Showing 144001 words to 147000 words out of 557259 words

Chapter 49 - πƒπ”ππˆπ˜ATA BOOK1 AND 2 HAUSA NOVEL

HUGUMA   

03 Nov 2025

463

gagarumar barauniyar data yasheni tas......bama ni ta yasheba tukunna......ta taba dukiyar kamfanin jadda ne!".

Zaro idanu mato din yayi waje yana janye jikinsa baya da sauri kaman yaga wani abun tsoro tattare da mika'il din

"Anya yau bakasha barasar da kanka baya dauka ba?,kasan maganganun da kakeyi?,barauniya fa kace,kuma macace?,sannan data tashi dukiyar Muhammed jadda ta kwashe?" Ya qarasa maganar kaman zaiyi ruku'u. Ba kuma ruku'u din zaiyi ba,kawai yayi hakanne don ya samu damar ganin fuskar mika'il dake zaune sosai,yanason kuma samun tabbacin maganar haka take ko kuma akasinta.

"Duk yadda kaji ka sake kuma fada hakanne" Ya fada a galabaice yana tsananta fatan samun mafita daga wajen mato.

Ga mamakinsa sai yaga mato ya juya yana neman hanyar fita daga dakin. Da wani irin hanzari mikail ya miqe ya damqo rigarsa yayi qarfin halin jawoshi baya sannan yasha gabansa

"Ina zakaje kuma?" Kicin kicin yayi da fuska

"Ka dauko bala'in da yafi qarfinka ai me gida,ni kuma bani da wani gatan da zan iya tareshi,kaga gwara na yiwa kaina qiyamulallaili nasan nayi". Sakinsa mikail yayi har yana taga taga kaman zai fadi. Cikin fusata da fushi yake duban mato,yayi taku biyu a gabansa sannan ya tsaya yana sake kallonsa

*D U N I Y A T A*

*_H U G U M A_*

PAGE 78


"Kai butulu......na dade da sanin alaqar bariki bata da riba.....kuma bata wanyewa lafiya qalau.....amma inaso ka sani.....ni mikail baka isa ka gwadamin wannan halin ba saboda yadda kaci a jikina,komai ka zama ta silata ne.....to ga hanya nan......kana iya tafiya......amma ka sani,wallahi.....wallahi duk abinda zan shiga zan bada sunanka da tabbacin tare mukayi komai".

Ji mato din yayi kaman ya debo qarfe ya jibga masa saman kanshi,sai ya koma ya sulale ya zauna

"Ya zakayimin haka oga?,kasan tun safe naga qishin qishin abun?,ya baza jaridu da jafafen yada labarai?,amma ban taba tunanin kaine a ciki dumu dumu ba?"

"Mune dai a ciki,kuma zanyi maka haka muddin kaima kayimin hakan". Ya bashi amsa kai tsaye yana duban tsakiyar idonsa.

Wata wawiyar ajiyar zuciya ya sauke yana yin collapse. Nadama da dana sanin taba sanin mikail a rayuwarshi tana sauko masa. Shikam ina zai iya tarar case da Muhammed jadda?,wanne ganganci ne ma zaiyi saken da koda sunansa zai shiga list na sahun wadanda ake tuhuma.

Shuru yaci gaba da wanzuwa a dakin tamkar dukkaninsu ba xasu sake magana ba kafin mato ya magantu

"Ita yarinyar wacece ita?,zaifi kyau kabi sawayenta ka bincikota ka damqawa jadda ita a sauqaqe su tuhumeta". Wani banzan kallo ya watsawa mato

"Inda nasan ita din wace da ta yaya ma zan batawa kaina lokaci ina neman shawarar butulu irinka?......tun haduwata da yarinyar na karanci tasha banban da sauran yammata dama mata gaba daya.....tun daga yanayin kyau siffa da kuma jan ajinta......bata sake shallake tunani ba sai a yau dana karade dukkan guraren da muka saba haduwa ko na saba ganinta amma na kasa zaqulota,......ta shafe dukkan wani footprint nata,bani da sauran hanyar da zan iya lalubota".

