Showing 390001 words to 393000 words out of 557259 words

Chapter 131 - πƒπ”ππˆπ˜ATA BOOK1 AND 2 HAUSA NOVEL

HUGUMA   

03 Nov 2025

3482

Mamaki ya sake kamashi ganin yadda ta birkice,yaga dai koma meye duk inda sukaje a gidan zasu dawo su kwana.....amma duka me ya kawo wannan yanayin mara dadi?. Yankewa kansa wahalar tunanin yayi ya juya a salube yana fita a dakin.

Tana zaune daga gefan gadon tana duba hotunan da amna tace ta dauka a wayarta sanda saqon ya isketa. Ta daga kai tana duban musaddiq a mamakance.

"Taje inji maamah" Ta sake maimaita saqon tana zubewa musaddiq dubanta. Tana juya dalilin kiranne da kuma abinda zai iya biyo baya a kiran. Bawai tana tsoron zuwa bane.....babu shakkarta ko dis cikin ranta.....bata wani tsoro ko shayin fuskantarta......kawai tana duba girman musaddiq ne da tabbas zata ce masa yaje yace mata bata zuwa.

"Gani nan zuwa" Ta amsa masa tana aje wayar a gefanta sannan ta miqe tana zura qaramin Malaysian hijab dinta ta taka a hankali tana dosar qofar fita a dakin. Zuciyarta fal saqe saqe,cikin jikinta takejin koma meye ya sanya ta kira BA ALKHAIRI BANE.....koma meye kuma ta shirya fuskantarta.

Tana tsaye ta zubawa qofar idanu tana dakon shigowarta,tana jin kaman tayi nawar isowar.....a haka ta murza qofar ta shigo kai tsaye ba tare data maida qofar ta kulle ba. Kallon kallo suka yiwa junansu me wani irin zurfi kafin maamah ta soma magana.

"Bakisan adadin kuskure da wasan da kikayi da rayuwarki ba sabreen......bakisan gona da adadin iyakokin da kika sanya qafa kika tattaka ba......amma koma meye a yau zan yanke wannan alaqar da kike taqama dashi......yau dinnan.....kuma a nan wajen zan tabbatar miki da tsinkewar igiyoyin aurenki". Manyan idanunta ta maida ta lumshesu a nutse sannan ta budesu.

"In har don wannan ne ni banga dalilin kirana da kikayi ba......wani abune da ke daya ya shafa maamah.....don Allah saboda daraja da mutuncin musaddiq da nake gani na roqeki kibarni na huta..... Allow me to rest.......tsakanina dake ba kare bin damo. Contract ne nace bazanyi ba dama ba tun yau ba,yana da wahalar gaske na yiwa rayuwata hukunci ayi challenge dina a sakani warwareshi......na bar miki contact dinki......na karbi rayuwar qannena kuma akwai abinda yayi saura?" Ta qarasa maganar tana zube mata idanunta wadanda suka fara tunasar da maamah wace ainihin sabreeen din......ta fara juyewa kuma zuwa tsohuwar sabreeen da ake dab da jana'izar halayenta.

Wani irin mamaki maganganunta suka bawa maamah din,ranta ya sake dugunzuma.

"Kina tunanin kinci bulus?,rayuwar yarona zaki gwadawa bariki?,a gaban idanuna zaki gwada aiki a kansa?"

"Wanne yaron naki?" Ta fada cikin calmness.

"Indai wannan ruhin dakike burin mallaka ne kike tunanin nayi wani abu a kai to ki hutar da kanki......banason wata hayaniya akan hakan don bani da sauran buqatarsa a rayuwata".

"Yanzu kuwa zan tsinke duk wasu igiyoyi da suke tsakaninku" Ta fada a zafafe tana sungumar wayarta. Tana jin ya mata tsaho ta jirayi dawowarsa......ya mata tsaho har sai sanda ya dawo gidan ta gwada mata koda magani ko babu akwai sauran power na uwa da zata iya sakashi ya mata dukkan abinda tayi niyya.

Mamakin maamah din ya sake cika sabreeen din. Tanaso ta gogewa matar haddar kanta tsaf.......tanaso ta gwada mata wani abu kansa amma inda akaci sa'a har yanzun da take tsaye bata jin jituwar halayensu shi da ita.....tabbas don a tsukin kafin ta hada karonta tabar rayuwarsu saita aje mata zazzafan darasi.

