Showing 537001 words to 540000 words out of 557259 words
bane da zatayi zaton zai kasance haka a nan kurkusa ba.
Gabanta ta qarasa ta kuma tsugunna tana fadin
"Sannu da zuwa maamah......barka rana,ya jikin?,Allah ya qara lafiya". Wani kallo ta dago ta dan watsa mata. Da tana da iko zata tambayeta ne uban me sukeyi a sama kusan sama da awa daya suka bar kula da yara hannun masu aiki?,haka sukeyi kenan cikin gidan?,shi ya ajiye fita office ita ta saki ragamar gida kamar su kadaine suka rage a duniyar?,kaman ba wani abu me rai da yake rayuwa a duniyar saisu?.
Saidai ba wannan damar,sai dai kallon tuhumar data gabatar mata tana jin ya kawo mata dan sassauci a zuciyarta. Sarai taga kalar kallon,to amma ita kanta tasan yasha banban da kallon qiyayya da takeyi mata,wannan din akwai sassauci qwarai a cikinsa,duk da cewa akwai alamu na jin haushi a cikinsa da batasan haushin meye ba?,sai daga baya zuciyarta ke raya mata na barin yaranne a hannunsu salwa?.
Saida salwa ta kawo komai sabreen ta jera mata a gabanta,sannan ta umarceta ta karbi yaran ta bata abincin taci,amma qememe taqi bayar da yaran.
Sanda fu'ad ya sauko ana wannan drama din,don sabreen ta haqura ta koma gefe tana kallon ikon Allah,yadda ta tattara dukka hankalinta akan yaran,kamar bata da wani sauran abu me muhimmanci a duniyarta sama dasu,duk kuwa da cewa ita din daga wannan kallon guda biyu bata sake samun wani kallon ba.
Shima nasa kallon aka aje masa,sannan ta kauda kanta bakinta yana motsawa kaman meson yin magana amma kuma ba dama. Mutuwar tsayen da yayi yafi na sabreen,don har sai da maamah din ta sake daga idanu ta kalleshi tana masa nuni da ya zauna ya tsaya mata a kai.
Kaman yadda sabreen tayi mata shima still hakan,saidai shi dinma ba wani muhimmanci ta bashi ba. Ganinta riqe da yaransu kuma gudan jininsu cikin hannuwanta da wata qauna data gaza boyuwa daga cikin qwayar idanunta yafi komai yi musu dadi shida sabreen din. Suna zaune zaman kurame kawai,amma lokaci lokaci suna satar kallon juna shida sabreen din,har zuwa sanda tayi alama da hannu aka bata abun rubutu.
"Ka kiramin driver ya maidani gida,kada ku sake barin yara har tsahon sama da awa a hannun masu aiki ba tare da kuna zagayosu kuna dubasu ba" Iya abinda ta rubuta kenan da rarrababben rubutunta.
Ya dauka idanunsa ne suke masa gizo ko suke nuna masa ba daidai ba,sai kawai ya miqawa sabreen din paper ya qarasa ya karbi yaran ya ajiyesu sannan ya tura wheelchair din da take kai da kansa.
Sanda yake turata da kansa sai taji wani abu yana sauka saman zuciyarta,tana iya qididdige takunsa da kuma yadda yake tura kujeran cike da karsashi,sai takejin kaman ba'a taba tafiya da ita saman wheelchair din irin haka ba.169
Koda suka isa key ya karba hannun driver din,yace su biyoshi a daya motar. Shi yayi driving nata har gida,ya kuma danganata da bedroom dinta. Tsugunnawa yayi a gabanta a hankali,yana jin wani abu me kama da qaqqarfan farinciki yana dawainiya dashi.
"Zan koma......ba wani abun?" Kai ta girgiza masa alamun ba komai,sai ya miqe a nutse yana furta.
