Showing 477001 words to 480000 words out of 557259 words

Chapter 160 - πƒπ”ππˆπ˜ATA BOOK1 AND 2 HAUSA NOVEL

HUGUMA   

03 Nov 2025

429

Har ya fara takawa zuwa motar da Jordan ya bude masa ta jawo yatunsa,ya dawo da baya yana kallonta da narkakkun idanunsa.

"Yadai?.....ko na fasa ne?" Kai ta maqale sannan ta girgizashi.

"BB ne fa......idan banda BB dinne ba wanda zan bawa aronka....."

"Nima banda ina kishin a kallemin ke.....banda ina tattalin 'ya'yana ba abinda zai sanya na tafi na barki"

"To amma...." Ta fada tana turo baki ba tare data qarasa magana ba. Idonsa ya lumshe ya kuma budesu yana kallonta,ya mata alama daka akan ta fada.

"Banason ka kalli kowacce mace please...." Tayi maganan tana juya masa baya alamun kunyarsa takeji. Qaramar dariya ya qwace masa,yasa hannu.ya juyo da ita yana fadin.

"Say it mana.....Louder please!,with all your might" Ya furta yana mata sassauqar runguma ta baya,yadda ta nuna kishin na faranta masa kaman farincikin na neman masa yawa.

Kai tsaye ta juyo ganin abun na masa dadi,ta saka idonta cikin nasan tana dubansa.

"Your eyes belong to me,don't look at any other women please,na maka alqawari a karan kaina.....my gaze is fixed on you alone,bana ganin kowai sai jadda na" Ta fada tana rungume Hannayensa". Sulalewa yayi sai gashi saman gwiwarsa a gabanta,abinda ya sanyata zaro ido ta fara kallon mutanen dake wajen.

Dukka guards nashi sun juya bayansu,ba wani guda daya da yake kallonsu,saima kaman katanga da sukayi musu ta yadda ba wani a farfajiyan gidan da zai ganin ainihin abinda ke faruwa.

"Karki damu,My men are extremely competent" Yana kaiwa nan ya kamo yatsuntsa masu kyau da taushi. Kafin yace komai wayarsa ta dauki tsuwwa,yadan yamutsa fuska yana cirota a aljihunsa. CP ahmad nuhu ne,don haka ya daga kai tsaye ya sanya a kunnensa.

Cikin ban girma suka gaisa,kafin ya soma gabatar masa da bayanai.

"Sir dukkaninsu a yanzu sunyi taushin da kowanne bayanai muke buqatar tatsa daga wajensu zamu sameshi in sha Allah,don yanzu haka bibo da zuwaira ma mun samu dukkanin bayanan da muke da buqata,ban sani ba ko zamu iya aike maka ta email?"

"Good job sir.....thank you,basai ka turo ba,don yanzu haka mun fara hidimar bikin dan uwana.....but zuwa Monday dukka zamu zauna dasu,akwai yiwuwar wanda za'a sallama a cikinsu.....thank you sir"

"Okay sir.....in sha Allah" Cp din ya fada suna sallama cikin farinciki da mutuntawar yadda dukiyar FU'AD din bata sanya yana musu kallon na qasa dashi ba. Ya basu dukkan wani girmamawa da dama na gudanar da ayyukansu.

Kashe wayar yayi duka ya sanya a aljihu don kada wani ya katse masa shauqinsa,sannna ya sake riqo tausasan tafin hannunta da har yanzu yake jiyo wannan sassanyan qamshin na jiya (incense by kabo daughter+234 803 211 9803 Da gaske turarenta kwana yake a jiki,kama gida kuma da wuri yake,khumrorinta dukka na dabanne bare akai ga turarenta).


"Ni muhammad FU'AD jadda,an halicci ruhi Zuciyata dama gangar jikina gaba daya saboda ameenatu sabreen........har abada gangar jikina da zuciyata sun haramta ga wata diya mace ba ita ba......mata gaba dayansu wallahi wallahi kallon maza nake musu 'yan uwana,daga kanki an gama haifar wata diya mace har abada,amana daya ce......kuma kin sameta,bana canza magana,bana sauya alqawari" . Tasha jin ana cewa maza basu da magana daya.....ta gani da idanunta yadda maza suke zama wasu ababen tsoro game da mata,amma a yanzun saita samu kanta da amanna da maganganunsa.

