Showing 414001 words to 417000 words out of 557259 words

Chapter 139 - πƒπ”ππˆπ˜ATA BOOK1 AND 2 HAUSA NOVEL

HUGUMA   

03 Nov 2025

540

qaraso?,sai kuma idanunta sukayi mata kyakkyawan gani.

A nutse suke takowa da wani irin qyallin da idan ka kirashi na amarci bakayi laifi ko kuskurr ba. Kanta yana aje saman kafadarsa wanda tayi hakanne bisa dole saboda jiri jiri data fara ji. Da farko taqi ganin zasu shiga jama'a ne,amma daga baya dole ta kwanta din saboda indai batayi hakan ba tana iya faduwa ko ya dagata ya dauketa in ya tabbatar hakan zata faru. Tsakiyar qirjinta kuma wani abune ya dunqule mata,tana jin kaman amai ne yake taruwar mata,saidai bata gasgata hakan ba ganin lafiya qalau take ai,bataci wani abu daya bata mata ciki ba bare tace.

"Na shiga uku......la haula wala quwwata" Maamah ta fada tana jin yanayinta yana hautsinewa gaba daya.......

"Anya.....anya.....anya?" Ta dinga maimaitawa cikin zuciyarta tana tsoron furta abinda ke cikin zuciyarta.

"KINYI KUSKUREN ZABOTA" Maganar bokan ta sake maimaita kanta cikin kwanyarta.

"Bazai faru ba.....saidai ita tayi danasani" Ta fada tana furxar da iske me qarfi daga hunhunta zuwa bakinta.


_uhmmmmmmmmm_




*_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_*
08187255862




𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓 𝐀
_Zafafabiyar_

ΜΆBΜΆOΜΆOΜΆK ΜΆ2

β±§Ι„β‚²Ι„β‚₯β‚³

π™‹π˜Όπ™‚π™€ 108




108


Idanunta ta dan lumshe kana ta budesu,tana iya hangen maamah dake farko,farouq daga gefanta kadan yanata amsa waya,anni daga can gaba ita amna. Musaddiq da saddiq ne bata hango ba,ko kuma yadda amai din yaketa faman mata kai kawo tsakanin cikinta da maqogorone ya hanata ganinsu oho

"Amai nakeji" Ta fada qasa qasa kanta a kafadarsa,don ta tabbatar zai iya kufce mata tsaf kafin sukai wajensu. Hannunsa yasa ya riqe hannayenta sosai,kafin ya sake riqe tafin hannunta da kyau yana cewa

"Ga can hanyar washroom,zaki iya qarasawa?" Ya tambaya a tausashe. Kai ta jinjina masa

"Oya.....be fast" Ya fada yana mata riqon da zataji dadin tafiyan da kyau,duk da ba haka ranshi yaso ba,yaso ace ta bari ya rage mata wahalar tafiyar kawai.

Murmurshi farouq ya saki,daga inda yake yana kallonsu,duk kuma da bayajin abinda suke fadi amma yadda yake kaffa kaffa da ita ya tabbatar masa dude dinsa ya qarasa zarewa......hauka tuburan na soyayya yasan ya sameshi,baisan kuma ya za'a qare da lamarin kula da gold da diamond ba,lokaci yayi na daukan sabbin ma'aikata kenan amintattu na kusa kusa dasu.

Ta bangaren maamah kuwa ta shaqa iya shaqa,wannan karon kasa riqe ashar dinta tayi sai data furtata,ta furzar da iska tana dan dukan gefanta. Ta yadda duk macen data taba bariki.masifa ce,abune a jininsu da komai dadewa sai an saida hali. A nata tunanin sabreen tana sane tayi hakan,tunda ta ganta,tayi ne kawai don kada su hadu da fu'ad din kai tsaye,tayi ne kawai don ta nesantata dashi,daga qarshe kuma tayi ne kawai don ta gwada mata tata iyakar.

"Zakiga taki iyakar a sanda kika qare a gidan tabbabbu mahaukata" Ta fadi a fusace tana qoqarin danne abinda takeji. Tanajin kaman ta saka hannu aka ta fasa ihu,tana jin kaman yanzu yanzu ta bude ido taga babu sabreen an shafe babinta daga tarihin rayuwarsu.....akwai lokaci abinda zuciyarta keta nanata mata kenan. Ta yarda da hakan,to amma shi lokacin yaushe xaixo?,amsar tambayar da bata santa ba kenan.