Mummunan faduwa gabansa yayi sanda kiran ya shigo wayarsa,abinda zai iya cewa ya manta rabon da ya jishi.

"Ya hayyu ya qayyumu bi rahmatika astagis......aslih li sha'ani kullahu fala takilni ila nafsi darfata ainin" Ya motsa bakinsa a nutse ya karantata kafin ya daga wayar ya hadata da earpiece din da ya jawo ya saka a kunnensa,don ba kasafai yake magana da ita a hands free ba.




*_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_*
08187255862


𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓 𝐀
_Zafafabiyar_

ΜΆBΜΆOΜΆOΜΆK ΜΆ2

β±§Ι„β‚²Ι„β‚₯β‚³

π™‹π˜Όπ™‚π™€ 97


97

_An rawaito daga manzan Allah S A W yana cewa"babu wanda zai shiga aljanna alhali akwai qwayar zarra na haqqin dan'uwansa a kansa_

_Bukhari da muslim_


"Muhammadu kana jina?" Tayi lafazin da wani irin kaushi.

"Ina jinki maamah"

"Indai ni uwarka ce dana haifeka.....na shayar dakai nono na har ka zama mutum.....ina umartarka a duk inda kake ka dawo gida yanzu yanzu......a sanda kake shigowar kuwa ina buqatar shaidar sakin matarka sabreeen......ma'ana ka datse dukka igiyoyin aurenka dake wuyanta.....muddin baka dawo ka aikata hakan ba daga yau ka dauka sunanka tsina......". Da wani azama ya latse kiran don bazai iya saurara ba. Sauti mafi muni da zai iya cewa kunnuwansa sun sake saurara kenan bayan tsahon shekaru.....sauti na biyi da ya kusa sanyashi kaman zai zare bayan sautin ALLAH YAYI MASA RASUWA ME BABBAN SUNA.....KUYI HAQURI...a ranar da ake gaya masa rasuwar mahaifinsa.

Subuce masa steering motar yayi abinda ya ankarar da farouq kenan,ya sanya hannu da wani irin zafin nama ya kamoshi yana furta.

"Subhanallah" Da wani irin qarfi. Karbar steering yayi yana qoqarin maida hankalinsa jikinsa amma sai yaji hakan ya gagareshi,wannan ya sakashi gangarawa gefan titi ya tsaida motar yana fita daga ciki.

Numfashi yake ja sosai zuwa hunhunsa yana jin iskar da yake shaqa ta masa kadan,ko tambaya daya ya kasa amsawa farouq dake gefansa,sai daga baya ya fusgi kalmar

"Mu koma gida farouq.....now" Bai musa ba ya bude masa murfin motar,ya taka da wani irin yanayi yana shiga,shima ya shiga mazaunin driver ya kunna motar yana juya kanta zuwa hanyar da suka baro.

Ga mamakinta sanda ta sauke wayar a fusace saita samu idanun sabreeen a kanta da wani irin nutsuwa tana dubanta.

"In don wannan abunne.....ai da basai kin tasoni ba,zaki iya aiwatarwa koda bana wajen" Ta fada tana zama saman stool din dakin tana kallonta.

"Sabreeen tana zaman zamanta aka gayyatota kan abinda bai cikin tsarinta......sabreeen tace bataso.....ba zatayi ba akayi amfani da rayuka uku masu matuqar muhimmanci fiye da nata ruhin aka sakata yin abinda bata taba yiwa wani ba......ta yaya a yanzun saboda ita din ba kowan kowa bace za'a cisgeta daga inda aka dasata?" Kai ta girgiza.

