Showing 96001 words to 99000 words out of 557259 words

Chapter 33 - πƒπ”ππˆπ˜ATA BOOK1 AND 2 HAUSA NOVEL

HUGUMA   

03 Nov 2025

3286

a bunqasata?,ta ina faduwa take ayi hanzarin bawa gurin kulawa da kariya?.


*D U N I Y A T A*

*_H U G U M A_*

PAGE 52


Yana jingine da motar yana kallonsu,idanunsa fes a kansu. Yana masa dadi yana kuma sanyawa ya manta cewa fu'ad ba dan uwansa bane na jini a duk sanda ya ganshi kamar haka da Alhaji hamza din. Yana alfahari yana kuma qara ninka alfaharinsa akan muhammad fu'ad din. Shi kansa ya sallama......jajirtaccen mutum ne da jajircewa take a cikin jinin jikinsa.

Ya maida idanu a hankali akan yanayin takunsa. Tafiya ce me cike da ginshira gami da cikakken kuzari da karsashin da zai bayyana maka adadin cikakkiyar lafiyar da yake da ita.

Daga abban har fu'ad din hankalinsu baya wajen,yana duba wani qaramin takardu da suke dauke da bayani da taswirar burinsa na gaba wato ginin katafaren kamfanin samar da kayan ado na sarqoqin mata da zai dinga amfani da wani sashe na ma'adanan da yake haqowa.

Tun daga fitowarsu gaba daya security guards dinsa da ya bari a gida kowanne ya koma kan aikinsa. Dukan inda ya ajiye qafarsa nan suke maida tasu.

Murmushi ya subucewa farouq,ya dawo kenan,kuma yanzun za'a fara. Bayaso abba ne ya tilastashi daukan guardsmen duba da yanayin qarancin tsaron da ake fama dashi. Uwa uba ma zaiyi wahala a nasibin rayuwa daya samu......da irin mu'amalarsa ace ya zauna haka gayansa yana yawo babu masu tsaron lafiya tattare dashi.

Wani lokacin idan yaso yana kubce musu ne yayi fitarsa shi kadai a mota yasha iska ya dawo. Ba kasafai ya fiya son fita qasashen waje sai idan harka haka ta taso takai kayan da sunyi yawan yayi wakilci......amma yanzun ya koyi fita din lokaci bayan lokaci haka siddan ma don ya samu ya sarara yayi rayuwarsa shi kadai. Mutum ne da bayason matsi,bayason takura,zai iya rayuwa me dogon zango shi kadai a wani muhalli na daban,shi yasa ko a yanzun a sassansu gini ne me zaman kansa dake dauke da bedroom and parlor da toilets kowa shi kadai. Saddiq da musaddiq sun hade dakunansu saboda kowa nashi apartment din ya masa girma. Amma oga fu'ad shi daya ne a nashi,hakama farouq,sai shi farouq din da lokaci bayan lokaci yakan dawo sassan fu'ad din yayi kwanaki yana kwana a nan sannan ya koma wajensa.

Kullum ya hangi fu'ad din daga nesa ba abinda yake tunawa sai wannan matashin dan bautar qasar,mara tsoro kuma mara shakka,cikakken jarumin daya shiga yankin daba nasa ba,yayi abinda koda haifaffen yankinne ya aikata bazai sha ba.....ya kubuta da tarin nasara. Farouq yadan sake murmusawa yana tuna yadda yaci wahala bayan uban gudun da sukayi,ya tuna yadda fu'ad din yayi jinyarsa tamkar ba dashi akayi gudun ba

"Ba abinda nakeji man.....ni dakai ba daya bane,sau nawa ana gaya maka ka dinga gym saboda yuwuwar samuwar irin wadannan lokutan na qwatar kai?,sai kuyita zama kaman mata,baku da wani banbanci dasu?" Ya tambayi farouq din a wancan lokaci yana dage masa dukka girarsa bayan ya bashi maganin ciwon jiki yasha.