Tana tsaye har dukka motocinsu suka bar harabar gidan,sai ta juya ta koma a hankali tana jin kaman ita kadai ce ta rage a duniya. Bata dauki lokaci ba itama sai kawai ta shirya,ta yiwa securities din daya bar mata magana suka shirya motoci ta fice zuwa gidan anni.

Ta samu amare sunata wani glowing kaman wadanda anni ta dauka ta jefa cikin engine aka sauyo mata da wasu,duk da dama daga amna har huda kyan fata garesu.

"Aah,mrs saddiq and musaddiq" Sabreen ta fada cikin salon tsokana. Abun mamaki wai yau ita suke kunya,kowacce sai ta sadda kai,saidai kuma yanayin amna data gani kaman ba yadda ta saba ganinta ba.

Duk da akwai surukuta sosai tsakaninta da anni,amma ta dan sake wasu abubuwan da ba zasu zamto zaqewa ba ta shiga anyi da ita. Lefen data gani wajen anni akwati ashirin da hudu na huda ashirin da hudu na amna,guda biyu arba'in da takwas kenan. Daki daban anni ta saka ta shiga tana nuna mata wasu designers akwatunan guda sha biyu samfurin shekara mai zuwa,wanda akayi lunching nasu a dubai cikin satinnan. Ita tsoro ne ma ya kamata da anni take gaya mata wai nata ne,ya ilahi ina zatakai wadannan?,kada ya jawo mata baki fa na jama'a.

A daren suna video call take jeranta masa kalaman godiya,kalaman da suka sake kashe masa jiki da zuciyarsa,yaji kaman zai narke saman sofa din da yake kwance akai.

"Sabrrrr" Ya kirayeta,wanda kiran kawai ya gaya mata yanayin da yake ciki.

"Anya ba gobe zan taho ba?,anya duniyata?". Dariya ta qyalqyale masa dashi tana tsokanarsa.

"So kake BB da fannah suce nice na hanaka?,kayi haquri please,awa arba'in da takwas ne kawai".

"Allah ka bani juriya" Ya fada yan lumshe ido,yana jin wata kewarta tako ina,tattausan skin dinta me qamshi laushi da santsi.

β˜…Randa FU'AD ya sauka ranar fanna tayi bridal dinta,baije ba farouq ma bai matsa ba tunda yasan bame son zuwan bane. A rana ta biyu ne akayi zaman ajo,wanda a wannan zaman kudi sukayi rana.....dukiya tayi kuka da idanunta,ya nunawa BB dinsa qauna irin wadda ta sanya farouq tara hawaye sosai a Idanunshi.

"Karka yadda kayi mana kuka gaban mata da tarin mutane,idan kayi hakan bamu yafe maka ba.....wannan kukan ka riqeshi sai sanda kuka kebe......idan ba haka ba za'a dauka lusari ta aura" Ya fada kadan a kunnen farouq bayan ya gama zazzage pound cikin abinda aka ajiye saboda zuba ajo din,don yana gama zubawa aka dauke abun,ya riga ya cika sai wani aka sanya.

Tofa......nan idanu dama hankulan 'yammata dama zaurawa masu lokaci yayo kan FU'AD din,taron mayu bawai na maita ba......mayun mata.....ma'abota son kyakkyawan namiji me abun hannunsa hankulansu ya tashi. Kowacce isassace me aji tana jin takai,don me qaramin class ma baya suka dinga ja suna rufawa kansu asiri,saboda sunsan kalar zaren ba kalar yadin bane......saidai su kansu isassun sai rab'e rab'e,an rasa zaqaqura me qarfin halin tunkarar me jadda din.....kwarjini yanata aikinsa.

Mota ya koma yayi zamanshi suns hira da duniyarsa,video call kaman ko yaushe,ta daga masa hannuwanta da sukasha wani irin jan lalle,tun daga tafin hannun har zuwa bayan hannun nata.

"Ya salam" Ya fada yana jin wani abu ya harba a jikinsa.

"Nawa me qunshin nan takeso a bata?".

"Anni ta biya mana ni dasu amna.....beside ma ai ka ban kudin da zai isheni kalar kowacce hidima".

"No....kudin dana baki ban bakishi bane don kiwa kanki komai ba,na baki shine don ki wata hidimar daban,zan saka miki a dollar account dinki,saiki cire".

"Allah yabarmin kai jadda na.....Allah yajamin da ranka uban 'ya'yana" Ta fada tana jin kanta yana fasuwa,bada komai ba kuma,da zallar kulawa.....da kalar mijin kuma data samu.

