Showing 198001 words to 201000 words out of 557259 words

Chapter 67 - 𝐃𝐔𝐍𝐈𝐘ATA BOOK1 AND 2 HAUSA NOVEL

HUGUMA   

03 Nov 2025

500

Duk yadda bibo ke fama da habaici a ranar kasa komai tayi. Wani irin baqinciki ke nuqurqusarta kaman ta hadiyi zaciya. Inda tasan lalacewar sabreen ba wani abu bane da zai zame mata illa ba ya hanata auruwa da tuntuni ta dade da sanya hannu a lamuranta ta kadata tayi nesa dasu bare yau taga wannan abun takaici. Lefe ya kasa dauke qasan?,sai babban falon marigayi mahaifinsu na sama aka kaishi aka zube a can?. Didi ta sanya muqulli ta rufe don sunyi yawan da za'a ce wai anzo kallo an zauna an bisu daya da daya an kalla kamar yadda aka saba ganin lefe. Wanda gulma ta qarewa kuwa saidai ya leqa ta windo ya kalla,iya Kalllon bayan akwatin kawai ba tare da ankai ga budesu ba wani abu ne me qayatarwa a idanun me kallo.

Tana kwance kamar kullum har akayi didifniyar ajiye lefen dama komai da komai,idanu take budewa kawai lokaci bayan lokaci ta kalli su huda.

Ba wata damuwa sam sam a tattare dasu,sai take hangowa ma kamar farinciki suke ciki. Sun samu didi da yanzu duk inda ta motsa suna wajen ta zame musu uwa na wucin gadi. Tausayinsu takeji qwarai,a ina zata barsu randa aka maqala mata wannan maqalallen auren?. A yanxu kam akwai walwala me yawa tare dasu saboda qishirwar UWA da suke kasheta tare da didi din.

"Anata hidima anata hidima......amma mu har yanxu bamuga qyallin ango ba,bamuga yazo gaisuwa ko ganin amaryarsa ba bare akai ga batun gaidamu iyaye" Irin lafazin da ya fita daga bakin me biwa bibo kenan bayan ta yaye labulen dakin suna gaisawa da didi.

Dan murmushi didi da tasaki,duk da itama abun yana ranta,bata taba ganin ya kirayi sabreen din ba duk da tasan zai wahala ta daga wayar a yadda ta kafe dinnan bataso......bata taba jin ance gashican yazo ba koda ba zata fita ba

"Danku ne fa?,me kike ci na baka na zuba?,ai har sai kun gaji da ganinsa"

"Aiyo to......naga mun aurar amma ba haka mu muka saba gani ba,koda yake sha'ani me arziqi daban dana talaka" Daga haka ta saki labulen tana wucewa don saqo ne takeson ta isar ta kuma tabbatar ya kai inda take da muradi.

Sanda didi ke zaune saman kanta tana jefa tambayar kanta,sai ta mayar da idanunta kawai ta rufe tana cewa

"Ki tambayi kawu" Tana ganin shike da cikakkiyar amsar bada ita ga wulaqantaccen aure irin wannan. A duniyar auren hadi.....a kuma duniyar auren dole bata taba ganin kalar nata auren ba......ki sau daya bai taba tako qafarsa unguwarsu bama bare akai ga isowarsa qofar gidan mahaifinta da zummar nemawa kansa ita kamar yadda kowanne d'a namiji yakeyi. Sai damunsu akeyi da kawo dukiyar data tabbatar tamkar magana ce a fakaice ake gaya mata na sun zabi kudi ga kudi nan.......kawu yayi mata abinda ba wani mahaluqi daya isa yayi mata shi,hakanan ba wanda ya kwatanta yi mata hakan sai shi. A kullum kalmar UBA da Allah yabashi wannan take dubawa take dauke masa qafa da idanu akan wasu abubuwan,banda haka bata tunanin akwai wanda zai mata hakan ta lamunta.