A nutse ya koma baya yana qare mata kallo bayan ta gama aman tana wanke kyakkyawar fuskarta da take wani fresh da ita. Ta kammala ta gyara hijab dinta sannan ta juyo,saidai ba zato ba tsammani ta sameshi tsaye yana qare mata kallo kamar yau ya fara ganinta.

Qaramar harara ta watsa masa da fararen idanunta,sai ya daga hannayensa sama alamun surrender sannan ya hade tafukan hannayensa alamun ban haquri kafin ya sauke yace.

"Kinci wani abune da yake baki reaction?" Ya tambaya da yanayi na seriousness. Dan shuru tayi tanason tunawa,saidai kuma iya saninta ba wani abu da taci din. Kai ta girgixa masa tana tsane hannunta da towel din daya miqo mata. Taku biyu yayi ya matso gabanta,ya cire hannunsa a hankali yana taba fuskarta kafin ya xare ya xurashi ta qasan hijabinta yana tattaba dogon wuyanta. Abinda ya dauke mata numfashinta kenan na wucin gadi,don bayan jin temperature na jikinta sai daya hada da tsokanota har sai da taja baya tana ture hannuwansa. Jirin da taji yasa ta tsaiwa tadan dafe kanta,kaman walqiya yakai gareta tana riqota jikinsa.

"Idan bazai yiwu ba mu wuce Seychelles......ki qara hutawa a can saimu samesu......xatafi burgeki akan Maldives" Ya qarasa maganan cikin kulawa. Fararen idanunta ta sake watsa masa. A abinda take gani cikin idanunsa ba hutawa zai barta tayi ba,saidai ya qara mata lalura ne kawai. Batasan inane Seychelles ba.......iya Maldives ma ya suka qare ya kaita qasan ruwa?,ita kuma Seychelles ai qila cikin cikin kada(crocodile)xasuyi rayuwa. Ta fahimci a son ranshi kowa ya mutu a barsu su rayu su kadai.

"Muna sake makara" Ta fadi a shagwabe kaman xata narke. Abunda yayi masifar qayatar dashi,har sai da yaja baya yana gwada yadda tayin. Dariya taso qwace mata amma tayi hanzarin kauda kanta,sai kawai ta dauki wayarta ta soma takawa zata tafi ta barshi.

"Ganganci ma kenan" Ya fada yana zaburowa ya daidaita tafiyarshi da tata.

Wannan karon farouq suka fara taraswa,suns hada ido da farouq din dai ya wani basar,yana dauko wannan tsohon dabi'an nasa na miskilanci wa mutane ya azawa fuskarsa.

"To waye ya damu dakai?" Farouq ya fada yana jifansa da harara,ya maida kallonsa ga sabreen da kunya ta fara mata qawanya. Tanaso ta zame hannunta ne daga nashi amma yaqi bata damar hakan

"Madam barka da zuwa......inajin xamu iya wucewa ayi miki screening,minti arbain ya rage lokacin tashin yayi dama" Farouq ya fada a girmame.

"Izinin wa ka nema da xaka kama yiwa mutane magana da mata?,if kana da wani important issue da kakeso lallai kayi magana da ita a kai ba gani ba?,dani zaka fara magana na nema maka izini ai ko?" Fu'ad ya fada sounding seriously. Dariya ta kama farouq sosai,yaja da baya ya kama kabbara kafin yace

"Dole ne kam,dole ne na nema izini ai.....don ko bugeni kayi na fadi ai ba'a shari'a da wanda ba cikin hayyacinsa yake ba......madam kiyi haquri kinji......wannan zama dashi sai me haquri".

" Na rantse harda Allah farouq kana qarawa kanka da kanka kwanakin bikinka ne" Fu'ad ya fada da gaske gaske,abinda ya sanya farouq ya fara shiga taitayinsa kenan. Yasan halinsa,idan har yace abu yasan ta yadda zai maida abunnan yadda yace din,shi kuwa wannan ruwan madarar soyayyar da yaga ana aiwatarwa shi a haramta masa wanzuwar tasa ai anyoshi......gwara yaje ya dandana shima kam.

"Nif bance komai ba.....daga welcoming naku?.....madam ki qarasa ciki"

"Ba ruwanka......banason kana min magana da mata fa,kana takurata,banaso kana sata magana.....she's sick".

