Showing 276001 words to 279000 words out of 557259 words

Chapter 93 - πƒπ”ππˆπ˜ATA BOOK1 AND 2 HAUSA NOVEL

HUGUMA   

03 Nov 2025

573

yake gudu saboda yadda suke qara karatun da yawa. Ta sallama da gaske karatun yana gudu ne saboda wata irin sharp brain da Allah ya bawa sabreen din,irin kwanyar da bata taba ganin irinta ba. Don duka karatun da sukayi da yammaci,zuwa wani yammaci din sabreen din ta narkashi ya koma cikin kwanyarta.

Tun asali tana da bala'in son karatu,musamman na addini din,saidai wani dalilin me zuwa ya ture wani. Ratayuwar hidimar qannenta saman wuya da kafadunta ya sanya tilas ta haqura da komai ta tattara ta ajiye,a yanzun kuma data fara shiga cikin abun sosai sai takejin komai kamar an yaye mata wani hijabi ne da da ya lullube kwanya da idanunta.

Tun sanda ta fahimci ya ajiye cook dinsa cikin gidan saita saita lokacin ta,sanda zata fito tayi sabgarta daga shi har cook din nasa basa gidan,hakazalika kafin su dawo ta kammala komai ta koma daki abinta.

Tayi mamakin yau da taji yunwa da safe da wuri haka,to amma kuma idan ta tuna ba wani abun arziqi take ci ba musamman jiya da dare bata saka wani abu me muhimmanci a bakinta ba sai taga ba abun mamaki bane.

Indonesian hijab down squeeze ta saka saman soft and cotton nigh gown din jikinta da bata fidda siffarta ba,saidai tadan lafe mata a mazaunai saboda taushinta. Hijab din ya qara qawata mata fuska,fuskar data fita sosai ta tsakiyar hijab din da wani irin kyau kai kace itama haifaffiyar Indonesia dince. Ta qarasa gaban mirror ta qara turare a jikinta dan kadan kamar yadda ya zame mata wajibi,sai ta tsaya tana duban fuskartata. Wani irin glowing skin dinta yakeyi wanda ita kanta ta rasa dalili,saidai a yawancin lokuta tana bawa kanta amsa da wataqila zaman guri daya ne,sabanin baya da kullum muddin gari zai waye rana ta fito to zata saka qafarta a waje ta fita.

A hankali take tako hallway din,yau kawai tana jin nishadi cikin ranta sosai da cikakkiyar nutsuwar da batasan dalilinta ba,kwanyarta tana bitar wasu daga cikin karatuttukan data haddace,a haka ta rasa parlour na farko ta wuce zuwa na biyu.

Tana murza glass door din ta sanyo qafafunta ya daga idanunsa a hankali daga inda yake zaune ya zubesu fes saman fuskarta,idonta ya shiga nasa,sai ta janye nata idon a hankali,ta kuma ja da baya tana komawa da bayan a maimakon fitowa da tayi niyyar yi. Sam bata qaunar gamuwa dashi,a kwanakin data janye kanta daga komai da zai sanya su hadu ta kama karatunta sai take samun wata irin nutsuwa a zuciyarta. Ta dauki kwanaki rabon daya sanyata cikin idanunsa,daga shi har maamah sai takeji kamar Allah ne yayi mata maganin matsalarsu.

Janye nasa idanun yayi shima bayan ta koma da baya tana kuma komawa ciki. Yadan jijjiga kai kadan yana daukan mug din gabansa ya sanya a bakinsa. Tana gyara bedroom dinsa kamar yadda sukayi sharadi,saidai daga wannan ko gilmawarta bai sake gani ba tun daga ranar. Can qasan zuciyarsa tana cike da wasi wasi da kuma qiyasi akan abubuwa da dama. Sai yake zargin shurunta dana maamah dukka kamar akwai wani magana a qasa,don haka ya jawo wayarsa ya kira me sunan malam. Cikin qasa da second ashirin suka gama magana,ya shaida masa ya nema farouq ya turo amintacce kuma sirrintaccen me musu installing CCTV.

