Showing 165001 words to 168000 words out of 557259 words

Chapter 56 - πƒπ”ππˆπ˜ATA BOOK1 AND 2 HAUSA NOVEL

HUGUMA   

03 Nov 2025

489

Daga bakin qofa ya fara tsaiwa,ya harde hannayensa a qirjinsa yana qare mata kallo. Tana kwance cikin lallausan blanket da aka rufeta dashi har zuwa qirjinta. Ba qarin ruwa babu na jini.....baiga oxygen ba,saidai akwai canola daya kula da ita a hannunta.

Idanunta a rufe suke,a haka tafi kama da me bacci. Sake nutsa idanunsa sosai yayi saman fuskarta yana karantar fuskar bayan wucewar kowacce daqiqa har ya samu matsaya cikin zuciyarsa dangane da ita,ya sauke hannayen nasa yana sake qarasawa ciki,takun likitan kuma sai ya biyo nasa takun.

Fasa qarasawa yayi bakin gadon,ya zube hannayensa cikin aljihun wandonsa ya waiwayo a nutse yana amsa sallamar likitan gami da zube masa idanunsa.

Dan tsamurmurin likita sanye da lab coat,hannunsa kuma riqe da wani file,yayin da wuyansa ke rataye da abun auna gudun zuciya.

Ta cikin farin gilashin idanunsa ya kalli fu'ad. Kallo qwaya daya tak daya mamayi zuciyar likitan da wani irin mahaukacin kwarjini tare da zallar mamakin wanzuwar muhammad jadda cikin asibitinsu.

"Meye ya kawo mamallakin jadda diamond chore resources asibitin?" Ya tambayi Kansa da kansa tsoro da kwarjini suna cikashi.

"Kada dai ace da gaske suke da suka gaya masa ita din mamarsa ce?" Wannan maganar ta sake tsarga masa wanda hakan ya sake sakashi jin rudani yana mamayarsa. Yasan waye muhammad jadda,bazaiso kuma fadawa matsala dashi ba,ba zayaso fadawa hurumin da ba nashi ba da karatunsa daya samu yake riqe kansa da iyalansa.

"Shine likitan?" Fu'ad daya gama qarewa likitan kallo ya furta yana duban musaddiq daya qaraso daga ciki yayi tsaye gefan fu'ad din

"Shine hamma" Ya amsa masa shima yana maida dubansa kan likitan.

Duk wani qoqari nasa ya tattaro,ya kalato yawun bakinsa yana dora murmushi saman fuskarsa

"Barka da zuwa asibitinmu yallabai.....munyi farinciki da shigowarka yau asibitinmu......hakan ba qaramin qarin kima da martaba bane ga asibitinmu damu kanmu gaba daya". Hannayensa zube a aljihun wandonsa,kamar yadda idanunsa suke a Kan likitan.

"Madalla.....inason magana dakai if possible"

"To......ba damuwa.....ba matsala hakan,muje ne ko a nan zamuyi?" Yayi tambayar yana raba idanunsa tsakanin fu'ad din da musaddiq.

"Qaraso ka duba patience dinka".

"Aah yallabai..... Ai ba za'a barka a tsaye kana jira ba.....hasalima ban jima da fita a dakin ba ai". A nutse ya debe dubansa daga kan likitan,sannan ya fara takawa a nutse yana fita a dakin musaddiq ya mara masa baya.

A hankali yaci gaba da takawa yana fita a asibitin. Bai dakata ba har ya isa inda motarsa ke ajiye. Kafin ya qarasa daya daga cikin guard din ya zabura ya bude masa sannan ya jira isowarsa

"Kada ka rufe.....zanga baqo"

"Yes sir" Ya fadi yana barinta a bude kaman yadda ya buqata. Budewar data bash daman kallon likitan da kuma karantar kowanne motsi nasa cikin wani kallo da ba na kai tsaye ba wanda ke cike da hikima.

Wani irin bugu zuciyarsa keyi musamman sanda ya tsinci kansa tsamo tsamo tsakanin Jordan da abdulbasit da suka kusa rufa tsahonsa. Ya daga kansa yana duban fuskokinsu da suke manne da baqin gilashin idanu.


