Showing 153001 words to 156000 words out of 557259 words
matsayin da Allah ya bashi?. Saidai a nashi bangaren malam din tamkar wani jigo ne a rayuwarsa.......ya zame masa fitila me haska masa duhu.....domin shine mutumin daya shayar dashi ilimin addinin da a yanzu haka ya zamewa rayuwarsa haske da kuma garkuwa.
Silalowar motocin da kuma nishin isowarsu wajen yadan dauki hankalin da yawa daga cikin almajiran. Saidai da yake daliban malam auwalu daban suke da sauran almajirai ba wanda yayi wani motsi na hayaniya ko fita daga tsari,saidai idanu da suke bin motocin dashi wanda ke qoqarin gyara parking a muhallin da suke ganin zasu iya tsaiwa. Idan ka duba da kyau fuskokin manyan cikinsu murmushi ya sake wadata,domin sun sani mutum daya ne tak me irin wadannan motocin sak....dake zuwa wajen malam,wanda duk ranar da yazo kuwa kakar kowa ta yanke saqa,duk da cewa qalilan daga cikinsu ne suka samu nasarar shaida fuskarsa.
"Bari hamma na fita na duba ko yana ciki" Musaddiq ya furta yana duban fuad da ko sanda motar ta tsaya bai daga kanshi ba,hankalinsa still yana kan waya
"Okay" Ya fada a hankali kaman wanda bayason yayi magana.
A nutse ya bude motar ya fiddo qafarsa dake cikin rufaffen takalmin kamfanin Hermes. Ya qarasa fitowa daga motar yana gyara hannun rigarsa sannan ya fara takawa a nutse yana dosar rumafar malam din daya daga cikin guard yana biye dashi.
Daga shigowar motocin har tsaiwarsu a wajen bata wani basu muhimmancin da zasu dauke hankalinta daga aikin da take ba,don Allah Allah take ta kammala ta wuce gida saboda yadda tunanin huda yaketa mata yawo saman kai abinda bata taba tsintar kanta a ciki ba kenan.
"Hamma malam fa idan ba da gaske akayi ba bazai koma sabon gida da makarantar daka gina masa ba" Sadiq da idanunshi kekan almajiran ya fada yana leqo kansa first set din da fuad ke zaune.
A nutse ya zare lumsasssun idonsa akan wayar yana waiwayawa gefansa ya kuma aza idanunsa a muhallin da yake kyautata zaton a kanshi Sadiq yake magana. Saidai kuma duk da tarin almajiran daketa miqa hannu suna karbar wata takarda idanunsa basu sauka a ko ina ba sai a saman fuskarta.
"Yanzu banda abun malam.....ga gini can a wadace,ga makarantar zamani amma yace sai yayi shawara?,har yanzu kuma bai gama shawarar ba?" Sadiq ya sake fada yana dariya qasa qasa,dariyar da bata samu isuwa ga kunnuwan fu'ad ba duk kuwa da cewa yana wajen.
Sosai ya zuba ma fuskartata idanu bawai don tayi masa kyau ko kuma taja hankalinsa ba......aah.....sai don tuna a muhallin daya soma ganin fuskar duk da ba wani kyakkyawan kallo yayi mata ba.
"Office din mikail......a ranar da incident din zai faru" Sashe mafi saurin harbawa cikin kwanyarsa ya bashi amsa
*D U N I Y A T A*
*_H U G U M A_*
PAGE 83
"Exactly....." Ya furta har labbansa suna motsawa,yayin da wani qaqqarfan tunani ya darsu a ransa.
Bai dauke idanunsa daga sashen ba musamman ganin musaddiq ya doshi inda take kai tsaye......amma kuma kafin ya qarasa din ta juya tana takawa zuwa cikin gidan malam din,abinda ya sanya musaddiq da bai kula da fuskarta ba ya soma tambayar wanda yafi kowa girma a wajen kan ina malam?,kafin ma ya bashi amsa muryar malam din ta ruskeshi yana basu umarni su fara daura alwalar sallar magariba.