Mules din qafarsa ya maida,sannan ya ciri napkin guda daya yana goge dan abinda ya bata masa hannu kafin yace da ameh.

"At night.....ka dafa paw paw leaves ka ajiyemin da duminsa.....daga yau inaso ya zama first drink dina for morning". Kai ameh ya jinjina cikin girmamawa

"As you wish sir". Sai ya sauka a nutse amma hankalinsa yana dan kan qofar kadan,yanason sake tabbatarwa komawa tayi ta fasa shigowa saboda yana wajen?.

Murmushi ameh yayi yana binsa da kallo,sosai boss dinsa yake burgeshi,yayi aiki kafin wajensa gidajen manyan attajirai da dama,amma baiga mutum me kiyaye lafiyarsa da yasan sirrin abinci ba irin boss din nasa ba. Yasan duk wani abu da zai gyara lafiyarsa a matsayinsa na namiji,yasan duk wani abu da zai gyara masa lafiyar ido da fatarsa,hakanan yasan duk wani abu da yake natural anti aging remedies kala kala. Ire iren abubuwan da shi yake tanadarwa manyan da yayi aiki a qarqashinsu don inganta lafiyarsu da gina garkuwar jikinsu suke qin ci ko sha don ba dadi a baki ko basusan muhimmancinsa ba......sai gashi shi kullum ne sai an tanadar masa da wannan abun morning and evening. Akwai hadin salad daya dinga mamaki sanda yaga yana cinsa farkon xuwansa,musamman da yake yasan yadda yake inganta qarfi da lafiyar d'a namiji,da yawan wasu abubuwan ma shike qaruwa dashi a wajensa. Baya son maggi da yawa a abinci,kaman yadda sanyi zaqi da kuma maiqo da abokansa bane sam sam
(Mata da yawa suna complain din rashin lasting din mazansu a other room,sunsha magani sunsha maganin amma a banza,anata samun sabani da sauran masu matsaloli,to wallahi wallahi da yawansu maggi shine yake kashesu,inda kinsan yadda maggi yake kashe lafiyar mazajenmu da kinyi mugun gudunsa kuwa,kiga mace ta saka farin magi a abinci,tazo ta saka wadancan cubes din kala daban daban,ta hada drink ta laftawa miji sugar,ga uban sanyi,abinci mai yana kwanciya,ba ruwanki da manja ma sam sam,to billahillazi kunji na rantse muku haka zaita zame miki mace,kuma duk irin maganin da zaisha fa a banza,muddin ana kan cin magin nan,tashi daya ba zaki iya dainawa ba,amna gradually zaki dinga janyewa,idan goma kike sawa ki koma bakwai daga haka ki koma hudu,tabbas indai zaki dimanci haka zaki ga canji,ki ajiye farin maggi kwata kwata,zaqi da maiqo duka ki rage masa,hadin wancan salad din in sha Allah zan kawo muku shi a gaba,ya gwada cin na sati biyu bayan kin janye magin kiga ikon Allah,koda me gida yana da lafiya ma normal ne kina iya hada masa shi ya dinga ci,amma ina maimaita muku ku raba kanku da kayan d'an d'anon nan,Allah yasa mu dace).

Kamar kowacce safiya muddin yana da isashen lokaci......ba baqi ba meeting na early morning da sauransu,zuwa duba lafiyar anni da gaida maamah din yana cikin schedule dinsa na kullum.

A farfajiyar gidan kamar ko yaushe ya samu guard dinsa,kowa na tsaye akan aikinsa. Bai qaraso bama amma tuni Jordan ya buda masa bugatti dinsa yana jiran qarasowarsa.

Cikin girmamawa da nuna kulawa suka gaidashi ya amsa yana bincikar lafiyar kowa kaman kowacce safiya,sai daya tabbatar da kowa lafiya sannan ya miqawa saddiq da kusan a makare yake isowa kayan hannunsa,wannan dalilin ya sanya baya samun shiga cikin gidan duk zuwan da yakeyi.

Sun dauki hanya sosai kiran musaddiq ya shigo masa,ya fidda wayar yana connecting nata da Bluetooth dinsa yana amsa wayar.