Shuru mato yayi abun yana tsimashi shima. Duk iya yawan duniyarsa bai taba cin karo da abun mamaki irin wannan ba.......duk budewar idanunsa da kuma son duniyarsa baiga gangancin da zai sanyashi tunkarar fada ko jayayya da mutum irin muhammad jadda ba.....hakan daidai yake da saida rai.....daidai yake kuma da Rungumar mayunwacin zaki. Amma irin wadannan maquden kudaden kuma ace diya mace ce ta diba?.

"Me afkuwa ta afku yallabai.......yanzu lokaci ya qure ya kuma matse da zaka tsaya nemanta da bayyanar da gaskiyarka.....don koda ka samota dinma ka gabatar musu da ita to ba shakka dole saika rasa aikinka.....na tabbatar zasu sallameka ne". Wannan maganar ta mato ta sanya gumi tsatstsafowa mika'il. Ya koma baya yana zama sosai tare da kamo habar rigarsa yana sharce gumin goshinsa.

"Don ubanka mafita nace ka bani bawai ka dinga haskomin makomata ba" Ya fadi da mugun tsaron ci gaba da jin sautin xai rasa gurbin aiki da kamfanin jadda diamond rashi na har abada,bayan a nasa mafarkin yana hangoshi ne wataran a kujerar CEO din ma gaba daya yana juya nasa kamfanin diamond din.

"Mafita kam na samota......amma sai idan ka amince.......zaka juya hankalin kowa kayi wasa dashi.......ka kuma binne batun kwashe kudin asusu ba tare da kowa ya fahimta ba".

Kaman an watsa masa ruwan sanyi haka yaji rahama tana sauka a zuciyarsa,baisan sanda ya kama hannun mato ya riqe qam qam ba abinda bai taba yi ba tsakaninsu

"Dama za'a samu irin wannan hanyar na kasa yarda da ita mato?,maza gayamin......gayamin don Allah".

Hannunsa ya zame yana mamakin yadda yau masifa da bala'i suka sanya ubangidan nasa zama maqasqanci a gabansa.

"Caca......a caca ne kawai zaka ciyo maquden kudaden da zaka iya cike babban gurbin da zai sauke fushin me jadda daga kaso dari zuwa ashirin". Ido ya zubawa mato alamun me gama Fahimtarsa ba.

"Nasan baka gane ba ko?,me gida......kana da nasibin da muddin ka zauna teburin caca saidai ka kwashe badai a kwashe ka ba,tunda kake baka taba zama teburin caca an cinye ka ba tsahon shekarun daka dauka,saidai ma ka tashi da gwagwabar ribar dake lunka arziqinka.......wannan zaman da za'ayi a gobe babban zama ne......akwai manyan gidadawan masu kudin da basu gama wayewa a sabgarba.....basu kaika qwarewa ba,sun sanya mugayen kudade masu nauyi cikin cacar saboda romon bakan shigowarka cikinta da nayi musu da yawan kudade masu nauyin gaske.......kudin da kowanne zai zuba ba qarami bane me gida......kuma ina da tabbacin kaine zakayi nasarar wawashesu......ka zuba kudade sosai ka saki jiki don ka sarqafo dukkan abinda zasu zuba.....bana jinka.....nasan da qwarewarka.....na kuma yarda dakai".

"Nima na yarda da kaina" Ya fadi kai tsaye cikin confidence da kuma yarda da cewa lallai ba shakka waraka tazo. Rungume mato yayi yana jin tsananin farinciki kafin ya sakeshi yana cewa.

"Muddin muka gama da wannan,na rantse da sarki Allah saina nemo yarinyar nan......saina nuna mata cewa ita din ba komai bace cikin duniyar bariki,sai na bar mata tarihi,saina sanyata tayi danasanin zuwanta duniya!!".

Tunda gari ya waye yake kwance kawai lamo,ita bame bacci ba hakanan ita ba idanunta biyu ba. Su biyu ne a dakin tun bayan wucewar nadra da haneefa makaranta,tana daga parlor huda na cikin uwar dakin qudundune a bargo da sunan bata da lafiya ba zata samu daman zuwa makaranta.

Ta shirya hakanne don tana sanya ran sabreen din zata fita ta barta a dakin kamar jiya,tasha hirar soyayya da hameed dinta,wanda a yanzu duk duniya bata jin akwai sauti ko muryar da takai tasa dadi da daraja.