𝘼𝙡𝙝𝙖𝙟𝙞 𝙝𝙖𝙢𝙯𝙖 𝙠𝙞𝙗𝙞𝙮𝙖 𝙤𝙡𝙙 𝙧𝙚𝙨𝙞𝙙𝙚𝙣𝙘𝙚


"Alhamdulillah" Ta samu kanta da furtawa tana shafa hannunta saman fuskarta bayan ta kammala sallar ishai a ranar. Rana ce data zama ta hidima sosai a garesu kai kace bawai lefe kadai aka kai ba......tamkar bikin ake gudanarwa a ranar. Gefe guda kuma cikin hidimar tashi suke daga gidan,akwai 'yan uwa sosai da abokan arziqi da kowa ke zaban furniture din da yakeso a sassan nata.

Har qasan ranta takejin farinciki idan ta tuna kwanaki bakwai kacal suka rage muhammad dinta ya zama magidanci kamar yadda kullum take da mafarkin wannan ranar. Abu daya ne ya tsaye.mata a rai,yake sake sanyata a shakka da kokwanto duk kuwa da abba hamza yayi qoqarin nusasheta tare da yi mata bayanin ta fidda abun a ranta wato batun mariya.

Komai da mariya akeyi,ayyukanta duka suna gwada yadda take dama dama da auren nan. Ta yiwa mariya farin sani,ba sanin jiya ko yau ba kawai......banza bata kai zomo kasuwa,hakana nan mariyar ungulu ce bata jewar banza......ta kasa aminta da haka siddan mariya keson abun nan ba wata adawa kaman yadda ta saba.....uwa uba kuma neman yazo daidai dana fuad din. A haka dai take kallon abubuwa amma kuma tanata qoqarin gamsar da kanta all is well kaman yadda abba ya shawarceta.

Sallamar musaddiq da farouq bayan sunyi knocking ta basu izinin shigowa su saka sanyata gyara zamanta yadda qafafunta zasu miqe sosai. Kaman ko yaushe tana dubansu bisa alfaharin samun 'ya'ya irinsu suka qaraso.

"Larai keson magana dake akan dakincan,tana tambaya shima zaa fitar da kayan ciki?,nace mata dai su kwashe kawai" Farouq ya fada yana shafar sumar kansa hadi da zama gefan annin musaddiq kuma ya yiwa kansa mazauni saitin qafafunta. Haka suke duk sanda suka sameta zaune koda su hudunne sai su sakata gaba a tsakiya kamar wasu yayayyu ko masu shan maama,sa. Basa ganin girmansu gaba dayansu indai suna gabanta ne.

"Eh yayi hakan....tashin nan ina jinsa kamar wasa wallahi" Anni ta fada tana alhinin bari muhallin da suka dauki shekaru a cikinsa,duk da cewa bawai sun barshi kenan ba.....nan dinma zaa sake zuba sabbin furniture da komai da komai cikin satin nan,idan sun gaji da waccan unguwar sai ta taho nan ta zauna......saidai ko kusa ko alama wannan gidan bai isa ya hada kafada da wannan din ba.

"Lokaci anni.....zakiso wancan gidan fiye da wannan fa" Kai ta kada

"Kayya.....ku yara kune qyale qyalen rayuwa ke mugu gardi.....faruqu......inason magana da surukata,ko zaka kiramin ita?" Ta tambaya farouq.

Zamansa ya gyara ya ciro wayarsa yana budeta

"Banajin ina da number surukar nan taki anni...." Ya fada a ransa yana tunanin fuad dinma baida ita,bayason kuma su fahimci hakan

"Amma bari nasa a turo sai na kira miki".

Kawu kawai ya kira kanshi tsaye ya nema number daga wajensa.

𝙎𝘼𝘽𝙍𝙀𝙀𝙉𝙉


Jujjuya wayar kawai takeyi a hannunta tana cije lips dinta zuciyarta na sake quntata. Tunda suka gama waya da matar da har yanzu ta kasa yarda wai ita din mahaifiya ce ga wancan dan rainin wayon ma'abocin girman kan mamaki yake sake cikata. Wayar mintuna talatin amma ta sanyata zaman minti ashirin tana tariyar kowacce magana data fita daga bakinta

"Duk abinda kikaga baiyi ba kiyi magana.....duk kudin da kike buqata ki nemesa a wajena zaki sameshi........burina guda daya tal shine ki cikamin burina da kuma manufar da ta sanya na nema miki auren d'ana.......wannan shi zai baki damar zama cikin jerin sahun masu kudi masu arziqi.....kuma shine zai zama kariya daga rayuwar 'yan uwanki.....domin har yanzu suna a hannun mu duk da kuwa mun sake miki su".

