Showing 258001 words to 261000 words out of 557259 words
wanda zai sauka daga kan tsari da kuma muradinta?. Zuwaira ce ta fado mata rai,sai taji tana samun sassaucin tsoron da kuma firgicin da take ciki.
Hannunta dukka biyun ta sanya ta dafe kanta.
"Huda,ya kula da ita ya bata magani tasha?,who's she?" Abinda ta dinga maimaitawa kenan. Hudan da har yanzu take ganin tana buqatar therapy tana buqatar counselling akan mikin da nasir yayi mata.......yanzun kuma tana shirin sake fadawa wani abun na daban?,kanta da zuciyarta kuwa zasu iya dauka?,ya kamata ta ciyar da d'anta ta kowacce siga muradinta.....idan yaso in taga dama bayan ta mallakeshi ta yayyankashi ta cinye.
Abu daya ta kasa jurewa ya kuma gaza barin zuciyarta huda,ta yaya zata ji muryarta?. Bata taba jin dauke wayoyin ya dameta ba irin yau,ta dinga jin kamar tayi hauka idan ta tuna ba wata sauran hanya da zata iya samun damar magana da huda.
Sosai tayi qoqarin ganin amna bata gane komai akan fuskarta ba. Ta kama mata aikin sukaci gaba dayi,tana ci gaba da mata hira tana bata labarin fu'ad. Kwata kwata bata jinta ma ballantana ta fahimci abinda amna din ke fada,a haka suka kammala amna ta fito tabar mata kitchen din. Sosai ta zazzaga dukkan abinda ya kamata ta sake juya abinci ya koma ainihin launinsa. Ta tsaya kaman ko yaushe ta zubawa abincin idanu zuciyarta na wani yamutsawa,mafi rinjaye na zuciyarta tana jin kamar wani yanayi mara dadi,wani yanayi da yafi kama da rashin jin dadi?,rashin kyautatawa?,ko aikata abinda ba daidai ba?. Itama bata sani ba,bata taba zaton da hannunta zata iya ciyar da kowanne dan adam abinda bai kamata yacishi ba......saidai abu daya ta sani shine....itadin guba ce ga duk wanda yace zai kawowa innocent rayukan nan guda uku farmaki.
Takun da taji dake alamta mata an shigo kitchen din shine abinda yayi bala'in razanata. Da sauri a kuma birkice ta daga kanta tana duban me shigowar. Zuwaira ce fuskarta da murmushi ta qaraso cikin girmamawa.
"Afuwa,dama cewa nayi bari nazo naji ko akwai aikin da za'a kama miki?" Tayi maganar tana duban warmers din da a gaban idanunta tana labe sabreen din ta cika aikinta tsaf. Idanunta ta lumshe tana jin yadda zuciyarta ke bugawa,sannan ta tattaro dukka qarfinta ta bude idonta akan zuwairan
"Wannan shine kuskurenku na farko,bana buqatar ki sake shiga wani guri a cikin gidan nan ba tare da kin tsaya kin nemi izini ba an kuma baki" Kai ta rusunar
"Ayi haquri bazai sake faruwa ba in sha Allahu" Bata iya amsa mata ba,sai kawai warmers din data mata nuni dasu
"Ki kaisu kan dining" Tayi maganar tana dosar qofar fita a kitchen din,don sam bata da qwarin tsaiwa ci gaba da magana.
Tana sanya qafafunta da zummar fita tana sako tata qafar abinda ya sanya suka kusa karo da juna,yatsun qafarta suna caki na sabreen haka gwiwarta saita tsaya cak bata ja baya ba bata kuma koma ba. Tsaiwa cak itama sabreen din tayi tana danjin qafarta na dan radadin kadan saboda qafafunta akwai alamun tana ajiye farce.