Amma ga sabanin mamakinta yadda taga sabreen din kwance yana gaya matane ba lallai bane ta fita ba yau din. Tayi tsaki cikin bargon yafi a qirga,tayi juyi daga hagu zuwa dama sau ba adadi. Tana iya ganin yadda wayarta dake qasan filo keta haske alamun kiran hameed wato naseer ne yake shigowa amma tsoro ya hanata dagawa.

A hankali a hankali ta dinga jin duk wata juriya tata tana qarewa,muradinta da burinta kawai shine yadda zata samu taji muryar hameed dinta. Sannu a hankali ta dinga jin hirarsu ta jiya tana dawowa

_akan sonki bana tsoron kowa,zan kuma iya komai a gaban kowa saboda ke....zan iya sadaukar da komai a kanki,zan kuma iya rabuwa da kowa,kefa?,zaki iya?,ki gwadamin wataran_.

Kalaman Hameed kenan ko yaushe a kanta. Muddin zai sadaukar har haka ita me zaya hanata ta sadaukar?. Tambayar data yiwa kanta kenan,abinda kuma ya cire sauran dan tsoron dake ranta ta jawo wayar ta daga ta kara a kunnenta.

Wata wawiyar ajiyar zuciya ya sakar mata kamar qaramin yaro

"Har na fidda rai.....huda kina azabtar dani,kullum kafin na samu jinki sai nasha baqar wuya?,sai na shafe awanni ina lalubenki?,bayan ni ko agaban waye bana iya wofantar dake huda?,koda waye a wajen zan ambaceki zan kuma yi waya dake.....me yasa huda ni bazakimin wannan sadaukarwar ba?". Yadda yayi maganar sai ya bata tausayi sosai,harma taji tana zargin kanta daqin daga wayar tasa tun dazu

"Allah huda idan aka wayi gari na mutu sonki ne ya kasheni" Duk wata tsiga ta jikinta sai data zuba......son da yake mata wai da gaske ne har yakai haka?.

"Kina mamaki kuma kina musu ko?,kinason tabbatarwa?" Cike da quruciya da rashin sanin kan rayuwa ta furta masa

"Eh"

"Nan da kwana uku xan dawo ya kama ranar Monday,zaki yarda na shigo makaranta na daukeki?.....zan kaiki inda zan nuna miki zallar soyayyata a gareki ki ganta quru quru.....kin yarda kinaso ki gani tawan?". Sai ta narke wuya zuciyarta na karkata gason ta gani din. Can qasan ranta kuma fal mamaki,tadai kusa ganin wannan soyayyar da yaketa faman zuguiguita mata ita......ta kusa ganin soyayyar nan dai da takeji anata magana a kanta.

"Zan miki tanadi na musamman,zaki gani da idanunki.....daga ranar nasan ba zaki sake musu shakka ko kokwanto ba". Janta yayi zuwa cikin hirar sosai duk da sama sama take amsa masa a darare amma hakan bai dameshi ba,sake jan ra'ayinta kawai yakeyi,yana kuma sake dulmiyata cikin kogin qaunarsa.

Kadan kadan takejin motsi daga dakin,to amma sai kunnuwanta sukafi tafiya zuwa tsakar gidan gidan nasu. Don ta tabbatar huda bacci takeyi ko sanda ta fito,ta share wannan maganar tana dauko wayarta ta lalubi number jib.


*D U N I Y A T A*

*_H U G U M A_*

PAGE 79


"Allah dai yaja kwana hajjaju......our young hajiya" Jib din ya fadi cikin fara'a.

Karamin tsaki taja tana kauda zancan,haka kawai ita batajin komai akan kudin,bata kuma jin wata walwala. Duk wani tsari da jib din yakeyi mata tana jinsa ne kawai,don nata lissafin duka ba'a wannan bangaren yake ba.

Uwa uba shi Kansa jib din bataji ya tsarawa kansa komai ba,ita kuma yanzu su dinne a gabanta da sauran yara marayun nan da take kwana dasu ta kuma tashi dasu cikin ranta.

"Ka sameni gidan marayun nan,zamu qaraso nida busari" Ta bashi saqon a taqaice

"Okay to ba damuwa.....amma ke me kika warewa kanki?"