"Sick?" Farouq ya tambaya,daidai sannan taji xamanta tsakanin drama din farouq da fu'ad ba nata bane,ta sabule hannunta ta qarfi ta soma yin gaba tana barinsu.

"Dude......ba sake lahani kayi mata ba ko?,wallahi wannan karon anni ba zata barka ba". Harara ya wurga masa

"Wai sa'anka ne ni farouq?"

"Inafa.....mutumin da yaje inda ni banje ba?" Murmushi ya saki,yasan da gaske farouq ya damu dashi da lamarinsu ne gaba daya,kowacce tambaya yana yinta ne don tabbatar da lafiyar kowannensu.

"Juts a fever" Ya maida masa a taqaice idanunsa suna kan sabreen data iss gaban maamah ta tsugunna tana gaidata.

"Allah yasa qwallonka ne ya fada a raga......zanso naga first born na gold runner" Sosai maganar taja hankalin fu'ad,sai ya kasa cewa farouq komai yadai bishi da kallo. Zuciyarsa bugawa takeyi so fast amma yanason dakatar da ita. Bayason maganan farouq ta masa tasiri,ya tasirantu da cewa shine kuma bashidin bane.

Sautin dariyar maamah a sanda take tsugunne gabanta tana gaidata shi yaja hankalinta,ta daga kanta a hankali ta kalleta. Qaqqarfan murmushi takeyi da gaske wanda yafi kama da dariya

"Kin gama naki......ni kuma zanyi nawa" Abinda tace da ita kenan kawai tana maida kanta ga wayarta.

"Tashi kije yarinya" Hakanan ta samu qwarin gwiwar aje mata murmushi itama sannan ta yunqura ta miqe tana fadin

"Hasbunallahu wani'imal wakeel,ni'imal maula wa ni'imannasir". Da kallo maamah ta bita sanda take takawa tana barin wajen. Ta aje mata shakka sosai cikin ranta,ta sani itadin kuma shaida ce,ba kasafai murmushin yarinyar yake xama alkhairi ba,so amma koma meye wannan karon ta shirya kawar da ita me gaba daya idan ta kama ayi hakan.

Amna ce ta rugo da sassarfarta ta kawo mata runguma,abinda ya kusa sabbaba faduwarsu gaba daya,Allah ya kawoshi ya sanya hannu ya tareta ta fada hannunsa.

"Ki kula" Ya fada adan dake sannan ya maida dubansa ga amna.

"Be soft with her amna" Kai ta gyada a sanyaye kunya tana kamata. Kwanaki ne kadai tayi bata ga adda sabreen din ba,amma sai taga ta canza mata gaba daya. Wani ajiyayyen kyau na musamman,qamshinta da komai nata ya zama wani na daban


*_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_*
08187255862


𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓 𝐀
_Zafafabiyar_

ΜΆBΜΆOΜΆOΜΆK ΜΆ2

β±§Ι„β‚²Ι„β‚₯β‚³

π™‹π˜Όπ™‚π™€ 109



109



a nutse amna ta riqe mata yatsu,duk da yadda ta fahimci fu'ad din kaman yafi so tabar masa kayansa,to amma itama sabreen ita ta naniqewa,saboda bataso yayi wani abu daban da zai sanyata jin kunya gaban anni. Tayi imani kuma dukka hankali da idanun maamah yana a kansu,nunawa ne kawai ba zatayi ba. Abu guda daya daya tsaye mata a rai,ya gaza barin kwanyarta ta huta duk da yadda takejin jikinta shine dariyar maamah din. Ta gama karantar kowanne taku da motsi na matar......ta kuma sake sallamawa al'amarinta daga labarin fu'ad din. Ta tabbatar ba wata halitta da bazata iya cutarwa ba tunda har ta iya cutar da mijinta da kuma d'anta. Directly or indirectly tana farautar rayuwar 'ya'yanta ne ba tare da tasan hakan ba. A ranta taji dole ta qara takatsantsan da ita fiye da baya,sai taji kaman a baya ma kulawa da kiyayewa al'amuranta da takeyi kaman tayi sakaci,tabbas inda tasan wacece ita har haka......inda tasan wacece ita irin sanin da tayi mata a yanzu lallai ba shakka zata kiyaye komai nata fiye da yadda tayi a baya.