Shirun da sabreen din taji ya sanyata daga kanta ta sauke dubanta akan laila. Tana tsaye cak ba alamun zata kauce mata ta bata hanya. Bisa dukkan alamunta tana jiran sabreen ne ta kauce mata,kota koma sai ita ta wuce. Cikin qasa da second biyu sabreen din taji wani abu ya saukar mata,wani abu me kama da izza da jin mallaka ya mamayeta. Ta lumshe idanunta sannan ta zubesu fes akan laila tana duban tsakiyar qwayar idanunta da wani irin kallo dake qure qarfin halin mutum. Da farko itama laila din ta zuba mata idanu,saidai a hankali wani kakkaifan abu ke ranqwafar da nata idanun. A hankali taji ta gaza jurewa,saita dauke dubanta daga kan sabreen din tana ja da baya,ba tare data sake dubanta ba ta rabata ta wuce a tsanake ba tare data sake duban sashen da take a tsaye ba.
Da idanu tabi sabreen din har ta wuce,ta maido dubanta cikin kitchen din tana jin kamar yau karon farko ta tozarta......a karon farko taji wata 'ya mace tayi mata kwarjini,har kuma ta juyata ba tare data furta kowacce kalma daga bakinta ba. Hada ido sukayi da zuwaira,sai zuwairan ta tabe baki tana dauke kai. Cike take dama da lailan,cike kuma take da yadda maamah ta dinga jaddada mata ta girmama lailan,don gidan fu'ad a wajen lailan tamkar gidan mahaifinta yake,tammar kuma gidan yayanta da suke uwa daya uba daya yake.
"Idan me guri yazo dai me tabarma nadeta yakeyi,nan din dai akwai macen data amsa sunan matar gidan,komai ayishi bisa takatsantsan". Sarai ta fahimci abinda zuwairan ke nufi,amma sai taga sam bata da lokacinta,don abinda sabreen tayi yafi tsaye mata a rai,yadda zaiyi handling nata. Da gaske komai na gidan yayi mata,da gaske zuwa yanzu tanaso ace itace mamallakiyar gidan. Ta cika gidan da izzarta da mulkinta da kuma ikonta kwatankwacin hajja,tako ina ta zama ME MULKIN gidan.
Samun amna tayi tana shirin tafiya.
"Har me?" Ta fada cikin nuna kulawa. Murmushi ta saki
"Driverna na aje adda tun dazun fa,daga cewa anni zanzo na miki sannu da zuwa". Fararen idanunta da a yau take jinsu wani iri ta kada,bata da energy din dogon magana.
Closet dinta ta bude kawai tayita fiddo abinda take ganin ya kamata ta bawa amna. Ta hada abubuwa cikin qaramar jaka me kyau da daukan hankali.
Ido amna ta fiddo tana nuna tsananin murna da mamaki
"Duka adda?" Ta fada da murmushi. Abun ya burge sabreen sosai,yadda amna din ta nuna,duk kuwa da cewa tasan tafi qarfin duka abinda zata bata din.
Fitowar zuwaira da laila daga kitchen din ya danja hankalin amna dake qoqarin ficewa,ta bisu da kallo kawai kafin ta juya a hankali ta fara takawa tana fita daga falon.
"Sai haquri ranki ya dade....laila kenan..... D'iyar hajja harira.....hajja harira 'yar majalissar zartarwa hajiya mariya maamah". A badini kyakkyawan masauki maganar zuwaira ta samu,hajja hariran da sukayi tattaki har cikin gidansu suka kai qudurin aurota don su cimma buqatarsu?,ta yaya zata manta wadannan fuskokin,ranar,dama abinda ya faru a ranar....har maamah din tana da qarfin halin ajiye budurwa irin wannan a gidan d'an data haifa?,wanne irin kwado ne wannan?,budurwar da babu wata alaqa tsakaninsu face ta zallar qawancen dake tsakaninsu?,a tsarin abota da mu'amala da zata fishshi dan adam tasu bata kan ko guda daya. Kai ta jinjina,information din ya mata kyau da ma'ana,amma kuma batajin zata sakewa zuwaira ko ta nuna jin dadin hakan.