"JIB....ajiye maganarnan haka a gefe,kada kabarmu mu jiraka please"

"In sha Allah" Ya fada mamakin halayenta suna sake ninkuwa a ranshi.

Kafin ta ajiye wayar tahau ta daya sim din data saba neman busari,ta tura masa saqo sannan ta ajiye wayar tana dan furzar da iska daga bakinta gami da zubawa labulen qofar falon idanu kamar me nazari akan yadda aka sarrafashi.

Kadan kadan ta dinga jin kamar dai motsinne daga dakin da kaman sautin murya a can qasa. Tun tana basarwa har ta miqe,ta taka a hankali ta soma nufar dakin.

"Eh" Kalmar da aka fadi qasa qasa ta shiga kunnenta sanda ta yaye labulen dakin. Hasken daya ratso falon zuwa uwar dakin ya ratsa blanket din da take ciki ya kuma alamta mata wanzuwar wani a dakin,sai tayi wata mutuwar kwance zuciyarta tana tsananta bugawa ta latse wayar tana turata tsakanin katifar da bagon gadon. Daqyar take iya hadiyar yawu saboda tsoro,tun yaushe nema aka shigo bata sani ba,kada dai ace ta jima a tsaye tana jinta?,wannan tunanin kadai ya sanya jikinta jiqewa da gumi kamar an watsa mata ruwa.

Hannu ta sanya ta yaye bargon,sai ta runtse idanunta

"Keda waye kike magana?" Sabreen ta jefa mata tambayar tana zube mata idanun nan nata masu kaifi.

"Magana kikaji yaa sabreen?" Shuru tayi dajin tambayar datai matan,sai ta girgiza kai alamun aah bayan ta gama qare mata kallo

"Wannan gumin fa?,ko zazzabi kikayi ya sauka?" Ta sake jefa mata tambayar amma wannan karon da salon son kamo abun farauta

"Eh.....eh nima haka naji" Idanunta ta maida ta lumshesu sannan ta bude. Ta gama bata hint,ta kuma gama hada dukkan wasu abu da takeso,ta sanyata a ajujuwa kuwa tun daga sauyawarta zuwa yau,kuma ta fadi a kowanne aji......tana jin sunzo matakin qarshe ita da ita,sai ta sake mata blanket din,ta juya tana takawa a nutse zuwa inda take adana kayan wankanta ta diba tana fita a dakin.

Da wani malalacin kallon ta bita har ta gama ficewa,haka kawai taji kaman akwai wani abu ba daidai ba

"Idan ma akwai.....idanma kuma ta gane aiba wan sabon Allahn kikayi ba" Wannan tunanin ya bata qwarin gwiwa ta tabe baki,ta maida kanta filo tana jin yadda zuciyarta ke bugawa sosai,daga bisani kuma ta koma tunanin hirarrakinsu da hameed kaman yadda ta saba.

Cikin qanqanin lokaci suka isa babban gidan kula da marayu,wanda yana cikin gidajen da suke karban kaso mafi tsoka daga dukkan abinda ta samu.

A yau din kabakin arziqin data kai musu ya faranta ran kowa. Hakanan list da tayi na abubuwan da zata aiwatar musun ya sanya kowa kokwanton anya da gaske take?. A duka shekarunta ina taga adadin wadannan kudaden?. Ayyuka ne da zasu canza fasalin gidan gaba daya ya canza cimarsu harma karatun yaran gidan. Tsari ne kuma data dauki sunayen 'yammatan ciki da suka isa aure suke da buqatar tallafin kayan daki da kayan kitchen harma da suturar fitar biki. A ranar gaba daya gidan a yamutse yake da tsananin mamakin ayyukan da tace zatayi din. Saidai daga bisani shigaban gidan ya basu nutsuwa ta hanyar fadin

"Ta iya yiwuwa 'yar wani hamshaqin attajirin ce mu bamu sani ba ta bad da sawu,ko daga suturar jikinta da fatarta zakasan cewa kaman hakan zai yuwu,kudai godewa Allah daya turo me dauke mana damuwarmu koda yaushe,gashi a wannan karon bayan tallafin data saba bayarwa zata mana aikin da mutanen dake da ikon yi masu yawan gaske suka gaza yi mana......zata mana aikin dana tabbata muddin ya tabbata matsalolinmu masu yawa zasu kauce".

