Showing 540001 words to 543000 words out of 557259 words

Chapter 181 - πƒπ”ππˆπ˜ATA BOOK1 AND 2 HAUSA NOVEL

HUGUMA   

03 Nov 2025

420

a dubai?,abun sai kanta ya kasa dauka,don a satin a gabanta ya bada izinin tura Dirham's masu nauyin gaske ga kamfanin da sukayi cinikayyar gidan.

A nutse ta juyo suna fuskantar juna,hannunta yayi sanyi sosai ta riqe nasa hannun.

"Hamma.......wannan kyautar tayi girma da yawa,wannan gatan yayi yawa". Sassanyan murmushin nan nasa ya saki,ya kama qugunta ya riqe yana mata wani tattausan kallo kaman zai hadiyeta.

"Me akayi ma my world?,wannan gidan wai?,kinsan gidaje na nawa a qasar nan?,wannan din kuma dama tun asali saboda ke aka siyeshi.......sabreen" Ya kirata da wani sound yana kama fuskantarta cikin hannunsa.

"Na'am muffin" Ta amsa masa idanunta suna cika da hawayen farinciki.

"Komai na fu'ad naki ne.....komai na muhammad jadda kin cancanceshi.........gata kuma ban nuna miki komai ba sabrrrr.......bana buqatar komai a wajenki illa ki cikamin gida da yara......ki cikamin gida da zuri'ar da zasu zamemin ababen alfahari.....haihuwa nakeso kiyita yi......ni kuma nayi alqawarin bazan barki kisha wahalar komai ba banda ta basu tarbiyya". Rungumeshi ta matso zatayi amma cikin jikinta ya tokaresu,sai taja baya kadan,yana dariya ya nuna cikin da yatsarsa,sannan ya juyata yana baga kyakkyawar runguma ta baya.

β˜…Wata takwas da sati biyu wanda yayi daidai da shekararsu fauxan daya da wata daya akayi mata wani CS din a garin madeena.

Kyawawan 'yan biyu ya haifa dukkaninsu maza. Manya manya har sunfi su fawad girma da wani irin kyau me daukan hankali,don kuwa kamanninsu bangare biyu suka debo,fu'ad din da sabreen din,saika kasa tantance da wa suke kama?.

Kasuwar 'yan uku ta tsaya,kowa so yake a bashi yaran,duk kuwa da cewa dasu aka tafi karban haihuwar 'yan uwansu. Amna naso,huda naso,fannah da farouq dinta sunaso,ga maamah a gefe da sai a ranar tayi kukan rashin magana da bata iyayi. Kuka tayi sosai me yawa,don kuwa taso tana da baki,da tabbas ko fu'ad baya so sai ta karbi wadannan yaran.

Wani irin kwarjini yaran ke dashi kaman ubansu ya roqa musu,ga wani irin energy da suke dashi da wani girma kai zaka ce shekara biyu suke ba daya ba. Bugu da qari kowannensu tafiya yake sosai,don tun suna wata bakwai suka fara miqewa,yanayin kulawar da suke samu ya sanya ba wani wanda yayi wani abu wai kashin haqori,banda zazzabi da sukayi na wasu kwanaki,sai bullar haqora kawai a bakinsu.

Energy dinsu ya sanya suke da fitina,haka suke fafatawa da anni. Gidan su kuwa tuni fu'ad ya sanya an dage komai sama wanda zasu iya jawowa ya illatasu,wanda bazai dagu ba yasa an daukeshi anyi replacing da wani abun na daban. An kwashewa sabreen flower verse dinta da yawa da take ado dasu,a ranar ta dinga fushi tana tura baki gaba.

"Tsakani da Allah......haka kawai a hana mutum ado......". Duba daya yayi mata ya dauke kai yana ci gaba da yankewa fawwaz farce sanda yake bacci saman cinyarsa.

" Yara dai da gidansu ba wanda zai hanasu sakewa,ni ba ta flower vase dinki nake ba.....ta lafiyan yarana nake,inda bazai cutar dasu ba zan bar musu suyita fasawa......qarqari ace dai mu biya ko?,mu kuwa baza'a mana gorin biya ba". Mamaki ya cikata,tayi sakato tana kallonsa yadda ya basar yana wani shan mur,ta danne dariyarta tana sake daure fuska

"Amma dai ba haka akewa yaro tarbiyya ba,a barshi idan ya fasa a zane masa hannu don yasan ba abun tabawa bane". Nail cutter din ya subuce a hannunsa,ya waro ido yana dubanta.

