Showing 69001 words to 72000 words out of 557259 words

Chapter 24 - πƒπ”ππˆπ˜ATA BOOK1 AND 2 HAUSA NOVEL

HUGUMA   

03 Nov 2025

534

za'a shiga wannan cacar.....yo ta ina zamuyi wasa?,bayan kai da kanka ka tabbatar min mutumin nan attajiri ne......ai ina maka rantsuwa da Allah baka bina bashin rantsuwa wannan karon arziqi ne yake kiranmu....inata buga buga naga na samu adadin abinda akeso a shiga cacar dasu....kada ka damu,zuwa nan da dare in sha Allahu zaka jini,yauwa na gode" Ya fada yana sauke wayar,ya soma laluben aljihunsa don maidata ciki yana sake magana a fili.

"Idan ma Allah ya taimakeni na haye da wadannan kudaden ina zaki sake jina?,ai nima na zama attajirin kaina don ubanki" Sai yaja qwafa sannan tsaki ya biyo baya,ya juya yana sauya hanya.


*D U N I Y A T A*

*_H U G U M A_*

PAGE 38


Sau biyu yana sake juyawa yana kallonta. Tun bayan sallamar da tayi yayin shigowa motar bata sake cewa wani abu ba.

A nutse take da dukkan nutsuwarta,nutsuwar data sake janye ra'ayinsa a kanta matuqa.

"Erhmmm" Ya danyi gyaran murya kafin ya dora da

"Na gode qwarai da baki wofantar da magiyata ba.....hakan ya nunamin kinsan darajar dan adam....." Maganarsa ta sanyata dawowa tunaninta tare da tunasar da ita a inda take. Batace masa komai ba,tadan dai motsa kadan alamun tana saurarensa,hakan ya bashi damar ci gaba da magana.

"Da farko dai sunana alhassan.....ko zan iya sanin sunan malamar?" Sunan daya kira kanshi dashi ya sanyata juyawa kadan ta kalleshi sannan ta maida dubanta ga kwaltar da suke bisa kanta. Kaman ba zatace komai ba sai kuma ta motsa bakinta

"Sunana....." Sai tayi hanzarin dakatawa. Shima kaman sauran?,yana buqatar a bashi stamp?,yana buqatar personal suna nashi tamkar dai sauran 'yan uwansa jinsinsa?. Eh yana buqata,saidai shi din bata jin zatayi wani doguwar mu'amala dashi da har zai buqatu ya zuwa stamp na musamman

"Da alama sunan nan me tsada ne ko?,sai na siyeshi?" Ya fadi yana dan satar kallonta kadan fuskarsa dauke da murmushi. Kai ta girgiza a hankali

"Sunana sawwama"

"Nice and good name.....me azumi kenan?" Ya fadi yana dubanta kadan. Kafada ta daga,koma meye ma'anar sunan bai zame mata damuwa ba,kawaidai ta bashi sunan ne don shine sunan da yazo kanta.

"Ma sha Allah......gashi mun iso inda kika cemin,kuma ina da tarin abubuwan fadi don inason alaqar tamu tayi nisa,tafi haka zurfi,za'a bani wani abu kaman number waya ko adress nazo na sameki?"

"Wayata bata da guarantee adress kuma bani da" Ta bashi amsa ta kai tsaye daidai sanda yake tsaida motor din a inda ta nuna masa.

"Waya ba guarantee adress aishi zai zama babban guarantee ko?....me yasa kikace baki da adress?"

"Saboda bamu da gida" Ta sake bashi amsa kai tsaye sanda take dubansa da fararen idanunta masu sheqi da hasken rana ya qara musu qyalli,abinda ya sake daukan hankalinsa kenan. Murmushi ya saki yana jin tana sake burgeshi

"Alright.....nasan dai ba dan adam din dake rayuwa a titi.....amma bazan takurawa zabinki ba......zaki iya bani dama ta uku?,damar yin magana dake a nan?" Numfashi ta sauke a hankali tana jin ya takurata da yawa,ta daga hannunta dake daure da agogo ta kalla sannan ta sauke tana juya idonta daya sashen alamun qosawa

"Mintuna biyar kawai"

"Na gode" Ya fada yana gyara zamansa sosai.