"Yanzu wannan pain killer din da kake fana dashi......da warm water da fenugreek kake sha da yafi maka amfani". Harara ya balla ma fu'ad din yana dubansa

"Ba zaka qarasa kasheni ba da wadannan home remedies din naka ba" Sai ya juya ma fu'ad din baya yana sauke numfashin wahala yabar fu'ad din da sakin siririn murmushin nan nasa me tsada. Miqewa yayi yana dauke cup din

"Idan home remedies bai kasheka ba......son jiki da rashin exercise....aci a kwanta duka ya kasheka......naga wanda zai aureka da qaton tumbi" Ya qarasa maganar yana jefa kwalin lemo a dutsbin. Duk da farouq na cikin yanayi a sannan saida murmushi ya qwace masa.....fu'ad mahadin rayuwarsa ne kuma mahadin zuciyarsa ne kaman yadda ya tabbatar a wajen fu'ad dinma haka yake.

Kafadarsa y
Ta dama yaji an daka

"Murmushin me kake kai kuma?" Sassanyar muryar nan tasa sake cakude da wani deepness ta shiga kunnen farouq. Kallonsa ya dora saman fuskar fu'ad din yana jin yawan kewarsa da yayi

"Ina nan ina kallon gujajjen dan bautar qasar nan da bai kammala service dinsa ba sai a garin kano". Murmurshin nan da shi daya ke iya fidda masa shi daga kan fuska ya saki kadan yana sake kaiwa kafadarsa duka. Dariya kadan ya saki shima farouq din

"Ina hasaso yadda zasu cinye namanka danye duk sanda suka fahimci daga ma'adanin qasarsu ne aka samar da attajirin nan mamallakin jadda diamondchore company........" Murmurshin ya sake sanyashi saki,sai ya saka tafin hannunsa saman wuyansa yana dan karyar da wuyan kadan

"Naman muhammad jikan jadda yafi qarfin cinsu umaru...." Ya bashi amsa da anihin sunansa,abinda ya sanya farouq din sakin dariya sosai. Kafadar fu'ad din yadan bubbuga

"Na sani.....nafi kowa sanin wannan dan uwan nawa wanne iri ne......tun daga ranar da mukayi temple run dinnan na sake yadda da hakan..."

"A nan zaku gama hirar ne?,idan ku baku gaji ba ku tallafa ku kaini naga aminatu na" Muryar abba ta sauka kunnuwansu.

Fu'ad ne ya waiwaya don farouq yana fuskantar abban ne. Dan murmusawa kadan fu'ad yayi ya matsa yana yunqurin budewa abban qofa,amma farouq ya rigashi

"Dukkanku kai da abban yau qarqashin hidimata kuke....baqinmu ne ku daga South Korea".

"Sannu sarkin noma.....godiya muke" Shima abban ya fada cikin barkwanci bayan ya shiga motar.

Dashi da farouq din baya suka shiga bayan ya bawa shugaban security dinsa umarnin su bisu a baya.

Kusan duka a hanya ma dai tattaunawar ta kasuwanci ce. Farouq din yana bawa abban labarin yadda abubuwa suka kasance bayan tafiyarsu

"Amma tabbas sai ka sake sanya idanu akan mika'il.....ina suspecting wani abu tattare dashi,duk da bana ce gashi ba,amma nasan kai din zaka fini fahimtar komai" Farouq din ya furta.

Idonsa fu'ad ya dauke daga kan wayar hannunsa,wanda saqon mika'il dinne ya shigo,mutum na farko daya fara masa saqon barka da dawowa kafin kowa. Bai cewa farouq komai ba,amma kuma maganar tasa ta samu gurbi sosai a zuciyarsa ta zauna,sai ya gyada kansa a hankali yana sake maida dubansa ga wayar.


**"Anni an gama komai" Ta furta sanda take saukowa daga saman tsararren dining area din daya dauki kyakkyawan family dining table na wani mulmulallen tangaran kai kace an samar dashi ne daga burbushin diamond ko gold da kamfanin jadda ke wankewa su fiddashi. Fara ce tas,mai matsakaicin tsaho,saidai bata da qiba ko qanqani. Yanayin sumar gaban kanta kawai zai fada maka akwai suma me yawa a saman kanta wadda bata da duhu ta danyi brown kadan bame yawa ba. Yanayin yadda ta datsi daurin dankwalinta daga tsakiyar kanta shi zai baka daman ganin hakan sosai. Straight gown ce a jikinta ta atamfa me igiyoyi hagu da dama wadda ta daureta daga gefen qungunta guda daya.