"Yadda aka gayyatoni ba shiri......bazan fita a sanda ban shirya ba,saboda gaba a guji taba rayuka irin na ameenatu din.....da kin kwantar da hankalinki ma zan fita.....amma fa a sanda nayi niyya,a sanda koshi wanda kika hada alaqarmu dashi din bai shirya ba......amma tunda kin zabi na fita a sanda kikeso kaman yadda kika shigo dani a sanda kikeso......inajin ya kamata shi wanda akayi komai dominshi yasan yadda aka qulla abun aka kuma warwareshi.....don nagaya yanamin wani gani gani yana kuma kallona a matsayin makwadaiciyar dukiyarsa......bayan kuma ata nan gefansa akwai uwarmu gaba daya" Tayi maganar fuskarta da murmushi kaman me fadin wasu kalmomi masu dadi. Abinda kenan yake sake qule maamah......yadda qaramar alhakin ke zama tana yaba mata zance duk yadda taga dama. Iya wannan kadai ya isheta hujjar qwace suna da license na zama surukarta. Suruka take nema irin wadda zata juyata kaman d'iyar data haifa,wadda zata bita kaman yadda raqumi yake biyar akalarsa ba saba hanya.

"Kina tunanin ke dinnan qaramar alhaki kina da wani hujja dalilo ko qwarin gwiwar fadan magana akaina d'ana ya yarda?".

"Aah" Ta fada idonta akan wayarta tana dannawa wadda ke sake tsokane idanun maamah.

"Ni bance dole ya yarda ba....amma dai qila wannan zai taimaka" Ta qarasa maganar tana kunna wani sauti wanda sai data waiwayo dashi maamah ta fahimci video ne.

Tayi matuqar kaduwa,ta kuma yi mummunar razana da yadda ta gansu tarwai ita da Hajj harira......rana ta farko da suka fara takawa gidansu dakinsu suna gabatar mata da contract din aurenta da fu'ad. Komai ya fita kaman yanzu ake dauka,da sautin muryarsu da komai.

Boyayyen murmushi ta saki ganin yadda abun ya daki.maamah da wani.irin razanannen yanayi. Boyayyar CCTV camera din data saka a parlor din kenan ba tare da sanin kowa ba. Zama da JIB ya qareta abubuwa da yawa,tun sanda tayi noticing canzawar huda awancan lokacin da Naseer yaso bata ta,ta yanke ta sakata,wanda ita ta taimaka mata taga duk wani motsi na huda.....ya kuma sake qarfafa mata zargin da shi yayi sila ta gano komai.

"Wannan kawai zan nuna masa don yasan cewa bani na kawo kaina rayuwarsa.......ba sonshi nake ba.......ban taba kuma sonsa ba.....banajin kuma zan soshi din.......rabuwa da zaiyi dani kaman ragemin aiki yayi......" Maganarta ta tsaya a nan sanda lallausan qamshinsa ya marabci hancinta.....kaman giftawar walqiya kuma sai gashi a wanze cikin dakin a wani birkitaccen yanayi.

Wani irin kallo da yake saukar mata shi ya sanyata zare idanunta daga kanshi. Wani irin birkitaccen kallo yake mata zuciyarsa na wani mahaukacin bugawa da kalamanta na qarshe da kunnuwansa sukayi katarin ji

"Ba sonshi nake ba......ban taba kuma sonsa ba,bana jin kuma zan soshi din......rabuwa da zaiyi dani kaman ragemin aiki yayi......". Inda tasan girma da nauyin da kalaman sukayiwa qirjinsa tabbas ba zata fadesu ba.

Janye nasa idanun shima yayi daga kanta da suke sake sauya launi saboda bacin ran da yakeji cikin ransa. Yayin da idanun maamah suke zube a kansa ita kuma.....zuciyarta na quna tare da jaddada mata baqar mallaka sabreen din tayi masa da yake kasa sukuni a duk sanda take waje......yake kasa aza idanunsa akan kowacce halitta idan ba ita ba.

Da confidence dinsa ya shiga cikin dakin,yana jin cewa idanma tazo ta gayawa maamah ne bata sonshi don ta sanya su rabu.....ba shakka ta dauko aikin da bazata iya qareshi ba.....a yanxu a kuma yadda yake jinta a kusa da kowacce jijiya ta jikinsa.....ko mutuwa bayajin xaya lamuncewa ta rabashi da ita.

"Gani" Ya fada yana dosana gefan sofa din dakin.