Kai ta jinjina tana sake cije lebe.....har yanxu matar bata santa ba......batasan wacece Sabrina da iya adadin abinda zata iya aikatawa ba......inda ace ta sanya harsashin wasan tsakanin ita da ita ne data nuna mata tata zallar qwarewar......to amma inaaaa......bisa rashin sa'a ta sanyo da rayukan da suka zama sune K'ARFINTA kuma sune RAUNINTA dole tayi komai bisa lura da kuma tsari.

Bataji nauyin gaya mata kai tsaye ba.....ta shaida mata cewar

"Bani buqatar ku nunawa duniya ni.....duk wani events bani da sha'awar zuwa.....koda kin tsara hakan dani ki cireni a ciki" Amsar data bawa maamah sanda ta bata daman shirya duk kalar events din da take da buri ko mafarkin gudanarwa koda kuwa wasu qasashen take so ayi jigilar qawayenta don gudanar da komai a can. Ta bude mata komai ne don a nata karatun.....gogaggiyar mace kaman sabreen da tasan dadin kudi da bariki.....tabbas zataso cikin manyan burika dama mafarkanta tayi kalar bikin daya zarce na kowacce yarinya dake tashe ko kuma take jin kanta ko ubanta wani ne.

"Ma sha Allah.....alhamdulillah,to Allah ya tabbatar mana da alkhairinsa....gata bari na bata" Muryar didi kenan data shigo dakin riqe da wayarta

"Ga surukarki.......karbi mana" Didi ta fada tana miqawa sabreen wayar. Kanta ya daure,wacce surukar tata kuma?,wata dabance bayan wadda ta gama tumasanci yanzu ko kuwa?. Yadda didi ta tsareta da ido......ba wani sauran abinda zatayi saita saka hannu ta karba din.

"Assalamu alaikum warahmatullah" Anni tayi cikakkiyar sallamar da wannan muryar tata data cika da nutsuwa da dattako,muryar data tsarga tun daga zuciyar sabreen din ta sace wani nauyi da fushi daketa kai kawo a qirjinta cikin mintuna qalilan ba tare data ankara ba

"Wa'alaikumussalam warahmatullah" Ta samu kanta da amsawa da wata nutsuwa data sameta ba tare da tasan daga ina bane.

"Allah yasa zaki iya shaida wannan mamar taku,ina fatan ya gaya miki komai a kaina?" Anni tai maganar da sautin murmushi a muryarta. Dif tayi don batasan me zatace mata ba.....me zai gaya mata mutumin da ko fuskarsa bata gama tantancewa ba bare duk wani abu daya shafeshi.

A taqaice anni ta yiwa sabreen bayanin matsayinta. Bayanin daya dinga zillo saman zuciyar sabreen yana sake rikita mata lissafi,iyayensa biyu?,masu mabanbantan dabi'u da halaye,wadannan sune kawai abinda tafi riqewa tanason kuma tantancewa amma kawo yanzu kanta ya tsuke gaba daya.

"Ki daukeni tamkar mahaifiyarki sabreen.......duk wani abu da uwa kewa 'yarta zaki sameshi a tare dani in sha Allah". Kalmar data daki qirjinta ta kuma saukar da wani abu me sanyi saman ranta

"Suna da banbani" Taji ana gaya mata daga can saman kanta bayan ta sauke wayar da suka gama da ita. Tana tariyar maganganun data gaya mata cike da harshe me hikima da fasaha.....sam babu hadi ko a iya kalamai tsakaninta da waccan dake iqirarin ita ta haifesa

"Zanso nasan wacece uwar ta gaske" Ta fada qasa qasa tana duban didi dake shigowa.

"Saiki kintsa kanki.....don tace zatayi aiken me gyaran jiki da zasu fara aikinsu daga gobe har zuwa ranar da zaa daura aure.......amma sabreen" Didi ta fada tana neman wajen zama gefan sabreen din ba tare data damu da damuwar da batun gyaran jikinta ya saukar mata ba.