"Ma sha Allah.....sannunku da qoqari....sun wuce ne?" Anni data daga kanta daga tab din hannunta da take duba wasu addu'o'i ta fada.

Fuska tadan yamutsa kadan tana zama kujerar gefan annin gami da ajiye qaramin towel din hannunta a side table sannan ta dauki wayarta dake ajiye akai tana qoqarin budeta

"Kowa ya wuce......yanxun abba da hamma kawai muke jira" Ta qarasa maganar murmurshi yana subuce mata.

"Umhummm......wato shi saddiq shine marainin wayonki da baki ta tasa ko?" Anni ta fada tana maida idanunta ga addu'o'inta . Fuska ta yamutsa,duk da bata kalli annin ba amma ta amsa

"Bar wannan anni,wa yake ta tasa,ba abinda ya iya sai takurawa mutum ba dalili......hamma takurawarsa me dalili ne idan bakayi abinda yace ba ko baka kiyaye dokarsa ba......amma yaa saddiq.....hmmmm....ko wayar nan yanzun ya shigo yana ina dannawa sai yayi challenging dina" Ta qarasa maganar tana zamewa ta kashingida saman kujerar tana maida hannunta kan shafinta na X.

Ita da annin kowa ci gaba yayi da uzurin gabansa,wannan ya bawa falon daman daukan shuru na wani lokaci kafin ta daga kanta. Haka kawai ta qarewa anni kallo sai ta saki dariya

"Anni.....kinsan tsadar kayannan?" Ta fada tana kallon kwantaccen lace din jikin annin dake wani yauqi da santsi duk kuwa da cotton ne. Peach color da ratsin green,bashi da nauyi ko kadan

"Saikin fada 'yar kasuwa......" Ta amsa mata ba tare data dubeta ba

"Anni Allah hamma yana shagwabaki......ki zauna da kaya me tsada haka a gida duk dogayen rigunanki?....amma dai....to,hala abba aka yiwa kwalliya?" Ta fada qasa qasa tana qunshe bakinta da hannu. Kadan ta dubeta ta harareta

"Akwai kayan da sukayi tsadar da zan kasa yiwa abban kwalliya dasu?" Kai ta girgiza tana qoqarin maida kanta ga wayarta tana qoqarin boye dariyarta

"Babu anni.....anni ta abbanmu".

"Amna.... Qoqarin maidani kakarki kike ko?"

"Aah anni wallahi" Ta fada da sauri tana duban anni still tana son shanye dariyarta

"Kici gaba.....inajin zan dauki shawarar farouqu ne,zaki komawa nanna ne kiyi zamanki a can". Kyabe fuska tayi da kyau tana aje wayarta gefe kaman zata saki kuka

"Dama haka yaa farouq din yace?,duk haqurin zama cikin mazan da nakeyi ban da sister?....."

"Oho koma.meye gwara ki koma can,tunda kinga can dinma akwai mata 'yan uwanki sai kinfi jin dadi". Sosai ta sake kwabe fuska tana duban anni

"Da gaske anni zaki iya bayar dani?" Daga kai tayi ta dubeta

"Ba mace bace ke?,wataran ba aure zakiyi ba?" Ta tambayeta,ai kuwa saira soma matsa hawaye tana juyawa annin baya

"Ai dama na sani......gidan nan babu wanda yake sona sai hamma da abba na......shi dama yaa farouq kaman ya bayar dani kyauta yakeji.....ni bazanyi aure ba.....dake zan yita zama". Yadda tayi maganar zata yita zaman da ita sai ya bawa anni dariya amma ta dake

"Sai kiyi kuma" Tace tana ci gaba da scrolling sama tana duba adduo'inta.

"Kinga.....ki daina biyewa ta BB farouq.......indai ina nan ba wanda zai matsa miki.......i swear" Muryar musaddiq ta biyo bayan sallamarshi. Tuni ta miqe ta zauna sosai tana qoqarin goge hawayenta.

"Kaima kana biye musu yaa musaddiq wani lokacin.....amma dai ka fisu" Ta fada tana daidaita zamanta saman kujerar.

