Showing 180001 words to 183000 words out of 557259 words
bani da lokacin masa bayani......lokacin kawai nace ka shaida masa.......sadakin aure kudin sanya rana da sauran bidi'o'i ya lissafa ya cire cikin kudadena da suke kwasa,canjin ya rubutasu aci gaba da lissafi har zuwa ranar da zan fashesu gaba daya......don ba wanda zaici kudin jadda ta wannan hanyar ya tsira".
Da idanu farouq yake binsa,dariya nason kamashi amma yana dannewa
"Amma malam ya kamata ka koyi ladabin magana zuwa yanzu,ko ka manta yanzun suraki yake a wajenka?" . Harara ya watsa masa da fararen idanunsa yana zama saman sofa
"Kaci gaba da gayamin haka,wataran zaka wayi gari da haqoranka a hannu" .
"Zaka aikata.......ai gwara da aka saka ranar auren 3weeks,kafin aljanarka ta dawo ta sanyaka kace ka fasa.....kaini koma wanne irin aure ne fa gwara kayishi,a qalla addu'ata bata fadi qasa banza ba,zaa yiwa aljana kishiya.....naci nasara" . Duk da baijin dariya ko wani raha sam a ransa.......amma saida maganganun nan na farouq suka sanyashi sakin wani miskilin murmushi kafin kuma ya waske kaman bashi ba.
Yana tsaka da cin abincin dare kiran ya shigo masa,ya daga wayar ya sanyata a hands free yana adduar koma waye ya kirashi Allah yasa alkhairi ne.
Tunda farouq ya gabatar masa da kansa gumi ya fara yanko masa,gaba daya yaji abincin ya gundureshi ya fita a kansa,sai ya tsame hannunsa daga ciki ya miqe tsaye yana sauraron farouq jikinsa yana kyarma
*D U N I Y A T A*
*_H U G U M A_*
PAGE 97
"To.....to shikenan......in sha Allahu zan shaidawa dangin uwarta.....to Allah ya nuna mana....to godiya nake a gaida alhajin". Ya qarasa fada jikinsa yana rawa wayar kaman zata sulale ta fadi
" Na shiga uku na lalace ni rufai" Ya fadi a sarari yana zama dabar saman Kujerun da kwana uku kacal da zubasu sumame daga jadda company ya riskeshi. A da mugun laushin Kujerun yake ji,amma a yanzu yana jjnsu tamkar kujerun da aka sarrafa da bishiyar qaya.
Kansa kawai yake mirginawa daga hagu zuwa dama. Duk da ya iya tijira ya kuma iya tubura,amma wannan karon sai ya tsinci kansa da tsananin shakkar yadda zai tunkari sabreen din ya gaya mata ya bada aurenta a madadin kudin cacar wasu da yaci,da kuma nata kudaden data kwasa.
Bata iya doguwar magana ko rashin kunya irin na 'yan uwanta ba.....amma idan tayi maka wani abun har sai ka gwammace baki ta bude ta gasa maka rashin kunyar.
"Yanzu meye mafita?" Ya fada a sarari yana juya hannaye irin na wanda ya banu ya lalace,daidai nan matarsa umma asabe tayi sallama ta shigo dakin.
Kusan duka wayar da farouq din keyi da kawu nashi hankalin yana kan news da suke hasko faduwa da tashin hannuwan jari a kasuwa a yau din. Yaji suna sallama da kawu rufai din,sai wayarsa dake ajiye a gefe ta dauki ruri.
Kamar kowanne lokaci da bayyanar sunanta saman fuskar wayarsa ke sanyashi jin wani iri haka ma yanxun. Ya miqe ya zauna sosai yana sauke qafafunsa dake harde a dazun,ya daga wayar ya saka a kunnensa yana yin sallama.
"Wa'alaikumussalam..."
"Barka da dare" Ya fadi a nutse yana qoqarin saita kanshi.
"Barka kadai......idan kana gida ka shigo yanxu inason yin magana da kai". Dan shuru yayi kafin ya amsa a taqaice da
"Okay" Amsawar tasa ya bata daman katse kiran,ta ajiye wayar tana sake hada kalaman da zata tunkareshi dasu.