"Ya kamata ki dinga tsaiwa a iyakokinki kawai" Abinda tace da ita kenan tana takawa zuwa hallway dinta don komawa dakinta,duk da har yanzu ba wani cikakkiyar nutsuwa ko sukunin data samu daga uban tunanin dake addabarta,gefe guda kuma tana cike da fata da fargabar sanya abincin a bakinsa ya zarce zuwa cikinsa.
*_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_*
08187255862
π π π π π π π π
_ZAFAFABIYAR_
ΜΆBΜΆOΜΆOΜΆK ΜΆ2
β±§Ιβ²Ιβ₯β³
ππΌππ 33
_Daga nana Aisha R.A tace:manzon Allah S A W yace:Duk matar da tayi aure ba tare da izinin waliyyinta ba,to aurenta batacce ne,idan mijin ya tare da ita taci sadakinta saboda halastar farjinta a gareshi_
33
β
"ma sha Allah,sannunta da qoqari" Anni ta fada sanda ta gama ganin kayan da amna ta kawo wanda sabreen ta bata.
"Tana da kirki anni......amma sai nake ganin hamma me irin halinsa ya dauko,she's so quite,batason hayaniya da yawa,bata fiya bada amsa ba ko magana,tafi yawan murmushi kawai". Murmushi anni ta sauke,har zuciyarta tana sake jin yarinyar tayi mata,a duk wani lokaci da maganarta zata tashi tana sake jin sabreen ta kwanta mata ne.
"Ai dama sai hali yazo daya ake iya zama ko?,Allah ya qara hada hankulansu......yauwa farouq yayi nemanki kuwa sanda kika fita......naji kaman yana maganar zaku abuja passport dinki yayi expired,za'a sake miki wani". Idanu amna ta fiddo sannan ta qanqame anni
"Anni hala Lokacin tafiya ya kusa?". Dan tureta kadan tayi daga jikinta
"Gashi kuwa kin gani keda tafiye tafiye basa isarki" Dariyar jin dadi ta qyalqyale dashi.
"Amna wannan tafiyan daban yake a rayuwata Allah,ba wani trip da yakaimin wannan dadi....whole family fa anni.....wannan karan kuma abun zaifimin dadi saboda nima na samu partner addana,adda sabreen,na daina maqalewa su ya saddiq suna wulaqantani,wannan karon tafiyar zai zama na musamman" Tayi.maganar with full excitement. Da kallo kawai amna ta bita kafin ta saki murmushi,ita kanta tasan tafiyar zata qara dadi musamman da idanunta zasu dinga gane mata fuad dinta da iyalinsa a gefe,cikon mafarkinta kenan
"Anni bari naje na sameshi" Ta fada tana daga yatsunta gami da lissafa watan da tafiyar tasu zata kama
"Yes" Ta furta tana jin farinciki yana lullubeta,saita cilla da sauri zata fita tana cewa
"Dis time har abba fa sai na karbi kudin tsaraba a hannunshi,komai bibbiyu zan dinga siya nida addana"
"Kunfi kusa ai" Anni ta bata amsa. Dakatawa daga fitar da anni taga amna tayi shi ya sanyata daga kai tana dubanta zuciyarta cike da tambaya. A sanyaye taga amna din ta dawo tana zama gefanta
"Lafiyarki ke kuma?" Ta tambayeta tana nazartarta da kyau
"Wani abu na gani anni a gidan hamma". Jin an ambaci fu'ad din ya sanyata tattara hankalinta akanta
"Me kenan?" Ta amsawa amnan cikin zuciyarta tana fatan ba wata matsala bace a tsakaninsu.
"Anni.....me aikin gidan maamah na gani,ita da wata budurwa......bansan budurwar ba amma tana kama da wannan qawar maamah din aminiyarta dinnan....."
".....hajja harira" Anni ta samu kanta da fada ba tare data shirya ba
"Eh ita" Ajiyar zuciya anni ta fesar
"To shine me amna?" Ta furta cikin hikima. Tun asalin tarbiyya anni irin matannan ne da basa bari yaro yana kawo musu hira ko maganar wani guri. Qasa amna tayi da idonta
"Ba komai,kawai anni ji nayi jikina bai aminta dasu ba,daga yanayinsu fa anni kamar a gidan zasu kwana fa,qilan ma komawa gidan sukayi Allah anni". Ta fada tana bata rai. Da kallo tabi amnan,amna din ba yarinya ce qanqanuwa har can can ba,kome ake ciki ko yake faruwa tabbas dole tana gani tana kuma fahimta.