"She's a suspect" Ya fadi a hankali yana zare idanunsa daga kanta sanda ta kammala shigewa malam ya bayyana. A nutse ya waiwaya ga sadiq yana kallonsa.
"Kiramin jordan" Ya furta a nutse yana qoqarin bude side din da yake zaune. Baiyi wahalar komai ba ya janye dogon hannun rigarsa ya danna wani abu,cikin qasa da minti daya hotonsa tsaye jikin motar ya bayyana ta qaramin allon computer dake maqale a set din gaba fu'ad
"Ka fita ka cewa malam gani nan shigowa.....ka cewa jordan din ya shigo". Ya danyi mamaki kadan da hakan,amma bai damu ba ya amsa masa yana bude murfin motar sannan ya fice yana gayawa jordan saqon boss din nasu.
"come in" Yace ma qaqqarfan mutumin da yayi tsaye bakin motar cikin rusunawa.
Cikin jin nauyin hada mazauni daya da boss din nasa ya shigo. Sai fu'ad din ya bashi umarnin rufe motar. Yayi kaman yadda yace din yana maido dubansa ga fu'ad din yana satar kallonsa.
Duk yadda yakejin qarfi a ginannun tsokokin jikinsa a yanzu da yake zaune kusa da boss din nasa sai yaga ashe bai fishi da komai ba.
"Kayi noticing wata girl a cikin yaran can tana raba musu wani abu?" Yayi tambayar kanshi tsaye,don yasan mutum ne shi me tsananin kula da motsin kowa
"Yes sir" Ya gyada masa kai cikin qwarin gwiwa da confidence
"Good.......i want every single details of her.....but don't forget.....make it secretly"
"Done sir" Ya fadi a yanayinsa da muryarsa suna bawa fu'ad din tabbaci.
Tun daga fitarsa a motar ya soma aikinsa,tun tana daga cikin gidan malam din fitowarta da tafiyarta hankali kwance saboda tasan bata da wani issue da kowa a nan area din......hasalima ba wanda yasanta a yankin don haka take tafiyarta a tsanake.......ya riga yayi waya da duk wanda ya kamata,don haka qarqashin kulawarsa take,tun daga abun hawan data samu zuwa isarta gidansu.
Can qasan ran malam din yake mamakin dan dadewarsa wajensa a yau,duk da cewa ya maisheshi tamkar uba kaman yadda ya daukeshi d'a. Tun malam din yana tsoron asan cewa fitaccen mutum kuma attajiri irin muhammad fu'ad na zuwa wajensa har ya soma sakewa.
Duk zuwan da zaiyi din kowa yana tsaiwa a waje ne amma shi da Sadiq ko musaddiq ko farouq idan tare sukazo suna zama ne tare dashi.
Magariba dama ishai duka tare sukayi da malam din. Duka yana sane yana yi yana duba agogonshi bayan ya sanya musaddiq ya kashe wayarsa,tasa wayar kuwa dama shigowar kira yana bisa qa'ida ne so baida damuwa. Yadda zaman yaga ya miqa malam din yasa aka fito musu da tuwon dare daga cikin gidan. Yace a fito dashi dinne kawai saboda karamci irin nasa,bawai don yana sanya rai zasu iya ci ba. Saidai ga mamakinsa Sadiq da musaddiq din cin abinsu sukayi sosai,daidai lokacin shi kuma suke tattaunawarsu da fu'ad.
Kudin daya saba bayarwa malam ya rabawa mabuqata duka wata ya ajiye,ya bada na malam din wanda kamar ko yaushe sai yayi kaman bazai karba din,yakance
"Muhammadu......nikam bani da matsala ci sha sutura ko.muhalli,ina ganin a baiwa bayin Allah dake da tsananin buqata mana". Ko yaushe shi kuma yakan maimaitawa malam din.