"Bari na tafi kai tsaye kada na cinye mintunana ko?" Ya furta yana sake sakin murmushi. Batace masa komai ba still,saidai ta kafe idanunta ne saman qofar gidan dake gabansu kadan. Tunaninta yafi karkata akan gidan,tana tunanin me zataje ta taras?,wanne abu zata samu cikin gidan.

"Tunda na ganki sawwama naji zuciyata ta kwanta dake.....ta kuma kamu da sonki......naji kuma a raina na samu matar aure.....ina fatan zaki bani dama....." Statement dinsa na qarshe data samu fahimta kenan.

Waiwayawa tayi ta dubeshi,shima idanunsa yana kanta,da alama ya gama dukkanin bayanansa ita yake da buqatar jin ta bakinta. Dauke duban nata tayi,sannan ta saka hannu ta bude murfin motar ta zura qafafunta ta fito. Da mamaki yake binta da kallo har zuwa sanda ta maida masa murfin motar ta rufe,tadan rage tsaho kadan tana dubansa da shiny eyes dinta

"Na gode da karamcinka......amma kayi haquri.....babu aure a rubuce cikin rayuwata.....na barka lafiya" Ta motsa labbanta a hankali sannan ta janye jikinta daga motar.

Soma takawa tayi a hankali tana barin wajen,AURE na daya daga cikin abinda take mantawa dashi a rayuwarta. Aure yana cikin abinda yake a lissafin qarshe cikin abubuwan da suke ba dole ba a rayuwarta. Aure yana daya daga cikin abinda take masa wani irin kallon da batasan ajin data zubashi ba.....babu shi ko kadan a dictionary dinta,idanma anyi zancensa,tana masa kallon wani baqon abu wanda batasan ranar da zata saba da ji ko ganinsa ba,bare azo da batun wanzuwarsa akan kanta.

Ko kadan bata damu da tsaiwarsa a wajen ba,abu daya ta sani.....kaman sauran mazan,yadda basu da masaniyar daga inda ta fito......hakanan bata basu qofa ko qanqani game da sanin inda zata ko inda zata shiga. Don haka bata kutsa kanta cikin gidan ba sai data kadar masa da hankali,ta kuma tabbatar ya bar layin.

Da sallama a bakinta ta shiga madaidaicin tsakar gidan dake shimfide da sabon simintin da bata jima da sanyawa ayi musi shi ba saboda jin dadinsu.

Yara ne aqalla kusan guda biyar wadanda shekarunsu bazai haura goma zuwa sha uku ba. Biyu daga cikinsu wanki sukeyi,daya kuma tana wanke wanke,yayin da guda dayar take jawo ruwa a rijiya tana zubawa a babban mazubin ruwan da suke amfani dashi a gidan.

Sallamarta ya sanya kowacce ta watsar da abinda takeyi,suka kuma rugo da gudu suna rige rigen isa inda take. Kyakkyawar fuskarta ta fadada da fara'a itama ta buda hannunta tana tarbarsu,daidai sanda muryar matar ta iskesu

"Ku da waye haka?" Ta bayyana tare da qarashen tambayarta tana qoqarin daura dankwali saman kanta.

Murmushi ne ya wadaci fuskarta itama,kakkaurar matar ma'abociyar tsaho da qiba,saidai alamu sun nuna yanayi na rayuwa ya sanya qibar zubewa sai saura data zama halittarta ce ba zata iya rabuwa da ita ba. Baqace wannan ya sanya dukka kamanninta sukafi karkata ga kamannin babarbariya.

"To ku barta ta qaraso mana" Ta fadi tana juyawa cikin dakin da ta fito,dukansu sai suka bi bayanta harda sabreen daketa jefawa yaran tambayoyi.

Tare suka zauna da yaran saman shimfidaddiyar dardumar da matar ta shimfida saboda sabreen din,daya daga cikin yaran ta miqe ta fice sai gata da ruwa adan qaramin jug da cup,yayin da sauran sukaci gaba da zama a kewayenta.

"Ina Ayshatu?" Tambayar farko da sabreen tayi mata bayan sun gama gaisawa,tambayar data sanya yaran suka miqe daya bayan daya suna fita a dakin.

