayi,sam bai dauka lamarin aurensa ya zaune musu a rai ba har haka saida wannan maganar ta taso,ko da wasa bai taba qiyasta zasuyi farinciki har haka da zancan aurensa ba,tunda duk sanda farouq ya sanyashi a gaba game da lamarin auren cewa anni take

"Ka shiga hankalinka fa......matar mutum kabarinsa.....komai komai nada nasa lokacin.....kar ka sake kiransa mijin aljana......yarona yana da ibadar da ba wata halitta data isa ta cutatar min dashi".

"Sunanta sabreen......kuma marainiya ce" Abinda yaji kawai farouq ya fada kenan. Kallon gefan ido ya yiwa farouq din,a nasa zaton zai tona asirin plan dinsa......sai baiyi hakan ba......amma ya jishi kuma yana isar da wani zance da baisan sanda suka yishi da farouq din ba.

"Dukkaninmu ya fimu iya shiri anni......yanason aje nema masa auren,kuma sati uku kawai yake buqata". Shuru suka danyi dukansu,don abun yazo musu a bazata. Sun dauka zaya jera ne tare da 'yan uwansa ayi komai lokaci guda?.

"Anni......komai na gininku ya kammala......da bude company da tarewarku duka duka sati biyu ne ya rage......ayimin afuwa idan abun yazo muku a gaggauce......inason ku zama wakilai akan komai kafin mubar nan din". Yayi maganar cikin sunkuyar da kai tare da mamakin me yasa farouq yin hakan?. Bazai iya qaryata farouq din ba ko yace ba haka bane a gabansu annin,dole ta sanya ya dora da nasa bayanin. Baida wani plan na a daura auren sam a yanzu,yanason ya fara sanya mata shamaki ne ta hanyar maidata property dinsa. Shiga ko fita saida izininsa,hakanan yana buqatar kowanne motsi nata ya kasance qarqashin umarninsa,matakin quntatawa na farko kenan da yakeso ya fara aiwatar mata wanda zai sanyata jin ta qasqanta,kuma ita din batakai inda take tsammanin ta kai ba.

Murmushi abba ya saki yana cewa

"Banda abinka ko a yau iyayenta suka baka ita ai bai haramta a daura muku aure da ita ba......zan samu mamanka a sanar mata ko akwai wanda zai zama nata wakilin wajen zuwa neman auren......zanyi magana da bangaren mahaifinka suma,in sha Allah bazai wuce wadannan satikan ba".

Har suka isa sashensa baice da farouq ci kanka ba,sai da suka isa falon. Qarasawa yayi gaban freezer a nutse ya bude,ya ciro ruwa me sanyi abinda yadan jima baisha ba,yau dole zaisha din saboda yadda tsarin farouq yazo masa a bazata,ya kuma busar masa da maqoshinsa.

Sai daya gama sha ya dire robar saman dining,ya kuma fara saukowa daga steps din dining din cikin tafiyar nan tasa me cike da ginshira.

Ba zato ba tsammani farouq yaji saukar waya sama cinyoyinsa,sannan fu'ad din ya tako gabansa ya tsaya hannunsa zube a aljihun wandonsa.

"Tunda kai ka tsara komai ai sai ka qarasa aikinka......ka kirayi wancan tsohon ka gaya masa yadda ka tsara din,don

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login