"Koda kullum zaka rubuta adadin mutanen da idanunka suke gani suna da buqata ta aikemin dashi malam za'ayi musu komai kuma hakan bazai hana ayi maka ba......a duk sanda ka hadu da mabuqaci kada kayi shayi ko shakkar alqawarta masa taimako,tabbas za'ayi masa dukan abinda ka buqata". Ko yaushe ya fadi haka malam ka jinjina kai. Girma da kimar malam a idanunsa tana da dimbin yawa,ya taka rawa me yawa a rayuwarsa,ya kuma tallafeshi da abinda baida abinda shi din zai iya saka masa dashi.
Sai daya tabbatar tara na dare tana musu sallama sannan sukabar gidan malam din.
Sanyin Ac din dake kadawa cikin motar ya sake saka masa kasala tare da taso da gajiyar jikinsa,saidai shi kuma ba wannan bane a gabansa yanxu. Gaba daya hankalinsa ya karkata gason jin komai daya shafi yarinyar,yana ji a jikinsa kamar akwai wani abu a qasa,kamar akwai wani abu.
Ko sanda suka isa gida ma goma ta gota,saidai ya samu abba da anni zaune a falo da alama hira suke,duk da abban akwai takardu da yawa a gabansa yana rubuce rubuce.
"Jiya da yau dai duka ba zama.....yarona ya rantse sai ya zama mutumin arewa na farko daya bawa 'yan kasuwa da masu arziqin arewa sample na kishin yankinsa" Anni ta fada tana murmushi. Shima murmushi ya saki,a koda yaushe yana alfahari da anni da kalamanta da suka zama sune qarfinsa. Bata tsareshi da yawa ba haka shima abban suka sallameshi ya wuce sassansa.
Ta isa gidan bayan magariba da kadan,sanda tsakar gidan nasu ke cike da hada hadar ahalin gidan. Masu wankin uniform sunayi,masu zaman hira na zaune,masu kwashe tuwo da abincin dare kowa yana sabgar gabansa. Koda tayi sallama ba ta tabbatar babu wanda zai jita bare ya kalleta,idanma sun kalletan......zasu kalleta ne da mummunan kallon nan da tasan babu wanda ya isa ya wankeshi daga idanunsu sai randa ubangaji yaso,don haka ta zabi wucewa ciki salin alin ba tare data tankawa kowa ba,saidai duk da hakan bata tsira ba daga jiyo kalaman nan masu muni daga kunnuwan bibo
"Hala yau barikin batayi ribaba.....dawa kuma batayi nama ba.....naga fuskar ba fara'a bare walwala......."
"Ita bariki daman ai alalan gero ce......idan baka iya ba ta kwabe maka.......ta fara hangen wannan din inaji shi yasa ta soma yiwa 'yar uwar training......gashi an fara da fitar dare?" Yabi ta taya bibo din fada.
Wata mummunar faduwa gabanta yayi,jikinta ya dauki rawa da jin kalamansu na qarshe,ta sanya hannu tana dauke hawayen daya silmiyo mata sanda taga daada na dauke flask din abincinta tana wucewa dashi dakinta. Hakan ya tuna mata da rayuwar gidansu,duk da yawansu abinci baya daya daga cikin matsala ko damuwar rayuwarsu,abinci na daya daga cikin abinda muddin kai haifaffen jinin gidanne ko maqoci ko abokin huldar arziqi tabbas kafi qarfinsa!. Abinci me kyau bawai irin abincin da za'a ci ba kawai saboda kore yunwa ko babu yadda za'ayi,yau sai gashi abinci ya zama matsalar gidan ta farko!,abinci ya zama damuwar gidan.....abinci kuma ya zama abu mafi wahalar samu garesu haka abu mafi daraja da tsada a gurinsu.