Idanu maamah ta zuba masa tana jin wani irin abu yana birkitata. Ga qoshi ga kwanan yunwa,gashi a gabanta cikin qasa da mintunan data nema ya isketa......gashi a gabanta cikin neman umarninta ya kuma cikashi.....rijiya ta bada ruwa guga ya hana. Ko sau daya koda a cikin mafarkanta na zahiri da na badini.......bata taba tunanin sabreen din nada kaifin basirar ajiye kowacce hujja data shafi rayuwarta ba.....tunanin hana faruwar hakan ya sanyata bata waya ta musamman da zasu dinga communicating......wadda bata nadar komai....komai din kuma idan ya nadu ma zai goge kanshi da kanshi ne automatically.

"Tashi kaje kawai.......zan sake nemanka a lokacin da ya dace" Ta fada tana zubewa sabreen wani kallo dake nuna zallar gargadi da yiwuwar afkuwar komai a karonsu na gaba.

Sam sam sai yaji hankalinsa ya gaza kama maganar maamah din.......kamar ba ita bace ta kirashi ga waya mintuna kadan da suka shude ba cikin wani irin zazzafan yanayi?,to meye ya sauyata da sauri haka?.

Waiwayawa yayi kai tsaye yana duban sabreen,saidai idanunta kaf baya kansu yana kan wayar hannunta. Sake maido dubansa yayi ga maamah,har yanzu shi take kallo......saidai kuma da alama kalaman bakinta na sallamarsa ba sune a qasan zuciyarta ba.

"Kaje nace" Ta sake maimaita masa tana fargabar kada yaci gaba da zama ta kunna video din a gabansa. Kaman bazai miqe ba sai kuma ya miqe din,ya sake duban sabreen da still tayi kaman bata wajen kaman kuma ba kowa cikin dakin. Maganganunta suka dinga tsikarar zuciyarsa da wani irin ciwo. Girman qin da take masa har yakai ta zauna ta fayyacewa duniya?,ta fayyacewa kowa?,shi kam idan bai dasawa sabreen jarababben sonshi ba rako maza yayi duniya kenan,da wannan zafin da fushin ya fice a dakin.

Miqewa tayi sanda ta tabbatar ya fita,tadan kalli maamah din kadan,kaman zatayi magana sai kuma ta shanyeta tana tuna cewa ba sa'arta bace.

"Karki saki jiki kiyi farinciki da tsammanin kin kubuta ko kinci nasara akan mariya.....a'ah....wasa farin girki wannan,hausawa sukace somin tabi ne wannan hatsin gara a buta". Dan waiwayowa tayi,sai ta sake mata murmushi kawai tana sanya qafarta waje.

Bawai kaman jiran fitowarta yake ba......dama jiran fitowartata yake......ba zato ba tsammani taji ya cafke hannunta,bai kuma tsaya sauraren komai ba ya soma tafiya da ita zuwa bakin qofa.

"Ina zaka kaini?.....ina zamuje?.....ka sakarmin hannuna......wannan bai kamata ba,ni ba inda zanje......ka sakeni......wai ina zamuje?" Ta sake tambayarsa da qarfi wanda ko sau daya bai waiwayo ya kalleta ba sai daya tabbatar ya sanyata cikin motar ya kwashe qafafunta ya maida ciki ya rufe ya kuma zagayo ya zauna gefanta.

Wani irin zama da ya bata daman jin irin hucin dake fita daga can cikin zuciyarsa har saman fuskarsa. Ya tsareta da kallo da idanunsa da sukayi kaman kwanciyar jini daga qasansu saboda zallar bacin rai.....farar fatar fuskarsa itama ta canza launi zuwa reddish kaman wanda aka dinga yamutsa fuskar da maruka.

"Zan kaiki na killace......a muhallin da ba wanda ya isa ya ganki......zan kaiki inda zamu rayu daga ni sai ke.....zan kaiki inda ba zaki sake ganin kowa ba sai muhammad fu'ad.....zan kaiki wajen da soyayyar fu'ad ce kadai 'yancinki da zaki samu" Yayi maganar yana sauke don rage radadin da zuciyarsa ke masa. Kafin tace wani abu ta fahimci motar tasu ta fara motsawa tana fita daga gidan.

Hankalinta ya dan tashi,saboda sanin halinsa da tayi,to amma sai tabi shawarar zuciyarta ta hanyar dakewa kaman abinda ya fada din bazai tabbata ba ko bai dameta ba.