Sanda suka koma guest in dinsu farouq shine qarshen shigowa,bai kuma tashi shigowa ba sai daya na dare. A sannan FU'AD yana zaune saman abun sallah yana addu'o'insa,wanda duka ta neman dacewa da alkhairai ce duniya da lahira shida 'yan uwansa dama dukkan wani masoyinsu(harda ku fans na DUNIYATAπŸ˜„πŸ«ΆπŸ½).

Ido suka hada FU'AD ya janye idanunsa yana hade rai.

"Wanne irin abune wannan?,zaka ajiye.mutane kuma ka tafi,baka tashi shigowa ba sai tsakiyan dare kaman wani barawo?" Wani dariya sosai Farooq ya saki yana qoqarin cire babbar rigar jikinsa.

"So sorry dude.....kasan abinka dame iyali kuma farin shiga.....inacan ina lallashinta wai yatsunta sun gaji......ga tafiya kano gobe donma flight ne.....".

" A gidan ubanwa ta zama iyalin naka?" Ya fada adan fusace,don ya kira sabreen yaso suyi hirar dare bai sameta ba.

"Ka rabo mutane da iyalinsu kuma kazo ka ajiyesu?". Ido farouq ya fiddo,yanason fashewa da dariya amma ya danne

"Ikon Allah....to ni me zan muku idan nazo din?,qarqari muyi hira fa?,kuma yanzu tsakani da Allah saboda rashin imani wanda keda sabuwar amarya ai abun a masa uzuri ne ko?.....to kuma ma naga wancan lokacin naka daurin auren.....qasarma ka bari kaqi dawowa ka barni da amaryar da abokan gaba daya.....wannan rashin adalci ne dason kai dude".

"Farouq....gori zaka yimin?....gate out please ka barni naji da damuwana" Wannan karon duk yadda yaso boye dariyar ya kasa,sai kawai ya saki abarsa yana nufar toilet.

"Bani nakar zomon ba.....ratayar ma ba'a bani ba.....iyali me dadi.....ashe haka lamarin yake dama" Ya qarasa fada yana shigewa gami da turo qofar.

Qwafa fuad ya saki,sai kuma murmushi ya qwace masa. To meye ma laifin farouq a ciki?,ita kanta sabreen din bata da laifi tunda tace masa zata aje wayarta dama,kawai dai iya shegensa ne ya motsa,da alama kuma ramuwa yakeson yayi masa.


*_ALQAWARIN ALLAH baya tashi_*


"An daura auren umarul farouq hamza kibiya,da fannah maisharif babaghana......jama'a kun shaida?". Sautin daya sanya fu'ad sakin tattausan murmushi yana furta.

"Alhamdulillah......alhamdulillah"


*_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_*
08187255862



𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓 𝐀
_Zafafabiyar_

ΜΆBΜΆOΜΆOΜΆK ΜΆ2

β±§Ι„β‚²Ι„β‚₯β‚³

π™‹π˜Όπ™‚π™€ 140


*_Bgawo's KITCHEN AND APHRODISIAC_*


*_WATA KILLATACCIYAR MASARAUTA CE,WADDA KE QUNSHE DA DUKKAN NAU'IKAN ABINDA KUKESO_*


*_GIRKE GIRKE NA ZAMANI_*

*_KAYAN MAQULASHE DA NAU'IKAN DRINKS KALA KALA_*

*_INGANTATTUN TSUMAMMUN MAGUNGUNAN GYARAN MUTUNCIN 'YA MACE......GYARA IRIN NA IYAYE DA KAKANNI DA INGANTATTUN MAGUNGUNAN DA BABU DUNGUSHE KO KOKWANTO A KANSU_*

*_KALAR MAGUNGUNAN DA SAO WAJEN IYAYENMU NA DAURI.....INGANTATTUN SAUWOYI DA SAQE SAQI DA AKA SARRAFASU ZUWA MAGANIN GYARAN DIYA MACE_*

*_BIKI KUKE DASHI KO SUNA?_*

*_SAUKAR KARATUN QUR'ANI?_*

*_KO KUMA WALIMAR AURE QARIN MATSAYI A GURIN AIKI KO KUMA WANI QWAR QWARYAN TARO?_*

*_KO YAU DIN BAKIJIN SHIGA KITCHEN?,TSAFTATACCE KUMA INGANTACCEN ABINCI KIKE BUQATA A CIKIN WARMERS DINKI KO FOOD FLASK?_*