"Hamma na gama komai......sai yaushe zan dawo?" Musaddiq din ya amsa a karye da alama gida yakeson dawowar.

"Ka dawo kayi me?" Ya tambayeshi yana jin tantama a dawowar tasa.

"Hamma nayi missing anni......nayi missing saddiq". Iska kadan ya furzar daga bakinsa wadda ta fita da qamshin mint leaves saboda mouth fresh dinsa kenan na dindindin

" Anni kuna waya haka saddiq.....kuma ko ita nasan bata da damuwa me yawa a tafiyarka.... Dude ne kawai nakeji ban kyauta masa ba dana dauke masa personal assistant......shima nasan ya fahimceni.....oops......anyways......nan da sati biyu zamu hade a madeena in sha Allah,it was family trip time". Har a muryarsa yaji dadi

"Hamma na Manta da lissafinma.....okay..."

"Hope komai naka ba matsala ko?,daga can zaka iya shiga koda Jeddah ne sai ka qaraso madeena"

"Direct entry zanyi hamma.....i can't wait to see my family".

"Alright....ka kula da kanka" Ya furta cikin kulawa

"Na gode hamma" Ya ambata suna ajiye wayar. Wayar ya zubawa idanu yana tuna wasu abubuwa da suka shude..... Ita rayuwa dukanta tana komawa tarihi ne watarana......bai taba zaton a rintsin da suka fuskanta shi da musaddiq ba akwai ranar da zatazo kamar haka komai ya wuce ba......yadda kula da musaddiq da bashi rayuwa me kyau ya sanya hannuwansa sukayi kanta.....tunaninsa ya dimauta,kwanyarsa ta kusa jirkicewa da daina iya tuna kome me kyau.....ambaton sunan maamah ya zame musu kamar wata jarabawa.

Hannunsa yasa ya shafi fuskarsa yana son ajiye tunanin a gefe.....yanzu yanzu zai iya rasa kowacce nutsuwa tasa,ya kuma rasa duk wani courage na aiki daya fito dashi a yau din.

"Gidan maamah zai fara tsayawa" Yace da saddiq don ya shaidawa driver din shi kuma ya sanar da ayarin motocin. Yayi hakanne don yasan muddin ya shiga gidan maamah a yanayin da yake ciki na tuna munanan abubuwan data aikata baga rayuwarsu kadai ba......anni itace zata zamewa zuciyarsa yayyafin ruwan sanyin da zai wanke duk wani baci da ransa yayi.

Kamar kullum da qafa ya taka daga inda suka ajiye motocin zuwa cikin gidan. Malam sa'adu ya matso da sauri yana bude masa qaramar qofar kasancewarsa shugaban masu gadi na gidan a yanzu. Tunda aka mallakawa maamah din wannan gidan yafi qarfin gadin malam sa'adu shi kadai,dole sai daya hada mata da security,amma kuma kowa yana qarqashin malam sa'adun ne wanda shike da permanent chair. Har kullum burgeshi hali da dabi'ar muhammadun takeyi,ya taka dukkan wani matsayi da bawa zaizo ubangiji ya kaishi a rayuwa,amma bai dauki hakan a bakin komai ba.

Gaisawa sukayi kamar kullum,sannan ya taka yana shigewa cikin gidan da ma'aikatan dake bakin aiki kowa yake zubewa yana gaidashi.

Daidai sanda yake sallama a falon daidai sanda take fitowa daga kitchen din gidan,Hannunta dauke da qatuwat warmer kamar ma rinjayarta takeyi.

Huda ce,ta bishi da kallo tana amsa sallamar tasa cikin kallon baqunta. Yadan sake dubanta kadan,sai yake jin kamar yasan fuskar,amma kuma sai ya kauda wannan tunanin yana neman wajen zama,daidai sanda take gaidashi cikin ladabi daya zame musu jiki tun tale tale

"Ina kwana?" Ko daya maida dubansa kanta sai yaga har ranqwafawa tayi irin na ban girman nan

"Lafiya la....." Amsa gaisuwar ta katse saboda yadd warmer din taso subuce mata daga hannunta. Cikin zafin nama ya isa ya karba yana fadin

"Kibi a hankali......" Sai ya taka yana kaita saman dining din ya ajiye.