*D U N I Y A T A*

*_D U N I Y A T A_*

Page 89
________________________
https://chat.whatsapp.com/DT97XBDyEfyEwniN0a09Cz

*_assalamu alaikum warahmatullah_*

*_kina ta ganin kaya kala kala online?,kinason siya amma kina tsoron damfara?,tsada ko rashin ingancin kaya?_*

*_wannan tsoro da taraddadi ya yanke miki indai da HUGUMA CLOSET_*

*_muna da nau'ikan kaya kala daban daban bisa farashin da ba kowanne dan kasuwa ke iya bada kayansa akan hakan ba_*

Shadda
Laces
Atamfa
Kayan yara English wears dana jarirai
Qawatattun handbags
Mayafai
Abayas da jallabiyas
Inner wears
Huluna na maza da mata yara da manya socks
Takalma na maza da mata yara da manya
Lafayas
Sarqoqi agoguna banguls da rings

_kai komai daya danganci kayan ado na fita kunya wa dan adam_

_bisa farashin da zaiyi daidai da buqatarka_

*_Me kike jira sallah na gabatowa?,ana can ana ruwan suturu daidai da qarfin kowa?_*

*_masu manyan qarfi da matsakaita?_*

*_ki dinga siya da kadan kadan kina saka kudin kina tara abinki har sukai sanda zaki karba?,ko ki siya lokaci daya a kai miki_*

*_muna aika kaya ko ina a duniya in sha Allah_*

*MUNA BONONZA LOKACI LOKACI NA DUKA ABINDA RABO YA TSAGA*

*_MASU REPOSTING DA MASU SARI DUKA BA'A BARSU A BAYA BA,KI SIYA KI SAIDA KI SAMU RIBARKI HANKALI KWANCE,BA TARADDADIN INGANCIN KAYA KO WANDA KIKA BAIWA KUDINKI_*

*_KIYI JOINING KI TURAWA 'YAN UWA DA ABOKAN ARZIQI_*

*_INGANCI RAHUSA GASKIYA DA AMANA SHINE TAKENMU_*🫢🏽🫢🏽✌🏽✌🏽✌🏽✌🏽
https://chat.whatsapp.com/CKY0xZDtpby6MTkGrPkXLr
_________________________

PAGE 89


"Enter" Jordan yace dashi yana jiyowa sosai gareshi gami da nuna masa cikin motar. Bashi da abunda zai ce don shi kansa yasan nan din ba wajen wasa bane,ya daga qafafunsa da yaji sun fara masa nauyi yana sanya jikinsa cikin motar,yana kuma jin yadda gumi yake tsargo masa daga kowacce kafa ta jikinsa.

Set din dake opposite nasa ya masa nuni,hakanan ya zauna yana qoqarin gyara lab coat dinsa yana hadiye wani miyau me kauri. Idanu kawai fu'ad din ya sake zuba masa duban daya sanyashi kasa nutsuwa ya dinga gyare gyare,daga gyara agogo zuwa gyara rigar jikinsa da kuma hannun rigar.

A nutse ya janye masa idanun,sannan ya motsa bakinsa

"Ya sunan doctor din?"

"Ni....Dr kamal......sunana Dr kamal". Kai fu'ad ya jinjina yana lumshe ido gami da budesa sanan ya maimaita sunan a hankali

"Good Dr kamal,ina maka murnar samun damar zama likita ga mahaifiyata......am.....inaso nasan da meye da meye suka ce ka gaya mana a matsayin cutar dake damunta?". Sosai maganar ta rudashi saboda tazo masa a bazata,ya dubi fu'ad yana qoqarin nuna masa gaskiyarsa

"Su waye?.....Ni ba wanda yacemin ga abinda zan fada sai abinda bincikena ya gano".

"Kamal!" Fu'ad ya kira sunansa da wata irin deep voice dake dauke da amo me tsoratar da wanda ake magana dashi.

"N...na'am"

"Lookat me......" Ya sake fadi masa yana tsareshi da idanunsan nan da suke sanya Dr kamal jin kamar zaya narke.

"Kayi haquri yallabai" Dr din ya sake fada kansa tsaye ba tare da fu'ad din ya sake cewa komai dashi ba. Wani irin rudani da firgici suna ratsashi.....gaba kura baya sayaki,yasan hajja harira ba sanin shanu ba,amma ta yaya zai yadda yayi jayayya da mutum irin muhammad jadda din?,wanda yayi imanin ita kanta inda hajja harira ta gama sanin wayeshi da kyau ba zata saka kanta cikin wannan wasan ba.