Bata ce komai ba matar saita miqe tana dosar wata qofa dake maqale a falon,itama batace komai din ba ta miqe ta biyo bayanta.

Yalwataccen daki ne dake wadace da tsafts,ba komai a qasan sai wata lamusashiyar katifa guda daya yashe a qasa. Daga samanta idan ka duba da kyau mutum ce a kwance data lulluba duka jikinta. A sanyaye sabreen ta qarasa gaban katifar,ta saka hannu ta yaye rufar bakinta yana rawa ta kira sunanta

"Aishatu?" A hankali ta ware idanunta akan sabreen din,sai kuma wani busashen murmushi ya subucewa kyakkyawar fuskar yarinyar

"Aunty....kece kika zo?" Ta tambayeta da siririyar muryarta. Kasa riqe kanta tayi,sai kawai tayi qasa da kanta hawaye yana diga daga idanunta. Tana jin tausayin yarinyar kamar zai fasa zuciyarta,tana jin kamar zata narke a wajen,tana jin inama ace tana da ikon fidda ciwo ta farat daya daga jikin mutum a yanzu yanzu basai anjima ta cisgeshi daga jikin ayshatu

"Ko baki da ikon cire mata shi yanzu yanzu.....kina iya sama muku dama ke da ita na samo mata lafiya a duk inda lafiyar take a fadin duniya" Wani sashe na zuciyarta ya bata amsar data motsa mata wani qwarin gwiwa daga can qasan zuciyarta. Wannan ya sanya ta sake daga idanunta tana kallon aysha. Allah ne kadai yasan bila'adadin mata da yaran da suka shiga irin yanayin da ayshatu ke ciki duka sanadin TAIMAKO. Lalacewar al'ummarmu abune me matuqar ban mamaki da daure kai. FYADE ba'a daukeshi da wani muhimmancin da me aikatashi zai fuskanci hukunci mafi tsananu ba a tsarin doka. Tana iya tuna yawan kudaden data kashe,shige da ficenta da kai kawo data dinga yi kafin ta samu ayiwa azzalumin hukuncin da doka ta tanada. A abinda ya yiwa aisha,ba hukuncin daurin shekaru take da buqata ba......lahira yafi kamata ya baqunta yaje ya hadu da hukuncin mafi iya hukuncin masu hukunci.

Sosai ta bawa zuciya da gangar jikinta qwarin gwiwa,ta zauna sosai ta yiwa yarinyar komai. Ta bata abinci ta kuma dinga hilatarta,har suka dinga hira tana saurarensu murmushi yana subuce mata. Hakan ya sanyaya ranta kafin su kebe da ummaa ta sake mata bayanin data yi mata a waya.

"Waje nakeson a fita da ayshatu,inason ta warke sumul taci gaba da rayuwarta,duka duka shekarunta sha uku,ya kamata ta rayu kamar kowa" Ta fada zuciyarta tana mata zafi. Allah ya dora mata tausayin yaran da matar kanta da batasan asalinsu ba,amma dukka dawainiyarsu kusan kaso tamanin cikin dari tana a wuyanta,hatta da hayar gidan da suke zaune a ciki kuwa,banda abinci da ma karantarsu rayuka shida.

Da idanu ummaa take bin sabreen. Tasan cewa dukkaninsu babu wanda suka hada dangantaka a tsakaninsu,amma suna jin juna kamar 'yan uwa,suna kuma ci gaba da tsananin shaquwa da juna.....kuma a yanzun sune 'yan uwan kawunansu.

"Sabreen......kiyi iya abinda zaki iya mu barwa Allah sauran.....samun maganin ayshatu a gida Nigeria ma miliyan nawa ya kama bare ayi batun fita da ita waje?,kinsan miliyoyin kudin da za'a cajemu?,daga visa passport masauki abinci da zaman asibiti zuwa kudin magani?" Shuru sabreen tayi tana saurarenta,tana jin zuciyarta na wani irin ciwo,irin ciwon da mutum kanji a duk sanda yake tsananin son abu amma babu ikon samuwar wannan abun gareshi. Numfashi taja sosai ta aje tana duban maama

"Allah zaiyi cikin iko da isarsa......na tabbatar Allah bazai taba wofantar da bayin da aka zalunta ba" Kai ummaa ke jinjinawa tare da yaba tauhidi da yaqinin sabreen.