"Hannunki dumi adda.....kaman akwai zazzabi a jikinki" Amna ta fada cikin kulawa dab da zasu qarasa kusa da anni. Kai ta girgizawa amna din tana sanya murmushi saman fuskarta

"Ba wani me yawa bane......zai sauka in sha Allah,karki gayawa anni ki daga hankalinta" Dan jim tayi kaman ba zata amsa ba,don bataga dalilin da mutum baida lafiya ba kuma sannan yace kada a fadi.

Hannu anni ta miqa mata sanda take shirin durqusawa ta gaidata.

"Dawo nan ki zauna" Ta fada qasan ranta wasai da farinciki. Iya yadda taga fu'ad din ya koma a 'yan kwanakin da baya kusa dasu kadai ya bata tabbacin lallai komai yana tafiya daidai,ba fu'ad kawai ba.....hatta sabreen din ta canza mata gaba daya. Fatarta wani glowing kawai takeyi,hakanan idanunta sun qara haske da kuma girma.

Tsananin kunyar anni takeji kaman zata nutse......ko kusa ko alama yadda takejin nauyin anni yana kamata batajin koda kusa da haka akan maamah,bata ce kuma ga dalili ba.

"Sai kuma ka buge da sacemin diya ko?" Anni ta fada tana duban fu'ad daya gaidata. Karon farko shima kunyar anni ta kamashi,tattausan murmushin nan nasa da anni ta jima bata gani ba ya subuce masa,yasa hannunsa ya shafi baqa sidik din sumarsa da kudin da take lasa yayi jarin mutane da yawa.

Matsawa amna kadan tayi kusa da anni tana rada mata sabreen din zazzabi takeyi. A nutse amna ta dubi fu'ad

"Me ya samu ameenatu?" Fararen idanunsa ya sauke kan fuskar sabreen din sannan ya dubi anni.

"Dan zazzabi ne dazu da zamu fito ya sauko mata......nace ma muje ta karba magana but ta dage wai zatayi managing" Kai anni tadan kada kadan.

"Manage da ciwo?......to Allah ya sawwaqe,idan muka sauka dubai bai tsaya ba sai taga likita,ba kyau zama da ciwo ai"

"Ameen" Ya amsa yana satar kallon sabreen din. Jinsu kawai takeyi,amma wani sabon amanne suketa kokawa dashi.

"Bani ruwa amna" Ta fada a hankali tana tunanin idan tasha ruwan zai fada mata. Motsin bakinta kadai ya kalla ya fahimci me tace,ya matso a hankali bayan ya karbi gorar ruwan hannun jordan dake nesa kadan dasu,ya bude mata ya tako inda take yana tsugunnawa saman qafafunsa yakai robar bakinta.

Tsam maamah ta dauke idanunta tana kullesu gaba daya,qirjinta na sake bugawa sosai tana jin kaman haki yanason kamata. Zazzabi?.....wanne irin zazzabi bayan ba'a Nigeria ake ba ballantana ace malaria ce?,wannan tsugonnan bata ruwan......ko ita da take uwarsa ba zata iya tuna ranar daya tsugunna haka gabanta yana bata ruwa ba......lallai dole ta batar da yarinyar nan bat daga duniya.

Kai ta girgiza masa alamun xata iya sannan ta karba da kanta. Kurba uku tayi taji kaman ya isheta,sai ta miqa masa robar.

"Is okay?" Ya fada yana motsa labbansa a nutse idanunshi a kanta kaman me tsoron kada ta bace masa. Kai ta gyada a kunyace tana saka kanta cikin mayafinta,bataso batason wannan kallon,halakata yakeyi gaba daya.

"Kai Muhammadu" Maamah data gaza jurewa ta qwala masa kira,tana jin ya kamata ko yaya tayi wani abu da zata shiga lamarin ciwon don samun report da zai bata daman aiwatar da duk abinda ya dace da gaggawa.

Tsam ya miqe yana amsa mata,sannan ya fara takawa gabanta sanda farouq ya iso yana gaya musu lokacin tashinsu yayi.

"Sakamin takalma na......bazan iya durquso ba" Ta fadi tana qoqarin saisaita fushinta. Baice komai ba ya tsugunna gabanta yana tura mata takalman,ta fara saka qafafunta a ciki qirjinta a quntace.

"Ita matar taka me ya sameta da ni bani da mutuncin sanin komai saidai naji daga bakin bare?". Daidai sanda ta gama zura takalman sai ya zare hannuwansa yana shirin miqewa.