"Du me?,ke waye ya dakeki?,ashe kina so anni da abba su shigo sulhu kenan......wa yace miki akwai duka cikin tarbiyya?,wait.......tsaya ma......bakisan yaro muddin ba'a barshi yayi wasa yadda ya dace ba hakan yana zame masa naqasu a gaba?,ina manya da zakiga sun girma suna wasanni kaman yara?,har wata tsokanar idan sun maka ya baka haushi?,alhali bawai tarbiyya ne basu dashi ba?,to yawansu rashin barinsu suyi wasan da zasu qoshi ne". Dole dariya ta subuce sabreen ganin yadda ya gyara zama yake mata jawabi bilhaqqi da gaske.

"Malam hamma....ban taba jin karatun nan ba sai a kanka".

" Zaki jine da kyau.....nidai na fada abar yarana suyi yadda sukeso". Ya fada yana ci gaba da yanke masa farcen

"Hamma" Ta kirashi a tausashe,kai ya daga ya kalleta ganin yadda ta kirashin.

"Ina gudun kada soyayyar yaran nan ya rufe maka ido ka kasa tayani basu tarbiyya me kyau". Wani murmushi ya sakar mata yana ci gaba da aikinsa.

"Zaki gani.....Allah ya bamu aron rai" Abinda ya fada kawai kenan. Shi kadai daga shi sai Allahnsa sukasan irin burin da yaci akan yaran,shi daya yasan kalar rayuwar da yayi musu tanadi.....ba iyasu fauzan ba,dukka yaran da zai samu daga nan har ya qare rayuwarsa.

Ranar da zasu bar asibiti zuwa gida tana zaune suna hira da huda dake rungume da babynta wanda ya gama rigima bacci ya soma daukansa taji sallamar kawu rufa'i.

Farar jallabiyya ce a jikinsa harda hirami,ga wani farin carbi a hannunsa.

"Assalamu alaikum warahmatullahi ta'ala wabarakatuhu yake d'iyar aljanna mabudin arziqin ahalinta gaba daya". Bushewa da dariya huda tayi tana kallon kawun. Gaba daya ya canza,quruciyarsa kuma sai dawowa takeyi saboda wadatar daya soma tsumbula ciki.

"Kawu waye ya kawowa madeena?,kamar bakafi wata shida da komawa bafa" Huda da dama can tasu bata jiquwa ta furta.

Harara ya dalla mata yana neman wajen zama gami da kalmashe carbinsa.

"Ni yanzu har ayimin maganar hawa gajimare da sauka......mutumin da yake da suruki irin me jadda gidan gold da diamond?,to bari kiji yarinya,a yanzu haka aminaina guda biyu dukkaninsu hajjin bana dasu Zamuyi gaba daya,albarkacin me jadda.....albarkacin d'iyar da aka haifa tsiya tana bacci kariris". Neman wajen zama huda tayi saboda kada dariya ta kayar da ita,kawun ya gama bata amsa daidai da ita,saiyayi banza da hudan yana maida hankalinsa kan sabreen.

"Sannu d'iyata.....sannu 'yar nan.....ashe ni ahmadu da fateema suka haifawa ke ban sani ba?" Ya qarasa fada yana matse hawayensa da wasu sabbin qwalla da suka fara taruwa lokaci guda.

"Dama na dade inaji a jikina zanyi kudi.....na dade inaji a jikina zanyi arziqi ashe ta sanadinki ne,ubangijin al'arshi yayi miki albarka,dukka gidanku yanzu ya koma qarqashin kulawarki,masoyanki da maqiyanki,harda 'yan uwanki na dakin aure,Allah ya qara miki riqonda zumunci da kuma zuciyar yafiya da afuwa"

"Ameen ameen kawu" Sabreen ta fada tana murmushi. Gaba daya kawun nata ya canza kaman bashi ba,wata kamala duka ta saukar masa,ga alamun jin dadi da hutu duka tattare dashi.