"Maamah ko?" Ta tambayeshi qasa qasa kaman me tsoron tambayar,don itadai yana mata kama da mijin adda sabreen din su. Kai ya jinjina kadan a ransa yana mamakin ina kuma maamah ta samota?.

"Bari na kira maka ita" Ta fada da dan saurinta,can qasan ranta yana cike da murna,yau kam taga wani daya danganci addansu.....ko gaisuwa ta aike mata tunda yawan lokuta maamah tana cewa ta kira basa kusa. Wayar hannunta da maamah ta bata kuwa da komai akai,hasalima suna waya kusan kullum da momma bahijja,amma batasan me yasa number adda sabreen din kota kira sam sam bata shiga ba.




*_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_*
08187255862

𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓 𝐀
_Zafafabiyar_

ΜΆBΜΆOΜΆOΜΆK ΜΆ2

β±§Ι„β‚²Ι„β‚₯β‚³

π™‹π˜Όπ™‚π™€ 43



A step na biyu taga maamah din tana saukowa daga saman,hannunta cikin na haneefa daketa bata labari.

"Yammatana ya akayi?" Ta tambayi huda tana dan sake mata murmushin nan nata da kusan sun sana dashi.

"Baqo ne kikayi" Ta fada tana dan waiwayawa inda fu'ad ke zaune,hannunsa dauke da remote yana sauya tasha,bawai kuma don yanason kallon bane aah....sai don kawai bayason kallon fuskar maamah din sakamakon abubuwan daya tuna da suka motsa ranshi.

"Muje to" Ta amsata har qasan ranta tana jin dadin yadda huda din ta kasa gane wanene. Tanason sanyata ta koma daki don kada suyi wata magana da zata fahimci wayeshi a wajensu?,amma kuma ta rasa wanne uzurin zata bata tunda dai abinci zataci akan dining. Uwa uba kowanne motsi nata da maganganunta tana yinsu ne a ankare,bata bari tayi wani abu da zai sanya shakka a ransu ko ta gaza juyasu yadda takeso.

Tunda suka sauko din haneefa ta zubawa fu'ad ido. Tabbas shine mijin adda sabreen,ta ganshi har sau biyu bata kuma mance ba,sannan bata sake ganinsa ba sai yau.

Saman kujerar maamah ta zauna,haneefa ta zauna a gefanta still idanunta suna kanshi ta kasa daukewa. Sanda ya gama gaida maamah din sai nasa idanun suka sauka akan yarinyar. Kamanninta suka fusgi idanunshi sosai,ya sake ganin wata kamar ta daban bayan wadda ya baro dazu tana me komawa falo bayan sun hada idanu. Murmushi haneefa ta sakar masa sanda taga shima ya dan kafeta da ido. Ya murmusa kadan tana shirin janye idanunsa sai yaga ta zame tana fadin

"Ina kwana mijin adda sabreen?". Kallon mamaki yake bibta dashi,mamakin da bai gama sakinsa ba tace

"Sunana haneefa nice autan adda sabreen,'yar mitsisiyar dakinmu". Baisan ya akayi murmushi ya ratsa miskilar fuskar nan tasa ya bayyana ba,ashe masu son sarautar autancin suna da yawa. Yanayinta sak sai ya tuna masa da yanayin amna.

" Ya isa haka haneefa....kije kuyi break ko ki koma daki wajen nadra ku kalli cartoon" Maamah tayi hanzarin dakatar da tattaunawar tasu. A nutse ya cira kansa yana duban fuskar maamah din,haka kawai sai yaji yana da buqatar ci gaba da magana da yarinyar.

"Qyaleta muyi hira maamah....she's very smart" Ya fada da wani irin tone a muryarsa,wasu abubuwa da wani irin gudu suka fara bijiro masa,yayin da gumi ya fara tsargawa maamah ta cikin rigarta.

Ta sani,tafi kowa ma samin haneefa she's very smart,fiye ma da zatonta,wannan ya sanya tafi janta a jiki da kuma kaffa kaffa da ita.