Kaman bazai motsa ba sai kuma ya miqe,farouq ya miqa masa dayan wayan tashi
"Mun gama magana......"
"Ba wani abu me muhimmanci a ciki da saika sanarmin......ka riqe duk bayanansa zasuyi maka amfani wajen qarasa plan din daka tsara". Dariya farouq ya saki yana lumshe idonsa,ya kuma sake relaxing abunsa sosai cikin kujera
"Hakanma ni yayimun.....zakaga kalar tawa ja'irartar". Bai amsashi ba ya soma wucewa inda flip-flops dinsa ke jere nau'i daban daban cikin wata ma'ajiyar takalma dake bakin qofar shigowa falonsa,ya miqa hannunsa kan wanda ya fara gani,ya zarosu ya sanya a qafarsa ya buda qofa ya fice yana jin wata fargaba haka kawai tana saukar masa wadda baisan dalilinta ba.
Yau ma gidan ba kowa,banda malam saidu daya bude masa qofa suka gaisa ya wuce ciki.
Ita daya ce hakimce saman lafiyayyun kujerunta,falon bai cika hask sosai ba sai haske fitilun da aka qawata ginin POP din dake saman falon.
Da murmushi a Fuskarta ta amsa sallamarsa tana tashi daga kashingidar da tayi ta zauna sosai. Ya zare takalmansa ya barsu daga nan sannan ya qaraso ciki.
Kaman kowanne lokaci,ba kasafai ya fiya zama saman kujera ba idan ya shigo falon yauma haka,sai ya samu daura da inda take zaunen ya zauna yana tanqwashe qafafunsa kamar me shirin fara cin abinci.
"Bari na samo maka ruwa tukunna". Ta fada tana miqewa sannan ta wuce cikin kitchen. Bai dakatar da ita ba don gudun ballo wata rigimar daban kuma,saidai bayajin ko a gabansa akayi aikin ruwan zai iya aminta yasha shi. Kansa ya daga kadan yana kallon falon da ainihinsa nan din dakine na mahaifinsu ciki da falo......dakin da ya rayu yasha jiyya a cikinsa har ya koma ga mahaliccinsa.....dakin da nan ne waje na qarshe data sanya qafafunta ta tsallakesu ta fice......dakin da anan sukaci gaba da zama shi musaddiq da jadda cikin talauci har itama jadda ta tafi ta barsu. Yau ga dakin ya zama wata qawatacciyar duniya.....saidai wadanda suka cancanci suci arziqin abun sunyi qaura sun barwa wani sashe da basu da alhakin samun gajiyar abun.
"Bismillah" Ta fada tana dire masa tray din sannan ta koma saman kujera ta zauna. Idanunsa ya lumshe da suke masa wani irin radadi sannan ya budesu,ya miqa hannu ya dauki gorar ruwan swan ya balleta ya tuttula a cup ya dauki cup din kawai ya riqe a hannunsa
"Tashi ka koma saman kujera ka zauna sosai magana nakeso muyi dakai me matuqar muhimmanci" Tayi maganar tana soke yatsunta cikin na juna tana sassauta sakin Fuskarta zuwa daurewa.
Kallo daya tak yayi mata,sai ya dire ruwan ba tare daya ce komai ba ya miqe din ya zauna saman kujerar dake fuskantarta.
"Muhammadu" Ta kirashi kai tsaye da zallar sunansa,kiran da ya saka gabansa faduwa abinda ya mance rabonsa da yajishi
"Na'am" Ya motsa tausasan labbansa ya amsa da wata murya can qasa.
"Wacece ni a wajenka?" Ta jefa tambayar a gareshi tana kafeshi da idanuwa.
Jin abun yayi yayi masa banbarakwai kawai,yana ganin amsace bayyananniya ai da ba sai anyi dogon neman amsa ba.
"Mene ya kawo wannan tambayar maamah?" Ya fada a sanyaye
"Akwai.....amma kafin sannan inaso naji amsa daga bakinka.....don komai da zai taso daga baya din yana da alaqa da kalar amsar daka bani" Qasa yayi da kansa ransa da zuciyarsa suna sake jaddada masa tabbas akwai wani abu.