"Yallabai......sunce zasu biyani bayan barazana da hajja harira tayimin......sunce na kwantar da ita kawai na saka mata ruwa wanda zai qara mata kuzari ne kawai...........sunce tabbas zakazo...idan kuma kazo din na kambama ciwo da kyau,na nuna muku zaman kadaici da kewa ce take damunta,wanda muddin ba'a kula da ita da kyau ba.....an samu wani cikin wadanda sukafi kusa da ita take kuma yawan ambatarsu su zauna tare da ita ba to tabbas zuciyarta zata iya bugawa ayi hasararta......sunce idan.....". Dakatawa yayi ba tare daya qarasa fadin abinda zai fada din ba saboda daga masa hannu da fu'ad yayi. Shuru ya ratsa motar,abinda ya sake ruda Dr kamal,ya sanya hannun rigarsa yana goge gumin fuskarsa bayan ya cire gilashin idanun nasa.

"Sauka kaje....kaci gaba da riqeta.....zaka sallameta,but sai daidai lokacin da na baka umarnin yin hakan"

"Okay sir" Ya fada da gaggawa yana juyawa gami da laluben hanyar fita daga motar,don zaman motar duk da laushin kujerunta da sanyin Ac da wani ni'imtaccen qamshi da yake fita......amma ji yakeyi kaman yana zaune ne cikin qabarinsa.

"Dr" Ya sake kiran sunansa dab da zai sanya qafafunsa a qasa. Adan zabure ya waiwayo yana qoqarin saita kansa.

"Banda wannan harqallar.....ka tabbatar babu wata sauran haramtacciya ko miyagun harqalloli da kakeyi a boye......don idan hakan ta kasance ka tabbata ba zaka tsira a hannuna ba"

"Wallahi ranka ya dade ba ruwana......ni din mutumin kirki ne ka tambayi kowa ma"

"In kuwa hakane ka kyautawa kanka".

"Sauko malam" Jordan yace da Dr kamal din a dake cikin rashin son wasa.

Jinsa ya dinga yi kaman zai kifa sanda yake komawa cikin asibitin. Inda ace yasan da gaske take ita din mahaifiyarsa ce ta yaya zaiyi wannan kasadar?. Fadan giwa da damusa waye yake shiga?,sai wawa sai mahaukaci,shi kam qaura zaiwa asibitin bazai sake shigowa ba sai gobe,duk da yasan bashi da inda zaije yace ya guje masa.

Duk wani mamaki da maamah zata bashi a yanzu ya biyo bayan wanda ya gani a yanzu da shekarun rayuwarsa ta baya. Ko daya bai sake komawa asibitin ba,saidai kuma bai hana kowa zuwa ba. A kwanakin ma gaba daya yana qoqarin ganin ya gyara wasu abubuwa da yake ganin suna qoqarin tasowa can qasan kamfanin,wanda idan har ya bari matsalar tayi girma zata iya jawo asara mafi muni fiye data kudadensu da suka zirare.

A cikar ranar lahadi kusan kowanne bayani ya kammala samunsa,ya shigar da komai cikin documents,sai la'asar ya kammala,don haka daga nan alwala yayi ya wuce masallaci. Daga masallacin ya sake dawowa gida,ya leqa anni da bata jima da dawowa duba maamah ba,sai ya zauna falon bayan ta sanya amna ta dama masa yoghurt da fura.

"Muhammadu" Anni ta kirasa,sai ya dauke idanunsa daga tasha alhadath dake nuna yadda bani Israel ke dake ragargazar Palestinian,hankalinsa ya fara nisa kan hanyar da zai aika musu tallafi ya kuma isa garesu kai tsaye

"Na'am" Ya amsawa annin yana dubanta

"Jiya abbanku ke complain....ko sau daya ance ba'a ganka a asibiti ba......ni kaina ko sau dayan banji kace zaka je ba,sai zama da kaketa yi a sassanka?".

Hannu ya sanya ya karbi kyakkyawan tray din da amna ta jero cups da bowl me kyau dake dauke da dammen yogurt din,ya aje gabansa yana cewa

"Thanks lovy dovy". Qaramin murmushi ta saki,ta juya tana komawa kusa da anni ta zauna.