"Indai surutun haneefa ne saika gaji dashi......ni kuma magana nakeso nayi dakai,next time idan kazo sai kuyi hirar" Ta fada tana dan hade rai gami da gyara zama.

Sake dubanta yayi a karo na biyu,abubuwa biyu suka hade masa waje guda. Har yanzu dabi'ar nan tata tarashin son yara tana nan?,banbanci qarara me kuma fadin gaske na farko tsakaninta da anni. Indai haka ne yara uku ne cikin gidanma kenan?,akwai daya a cikin daki?. Me ya kaita dauko yara har uku?,ita da basu dameta ba?. Meye abun damuwa don yana hira da yarinya qarama?.

Agogonsa ya kalla,sai ya maida dubansa ga fuskarta.

"Ba damuwa ai,yau muna da enough time sama da kullum". Kafin ya sake cewa wani abu haneefa tace

" Zaka kaini naga adda sabreen?......don Allah hamma kada kace aah" Ta fada tana narke murya. Maganar taja hankalin huda dake saman dining,itama saita ajiye spoon din abincin da takeci ta maido hankalinta kansu.

Gumin dake tsatsatsafowa maamah din ya sake yawaita,da sauri kamar ana tankadata tace

"Aah fa haneefa......ni da kaina mukayi zan kaiku haka ne?".

"Eh amma har yanzu baki kaimu ba maamah,shi kuma hamma ma daga can yake ko?" Ta maida tambayar kansa. Kansa ya gyada a nutse yana karantarta.

"Maamah ki barshi ya kaimu ko anjima ne,in yaso saimu dawo da kanmu" Huda itama ta saka baki,don da gaske sunyi tsananin kewar sabreen din.

Sanda ta waiwaya da nufin yiwa huda din magana sai maganar fu'ad ta dakatar da komai.

"Jeki dauki hularki kuzo muje nasa a ajiyeku" Yayi maganar kansa tsaye,maganar data daki tsakiyar kan maamah da wani irin ba zata.

Har ga Allah kanshi tsaye ya fada kuma hankalinsa kwance,kawai dai a cikin zuciyarsa ya dade da rashin aminta da kowanne motsi na maamah din. Bashi da gamsuwa akan abubuwa da yawa sa suka shafeta,shi yasa a kusan komai idanu da zuciyarsa suna akai.

Cikin qasa da minti uku sai gasu kowacce da mayafinta. Dab da zasu fita daga falon ta kirayi sunan huda da yanayin da tunda hudan tazo gidan bata taba gani cikin muryarta ko sautinta ba. Fuskarta a dinke ba fara'ar nan da suke kwana suke tashi da ganinta akan fuskarsu

"Kada ku wuce ko ina,daga can ko dawo gida,zanwa driver magana zai biyo bayanku,karku wuce awa daya......." Idanu huda tadan zuba mata,sai kuma kawai ta gyada kai mamakin sauyawar maman tana kamata. Tasha musu alqawarin fa zata kaisu.......sai kuma daga baya tace ai wani uzuri ne ya taso sai bayan wani lokaci,duk da ta lura akwai permanent driver a gidan da yake zaune baya aikin komai.

Yana zaune daga cikin motar saidai qafafunsa suna a waje ba'akai ga rufe masa murfin ba suka fito. Yadan daga kai ya kallesu,dukkaninsu suna kama da ita saidai qaramar ta fisu daukan kamanni sosai da ita. Mamaki kadan yana dan kamashi na ganin banbanci muraran tsakaninsu. Dukkansu da alama suna da sauqin hali da kuma tarbiyya sosai,don ba wanda ya gaidashi a tsaye a cikinsu saida suka rusuna

"Ta fita zakka kenan" Ya gayawa kansa da kansa yana sauko qafafunsa qasa ya fito waje.

"Abdulgaffar" Ya kirayi shugaban tawagar tsaron nasa,ya matso da gaggawa yana rusunawa

"A cire mota daya a sakasu a kaisu gida" Ya bada umarni hankalinsa

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login