Ji take kaman iska ke tafe da ita har ta sanya qafafunta cikin falon nasu
"Ina huda?" Ta jefawa nadra da haneefa tambaya wanda suke zaune qasan carfet kawai. Sun tasa litattafansu a gaba bayan gama sallar magaribarsu kenan da alama.
"Muna dawowa islamiyya ta ajiye jakarta ta fita" Nadra ta fadi da karyayyar murya tana tuna yadda ta daka mata tsawa sanda taga tana shirin fita din ta tambayeta
"Inda kika aikeni makira sarkin tambaya!" Daga haka ta zuba mata manyan idanunta tana kallonta har ya fice.
Ji tayi qafafunta kaman suna lanqwashewa don haka ta samu ta lallabo ta zauna kusa da haneefa da take kallonta da idanunta da tasha jin ana cewa irin nata ne sak,sai ta jawota jikinta tana duban nadra tare da qoqarin rarrashin zuciyarta
"Bata gaya muku ina taje ba?" Kai nadra ta girgiza
"Bata fada ba"
"La haula wala quwwata illa billa" Ta fada muryarta nadan rawa kadan. Cikin qanqanin lokaci zuciya ta fara sawwara mata abubuwa masu yawa akan huda. Ina huda ta sani?,ina zata je?. A iya saninta huda bata da wata qawa illa nadra da haneefa,bata da wani wajen zuwa sai inda ita ta kaisu,bata da wajen zama idan ba dakinsu zuwa tsakar gida da farfajiyar gidansu ba.....to ina huda ta tafi?.
Zame haneefa tayi daga jikinta ta miqe tana qoqarin saita kanta,ta wuce kitchen ta duba abinda suka dafa ta zuba musu
"Kuci bari na shiga toilet" Saita fice zuwa tsakar gidan nasu.
Dariya taji qasa qasa daga shiyyar da mutan gidan ke zaune,bata waiwaya ba haka batace komai ba,saidai jikinta ya bata tabbas da ita ake.
Da qyar ta saita kanta ta cire pad din jikinta ta sauya wata sannan ta fito. Tana saka qafarta waje tana ganin shigowar huda wadda ta zarce dakinsu kanta tsaye. Tayi namijin qoqari qwarai da gaske wajen saita kanta ko don idanun jama'ar dake wajen tabi bayan huda a nutse zuciyarta kaman zata fado daga qirjinta.
Sanda ta tabbatar sun isa falon dukkaninsu sai saitinta ya kwance gaba daya. Ta miqa hannu ta finciko huda dake qoqarin wucewa daki kai tsaye
"Dawo nan......daga ina kike?" Ta jefa mata tambayar a tsawace tana dubanta da kyawawan idanunta da suka qara girma a yau.
"Gid.....gidansu qawat...." Sai ta kasa qarasawa saboda tsoron daya kamata na ganin Sabreen ta daga hannu tabbacin lafiyayyen mari tayi nufin sauke mata.
Tsit dakin yayi,a hankali ta maida dubanta sassansu nadra,saitaga sunyi tsumu tsumu suna kallonsu. Wani abune ya daki zuciyarta ya kuma karyata,abinda ya sanyata ja da baya wannan ya baiwa huda damar shiga dakin da sauri sauri.
"Kuci abincinku ina zuwa.....babu abinda zai faru" Sabreen din ta fadi wani madaukakin tashin hankali yana saukarwa zuciyarta amma tana qoqarin tausar kanta,ta kuma taka da dan hanzari ta wuce dakin itama.
Hijabin uniform dinta take qoqarin zarewa,sumarsu me tsaho da sulbi ta gado ta kwance,daidai sannan sabreen din ta miqa hannu ta sake jawota.
Jikinta ta fara duddubawa,sannan ta sanya hancinta ta fara sansana jikinta,abinda ya sanya huda mutuwar tsaye zuciyarta tana wani irin bugawa tana bin sabreen din da idanu kawai ba tare da tasan ainihin ma'anar abinda takeyi ba. Bakinta ta kama ta matse tana duba harshenta,sanna takai hancinta tana shanshana labbanta.