Ta jima dasu saidai hankalinta yana kan asibiti,don haka lokaci kadan ta qara akai tayi musu sallama bayan ta aje musu kudi kaman yadda ta saba da basa wuce cefane da zirga zirgar makarantar yaran.

Tana hanya zuciyarta kamar ta fashe,hakanan ta sake jinta a rikice bayan fitowarta daga asibitin bayan taji bayani daki daki na yadda zata fita da ayshatu waje ayi mata aiki.

Kudade ne masu kaurin da a yanzun bata dasu bata kuma bawa wani ajiya ba. Batasan tayi farautar kudi don ta ajiye ta tara abun duniya ba......tana farautarta ne don ta raba a tsakanin mabuqata marasa galihu irinta,yanzun ka buqata ta taso mata wadda take da girma da muhimmanci a rayuwarta. Sai taja numfashi mai nauyi,tabbas a yanzun zatayi FARAUTA ta ainihi,tsakanin MIKA'IL YA'AQOUB da kuma MASHKUR waye zaiyi aman wadannan maqudan?.

_tofa zamuji waye,komarta zatayi kamu ko kuma wannan karon ita zata shiga komar?_


*D U N I Y A T A*

*_H U G U M A_*

PAGE 39


Tun a hanya har takai gida zuciyarta na karakaina ne tsakanin sunyen mutum ukun MIKA'IL MASHKUR KO KUMA YA'AQOUB.

Da sallama ta shiga parlor din bayan ta tsallake tarin idanun da a kullum suke da tuhume tuhume da zarge zarge a kanta masu tarin yawa. Ta samesu suna hada uniform dinsu guri guda nadra zata wanke. Huda kuma na kokawar kammala abincin dare,don da alama basu jima cancan da dawowa islamiyya ba.

Takan samu cikakkiyar nutsuwa a duk sanda ta dawo gidan ta samesu lafiya lau kaman yadda ta fita ta barsu. Haneefa ta zaburo da gudunta ta daneta tana mata sannu da zuwa

"Auta na gaji.....mu zauna". Ta fada tana direta saman kujera itama ta zauna a gefanta.

Jakarta ta bude ta fiddo alawa cikin wadanda ta siyawa su aishatu ta musu tsaraba ta miqawa nadra da haneefa

"Karbi huda" Ta furta sanda huda din ta gama goge qasan tiles din inda suka zubda ruwa.

A nutse ta tako,ta zauna a hannun kujera ta miqa hannu tana karba din idanunta akan fuskar Sabreen.

"Komai lafiya ko?" Sabreen din ta tambayeta tana kallonta ganin kallon da huda din ke binta dashi.

Kai ta gyada tana kauda dubanta daga kanta

"Lafiya lau anty" Da idanu sabreen din ta rutsata tana kallonta,kamar ba zata ce komai ba sai kuma ta buda baki a hankali

"Ko yauma kunnuwanki sun sake ji miki wani magana daga bakunan mutanen gidan nan da kika sakashi a ranki?" Ta mata tambayar tana tattara hankalinta a kanta.

A hankali ta girgiza kai alamun aah

"Huda" Sabreen ta kirayi sunanta kanta tsaye. Daga kai tayi ta kalleta sai kuma ta qara sadda kanta qasa

"Dawo nan ki zauna" Ta fada tana nuna mata gefanta zuciyarta tana bugawa fiye da yadda ya kamata ace ta buga din. Ko kadan bata qaunar taga sauyawar yanayi daga motsin kowannensu. Duniya da mutanen cikinta tsoro suke bata matuqa.....irin tsoron da babu shi a cikin FARAUTARTA amma tana dashi cikin DUNIYARTA data 'yan uwanta. Sune dukka rauninta a rayuwa,sune tsoronta kuma sune kwanciyar hankalinta.