"Sai da safe,Allah ya huta gajiya" Ya fada yana dan rage Ac din dakin. Idanunta ta lumshe,wasu hawaye masu dumi suna silmiyo mata wanda ba nace ga dalili ba,ta miqa hannunta da qyar dake yawan yo mata nauyi tana goge hawayen fuskarta.
Riqe da paper din kuma a inda ya barta ya sameta a zaune tsakanin yaqini da kokwanto. Cak ya dagata yana juyi da ita sannan ya direta yana duban tsakiyar idanunta.
"Na gode sosai duniya.....na gode da tayani siyawa yaran nan soyayyar maamah......koda ni ko ke mun rasa soyayyarta.......soyayyar da zata bawa su fauzan ta ishemu". Da mamaki take kallonsa,sai ya lakace mata hanci.
" Ko an gaya miki bana sane da boyayyar addu'ar da kikewa iyalinki.....ni number one,addu'ar kariya samun nasara da cikakkiyar lafiya,yaranmu shiriya da zama nagartattu.....sai samun qauna daga wajen kakarsu" Kunya ta kamata,ashe dukka kukenta da fatanta cikin sallolinta na dare fakare yakeyi mata?.
β
Cikin kwanakin kwanciyar hankali da nutsuwa ta samu ga kowa,ci gaba ta fuskokin rayuwa kala daban daban.
Wata irin soyayya ake murmushewa cikin gidan me jadda me license,irin soyayyar da yaran da suka fito ma daga jikinsu saidai a sanmusu. Tsakanin DUNIYOYIN guda biyu wani irin dangantaka ce me qarfin gaske.....wadda ta gwada musu lallai WA YASAN GOBE? banda Allah?. Wata irin DANGANTAKAR ZUCI me tsakanin qarfi da power,wadda take sake basu yaqinin ABADAN ba wanda zai iya rayuwa ba dan uwansa. Sau da dama idan suka zauna labarin rayuwrsu ta baya suna jinjina lamarin ubangiji kan yadda ya tsara KUNDIN QADDARAr junansu,wani ALQAWARIN ALLAH ne wanda baya tashi. Komai na sabreen din tana qoqarin saitashi ya zama daidai da ALQIBLAr fu'ad din,komai nata tana qoqarin ganin bai saba da muradi da abinda me jadda yakeso ba. SIRADIN RAYUWArta kaf akan gidanta ne da yaranta,ta zage sosai wajen koyan abubuwa da dama da zasu maidata cikakkiyar matar gida,irin matar gidan da soyyayarta da kulawarta ke tsayawa a zuciyar mijinta.
Duk wata DABI'AR ZUCIYA da tasan zata kawo rauni a mu'amalarta da fu'ad tayi qoqarin nesanta kanta da ita,ta sake qoqarin zame masa GURBIN IDO ta fannin mahaifiya dama mu'amalarsa tako da yaushe. Kusan duk bayan kwana uku ko zataje ko bazataje ba ta koyawa faud daukan yaran bayan sallar ishai suje su gaida maamah. Hakan yana sanya maamah cikin farincikin da har baya kasa boyuwa saman fuskarta,tana jin yaran a jikinta qwarai,can qasan zuciyarta kuma idan ta kalli mahafinsu takanji kaman ta zama butulu KUFAN WUTA a wani zamani can baya daya wuce. Tun zuciyarta bata gaya mata harta fara gayawa kanta da kanta cewa A RUBUCE TAKE qaddarar kowanne bawa,ba wanda kuma ya isa ya sauya qaddarar wani face marubucin qaddarar.
Sabreen zata iya cewa ita din tana daya daga cikin matan da suka qaryata kalmar nan ta NAMIJI TABARMAR K'ASHI. Mu'amalar fu'ad da komai nasa na musamman ne kuma ya banbanta dana sauran maza. Duk da cewa GUDUN K'ADDARA GUZURIN TARAR DA ITA amma tayi imanin cewa addu'a tana iya sauya qaddarar bawa......tana fatan yadda ko yaushe ta sanya goshinta a qasa take roqar Allah madawwamiyar lafiya da zaman lafiya a gidanta.......ta kasance ita daya a rayuwar fu'ad din a matsayin matar aure,tana da yaqinin Allah bazai juyar da addu'arta ba duk da tabbacin data samu daga bakinsa.