Qaramar dariya ta qwacewa anni tana qoqarin ajiye tab dinta a gefe

"Uhumnnn..... Ai dama ba kasafai akewa amna abun arziqi ba.....wanda ke mata abun arziqi kai tsaye a gidannan Muhammadu ne......har kun dawo?" Ta tambayeshi tana duban musaddiq dake dariya qasa qasa.

"Eh anni.....su abban basu iso ba?"

"Sun sauka amma basu qaraso gidan nan ba.....amma na tabbata suna dab da isowa don tun dazu suka tafi daukosu". Ta amsa masa tana miqa hannu ta karbi purse din nata da yake miqa mata.

Tana yunqurin budewa su kuma suna magana tsakaninsu shi da amna. Ta zuge jakar cikin rashin tabbas da yaqini,ta bude ne kawai don taga meye yayi saura a cik,me ta samu?,amma ga mamakinta sai ta samu komai a muhallinsa ba tare da an canzawa komai waje ba bare a cire wani abu,sai wayarta data nuna low battery da alama ba'abi ta kanta bama bare a sakata a charge.

"Ikon Allah" Ta fada,abinda yaja hankalin amna da musaddiq kanta

"Ba abinda aka rasa a ciki musaddiq.....ba abinda ta taba kota dauka" Ta fada da mamaki idanunta cikin jakar

"Nima dana bude nayi mamaki,amma nace bari na kawo miki ki duba komai bansan ko akwai wani abun daban ba"

"Aiko yadda na zuba kudin a jere ba'a canza tsarinsu ba" Ta fada tana sake fiddosu

"Amma dai ka yiwa yarinyar godiya ka karbamin number wayarta ko?,ko mamarta na sake yiwa godiya?"

"She's not natural fa anni" Ya fada a taqaice

"Kamar yaya?" Ta tambaya cikin rashin fahimta.

"To nidai anni ko qyallinta ban gani ba,a bakin wani waje wani ya tareni ya bani,baicemin komai ba ya juya,nima haka na juya da kan motata na dawo gida"

"Ikon Allah......gashi bata bari ko sau daya na mata godiyar alkhairin data yimin ba.....na kasa manta damuwa da kulawar data nunamin" Annin ta fadi tana juya abun a ranta.

Bai samu ce mata komai ba saboda qarar bude gate da shigowar motocin da suke da tabbacin baqinsu sun iso

"Alhamdulillah" Anni ta fada tana murmurshi gami da ajiye wayar da jakar a gefe.


*D U N I Y A T A*

*_H U G U M A_*

PAGE 53



Dukkansu da sallaman a bakunnasu suka shigo. Suka amsa musu suna miqewa tsaye tare da dakon qarasowarsu cikin falon,saidai amna ta kasa jurewa. Da sauri ta taka zuwa bakin qofa ta riqe abbannata da kyau tana dariya idanunta saman fuskar fu'ad

"Abba sannu da zuwa....hamma....hamma sannu da zuwa" Ta furta matsanancin murmushi yana subuce mata

"Sannu 'yar abba qanwar hamma.....hamman dai aka matso a tarba aka fake da abba". Abban ya fada yana lakuce mata kumatu. Dariya suka saki fu'ad yana tayasu da murmushinsa

"Amnee......barkammu" Ya amsa mata cikin kulawa. Sakin abba tayi ta matsa dab da fu'ad din tana karbar briefcase dinsa

"Su amna an iya munahirci" Muryar sadiq ta shiga kunnenta,sadiq din dake tsaye ta bayansu abban. Gotasu tayi kadan tana leqensa,sai ta bata fuska

"Duk abinka bazanyi welcoming naka ba.....abba me yasa baku samu wata bolar South Korea kun yar dashi kun gudo ba?" Ta qarasa tambayar tana kallon abba a shagwabe. Ba wanda maganar bata bawa dariya ba a cikinsu

"Idan muka yar dashi ke zaki fara qorafin muje mu dauko miki shi ai"

"Allah bazan nemi wannan ba....."

"......me qarya?" Saddiq ya datsi numfashinta yana fadi idanunsa a waje

"Dan aljanna" Ta fadi tana juya idanunta abinda zai sake tabbatar maka da sauran quruciya a tare da ita,hakanan kuma tana fama da sakalcin auta da gasken gaske.