" Zazzabi ne kawai......shima din dazu ne yazo bawai a kwance take ba".

"Zazzabi?,tana iya cin abinci?" Kai ya gyada mata a nutse don baisan me zaice mata ba,ita sabreen idan ya sakata sahun masu cin abinci ma ya zalunci sakamakon da zai gayawa.me bincike.

"Akwai tashin zuciya?" Ta sake tambaya cikin bin qwaqwafi da son tabbatar da zarginta. Kai ta girgiza mata alamun a'ah.

"Ciwon mara ko ciwon ciki fa?" Ta sake tambaya tana kafeshi da idanunta. Kansa ya mayar gefe kafin ya dawo da dubansa kanta.

"Ban sani ba maamah.... Duka duka zazzabin na awa daya ne".

" Eh dama da irin sakacinnan naku sai ciki ya shiga ya fice abinsa ma baku sani ba......banason ganganci da rayuwa shi yasa nake tambaya,dama wani aikin ai sai uwa ita data damu da rayuwar 'ya'yanta damuwa ta haqiqa.......tana yin amai ne?" Tambayarta ta qarshe da yaji yakai bango,hannuwansa suna zube a aljihun wandonsa sai kawai ya zubewa maamah kallonsa. Karon farko kenan tun bayan shudewar shekaru ashirin kusan da hudu rabon daya kalleta tsakiyar qwayar ido irin haka. Komai daya danganceta yaji yana dawo masa.......gaba daya tambayoyin nan nata basu zama komai ba face suna sake bude masa wani abu da yake zargi a kanta.

Duk yadda ake maganar kwarjininsa bata taba yarda da gaske yana da wani irin kebantaccen kwarjini ba sai yau. Idanunsa sukayi mata wani irin nauyi,sai taji tana daburcewa.

"To Allah ya kawo sauqi,sai a bincika ai aji meye,ko tsohuwar malaria ce" Ta fada tana miqewa tsaye,wanda hakan bai sakashi dauke kallonsa ba a kanta,har sai da yaji muryar farouq

"Dude....." Waiwayawa yayi yana dubansa,sai ya nuna masa agogon dake daure a tsintsiyar hannunsa,wannan shine ya ceci maamah daga irin kallon nasa ya juya yana nufar farouq din.

"Wai......ka jini da yaro?,haka yakewa mutane?......muje zuwa,na rantse har da Allah muddin abinda nake zargi ya tabbata ga yarinyar nan bazan taba aminta na hada jini da ita ba......muddin wani me rai ne a jikinta ni mariyatu bazan bari ya taka duniya ba" Ta fadi tana cike da fatan ya zamana ma ba abinda take tunani bane.

Amna najin takunsa a bayansu ta zame hannunta daga na sabreen din ta qara sauri zuwa gaba ta cimma anni abinta suka jera tare. Matsowa yayi yana daidaita tafiyarta da tashi,ba zato y dauki hannunsa ya aza saman kafadarta yana jawota zuwa jikinsa.

"Kinga yadda kike tafiya kuwa?,you need my support......dont reject it" Ya qarasa fada yana furzar da iska.

"Inajin body temperature dinki kaman yana hawa......you need medical care........banaso komai ya tabaki duniyata" Ya fadi yana waiwayawa ya dora mata qwayoyin idanunsa. Nauyin nan dai taji,sai tadan basar tana dauke kanta gefe

"Zafin kaman na dazu ne,bai wani qaru ba" Ta fadi saboda batason yace zaa kaita asibiti. Idan tayi ciwo a Maldives ba zata damu ba......amma ciwo tsakanin makka da madina bata son hakan ta kasance,saboda qashene da take da burin xuwa a rayuwarta kafin ta koma ga mahaliccinta.....qasa ce da ta tara tarin shigifar addu'o'i take kuma kuma son tayi bajakolinsu a nan.....ba zataso wani abu ya kawo.mata tsaiko ba. Tana da tarin buqatun da batasan adadinsu ba,batasan kuma kwanaki nawa zata shafe kafin ta gama jerosu ba.

Ba idanun wanda sukayi masa nauyi,a haka suka jera suna taka steps na jirgin har suka isa ciki. Suna shiga din matuqin jirgin yayi salute nashi sannna ya bashi hannu sukayi musabaha ya buqaci magana dashi,wannan ya sanya ta zame jikinta suka jera da amna suna wucewa ciki don samun seat din

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login