Ta yita share qwalla me yawa a hanyar komawa gida,yaran suna mata gizo cikin idanuwanta. Wato maraya a wannan zamanin daidai yake da wani abu maras alfanu cikin al'umma muddin ba dukiya aka mutu aka bar masa ba?,hankula da idanuwan al'umma duka sun toshe?,me arziqi shine mutum?,me arziqi shike da amfani?,idan yau kana da abun hannu kowa qoqarin rabarka yakeyi?,kowa so yake ya hada dangantaka dakai komai qanqantarta?,kowa so yake ace kuna da alaqa kunsan juna?.

Anya mutane a yau kuwa sunsan iya adadin bala'i da masifar zubar ruwan hawaye a idanun maraya qwalli daya tak a garesu?,anya suna tunawa da girman haqqinsa da ma'aiki yayi gargadi da jan kunne akai?. Bibo ta fado mata a rai,saita dinga juya kai kawai,matar tana daya daga cikin mutanen da zasu azabtar dasu tsananin azaba inda Allah ya qaddari mutuwa ta dauke ummeensu a sanda suke dukkaninsu qananu......arrahmanu arraheem ubangiji da baya hadawa bawa abu biyu......sai ya dauke musu sanyin idaniyarsu a sanda ita nata hankalin da qarfin ya fara kawowa. Ya sanya mata qarfin zuciya da kuma qarfin halin iya tare musu tashin hankali da masifa komai girmanta,ya sanya rainonsu da kulawa dasu a hannunta tun bata wuce itama a raineta ba.

(YAKE BAIWAR ALLAH!....tabbas riqo yana da wahala.....riqo yana da daci yana da nauyi,amma kisani......DA KI RIQE YARO KI AZABTAR DASHI GWARA KI TUN FARKO KICE BA ZAKI KARBA RIQON BA yafi miki sauqi da mafita har a wajen Allah muddin kikasan zuciyarki ba zata iya jure da kiyaye wannan amanar ba.....AMMA WALLAHI
WALLAHI
WALLAHI kikayi kuskure kika karbi riqo don ki burge ko kada a zargeki,to wallahi idan nace KINA CIKIN MASIFA ma kadan ne.....ba zaki san girman bala'i da kike ciki ba sai ranar gobe qiyama......hatta ubangiji bayason kuka maraya shi da yayi kowa yayi komai ya kuma qaddara hukuncin maraici a kansa
IDAN KINSAN akwai maraya yanzu haka da kike banbanta riqonsa dana 'ya'yanki.....to ki gaggauta yiwa kanki hisabi tun kafin ranar zuwan hisabin na gaske.......idan har kinsan akwai maraya yanzu haka a hannunki.....to ki gaggauta gyarawa kafin ki barwa 'ya'yanki masifa da bala'in da zaiyita bibiyar rayuwarsu,kiyi qoqari kifi qarfin wannan tsokar dake qirjinki wadda ake kira da ZUCIYA.....kiyi qoqari kifin qarfin wannan maqiyin naki wato SHAIDAN.....Allah ya bamu ikon fin qarfin wadannan ababe guda biyu ameen summa ameen).

"Kaini gidan malam" Ta fadiwa busari a nutse,wanda bai musa ko ya tambayi ba'asi ba ya karkata akalar motar. Zuciyarsa shima cike take da farinciki,don yana cikin alherin tashi daga dan adadaita sahu,zuwa mamallakin shago sukutum da guda a babbar kasuwar kantin kwari nan da sati uku kacal.

Kusan duk wanda ya kwana ya tashi a kamfanin yasan da faruwar komai. Yayin da sake fitar labarin boyayyar badaqalar data afku qasa da wasu awanni ya sake sanya mutane da yawa na kamfanin mamaki musamman wadanda basu san komai ba,basusan kuma abinda ake ciki ba.

Kowa da kansa da kansa ya yiwa hisabi,don shigowar boss Muhammad kamfanin ya sake sanya kowa shiga taitayinsa. Masu zuba kunnen abinda

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login