β
Cikin dim light din dake kai kawo a dakin ta qaraso gabansa,sanye da wata sassalkar rigar bacci data qawata surarta dama fatar jikinsa. Duk da sau daya ya daga kai ya kalleta amma sai data fusgi hankalinsa,ya kalli agogo ya maida dubansa kanta sanda take tsugunne gabansa tana zuba masa hadadden kunun ayar data koya,kunun da tunda ta koyeshi ya zame masa JARRABI kullum sai yasha shi.
Sai data sake masa murmushi sannan ta miqa masa cup din,ya miqa hannu da nufin karba yana cewa.
"Inda malami kika saka yayimiki aiki akan soyayyarki a zuciyata,tabbas dana qara masa kudi ya qara tsananta aikinsa,don nasan babu me mace irin tawa a duniyar nan".
" Hamma....sonkai?" Ta fada da muryarta me sanyi,wadda shi daya take maidawa ita haka a kebantaccen guri irin wannan. Zai bata amsa zafin da bayan hannunta yayi ya dauki hankalinsa.
"Subhanallah.....zazzabin nan wai bai tafi ba?" Ya tambaya cikin tsananin damuwa yana ajiye cup din hannunsa.
Kai ta gyada masa a shagwabe
"Bai tafi ba hamma....."
"Bari na yiwa doctor mubeena waya ta shigo ta dubaki......zazzabin nan ya isa haka nan". Tasan koda tace masa ya bari bazai bari ba,yana damuwa da ciwonta fiye da yadda ita take damuwa da kan nata.
Sannu kawai yake jera mata,tayi tayi ka yasha kunun yace ta maida fridge.
Baa rufa awa ba doctor mubeena ta iso da kayan aikinta,kai tsaye suka wuce dan qaramin dakin daya zuba qananun kayan aiki a ciki saboda lafiyar iyalin gidan.
Shi da ita duka idanu suka zuba mata sanda take duba gwajin data mata saboda ganin murmushi yana fita kan fuskarta.
"Mr and mrs jadda......congratulations,madam nada juna biyu". Banda yasan doctor mubeena na tsananin girmamashi da sai yace tana wasa da hankalinsa ne,saidai duk da haka sai daya ce.
"Say it again please".
"I said madam nada juna biyu......she's pregnant". Suratul ikhlas kawai ya hau karantawa qafa uku,daga nan ya miqe ya sunkuci matarsa,daukan data saka Dr mubeena soma hada ya nata yan nata ta basu waje,saidai tana iya hangen tsoro sosai fuskar sabreen.
Abinda kawai yake yawo a kanta shine watansu fauzan hudu,cikin week dinma duka duka aka fara koya musu zama......likita yace aqalla tayi shekara daya so samu har biyu bata dauki wani cikin ba saboda ta warke yadda ya kamata,yanzu kuma dr mubeena na gaya mata juna biyu ne da ita?.
Cikin qasa da mintuna biyar dukka wannan tsoron yabi ruwa,cikin daqiqa kadan komai ya kwaranye daga zuciyarta. Yadda idanun fu'ad ke fidda qwallar farinciki......yadda bakinsa ya gaza hutawa dayi mata addu'ar
"Ke 'yar aljanna ce in sha Allahu sabrrrr.......ke alkhairi ce sabrrrr......don Alla ki gayamin me kike da burin mallaka a rayuwarki bayan gidan marayu da gajiyayyu da tallafawa marayu?". Kai ta girgiza a hankali,lallai ta jahilci irin tsananin son da fu'ad yakewa haihuwa.