Tana iya jin wata irin birkitacciyar ajiyar zuciya da yake saukewa,har tsakiyar kwanyarta takejin fitar ajiyar zuciyar wanda ba zata ce ga dalili ba. Ya maida bayansa yayi relaxing sosai jikin kujerar yana sauke numfashi kaman wanda yaci kuka. A hankali taji ya laluba tafin hannunta ya sanya nashi. Mannewa sukayi guri guda abinda ya sanya tsigar jikinta tashi,tana iya jin yadda dumin tafin hannunsa yake bin kowacce jijiya ta jikinta dake aika saqo,tayi yunqurin zame hannun amma ya hanata,saima ya sanya hannunsa guda daya ya tayar da motar,cikin qwarewa yake sarrafa steering din da hannu daya suna ficewa daga gidan.

Batace masa komai ba.....amma jikinta ya soma sanyi da ganin hanyar da suka dauka. Basu taba bin hanyar ba duk a fice ficensu.

Wani irin guri ne da zata iya cewa tsahon rayuwarta bata taba ganin gurin makamancinsa ba.....wani tsuburi na musamman dake kewaye da ruwa wanda kafin su qarasa dab da wajen ya ajiye motarsa,tun bai fito ba ma'aikatan gurin suka qaraso. Idanunta ta daga tana duban sunan dake maqale a signboard CONRAD RANGALI ISLAND RESORT. Sanda take dawo da idanunta ya kammala kashe motar ya zare belt din jikinsa,tattausan tafin hannunsa ya miqa mata yana tsareta da fararen idanunsa,a hankali ta kalli hannun sannan ta kalli fararen qwayar idanunsa da suka fara komawa daidai a lokacin.

Yayi wani irin laushi gaba dayansa,tun daga qwayar idanunsa zuwa gangar jikinsa zaka karanci hakan.

"Banaso.....karkimin musu.....na gaji.....na gaji da jin musu,taurin kai,saba maganata.....i beg you koda na awanni kadanne kawai kibi umarnina,koda na iya yau ne" Ya fada da wani sauti me matuqar laushi. Haka kawai taji wani abu me kama da tausayi yanason saukar mata.......duk wani izza da qasaita nashi duka ya zuge tsakanin tafiyarsu zuwa yanzu. Gefe guda halaye da dabi'un matar da take kiran kanta a matsayin mahaifiyarsa yana dawo mata. Wanne irin barazana wannan uwa keyi da rayuwar d'anta?, ta tambayi kanta. Tunawa take da rayuwar da tayi a gidansu,tsakanin kawunta da kishiyoyin mahaifiyarta,dabi'unsu da mu'amalarsu a kanta gaba daya wasu iri ne da basu da dadin ji ballantana gani.....ta fuskanci rashin nutsuwa da barazana me tarin yawa......yau inaga ace mahaifiya da kanta keyi maka haka?.

Tana tsaka da wannan tunanin ta tsinceshi saman kanta,har ya zagayo ya bude mata qofar side dinta,bai gaji ba ya sake saka hannunsa ya kama tafin hannunta yana tayata fita a motar.


*_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_*
08187255862

𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓 𝐀
_Zafafabiyar_

ΜΆBΜΆOΜΆOΜΆK ΜΆ2

β±§Ι„β‚²Ι„β‚₯β‚³

π™‹π˜Όπ™‚π™€ 98



98


_Manzan Allah S A W yace: Bawa zaizo ranar qiyama da tarin ayyuka da kuma tarin lada,yana murna zai shiga aljanna sai Allah ya dakatar dashi,ga tarin mutane da baisan daga ina suke ba.....dukansu masu neman haqqinsu ne a kansu a wajen Allah,yaci dukiyar wancan.....ya zagi wancan.....ya zalunci wannan,ana biyansu da haka da haka sai ya wayi gari bashi da komai cikin ayyukan ladansa,bayan ayyukansa sun qare za'a koma ana diban zunubin mutanen a maimakon biyansu da ladansa ana lafta masa,daga qarshe sai ya tashi baida komai sai tarin zunubai,sai Allah yayi umarni wa mala'iku su jefashi a wuta( Allah ka tsaremuπŸ™πŸ½)_

_bukhair da muslim_



Sosai ya riqeta yana zagayo da hannunsa zuwa qugunta,sai ta kasa janyewa kaman yadda ta saba saboda idanun mutane,zagaye da ma'aikatan suka

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login