"Jikin nata da sauqi ai anni......infact ma tun ranar ta samu lafiya.....yau ma zasu sallameta". Ya amsa ba tare daya kalli annin ba,don yasan yana yin hakan zata dago wani abu

"Duk da haka muhammad wannan din baiyi kyau da tsari ba....."

"Yanzu daga nan can zanyi anni kiyi haquri". Kalmar haquri idan ya fadeta da gaggawa haka to tabbas baison bacin ran annin ne,ta gama karantar hakan.

Jujjuya furar yayi sannan yayi bismillah yakai bakinsa. Fuska yadan bata ya daga kai yana duban amna

"Yaushe kika koma sakamin sugar a abin sha?". Kai tadan langabe

"Hamma.....kadan fa na saka maka wai don bakinka yayi taste"

"Zoki dauke abarki" Ya fada yana dan ture bowl din. Da sauri ta miqe tana fadin

"Ayyah hamma.....kayi haquri kada magauta suji kanmu....bari na hada maka wani wannan sai BB farouq yasha"

"Kayi zaton amnan taka tayi hankali ne?,kaima kai ka sowa kanka wannan gallafirin......wai sai yaushe zaka fidda mace ne Muhammadu?,bakasan duk girman namiji aure shike cikashe wani gibi ba?,gibin da babu abinda zai cikeshi face auren?......ita kanta amna yaushe ta fara iya riqe abinda ya dace da itama ballantana ta riqe abinda ya dace da waninta?". Waiwayowa tayi tana duban annin kamar zata saki kuka

"Wayyo anni.....yanzu duk qoqarin da nayi baiyi ba?,hamma don Allah ban canza ba?" Wani sassanyan murmushi ya kubce masa,ya maida kallonsa ga anni

"Tsokanarki fa anni takeyi.....kin canza sosai amna ta,kinyi kuma hankali,yauma nasan akasi aka samu,ki dama min wata ki sakamin apple a ciki da grapes ki ajiyemin,idan na dawo zan sha".

Tabe baki anni tayi tana kauda kanta

" Ai daman.....indai abu da laifin amna duk girmansa saika maidashi qarami......da tashi kayi kaje ka shiryadinma da zaifi maka". Murmushi ya saki ya miqe a nutse. Duk wani jini na anni girmansa yake gani martabarsa yake gani hakanan qaunarsa yakeyi.

"Hamma na shirya na rakaka?" Ta fada tana tallafe da tray din.

Bayason zuwa da ita,saboda ya tabbatar ba zata samu marabtar data dace da ita ba,amma bazai iya cewa bazaije da ita ba,don haka yace

"Ki shirya.....but be fast....banson jira"

"Yanzun nan hamma" Ta fadi tana qara hanzarin barin wajen.

Suna hanya tana cikashi da labarai kala kala wanda hakan yake masa dadi da debe masa kewa. Don amna din wajen quruciya da sakalci irin na autanni ba daga baya take ba.

Koda suka isa cikin asibitin sai ya kalleta

"Ko ki zauna a nan,ko na yiwa Jordan magana ya kaiki ki zabi duk abinda kikeso.....kina da 30 to 40minutes"

"Yay!.....thank you hamma na" Ta fada da tsananin murna.

Zaune take daga bakin gadon da kwata kwata cikin kwanaki ukun a duniya taji ba abinda ta tsana sama da kwanciya a kansa. Kwanciyar da babu alamun nasara a tattare da ita,kwanciyar da bata amfaneta da komai ba saima sake haska mata rashin nasararta muraran da ake sakeyi.

"Ba alamun nasara hajja......zuciyata tafi karkata akan na tafi plan C.....a plan C ne kuma nakejin cewa koda sharadina zai zama silar rugujewar fu'ad wannan karon basan sassauta masa ba......a wannan karon a shirye bake na gindaya masa sharadin da nayi imanin bazai iya tsallakeshi ba.....a wannan karon hajja......ban yarda koda da darsawa a rai ba zuciyata ta darsamin wai bazanyi nasara ba.....dole dole dole nasara ta kasance a tsagina.....hajja a yau zan bar asibitin nan,ina da buqatar na huta saman gadona nayi bacci me lafiyar da zai bani damar tsara komai da kyau cikin kwanyata.....na kuma wayi garin litinin da wannan shirin".