"Babu.....babu muffin,iya wannan qaunar da soyayyar da wadatar......iya wannan shauqin na samun iri daga jikina ya isheni farinciki har qarshen rayuwata". Ta furta maganar da dukka zuciyarta tana tuna wata mata da mijinta yayi mata duka ya watsota waje ya kuma saketa dukka a iqirarinsa na ta fiya haihuwa......da an tabata sai ciki.....dukka ubangiji ita bai jarabceta da wannan ba?.
Wani irin dare ne da bacci ya gagari idanun fu'ad,yayi sallah yayi addu'a har baisan iyaka ba. Itama da take kwance lamo kawai tayi,zuciyarta na sake cika da mamakin yadda yake tsananin son haihuwa,saita samu kanta da maimaita.
"Alhamdulillah......alhamdulillah" Har sau babu adadi.
β
Cikin lokacin wani kulawa yake bata data ninka ta baya,yana gida ko yana office dukka yana kula da motsinta. Ya sake qaro mata aminttatun masu aiki da suka sanya komai ya sake zame mata da sauqi,goyon ciki me 'yanci,kuma Allah ya bata da sassauci akan nasu fauzan,duk da cewa har a lokacin tana shayar da yaran,yace bai yarda ta yaye masa yara ba,idanma biyanta ne shi zaiyi a barsu susha nono su qoshi ko don saboda ginuwar kwanyarsu yadda akeso.
To shi ciki dai d'an duma ne inji hausawa,a hankali jikinta da dabi'unta suka fara nunata,duk da yadda take gocewa shiga cikin mutane don kada su fahimci cikin. Kunyar cikin take sosai,sau tari idan shagwabarta ta motsa sai tayita masa rigimar banza akai.
"Hamma don Allah kada ka gayawa kowa.....don Allah hamma kada ka fada,yayi wuri fa hamma.......duka duka watansu fawad nawa ne?,Allah kunya nakeji"
"Sabrrrr" Ya kirata kai tsaye a lokacin tana saman cinyarsa yana raba mata doguwar sumarta biyu hagu da dama don ta dameta.
"Wallahi wallahi ko cikin shege nayi miki bazan boye samuwarsa ba.....kuma zanso abina fiye da tunaninki,ballantana 'ya'yan halaliya 'ya'yan so". Yadda yace 'ya'yan so din har tsakiyar zuciyarta,tun daga ranar saita daina cewa komai akai,ta kuma tayashi da duk yadda yakeso.
Tasha tsokana sosai wajen fannah wadda itama nata cikin ya fara girma,amna da huda kuwa dukkaninsu yaya take a Wajensu,ba tsokana sai gulmarta a boye,uwa uba suma duk ta kansu sukeyi don cikinsu ya tsufa sosai.
Wata tara da bikinsu amna amna din ta dire nata yaron namiji. Maamah bata sanu ba sai bayan kwanaki bakwai,tana zaune saman wheelchair dinta sanda musaddiq ya ajiye mata goro da alewar radin suna. Hamza ya saka shima still saboda nuna yabawa bisa hidimar abban a kansu,sun masa laqabi da HILAL. Ba wani feeling data samu zuciyarta a ciki akan haihuwar,so ko qi itama bata san wanne layi take kai ba,saidai bata wani dorawa kanta tsananin tunani akan komai ba ta ajiye maganan,duk da lokaci lokaci idan aka kawo mata su fauzan yaron yana fado mata a rai.
Tsakaninsu da huda wata biyu kacal itama ta dire nata sojan. Saddiq ya nuna kara sosai,ya sanya masa sunan mahaifinsu sabreen wato ahmad,suna masa alkunya da NASEEM.
Ta kowacce fuska anni jinta take cikin alkhairin ubangiji,saidai a yanzun kwadayinta a samu 'yanmata kuma,don tana fatan samun garabasar nan na wanda ya raini diya mace biyu ya aurar dasu na alqawarin aljanna kai tsaye.