"Mamarsa nada kirki har haka?.....me yake tsananta damuwarki......duk wani motsi nasu yana alamta su din mutanen kirki ne.......wanda dukiyarsu bata rufe musu idanu ba.....don Allah ki kwantar da hankalinki......tabbas ina kyautata musu zato"

"Ba zaki gane ba didi,abinda kike gani a zahiri ba shine a badini ba.......to waima wanna jikin zaa gyara?" Tayi dukka maganar ne idanunta a kulle,amma wannan ta qarshen ta ware idanunta ne akan didin.

Kallonta didin takeyi tana jin kamar sabreen din bayan matsalar miskilanci da yake damunta harda matsalar jinnu.

"Wanne jikin kike dashi bayan wannan nakin?,ko kinaso kiyi ma dattijuwar matar me tsananin karamci gardama?" Ido ta tsurawa didi tana jin kamar fa bai kamata tace mata bataso ba ko?,to amma ai sam gyara jiki ma baihau ba a wannan bigiren da take kai ita,don haka ta mayar da idanunta ta rufe tana motsa labbanta

"Da zaiyiwu shine abunda nafiso ta janyemin". Didin ta jima a zaune tana kallonta mamaki yana sake kamata,sai data gaji don kanta kawai ta miqe tana cewa

"Allah ya kyauta" Ta fice a dakin.

"Anni da suruka.......Muryar nan kamar na santa anni" Musaddiq ya fada yana kallonta. Sai a sannan ta iya dauke kanta daga fuskar wayar kamar sabreen dince a gabanta,batasan me yasa ta jarabtu dason yarinyar da bata taba ganin fuskarta ba hakanan

"Ba mamaki ka taba rakiyar zance a boye ko jinsu suna waya da hamman naka" Dariya ta subuce masa

"Anni wannan soyayyar waye yasan sanda aka qullata?,banda ansan gidan su da sai nace mijin aljana ya bishi da gaske aljanar xaya aura"

"Ungo nan.....wato wannan dan kaniyar yayan naka ya koya maka ko?,maza ka fadi yaji,idan shi yasha a hannunsa kaidai kasan sauran"

"Tuba nake" Ya fada yana rufe bakinsa da hannunsa yana qoqarin boye dariyarsa.

********Tana kukan zuci qwarai da gaske wanda ke tattare da zargen abubuwa masu yawa data tanadi tunkarar kowa da komai......amma hakan bai hana zuwan me gyaran jikin da take aikinta da wata irin qwarewa tamkar zata sauya fatar jikin ta ta ainihi da wata ta daban ba.

Komai ta kawo idanu ta xuba masa kamar dai komai nata ya daina aiki.....saidai fa wannan kwanyar......wannan zuciyar suna nan suna aikinsu daidai.

A daidai sanda komai yake tafiya,shirye shirye suna nisa,kwanakin qulla auren da zai zamewa rayuwarsu 𝙈𝘼𝘽𝙐𝘿𝙄n tafiya bisa wata turba da basu taba kawowa zata bude musu......a wannan lokacin shirye shiryen maamah sukayi nisa itama.

Ta narka kudaden da batasan adadinsu ba wajen bokanta.....wanda ta saida tsaffin kadararrta ta narkasu zuwa kudin da zasu isheta aiwatar da komai.

Kowacce rana da gari zai waye,yana waye mata ne da tsananin farincikin ganin kusantuwar cikar burinta........sanin wacece yarinyar wacece SABREEN adan gamayyarsu ta qididdigaggun lokuta ya sanya ta gabatarwa da boka SUNANTA don tana buqatar aiki a kanta na musamman.

𝙏𝙪𝙧𝙦𝙖𝙨𝙝𝙞......𝙞𝙙𝙖𝙣 𝙠𝙞𝙣𝙖 𝙩𝙪𝙣𝙖𝙣𝙞 𝙝𝙖𝙣𝙜𝙚 𝙠𝙤 𝙝𝙖𝙨𝙖𝙝𝙚𝙣 𝙖𝙗𝙞𝙣𝙙𝙖 𝙯𝙖𝙞 𝙛𝙖𝙧𝙪 𝙥𝙖𝙧𝙩 2 𝙣𝙖 𝙡𝙖𝙗𝙖𝙧𝙞𝙣 𝙣𝙖𝙣 𝙩𝙤 𝙠𝙞 𝙜𝙖𝙜𝙜𝙖𝙬𝙖𝙧 𝙖𝙟𝙞𝙮𝙚 𝙝𝙖𝙨𝙖𝙨𝙝𝙚𝙣𝙠𝙞.....𝙙𝙤𝙣 𝙗𝙖 𝙡𝙖𝙡𝙡𝙖𝙞 𝙗𝙖𝙣𝙚 𝙘𝙖𝙣 𝙢𝙪𝙠𝙖 𝙣𝙪𝙛𝙖 😁😄