"Amma 'yar nan ya akayi haka?" Ya fada yana gyara muryarsa. Kai ta daga tana dubansa

"Me akayi kawu?".

" Kinyi qoqari dai.....amma ci gaba ya kamata a samu ai,'yan hudu ya kamata kiyi wannan karon,amma sai aka koma baya kikayi biyu,maimakon ki maimaita ukun?,kinsan innarmu sai da tayi 'yan uku da 'yan biyu kusan kashi biyar,duka rasuwa sukeyi,ni kadai da dan uwana ahmadu ne muka zauna,don ko babanki ai tagwaye ne,ni kuwa mu uku ta haifa,amma ni duka na fisu qwarin qashi ni kadai na zauna".

"Kaine dai Allah baiyi niyyar kashewa ba kawu ba wayonka bane" Huda data goya baby naseem da baby carrier ta fada duka cikin salon tsokana.

Daquwa ya watsa mata yana dubanta.

"Kinci ubanki.....banda kinci darajar mijinki da ya bani kyautar gida harda mota satin nan daya wuce yau da sai na karbi goyon na aza a bayana naci qaniyarki sannan na baki danki kici gaba da tafiya" Daga huda din har sabreen sai a sannan sukasan saddiq ma yayi kyautar,ba zatar data kashe rigimar kawu da huda ya koma magana da sabreen.


𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓 𝐀
_Zafafabiyar_

ΜΆBΜΆOΜΆOΜΆK ΜΆ2

β±§Ι„β‚²Ι„β‚₯β‚³

π™‹π˜Όπ™‚π™€ 171


*_HUGUMA CLOSET ON TIKTOK_*
https://www.tiktok.com/@huguma.closet?_t=ZM-8y1pf9yfIVZ&_r=1



171


"Allah ya sambada miki albarka,don Allah.........don Allah ki daure wata shekarar warhaka ki sake tunkudo wasu hudun" Ido ta zaro da mamaki

"Da gaske fa kawu kake?".

" To me zaki tsaya jira?,banda rainon cikin bakisan wahalar komai ba?,shi kuma iri kawai yakeso,ai faduwa tazo daidai da zama" Ya fada yana leqa fuskokin yaran.

"Tubarkallah wallahi.....haihuwar masu kudi daban data talakawa,su kansu yaran daban naku suke da namu".

" Wallahi idan banbar dakin nan ba sai kawu ya sanya cikina ciwo.....adda bari naje nima nayi sallah a masallaci" Huda ta fadi tana fita ta barsu.

Wannan karon halastacciyar walima jadda ya fara hadawa a birnin madeena. Walimar maza daban mata daban. Jirginsa daya siya bayan wanda yayi kyautarsa na JADDA WINGS 002 kawai ya bayar akayi jigilar 'yan uwa da suke cikin list na zuwa umra a wannan watan aka gabatar da walimar tare dasu,ciki harda maamah,wadda akan idanunta aka gudanar da komai.

Duk wani motsi na yaran nan guda biyar akan idanunta yake,ta saka damuwa sosai a kansu tana ganin kamar zasu bace ko zaa daukesu,saidai tana komawa daidai duk sanda ta tuna amincin da garin yake dashi.

Wannan karon Sabreen itama ta samu mahaifinta,wato AHAMD(Amaan),dan uwanshi kuma yaci sunan muhammad da kanshi wato takwaran babansa (AMEEN).

Tuburewan tsokana Sabreen tayi.

"Hamma wannan son kai ne.....ni me yasa ba'a fara jira an saka me sunana ba?" Ta fada tana turo baki gaba. Dariya ya saki yana murza yatsunta sanda take zaune tana shayar da muhammad ameen din.

"Ki haifomin baby girl ki gani DUNIYATA.....ke kika mana addu'an boys,gashinan ta shafi kowa cikin familyn jadda,duka maza suke haifa mana,muna da kwadayin mace dukkaninmu amma bansan kusancinki da Allah ba da addu'arki ta riga tawa tafiya ba.....at first nafison na samu daughters so samu.....don na basu tarbiyya na aurar dasu,na kuma rabauta da rabon aljannar da manzon Allah ya yiwa duk wanda yayi irin wannan aikin alqawarin samu". Dauke kai tayi tana sake tsuke bakinta cikin shagwabar nan da bata jin ta girma da yinta,kamar yadda shima baya ganin ta girma dayi masa ita.