Kai hajja ke gyadawa tana kuma sake juys Plan C din maamah data tabbatar zaiyi wahala idan ba abinda take hasashe bane ba.

"Hakan ma yayi,abun ni kaina ya soma shallake tunani na.....amma mariya anya shima baida hatsabiban da suke masa aiki?" Shuru maamah tayi,ko qwalqwalwarta bata kama muhammad yana biye biyen nan ballantana hankalinta. Tun daga haihuwarsa zuwa tasowarsa kawai tasan ya banbanta da sauran yara,quruciyarsa ma ta daban ce a cikin yara,zuwa sanda ya cika shekara goma cas a sannan ta sake ganin banbanci mabayyani a kanshi.

Shigowarsa dauke da cikakkiyar sallama sai ta zama tamkar amsa ga tambayoyin hajja harira. Bakinta yana dan rawa tana kamo amsar sallamar da qyar ta hada kalaman tana amsa masa.

A nutse ya tako ciki idanunsa akan maamah din data dauke kanta daga gareshi gabanta tana ji yana faduwa. Haka kawai ita kanta sau tari sai taji ya mata kwarjini,fargabar kada dai ace yaji wani sashe na tattaunawarsu yana cikata.

Duk yadda hajja ke qoqarin ankarar dashi tana wanze a dakin ta hanyar jera masa sannu da zuwa amma ta gaza samun hankalinsa. Bawai kuma don baijita ba,aah haka kawai yakejin wani abu na daban game da matar,sannan kuma kwanyarsa a kullum idan ya ganta takan yawaita qoqarin tunata cikin jerin sahun mutanen da yaga gilmawarsu a shekarun da abbansu yake raye.

Kaman bai lura da sauyawarta ba,yaja kujera gaban gadon ya zauna yana gaidata. Ta amsa masa tana hadiye bacin ranta. Fada takeson masa sosai ko zata samu sassauci amma kuma idan ta tuna a gobe akwai nata plan din dai ta danni zuciyarta,saidai duk da hakan sai data b'ara

"Kasan ina nan amma fu'ad ka banzatar dani?,ko ka manta ba'a canzawa tuwo suna?"

"Kiyi haquri" Ya jefeta da kalmar nan da har ta fara tsanarta saboda yawan fitarta daga bakinsa.

Shuru yaci gaba da ratsa dakin ba tare da kowa yace da dan uwansa komai ba,kafin daga bisani aka turo qofar.

Dr kamal ne,ya qarasa shigowa cikin takatsantsan da tsantseni,wanda dukkan me hankali yana kallonsa zai fahimci hakan.

"Kwanciyar haka ta isa?,xaki iya komawa gida?" Ya tambayeta a tausashe saidai kuma kalamai ne masu harshen damo da yawa a ciki.

Juyowa tayi tana dubansa maganar tana qoqarin fassara kanta da kanta cikin qwalqwalwarta. Ta zargi wani abu,amma kuma yanzun ba muhallin wannan bane,don haka ta dauke dubanta ta maida kan Dr kamal

"Ina buqatar sallama Dr,naji qwarin jikina".

" Yanzu in sha Allah" Ya fadi yana bude file dinta. Hannunsa yana dan rawa yayi rubuce rubuce ya maida ya rufe,sai fu'ad ya miqa masa hannu Kai tsaye,yadan kalleshi sannan ya miqa masa file din salin alin.




*D U N I Y A T A*

*_H U G U M A_*

PAGE 90



*_MONDAY_*
*_Tushen aiki,ko nasara na tsoronki_*


Cike da confidence take shiryawa cikin tsadaddiyar dubai abaya budaddiya data lullube jikinta ainun.

Wine color wadda aka qawata qasanta da kuma qasan wandon abayar da wasu irin stones da zare ruwan gold masu daukan hankali.

Gaban madubi ta matsa tana saka brush tana sake kwantar da doguwar sumarta me yauqi da rashin cika sannan ta ware madaidaicin mayafin abayar tayi rolling dinsa saman kanta,abinda ya bawa kyakkyawan fuskarta daman fita tarwai ta kuma haska da wine color din abayar jikinta.

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login