𝙄𝙙𝙖𝙣 𝙗𝙖𝙠𝙞 𝙨𝙖𝙢𝙪 𝙠𝙖𝙧𝙖𝙣𝙩𝙖 𝙥𝙖𝙧𝙩 𝙤𝙣𝙚 𝙗𝙖 𝙠𝙞𝙮𝙞 𝙝𝙖𝙣𝙯𝙖𝙧𝙞𝙣 𝙠𝙖𝙢𝙖𝙨𝙝𝙞 𝙠𝙞 𝙗𝙞𝙗𝙞𝙮𝙚𝙨𝙝𝙞 𝙙𝙖 𝙠𝙮𝙖𝙪......𝙙𝙤𝙣 𝙜𝙪𝙣𝙙𝙖𝙧𝙞𝙣 𝙡𝙖𝙗𝙖𝙧𝙞𝙣 𝙮𝙖𝙣𝙖 𝙖 𝙜𝙖𝙗𝙖

𝙕𝙖𝙯𝙯𝙖𝙛𝙖𝙣 𝙩𝙪𝙜𝙜𝙪
𝙈𝙖𝙠𝙞𝙧𝙘𝙞
𝘿𝙖 𝙬𝙖𝙩𝙖 𝙞𝙧𝙞𝙣 𝙗𝙖𝙝𝙖𝙜𝙪𝙬𝙖 𝙠𝙪𝙢𝙖 𝙗𝙞𝙧𝙠𝙞𝙩𝙖𝙘𝙘𝙞𝙮𝙖𝙧 𝙨𝙤𝙮𝙖𝙮𝙮𝙖

𝘼𝙠𝙬𝙖𝙞 𝙡𝙖𝙨𝙩 𝙥𝙖𝙜𝙚 𝙙𝙖 𝙣𝙖𝙠𝙚𝙨𝙤 𝙣𝙖 𝙨𝙖𝙠𝙖𝙧 𝙢𝙪𝙠𝙪 𝙬𝙖𝙣𝙙𝙖 𝙯𝙖𝙞 𝙭𝙖𝙢𝙖 𝙢𝙪𝙧𝙛𝙞 𝙜𝙖 𝙡𝙖𝙗𝙖𝙧𝙞𝙣
𝙏𝙤 𝙖𝙢𝙢𝙖 𝙞𝙙𝙖𝙣 𝙙𝙖𝙢𝙖 𝙗𝙖𝙩𝙖 𝙗𝙖𝙣𝙞 𝙙𝙖𝙢𝙖 𝙗𝙖 𝙯𝙖𝙢𝙪 𝙝𝙖𝙙𝙚 𝙗𝙖𝙮𝙖𝙣 𝙨𝙖𝙡𝙡𝙖𝙝
𝘿𝙪𝙠 𝙙𝙖 𝙯𝙖𝙣 𝙦𝙤𝙦𝙖𝙧𝙩𝙖 𝙣𝙖 𝙝𝙖𝙙𝙖 𝙢𝙪𝙠𝙪 𝙨𝙝𝙞 𝙞𝙣 𝙨𝙝𝙖 𝘼𝙡𝙡𝙖𝙝,𝙙𝙤𝙣 𝙯𝙖𝙞 𝙯𝙖𝙢𝙚 𝙢𝙪𝙠𝙪 𝙈𝘼𝙉𝙐𝙉𝙄𝙔𝘼.

𝙃𝙐𝙂𝙐𝙈𝘼𝙉𝙆𝙐 𝘾𝙀.




𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓 𝐀

̶B̶O̶O̶K ̶2

ⱧɄ₲Ʉ₥₳

𝙋𝘼𝙂𝙀 1



𝘼𝙢𝙗𝙞𝙩𝙞𝙤𝙣 & 𝙨𝙪𝙘𝙘𝙚𝙨𝙨

𝙈𝙪𝙝𝙖𝙢𝙢𝙖𝙙 𝙛𝙪'𝙖𝙙 𝙟𝙖𝙙𝙙𝙖

"Hustle until you no longer need to introduce yourself,push your self because no one else is going to do it for you". Kalamansa na qarshe kenan da tarin mayan attajiran da sukayi meeting na qarshe dasu wanda keson saka share dinsu cikin sabon kamfanin da kwanaki bakwai suka rage masa ya budeshi. Kalamai ne da suka dauki hankulan mutanen dake wajen,wanda dasu aka kammala zaman.

Sanda yake sallama dash fiye da rabin hankalinsa yana kan wayarsa da tun dazun ya lura tana haske. Sai da gurin ya rage saura shi daya da hudu daga cikin guard dinsa da wannan karon dasu yayi tafiyar wadanda ke nesa da inda yake,ya miqa hannu a nutse yana jawo wayar gami da fesar da iska me dumi daga bakinsa. Cikin kowanne motsi yana jin farinciki na yadda al'amuran bude kamfanin ke gudana da dukkan wani haske qyalli da kuma alamu na nasara,bai taba qwallafa rai akan wani abu kaman haka ba,baisan me yasa dukka tunaninsa da hankalinsa suka raja'a wajen son ganin cikar wannan mafarkin nasa ba. Tunda yazo samu cikakken zama na awa biyu cur ba,saidai idan dare yayi ya wafci wasu awanni ya tilastawa kansa kwanciya ya huta. Kowanne minti idan ya shude da amfaninsa a wajensa,ko baya din dama shi mutum ne me girmama lokaci tare da bashi muhimmanci qwarai.

Sunan farouq kawai daya gani ya sakashi gyara zama yana furta

"Ya salam" Qasa qasa fuskarsa nason fidda wannan sihirtaccen murmushin nasa da ba kasafai ake samun dacen ganinsa ba. Wani sirri ne kwance cikin murmushinsa dake qara masa haiba da kwarjini da fitar asalin kyan da ubangiji ya huwace masa. Yasan zayasha qorafi ne kawai wajen farouq din......don yace masa zai kirashi har baisan adadi ba......hakanan bazai ma iya tuna awar qarshe da sukayi waya ba.

"Hala baka da wani abu me muhimmanci cikin rayuwarka sama da business dinka?" Kalmar da farouq ya fara jera masa kenan. Boyayyen murmushi ya saki yana daga dogayen qafafunsa ya aza saman dunqulallen table din gabansa me azabar kyau. Wani irin shaquwa da fahimtar juna ce tsakaninsu dake sanyasu iya fahimtar mode din juna koda basa kallon fuskokin juna. Yasan zaiji fiye da haka ma a bakin farouq din,don muryarsa a dake take da alama har kan fuskarsa akwai alamu na qosawa

"Idan ka cire ku family na.......tabbas ba abinda ya fishi muhimmanci cikin duka kaf rayuwata".

"Aurenka da yarinyar su a wanne muhalli ka sakasu?....." Ya sake masa tambayar kansa tsaye cikin salo na kaiwa maqura da son masa titsiye.

"Aure?....yarinya?" Ya maimaita maganar har ga Allah cikin son neman qarin haske.

"Eheeennn" Farouq ya fada a taqaice,cikin ransa yana jin rainin hankalin jadda yana neman fin qarfin tunaninsa muddin ya gaya masa ya manta da lamarin auren dake gabansa.

"Mmtsewww......au" Fuad ya furta wani siririn murmushi yana sake qwace masa. Sai a yanzun kwanyar tayo masa tariyar karatun baya na abinda ya baro a nigeria. Kusan gaba daya sabgar ta shafe daga tunaninsa,abinda ya sanya a gaba ya mamaye tunanin komai daga kansa.

"Am sorry......kasan halin......"

"......halin mijin aljana.......zata sakashi ya aikata fiye da haka ma,saidai alhmdlh.....duk abinta a wannan karon munci qarfinta,kuma in sha Allah dan uwana bazai mutu babu aure ba". Dariya sosai ta qwace ma fu'ad din ganin yadda farouq din ke maganar very serious,abinda ya jima baiyi ba,ya rasa abinda yasa suka damu da auren nan......ya fuskanci gaba dayansu murna suke dashi.....ya

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login