"Hammanku majibancin lamura da jama'a ne,bazai zama abun mamaki ba idan anga sabbi ko baqin fuska a gidansa ba,kedai kici gaba da taya dukka 'yan uwanki da addu'a". Kai kawai amna ta gyada ba tare data samu cikakkiyar gamsuwa da bayanin anni ba,ta miqe tana fita daga dakin kamar yadda tayi niyya da farko.
Fitar amna dukka sai hankalinta ya dawo jikinta,sam sam taji bata gamsu da wanzuwar zuwaira da waccar yarinyar a gidan ba. Tasan wacece maamah,tasan kuma dukkanin wanda ya rabu da ita yaya dabi'arsa zata iya kasancewa. Indai da wata manufa ko wani qullin daban aran maamah din,muddin tana raye ba zata taba bari haqarta ta cimma ruwa ba. Koda ta dauke idanu akan abubuwa da yawa,koda tayi kawaici akan abubuwa masu yawa....amma a nan ba zata bari ba,ba zata bari tabi fu'ad har rayuwa cikin gidansa ta ruguzata ba. Saita jawo wayarta tana qoqarin danna kiran.
*SABREEN*
Batasan adadin sau nawa ta leqa dining din ba da zummar ganin ko ta samu nasara ya taba kayan abincin?. Saidai a duk gewayen da zatayi bataga wani alamun taba komai ba cikin kayan dake danqare a table din ba.
Ba iya yaci abincin bane kawai damuwarta ba aah......tanaso tayi amfani da wannan damar ta karbi wayarta a hannunsa,tanaso duk yadda za'a yi ta samu cikakken bayanin yadda su hudan suka koma qarqashin kulawa da mulkin maamah. Abun yana tsananin daure mata kai......ta yarda da momma bahijja....ta kumayi imanin haka siddan ba zata bari haka ta faru ba,duk dadai ma batasan ainihin wacece maamah din ba. Sam bata sako kawu rufai a ciki,shikam tasan ko ya fita sanin wacece mariya to zai aikata fiye da hakan ma.
Zuwa sha daya na dare haqurinta ya gaza,ta miqe da wani irin kaiwa maqurar haquri tana yafa mayafinta saman doguwar rigar jikinta ba tare data buqaci dankwali ba ta sanya slippers dinta tana bude qofar dakin ta fice.
Kamar magen dake kwanton farautar kamun bera haka ta dinga tafiya a hankali tana durfafar stair case din dake facing dinta. Duk taku daya sai bugun zuciyarta ya qaru,amma kuma tuna huda nadra da haneefa kadai ke qara mata qwarin gwiwa.
Tana jin a kansu zata iya komai,zata kuma fuskanta da tunkarar komai da kowa.
Cak ta tsaya a stairs din farko tana jin kaman wanda ke kusa sosai da ita idan ya qurawa qirjinta idanu zai iya ganin yadda zuciyarta ke bugawa ma.
"Shi waye?,mutum ne kamar kowa,mutum ne kamar ni,bashi da wuta bashi da aljanna,bai isa kuma ya yankani ya cinye namana ba" Ta gayawa kanta da kanta murya can qasa qasa dukka tana zaton BUGUN ZUCIYARTA zai daidaita. Aqalla ta tsaya jiran mintuna kusan goma amma still ba abinda ya canza,sai kawai ta runtse idanunta ta kama makarin stairs din ta fara haurawa saman da wani irin confidence da batasan daga inda ta aro shi ba.