"Amma dai it's not fair hamma......sai a jirani sai sanda aka samu baby girl din aka saka ameenatu".

"Ameenatu ta zama wajib akan dukka diya mace ta farko data fito daga tsatson jadda......take it easy maa.....ki qara himma next year by now ki ajiyemin girls" Idanu ta zaro ta bishi dasu,sai ya jinjina mata kai cikin bada tabbaci.

"In sha Allah" Ya fada da yaqinin daya sanyata bata sake cewa komai ba.

Sabreen bata yarda ta koma ba saida jini ya dauke mata,ta sauke umra. Addu'a tayi me tarin yawa akan rayuwarta data zuri'arta,addu'a ce me yawan gaske akan zaman lafiyarta dana familynta gaba daya,qannenta 'yan uwanta dama duk wanda yake da jibi dasu. Ta dade gaban dakin Allah tana neman me kyau a duniya me kyau a lahira(Rabbana Aatina fiddunya hasanatan wafil Aakhirati hasanatan wa qina azabannar/addu'a ce wannan me matuqar muhimmanci,ku dage kada kuyi wasa da ita). Ta roqi Allah dawwamammiyar soyayya a zuciyar mijinta,da kariyar Allah daga jinsa ganinsa da zuciyarsa dama al'aurarsa akan kowacce diya mace idan ba ita ba.

Cikin wani irin aminci sakewa da walwala take kula da yaranta dukka guda biyar din. Tana da wadatattun masuyi mata hidima,yayin da ita kuma ta tattara damuwarta dama kulawarta dukka akan mijinta.

Sai data warware sosai sannan yazo mata da komai da komai na kammaluwar ginin gidan marayu maka maka har guda uku a arewacin Nigeria,da kuma gina sabuwar foundation ta kula da marayu da zawarawa da yara marasa galihu.

Kukan farinciki sosai ta dinga yi,saboda cikar ragowar burinta kenan a rayuwa. Wani irin katafaren gida ne da aka tsarasu bisa tsarin ginin unguwa guda wato estate. Da makarantunsu tun daga primary har zuwa secondry,jami'a kuwa a qasar waje yayi planning ya dinga turasu qasashen musulunci,don yana sanya ran a can zasuyi karatu me kyau,ba tsangwamar mutane ba takurawarsu.

Komai an wadata gidajen dasu,abinci sutura wutar lantarki da kayan more rayuwa cikin kowanne gida da dakuna. Cikakken tsaro da tsari na addinin musulunci wanda aka ginashi bisa jagorancin malam da a yanzun shine babban me bawa jadda shawara akan duk wani abu daya shafi zakka da harkokin addini cikin rayuwarsa.

"Wannan gidan da komai dake cikinsa kuma mallakin su ayshatu ne......na kusa dashi kuma na JIB ne,sai kuma guda dayan na busari" Ido ta waro tana mamaki,ya akayi yasan su jib?.

"Maida idon ranki ya dade don ban gaji da kallonsu ba daga nan har qarshen rayuwata......karki ce komai,tun daga randa na sameki cikakkiyar mace na bibiyesu na kuma jawosu cikin rayuwata,yanzu haka busari shine shugaban drivers na kamfanina,Jib kuma yana jagorantar sashen tsaro na daya kamfanina dake lagos" A ranar idan farinciki yana kisa tabbas ta tabbatar sai buzunta. A yadda abubuwan sukazo tana buqatar ma'aikata ita kanta,tana buqatar su zauna su qarasa tsara komai kafin ranar da zaa qaddamar da qungiyar da kuma qaddamar da gidajen marayun dake kano kaduna da abuja.

Sosai ta tsananta bincike cikin danginta na uba harna uwarma,ta kuma zabi amintattu da zasu dinga gudanar da komai,nata aikin kawai tana daga cikin gida xatayishi cikin system sai waya idan ta kama,sai kuma ziyara da duba gidajen lokaci bayan lokaci da zata dinga zuwa,da kuma wani taron idan ya kama,kamar ganawa da ma'aikatanta da sauransu.