*_HAIHUWA KIKAYI?_*

*_KO GYARA ZAKIYI KAWAI A MATSAYINKI MA CIKAKKIYAR MACE?_*

*_BGAWO'S KITCHEN SHINE MUHALLIN DAYA DACE DA DUKKA WADANNAN BUQATUN NAKU_*

_Maza garzaya ki tuntubesu ta wannan number wayar_

08104553105
08127084190

*_zaki godemin qwarai da haduwa da BGAWO'S KITCHEN_*


*_BGAWO'S KITCHEN_*
*MATATTARAR BIYAN BUQATUNKU*



140


Daga nan inda yake yana hangen sadakin fannah dake bada tabbacin ta zama ta farouq dinsa halak malak......hakanan yana iya hango farouq dake tsakiyar abokansa wanda shigarsa bata da maraba data jikin fu'ad din,sak da sak kaman yadda sukayi a bikin fu'ad din.

Lafiyayyen walima aka gudanar a gidan gwamnatin jihar borno bayan kammala daurin auren da tarin abokansu masu jini a jika,wanda kowannensu wani ne shi ta fannin ilimi da abun duniya.

Ana gamawa fu'ad ya wuce masauki yabar farouq da tarin abokanshi,don shi bazai iyama wannan iya shegen nasu ba,sun sanyashi a gaba sunata abubuwansu daya tabbatar sai yayi trending a social media. Tunda akayi hotuna wajen reception din yayo gaba,don akwai shirin da yakeso yayi.

Ruwa ya fara watsawa ya fidda wayarsa,kai tsaye ya kira duniyarsa. Daidai lokacin tana zaune suna kallon reception da daurin auren da ko awa guda ba'ayi da yinsu ba amma har an warwatsa a media.

Kishin fu'ad ke taso mata sosai saboda ganin tarin comment din yammata a kansa. Shi kadai amma ya fita daban a cikinsu,komai nasa daban yake,wani irin kwarjini me hade da nutsuwa da suka qarawa fuskarsa kyau da kuma kamala.

_"Lallai baaba ma da babansa fa.....duk kyan azurfa bata kai ya gold ba.....the jadda.....guy dinnan daban yake faπŸ”₯❀️‍πŸ”₯"_ comment din wata daya gilma kenan daya sanya zuciyar sabreen quntata,ta kuma ture screen din daga fuskarta tana jan wani qaramin tsaki,can qasan ranta kuma tana mita.

"Bansan me yake damun 'yammatan yanzu ba,kamar mayunwata suke akan maza.....idan suka saka namiji a gaba baji ba gani?,ba kunya ba aji ba kamun kai?" Daga huda har amna sun fahimci me takewa qunquni,sai suka qunshe dariyarsu saboda zuwa yanzun suma suna jin tasu soyayyar da angwayensu har cikin jininsu.

Kayanta take hadawa dama,saboda tanason wucewa gida ne kafin su qaraso,tanaso ta kimtsa ta tarbeshi da kyau,idan yaso gobe sai ta dawo gidan annin. Kiran wayarsa ya sanya ta ajiye duk abinda takeyi,ta kuma daga kiran tana samun wajen zama.

"A ina kake?" Tambayar data fara masa kenan wadda ta bashi mamaki.

"Na dawo guest house masauki.......me ya faru?" Wata sassanyan ajiyar zuciya ta saki,tana jin dadi daya dawo din,at least ya tsira daga kallace mata shi da wadancan mayunwatan 'yammatan sukeyi.

"People are commenting about you everywhere
You're all over social media muffin" Ta fada da wata irin narkakkiyar shagwaba.

"What?" Ya fadi dariya nason qwace masa.

"Like nine angon?" Ya sake tambayarta.

"Am serous muffin" Ta sake fadi tana narke masa.

"Am all yours......am yours forever my World" Ya fadi da wani irin calmness daya bawa zuciyarta nutsuwa. Ajiyar zuciya ta sauke sannan ta soma gaidashi.

"Ya taron?"

"Alhmdlh.....but babu dadi coz bakya kusa dani".

"Nan da awanni kadan zamu kasance tare in sha Allah" Ta fada tana bashi confidence.

"In sha Allah" Shima ya maimaita. Lafiyan yaranshi shine next abinda ya qara tambaya,tayi murmushi tana dora hannunta saman mararta data fara tasawa tana bashi amsa.

"They're fine.....suna gaida abbunsu.....sunyi missing nasa"

"Me too my world.....akwai kyakkyawar gaisuwa tsakaninmu idan na dawo.....so get ready,be at home as soon as possible"

"Yanzun nake shiri in sha Allah"

"But.....karkice zaki fita da mota daya....ki jira su abdulgafar zasu kaiki har gida.....and nace su qara yawan security na gidan". Ya fada da serious murya.