"Mahaifiyata ce ke" Kai ta jinjina tana jin alfahari,tana jin kalmar har tsakiyar ranta,zamowa mahaifiya ga mutum irin Muhammad jadda ba qaramar takar sa'a bace ga kowacce mace.....ba qaramin zamowa riba bace ga kowacce uwa me haihuwa.....ribar qafa ce ta kowacce bangare.
"Shikenan......akwai buqatar da nake da ita daga gareka.......kuma umarni ne zan baka,bawai roqo ko neman alfarma nakeyi ba......ina magana ne da harshen uwa kuma mahaifiya........ba me cin alfarma ko darajar kowa ba cikin duniya......ina magana ne da baki na uwa wadda haihuwa ta karramata da wannan darajar..." Tayi maganar a jere cikin sauti da yanayin da ya sanya yaji kowanne noti na jikinsa ya qarasa kwancewa
"Wacce irin nannauyar buqata ce haka?" Ya samu bakinsa da subucewa yana tambayarta ba tare daya shirya hakan ba don dai kawai kunnuwansa sun kasa jumurin jiran jin me zai fito daga bakinta.
Gajeran murmushi ta saki tana gyara zamanta
"Na godewa Allah da tun yanzu ka gane girman buqatar uwa akan d'anta.......muhammad" Ta sake kiransa da sunan nan dake masa girma da nauyi.
"Ka jima kana bijirewa umarni na.....kana sabawa Maganata......ka dade ina fadin magana kana taketa,kana mata riqon sakainar kashi......ina dauke maka kai,ina maka kara ina maka alkunya......ina maka sassauci irin na uwa......ina da tarin buqatu......ina da tarin burika.....ina da mafarkai da yawa da nakeso na cikasu amma dukka ban samu wannan damar daga gareka ba.....a yanzu ina da wani babban mafarki akanka na samu macen auren dake sonka ba don dukiya ko abinda ka mallaka ba,macen auren data dace dakai ta gari wadda zata zauna da kai da zuciya daya......wannan damar da ita nayi amfani na laluba na kuma zaba maka nagartacciya guda daya......wadda nakeso kai tsaye ka karbeta saboda umarni ne nakai tsayen daga uwa zuwa d'anta!" Ta qarashe maganar da kakkaifan harshen daya sanyashi wata matsananciyar faduwar gaba da bai taba jin irinta ba
"Ya ilahal aalameen" Ya furta a zuci da bakinsa murya can qasa. Wanne irin lamari ne haka katsam lokaci guda?. Matar aure fa take magana maamah din......maamahn da bata gama zama nagartacciyar uwa cikakkiyar garkuwa ga 'ya'yanta ba ta kowacce fuska?,yaushe zata samu nagarta fahimtar nagartacciya cikin mata?.
"Maamah......aure ba abun wasa bane,aure ba tafiya ce ta yau kuma a kammalata gobe.....aure abune da akeso mutum biyu su gani su kuma aminta......"
"Dakata Muhammadu!!!" Ta furta a tsawace tana daga masa hannu.
"Ka manta a farkon zance na?,na gaya maka ba neman shawara nake ba?,hukunci na yanke ina gaya maka hukincin ne saboda kasan da wanzuwar abun.......zan nema dangin mahaifinka koda mutum qwara daya ne,da nawa ahalin mutum uku a ciki,su kadai sun isa suje neman auren.......bana buqatar komai naka a ciki......bana buqatar sisinka,zanyi komai.....abu guda daya tal nake buqata" Tayi maganar tana daga yatsanta dan manuni.
"Ka kula da ita yadda zaka kula dani mahaifiyarka......ka bata kulawa ka tattalata kamar yadda kowanne d'a namiji yake tattala mahaifiyarsa da 'yarsa da matarsa......idan kanaso ka hadu da mummunan fushi na kuma kalar wanda baka taba gani ba......ka gwada tsallake wannan dokar" Wani irin mawuyacin hali yaji yana neman fadawa,lokaci daya taji tamkar an daga duniyarsa ne an kifata daga sama zuwa qasa,yayi qoqarin tattaro muryarsa a raunane yanason sake fahimtar da ita,don shi ba abinda ya fahimta a wannan abun face wani kitsatse kuma shiryayyen al'amari da muddin ya rufta ciki rayuwarsa kaf yana hango rugujewarta
"Amma maamah......"