Kamar yadda ta buqata haka ta zamo ta zauna a gefanta,saidai har yanzu bata yarda sun hada idanu ba

"Huda.....kalleni nan" Ta fada tana kausasa muryarta. Yadda ta bata umarni kadai ya gaya mata bada wasa take ba,ta furta umarnin ne tun daga tsakiyar zuciya da kuma ruhinta,don haka ta dago din ta dubeta kai tsaye kaman yadda tace

"Zan maimaita tambayar dana miki,kuma ina buqatar ki bani amsarta kafin nadra da haneefa su sake dawowa dakin nan......mene a ranki?,meye damuwarki?"

"So nake ki daina fita yaaya......ki zauna a gida kaman kowa" Ta fadi muryarta tana rawa. Idanunta sabreen ta maida tadan lumshe kana ta budesu. Fargaba tadan saukar mata,yau huda ce ta fara tararta da wannan maganar,gobe sai nadra jibi sai haneefa?. Tambaya ta yiwa kanta amma kuma tana baiwa kanta yaqinin abinda zai faru kenan a zahiri.

"Kina zargi na ne kema huda?" Tayi mata tambayar takai tsaye tana kallon qwayar idanunta. Kamar maganar ta daketa sosai hakan ya sanyata daga kai da hanzari ta kalleta tana girgiza kai,sai kuma ta sake sauke kan nata qwalla tana gangaro mata.

"Yaushe kika soma zare audugar dana baki ki sanyawa kunnuwanki akan zancan mutane?,yaushe kika samu cikakken zaman saurara da fahimtar maganganun mutane?,yaushe hankalinki ya fara kaiwa nan huda?" Ta furta idanunta suna qanqancewa,wanda hakan zai nuna maka zallar radadin da takeji a zuciyarta.

"Ina nan yadda kika sanni huda.....babu kuma abinda zai canzani......gwagwarmaya da fadi tashin da nayi a baya bai sauyani ba bare yanzu dana 'YANTU.....karki bari zargi shakka ko kokwanto a kaina ya ratsa zuciyarki har ya samu gurbi......bazan iya zama ba huda......bazan kuma iya daina fita ba,don haka ki cire damuwar wannan daga ranki" Ta amsa mata tana miqewa a nutse daga saman kujerar,saidai dukka gabbanta sun saki da gajiya da kuma damuwar data saukarwa ruhinta.

Ta qasan idanu take bin sabreen din da kallo har ta shige dakinsu. Ta janye idanunta tana sanya hannunta gami da dauke qwallar dake tsiyaya daga idanunta. Anya ta kyauta idan har ta sanya zuciyar data sadaukar da komai nata saboda farincikinsu da ingantuwar rayuwarsu.....ta kyauta idan tayi silar sanyata a damuwa?.

Babu kyautawa ko kadan,idan har ta aikata hakan kenan bata da maraba da sauran gama garin jama'ar gari?. Bata da banbanci dasu?,tafi aminta dasu kenan akanta?. Nadama taji tana saukar mata a hankali. Bawai tayi komai bane da gangan,kawai ta kasa controlling din kanta ne akan batun,ta kasa jure abubuwan da takeji take kuma gani kulliyaumin,ita daya kuma tasan yadda takeji a duk sanda akayi magana akan yayartata halitta mafi soyuwa a gareta.

Tana zaune a wajen tana feeling guilty akan maganar,har sabreen ta sauya kaya zuwa wasu riga da wando silk me dogon hannu,rigar tadan sauko mata har saman cinyoyinta,yayin da wandon ya sauka har saman qafafunta. Tayi alwala ta dawo ita da haneefa,nadra na daga waje bakin fanfo tana dora nata ta kalleta

"Ki tashi kiyi alwala,ko kina fashin sallah ne?" Tayi mata tambayar cikin basarwa tana qoqarin zura jilbab dinta. Kai ta girgiza,ta miqe tana takawa a sanyaye tana ficewa. Sanda nadra ta shigo sai tace ta sanya hijab su jira huda din ta shigo sai suyi jam'i kamar yadda sukeyi lokaci lokaci. Zama tayi gefan kujerar falon kafin shigowar hudan tana duba saqonnin cikin wayarta. Tana jimawa bata duba saqon sms ba

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login