Idan ba jikinta da hancinta ne ya mata qarya ba,to tabbas atmosphere da weather na wajen daban yake dana kowanne bangare na gidan. Wani irin lullumsan yanayi da wani irin kebantaccen qamshi da bata taba jin makamancinsa ba. Bata taba lura da cewa shimfidadden carpet bane kan stairs din sai a yanzun da qafafunta ke barazanar nutsewa a cikinsa. Bayan qafafunta sun nutse din kuma wani irin sassanyan yanayi tafukan qafarta ke riska a can cikin carpet din. Duk yadda taso jure qauyancinta amma abun yafi qarfinta,dole ta dinga bin carpet din da kallo har zuwa sanda ta riski wata pivot door wadda gefe da gefanta duka glass ne da bazaka iya hango ainihin parlor din ba,yayin da daga tsakiya ta kasance ta gogagen katako da aka yima design na zamani wanda ya maidata smart door. Tun daga zubin qofar tasan wajene na musamman kuma kebantacce,ta bangare guda kuma taji dadin samun qofar a bude,banda haka da sai tayi tsaiwar da qofar zata gama tantance wace kafin ta bata daman shiga parlor din.
Mutum ne shi me wani irin jiki wanda baya qaunar zafi tun asali,saidai duk da hakan tsananin kare lafiyarsa ya sanya bai fiya kwararawa kansa A.c ba. Duk wanda ya sanshi ya sanshi da wannan dabi'ar na kaucewa abubuwa masu sanyi ciki kuwa harda ac din.
Zaune yake saman wata qawatacciyar minotti sofa qwaya biyu dake bayan qwatattun Belgium sofas din da aka yiwa yalwataccen parlor din ado masu wani irin design me daukan hankali. Daga bayan Belgium sofas din aka yi wani muhalli na daban da aka zuba minotti sofas guda biyu wanda suke bashi daman kashingida ko miqe qafafunsa a duk sanda yaso.
Dogayen qafafunsa na miqe saman sofa din,yayin da night shirt dinsa ke ajiye a gefe,daga shi sai gajeran wandon rigar wanda iyakacinsa cinyoyinsa. Hakan ya bayyana zallar halittar fararen cinyoyinsa dake lullube da baqa sidik din gargasa. Madaidaiciyar Ac ke kadawa cikin dakin,wadda ba lallai yanayin sanyin ya sanya ka fahimci itace ba saboda glass door din dake hannun hagu na falon da yake a bude,tatacciya iska me kyau dake tasowa daga jikin tsirran da aka qawata wajen dasu tana busowa zuwa cikin falon. Tattacciyar iskar data sanya masa kasala da mutuwar jiki,duk karsashin aikin da yakeyi ya soma raguwa.
Turo qofar da akayi shi ya sanyashi dauke idanunsa daga karanta saqon da William ya tura masa ta email da suke buqatar ya duba da kyau ya karanta ya kuma sanya hannu.
Fes yake ganin fuskarta wadda ke tsaye daga bakin qofar,fuskar data bayyana tsakanin lullubin mayafinta wanda yadan zame baya kadan ya bawa kwantacciyar sumar dake gaban goshinta daman bayyana sosai. Fararen idanunta da suke da wani irin haske ta zube a kansa wani abu na dukan zuciyarta saboda yadda ta sameshi.
Ba wani abu da gajeran wandon jikinsa ya suturta sai qasan cibiyarsa zuwa cinyarsa,don bai samu daman qarasawa gwiwarsa bama sam. Ginannen jikin nasa daya samu kulawa ta kowanne fanni,motsa jiki,tsananin tsafta da kuma cima me kyau. Kwantaccen gashin dake cike da qirjinsa shi ya zamewa faffadan qirijinsa tamkar adon baqin abu bisa farin yanki ko farar takarda. Wani irin kwantaccen gashi daya shirya kansa da wani irin siririn layi har zuwa cibiyarsa ya zarce har qasa.
Har cikin jikinta taji rudewa sosai,don wani abune da tsahon rayuwarta bata taba gani ba,hakazalika bata taba hasashen zata shigo ta sameshi a haka ba. Cikin zafin nama ta juya da niyyar komawa inda ta fito,don batajin