"Muhammadu.......muddin kace zaka gwada bijiremin.... To ka jira tsinuwa daga gareni da zata biyo baya......zan daga maka nono......zan maka Allah ya isan nonona daka sha?!!". Qas yayi da kansa yana jin wata zufa tana keto masa,duk kuwa da wadatar ac dama pan dake kadawa a hankali.
Jin jikinsa da kansa yakeyi gaba daya kaman ba nashi ba......yanajin kaman gini me hawa goma ne ya lafto saman kansa. Bakinsa yayi nauyi qwarai,yaji bashi da wata sauran kalma data rage masa.
"Kiyi haquri" Ya fada a mugun raunane.....raunin da a sannan idan abokan adawar kasuwancinsa suna wajen zasu rantse da Allah ba muhammad jadda bane.
"Naji......tashi kaje ka fara shiri" Abinda tace dashi kenan wani dadi yana ratsa qasan zuciyarta ganin alamun nasara baro baro a tare da ita. Zuciyarta fari tas sanda yake fita,tana jin wannan karon sa'arta ce,lokacin sa'arta yazo,sabreen kawai ta rage mata,sai kuma ta koma wajen boka ya hada mata dukkan kayan sa'a,ya bata kuma manya manyan bomabomai din da zata bawa sabreen ta shiga gidan dasu masu qarfin da sa'arta zata qarasa cimmata nan da nan.
Da qyar yake jefa qasarka gaba yana nufar gidan ba tare da cikakkiyar fahimtar inda yake sanya qafar tasa ba.
"Wannan wanne irin tashin hankali ne?,wanne irin shiri ne kuma daban wannan bayan shirinta nason ciyar da su da shayar dasu da kayan tsubbu da suka kaucewa hanya sunna da kuma koyarwar musulunci?" Ya yiwa kansa da kansa tambayar sanda yake zubewa saman kujerar falon kowanne sashe na jikinsa yana mutuwa.
"Wanne shiri ne daya wuce ta ajiye maka wadda zata baka komai kaci ka kuma sha kai tsaye ba haufi?,wadda zaku rayu tare qarqashin rufi daya?,ta yadda komai zaifi sauqin kama ka?"
"Yes!" Ya samu kansa da fada bayan dogon nazarin da kwanyarsa ta tafi me dogon zango.
Ba shakka kusan duk wanda ya sani tare da maamah babu wani halin dattako ko na alkhairi sam sam tare dasu,ta yaya maamah din har zata iya cimma MAR'ATUSSALIHA da irin wannan halaye da dabi'u nata?. Tsaftatacce sai tsaftatacce fa haka qur'ani ya fadi Allah da kansa kenan yake bamu labari.
"Wacce yarinya ce ke shirin jefa rayuwarta tsakanin runtsin da yafi qarfinta?,wacce yarinya ce wannan?" Yayi tambayar a fili yana qanqance idanunsa.
Anaso ayi amfani da maamah ne ko kuma maamah din keson amfani da wasu?. Ya sake tambayar kansa da kansa yana sake zurfafa nazarinsa wanda yaji kaman kansa zai tarwatse,sai yaji me yasa bai tsaya ya nema cikakken sani akan wacece ba?,sunanta?,d'iyar wace?,a ina take?. Yanaso ya sani da gaske.......yana buqatar sani,amma kuma bayaso yayi kowanne motsi ko taku da zai sanya maamah ta sake tsaurara aqidarta a kansa.
Tana a wajen tana juya girman nasara takun farko data fara samu ita da matar da takewa kallon aminiya wato hajja,ta kuma neman alfarmar ta shirya don rakata wajen boka nan da kwanaki biyu ko uku kafin masu neman auren sabreen sukai ga magabatanta saiga zuwaira ta shigo.