Irin girman da nauyin cikin ya sanya fu'ad wucewa da ita a wata tafiya da yayi zuwa spain ya tafi da ita. Bawai don yana da nufin tayi anti natal nata a can ba,saidon kawai a duba mishi ita duk da bata da matsalan komai,saina wani irin cin abinci da takeyi,abinda shi kuma yakeyi masa dadi sosai,har yakan zauna yana kallonta abinsa.
Scan din farko ya nuna twins ne a cikin nata. Wani iri ya dinga ji,tsoron Allahnsa yana sake kamashi. Dukka cikin addu'arsa ba wadda bai gani ta tabbata ba.....shin cikin ni'imomin Allah wanne ne a ciki zaiyi inkari?.
_Allah ka wadatamu da dukka ni'imominka na zahiri dana badini,ya Allah karka jarabcemu da gushewar ni'imominka a kanmu_
_on our way to the last episode's in sha Allah_ππ½ππ½πππ170
Tattalinta ya dinga yi,nan nan da ita yakeyi,baya yarda komai ya taba walwalarta ko kuma jin dadinta.
Duk wani abu da yasan zata iya buqata ya ajiyeshi......komai da yasan zata iya nema kafin ma takai ga tambaya ya tabbatar da samuwarsa.
Bata aikin komai,ba aikin fari bare na baqi,komai nata dana yara tana da amintattun masu aikin da take jinsu kaman 'yan uwanta na jini,musamman da suka kasance kusan dukkaninsu marayu ne wadanda basu watsar da maraicinsu ba.
Duk wannan gatan data samu.....duk wannan kulawar bata sanya ta saki hidimarsa ki qwaya daya ba. Yayi yayi ta barshi amma ita kanta tasan ba abu bane me yiwuwa tabar kula da mijinta,sai ya qyaleta a bisa dole,amma duk wani motsi nata da zatayi shike tayata,shike kama mata. Misali wani lokacin yakan yi mata wayo ya rigata tashi da safe. A kitchen din sama zai hada breakfast abinsa ya aje mata nata,ya hada ruwan wankanshi da kanshi yayi,ya watsa undies dinsu cikin washing machine ya wanke musu,ya kwashe komai dake tsananin parlor zuwa Bedroom din da suka bata. Idan ta farka saidai ta taras da sauran aikin,wanda baya wuce shayar dasu fauzan da kuma qarasa kintsa saman nasa,sai tayi wanka shikenan ta zauna cikin masu aikinta.
Idan ta gaji tana buqatar fita shike katse komai nasa ya dawo ya fita da ita,idan ma qasar ko garin takeso su danyi balaguro daukanta yake ita da duk wanda takeso su wuce suyi iya kwanakin da takeso.
Irin gatan da yake gwada mata saita dinga jin kaman ya mata yawa,kaman bata cancanci tattali irin haka,ranar data fara magana a kai suna tsaye ne saman balcony na wani qawataccen madaidaicin gida daya siya a dubai a satin. Gidan yana area me tsada ne wanda yake da clear view na garin dubai da guraren kallo masu kyau.
Ta baya ya rungumeta yana dora hannunsa guda daya saman qaton cikinta. Ta miqa hannunta ta bayan itama ta shafo sajensa tana sakin murmushi.
"Tunanina kike?" Ya furta a tausashe,saita gyada masa kanta.
"Ya akayi kasan sirrin zuciyata".
"Ruhi daya......zuciya daya.....qwaqwalwa daya.....gangar jikince kawai guda biyu,to menene zai boye a wajena?" Ya qarasa maganar yana tura mata wani file ta gefan cikinta. Murmushi ta saki tana jin maganarsa ba wani kuskure ko gyara a ciki,ta karbi file din ta bude.
Takardar shaidar mallaka ce ta wannan gidan da suke ciki,wanda ya rubuta da sanya hannunsa da komai kan ya mallaka mata gidan. Ganin komai take kamar a mafarki,batasan adadin gidaje da estate nawa ya mallaka mata ba.......amma wannan ya zama na daban. Mallakar gida sukutum da guda