"I hope komai lafiya ko?" Kai ya jinjina,kawai yana jin wani abu daban a jikinsa.

"Lafiya.....in sha Allah" Ya fada yana son tabbatarwa da kansa haka.

Cikin nuna tsananin kewa da qaunar juna sukayi sallama shida ita,kai tsaye kuma ya kira abdulgafar.

"Zamu qaraso gurin qarfe biyar......get ready please,a qara yawan security a airport da gida na harda gidan anni......har gidan farouq.....if possible inaso kowa cikin ku ya zama ankare da kowanne parts".

"As you wish sir" Ya fada cikin girmamawa.

"Ku rakata gida safely abdulgafar......bazan iya jurewa ba if something happen".

"Bazai faru ba sir in sha Allah"

"Good abdulgafar" Ya fada yana yanke kiran.

Iska me zafi ya furzar daga bakinsa yana dan wani gajeram tunani da shi kansa baisan na meye ba,sake daukan wayarsa yayi ya tura rubutaccen saqo ga duk wani guard da suke tare dashi a halin yanzu haka a maiduguri,sannan ya sauka yana laluben wayar farouq don jin yadda zasu shirya tahowa kano kada lokacin tashinsu ya fita.


β˜… Daga samanta tana iya hangen yadda duk wani shige da fice yake gudana cikin gidan hamza kibiya. Wani ajiyayyen qullutun baqinciki ne yake tsaye a wuyanta,shi bai fita ba shi bai sauka ba. Idan akace mata a baya nasararta zatazo da irin wannan salon tsaf zata qaryata......a irin wannan yanayin zata iya cewa bikin d'anta akeyi.......amma koshi yaron nata bata samu martabar ganinsa ba bare ta shiga lamarin bikin,balle kuma ta samu girma da daraja irin na kowacce uwa.

Agogo ta kalla,tana jin ta matsu ta kuma qagu komai ya faru,tana jin a ranta afkuwar komai din shine zai bawa abinda ya tsaya mata a wuyan damar fadawa.

Knocking akayi sannan aka turo qofar dakin. Bata damu ta waiwaya kota tambayi waye ba har zuwa sanda ta fara magana.

"Maamah ga abincinki fa,tun na safe bakici ba.....na rana ma haka,ga na dare a hanya,kuma likita yace ki dinga kula da abinci ko don yanayin ciwon...."

"Ciwon ubanki?.....nace ciwon ubanki?". Ta fadi tana katse laila da dukka tashin hankalinta ya tattaru ga ganin alamun maamah din tana cikin damuwa,tashin hankalin da takeji tana jin yafi wanda maamah dimma ke ciki.

"Maamah kiyi a hankali ki daina fushinnan ko don lafiyark......".

"Waini sa'arki ce?,to kiji na gaya miki na rantse da Allah kika qara Dangantani da wani cutar hawan jini saikin gwammace uwarki hajja bata haifoki na......idanma qullawa kukayi don ku cuceni ku kasheni saboda ba idon 'ya'yana ko to?,to kunyi qarya kun kwana da yunwa,ni mariya warki ce daidai qugun kowa.....ni mariya kuma ni kad'aice gayya......fita kiban guri" Ta dakawa laila tsawa tsawar da har saidata zabura.

"Allah ya baki haquri" Ta fada ta juya tana fita a dakin kaman zata kifa.

Fitar laila sai ya zama kamar ta fita da iskar da take shaqa ne,take taji iska tana mata kadan,wuyanta ya soma riqewa iskar bata samun daman isa ga hunhunta. A daddafe ta samu waje ta zauna tana qara gudun fanka da Ac din dakin,wani irin haki yana sarqeta. Likitan ya gaya mata,kada ta yarda ta fadi muddin irin hakan ya sameta tana a tsaye,idan ba haka ba komai zai iya faruwa.

Ta kusa mintuna talatin a haka kafin taji a hankali numfashinta yana daidaita har ya koma normal. Wayarta ta jawo,ta kira number wayar da take sanya ran shigowar kiranta tun dazu.

"Baki da damuwa.....muna ankare da kowa da kuma komai.....ki jira jin sakamako daga yanzu zuwa gobe da safe"..

"Godiya nake" Ta fadi tana ajiye wayar tana kuma sake jin relief sosai a

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login