Kasa jiran isowar abban tayi,sai ta taka ta ruskeshi a tsakiyar falon. Ta rusuna tana masa sannu da zuwa gami da gaidashi duka tare da qoqarin amsar qananun tarkacen dake hannunsa. Cikin nashi tsananin kulawar da kallon kewa yake amsa mata,fuskarsa ta wadatu sosai da fara'a yana tambayar lafiyarta dama ta jama'ar gidan gaba daya.

Hankalinsa yana kansu,qauna da kulawar dake tsakanin anni da abba sune abu guda daya tak da suka rage wadanda suke bashi hope din wataran qila zai iya aure. Soyayyar da sukema juna wani irin dasashen abu ne da har yanzu yake tasiri a tsakaninsu,babu alamun gushewa sam sam. Yanayin rayuwarsun yana burgeshi,wata irin mu'amala annin kewa abba,irin mu'amalar da bai taba ganinta ba tsakanin MAAMAHnsa da ABBEY dinsa ba. Mu'amalar da bai taba zaton akwaita tsakanin miji da mata ba sai a wajen annin.

Gabanta ya qarasa shima kaman ko yaushe,cike da ban girman nan da yake jinsa har cikin ruhinsa ya tsugunna yana gaidata. Bata iya tsaiwa saman kanshi ba saboda girman shima da take bashi sakamakon sunan MUHAMMADU da yake dashi......da wata ajiyayyar kima da martaba da take ganinsa dashi saboda dattakon halinsa data sani tun bai cika shekara sha takwas bama a duniya.......uwa uba yadda yake tattalin farincikinta kadai ya sanya kowanne lokaci takejin tamkar jikinta ya tsaga ya fito.

"Lafiya alhamdulillah me babban suna.....jiki na warware tun tuni......dama ta jima bata tashi ba,akasi kawai aka samu a ranar,nafi tunanin kuma matar da mukayi salla tare ne turarenta yayimin qarfi da yawa".

Dan qwarya qwaryar zama sukayi cikin falon na duba lafiyar juna,qananun zolaya tsakanin amna farouq da musaddiq abban yana shiga yana raba gardama kafin daga bisani anni tayi umarni

"Abinci ya zama ready.....zaku shiga ku watsa ruwa tukunna ko?" Ta fada tana duban abba me gayya me aiki

"Hakan yana da kyau ko me babban suna?" Ya maida tambayar ga fu'ad. Murmushi kadan ya saki,suna girmama ra'ayinsa qwarai,sunan da yake dauke dashi ya bashi wannan girman a iyalin da suka san girma da martabar sunan. Wani abu da sam sam bai gani ba ga maamah,tana iya kiransa a lokacin quruciya da sunan ta kuma zabga masa zagi fada da sauransu

"To abba" Ya amsawa Alhaji hamza yana miqewa. Farouq ne ya miqe ya dauki luggage din fu'ad din yana nufar qofa

"Muje na taka maka badon halinka ba......don wallahi ka shiga uku duk sanda mukayi aure muka barka kai kadai a gidan nan". Yayi maganar qasa qasa yadda su abba ba zasuji ba.

Harara fu'ad ya zabga masa yana jan qaramin tsaki

"Sannu tattabara sarkin aure?,yanzun ma idan kaga dama ka koma mana ka gani?......ni gwara fa ku qara gaba ku barni daga ni sai anni ko mayi kumari". Dariya ya fashe da ita harda buga qafa kadan

"Kayi asara wallahi.....kai ta qara qiba ma kake,kaci gaba da gandamewa a gaban annin?,idan bakayi wasa ba gaba gaba sadakarka za'a bayar Allah......"

"Munyi asara dai ni dakai mayen aure......idan kun tashi kuyi shelata a masallacin juma'a".

"Basai munkai ga nan ba......owner na diamondchore resources company guda.......ko a sirrance akayi shelarsa mugun ciniki zamuyi Allah,a zaba maka guda hudu qwarara......matsalar kawai har yanzun ni kaina bansan color na macen da kakeso ba.....". Shammatar farouq din yayi yakai masa wani wawan duka sai daya qame,don maganar ta fara isarsa,yasan kuma farouq baisan bari ba,baisan ya isa ba.

"Kaci bashi......sai na dauki fansa.....ka qarasa cikin da kanka na fasa rakiyar" Ya fada yana

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login