"Alhaji hamza ne yake son magana dake". Sosai zancan ya bata mamaki,ta dauke wayar daga kunnenta tana kasheta gaba daya cike da madaukakin mamaki. Alhaj hamza yau a gidanta?. Bai taba tako koda qofar gidan ba koda kuwa da wasa tunda ta dawo gidan da zama karo na biyu......ko a baya ma ba zata iya tuna sanda irin haka ta faru ba sanda marigayi yana da rai ballantana yanzu.
"Alhaji hamza kuma?" Ta sake jaddada tambayar ga zuwaira.
"Eh shi".
"Ce masa ya qaraso ciki,faduwa tazo daidai da zama......nima nemansa nake" Tayi maganar tana hade ranta da kyau tun Alhaji hamza din bai kai ga shigowa cikin falon ba,zuciyarta tana raya mata indai har daga fitar fuad ne yaje yakai masa qararta lallai sai ta saka sunyi nadama daga shi har fuad din. A wannan karon zata nuna masa shi da munafukar matarsa.....dama sauran dukkan munafukan dake gefe suna kallo cewa,itace fa ta haifi fuad harma da musaddiq......babu wani da yayi mata wahalarsu.......babu wanda kuma yasan ciwo da zafinsu sama da ita.
π π π π π π π π
ΜΆH ΜΆU ΜΆG ΜΆU ΜΆM ΜΆA
β¦β’βββΏPAGE 98βΏβββ’β¦
Cikin sallama da kuma cikakkiyar kamala ya shigo falon. Kujerar da tafi kusa da bakin qofa ya zauna tare da bismillah a bakinsa.
Ciki ciki ta amsa tana gyara nata zaman gami da harde qafarta ta dorata daya bayan daya don nuna izza da tata isar.
Bata jin zata iya gaidashi ko gabatar masa da wani ruwa ko lemo wanda mutumin dake da kima da martaba kawai akewa haka,sai ta jefa masa tambayar
"Ina fata lafiya ce ta kawoka.....sannan ina fatan alkhairi ne ya sanyaka takowa cikin gida na?". Wani murmushi ya sake dake cike da kamala da dattako. Shi ba mace bane,saboda haka bayajin yana da wani lokacin bata lokacin gutsi gutsin maganganu
"Batun d'anki kuma d'anmu shine ya taso dani....."
"D'ana dai....."
"Hakanma yayi.......jiya ya sameni da zancan samun matar aure da yake buqatar aje nema masa ita,kuma cikin qasa da sati uku yakeso a kammala komai".
Wani murmushi ta saki tana kada qafarta,shuru na kusan minti daya sannan ta soma magana cike da izza.
Malam hamza......ita kuma wacece?,a ina take?,shi yace yanaso ku kuma aura masa akeso ayi?.....koda yake duka wadannan tambayoyin basu da wani amfani......na yiwa d'ana mata.....kuma nan da sati uku in sha Allah ya zama magidanci,saboda haka ba wani batun wata yarinya da zan karba" Tayi zancan tana sauke qafafunta data harde.
Cikin son hadiye dafin maganganunta ya dubeta da duba na tsanaki
"Kin manta cewa a addinij islama muke ba wasu addinan na daban ba?.....laifi ne idan kin aura masa wadda yakeso shima ya auri wadda yakeso duka a lokaci guda mariya?". Yayi maganar hankali kwance yana tsareta da ido.
Kallonsa takeyi itama,saidai kaifin nasa idanun ya shafe nata,don haka ta nanye dubanta a kansa tana jin sam sam bata aminta da wannan zancan nasu ba. Zuciyarta kawai tana bata wata qulalliyar ce.....sun nemo masa mata ne kawai bisa hadin baki suna son cusa masa don a samu damar cin dukiyarsa da lasisi (ni kuwa nace uhmmmm.....idan mutum yana aikata abu sai ya dauka kowa ma haka yake?π€π€....kaico da uwa irin maamah).
"Koma wacece ni uwa ga Muhammed fuad ban karba ba ban aminta ba". Ta fada tana tura dankwalin kanta gaba.
Shuru ya ratsa na wasu mintuna,tamkar bazaice komai ba sai kuma ya miqe tsam
" Zai auri zabinki.....kamar yadda ba wanda ya isa ya hanashi auren zabinsa......abu daya ya rage miki ki bada komai akan