Abinda ya bata mamaki shine,albashin da fuad ya sanya mata na million din kudade. Abun ya qarasa kasheta da mamaki,itace shugaba,yayi dukka aikin ya mallaka mata,ya bata dama ta sakawa kowa albashinsa kuma zata dinga biyansa......sannan ita kanta kuma ya yanka mata albashin miliyoyin kudaden da batasan ma me zatayi dasu ba.

Kuka kam wannan karon barinta yayi tayi abinta,ta shimfida fuskarta saman kyakkyawan qirjinsa tayi kukanta yadda takeso ta kuma zarce da godiya ta baki da kuma godiya ta aikace. A ranar ta saje yarda da kanta,ta haukatashi da wani irin salo......ta sake godewa Bgawo's kitchen and aphrodisiac. Mama macace dattijuwar qwarai data iya gyara a gargajiyance,saboda cikar hankali da shekarunta da takai matakin dattijantaka,bata taba ganin gyara irin nata ba,gyara na dattawan tsofaffi da babu side effects akai sai tsimuwa da jikinki zaiyi da kyau,wanda sun shigo duniyar gyara ne saboda bada gudunmawa ga matasan mata dake tasowa cikin rayuwar aure a yanzu.08127084190/08104553105.

Yana jinta da kima a rayuwarsa fiye da duk wani abu me kima daya mallaka......yana jinta a matsayin abu mafi tsada da daraja a rayuwarsa,don haka komai nata ya zama na daban kuma na musamman.

Wani tsaro yake bata,guards ya samar mata na musamman,wadanda suke tare da ita a duk sanda zata fita ko zata tafi zuwa wani gurin. Ya samar mata 'yan sanda mata biyu jajirtattu da zasu kasance da ita a motor din da take ciki,bayan 'yan aikinta dake kula da lamarin yaranta,sauran motocin kuma duka guards dinta ne. Cikin lokaci qalilan Sabreen din ta zama wata me tsada,komai nata kuma ya kuma sake zama na musamman,ya canza mata mota tata ta hawa da duka sabbin motocin da masu tsaronta zasu dinga using.


*_BAYAN WASU SHEKARU_*

*JADDA'S VILLA*


JADDA'S VILLA shine sunan dake rubuce b'aro b'aro daga tsororuwa babban ginin gidan. Rubutun an yishi ne da ruwan GOLD jikin wani qawataccen allon qarfe da aka yiwa wani irin design me azabar kyau da daukan hankali.

Wani irin shimfideden gida ne,wanda a qalla ya qunshi maka makan mansions a cikinsa guda shida. Kusan komai na gidajen iri daya ne,saidai banbancin girma da wani gidan yafi wani yawan dakuna da kuma qawatuwa da kayan alatu na rayuwa,daidai da yadda mamallakan gidan suke da buqata.

Idan ka kira JADDA VILLA da aljannar duniya sam sam bakayi laifi ba,don inda akwai sunan da yafi haka nuna tsananin tsari da cikar suffa da haibar gida ya cancanci ka bashi.

Gidane daya mamaye jadda street gaba daya daga hannun dama,sai hannun hagun dake dauke da qawatattun gidajen hamshaqai masu fada aji cikin unguwar da sai ka isa wane zaka mallaki gida a cikinta cikin birnin tarayyar abuja.

Ba gidan kawai ba,unguwar kanta sai kabi matakai daya bayan daya kafin ka samu nasarar shigarta,bayan kuma ka shiga din zai zame maka barazana hanyar shiga JADDA VILLA. Birnin da ya shiga bakunan manyan masu kudin da suke ganin wuyansu yayi kauri a duniyar naira.....birnin daya girgiza zukatan al'umma da dama ciki harda manya manyan masu kudi na qasata dama qasashen duniya gaba daya.

Manyan gate gate guda biyu da matsakaici guda daya dukka saika wucesu kafin kakai ga shiga BIRNIN JADDA kaman yadda aka rubuta daga cikin gidan gate din farko.

Daga can cikin daya daga cikin gidajen dake cikin jaddas villa din,cikin tsakiyar wani qawataccen courtyard da aka

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login