Bataji sauyin komai ba daga gareta,amma yadda zuciyarta ke bugawa ya tabbatar mata lallai akwai alamun rashin gaskiya a tare da ita,sai ta sanya hannu ta tunkudeta,kai tsaye ta fada saman gadon tayi zaman 'yan bori,tayi taku biyi sabreen din ta tsaya a kanta gab da ita
"Ki gayamin daga inda kike tun muna mu biyu kafin duniya ta jimu!" Ta sake fada mata tana fidda idanunta da a yau suka qara girma saboda tashin hankali.
"Ni fa ba inda naje adda......gidansu qawata"
"Wacce qawar?,yaushe kika yita?,kuma a ina take?"
"A islamiyya muka hadu...." Ta fadi tana jawo qarfin gwiwa bayan ta tsinto wasu maganganu daga kalaman naseer da yake a matsayin bassam a wajenta.
Yadda tone din ta ya sauya farat daya yaja hankalin sabreen,saita gyara tsaiwarta
"Islamiyya?.....inane gidansu?,me yasa ni bansanta ba?" Tashin farko sai taji ranta ya baci,karon farko kuma a rayuwarta taji kaman yau yaa sabreen ta raina mata wayo
"To ai kowa ma yana da mutanen da yake mu'amala dasu,ba lallai sai uwa ko uba ko 'yan uwa sunsan da zamansa ba" Tayi maganar kai tsaye abinda ya zowa sabreen din a wata gigitacciyar ba zata
*D U N I Y A T A*
*_H U G U M A_*
PAGE 84
Dukkan wani motsi nata ya tsaya cak......cikin wani irin madaukakin mamaki take duban huda bugun zuciyarta yana canzawa da wani irin yanayi taji yana saukar mata na sanyin jiki tun daga saman kanta har qafafunta,wani irin sanyi jikinta yayi saidai duk da haka ta dawo da hayyacinta cikin jikinta
"Huda?......" Ta kira sunanta da sautin mamaki. A wannan karon sai hudan taji abun yadan mata nauyi,ta kasa hada idanu da sabreen din,ta juya tana son qarasa cire uniform dinta.
Kanta tsaye ta nufi gadon huda din,ta soma janye zanin gadon zuwa katifar tata. Sannu sannu a hankali ta soma birkice duk wani kaya na huda dake dakin,zuciyarta na raya mata akwai wani abu da huda kesha tabbas wanda shi ya canzata. Muddin kuwa hakan ta kasance batasan meye abu na gaba da zai faru tsakanin tata rayuwar data hudan ba.
Cikin abinda ta tsana mafi girma da muni shine shaye shaye,bata samu relief ba sai data tabbatar bata samu komai daya danganci maye daga fannin huda ba. Hudan da tayi tsaye kawai tana bin yayar tata da kallo. Wato a yadda ta yiwa dakin nasu a yau tayi imanin banda takai wayar an canza mata babba,kuma data shigo da ita tana jikinta a maqale babu abinda zai hanata ganin abinda take boyewar.
"Ki gyara dakin,idan kin shirya gayamin inda kikaje ki sameni a falo,idanma baki shirya ba duk daya" Ta bata umarni nakai tsaye tana takawa tana barin dakin. Qasan ranta ta riga ta gama yanke komai.....ta riga kuma ta gama yanke hukuncin da zata dauka akan huda din.
Har suka gama dukkan wani sabgarsu a falon ko leqowa batayi ba ballantana ta fito har ta sameta da wani batu,ko abinci bataga tazo ta diba ba. Wanna ya sake qona ran sabreen matuqa da gaske,ya kuma sake bata tabbacin eh lallai da walakin goro a miya.
Koda suka shiga dakin sanya nadreen da haneefa tayi suka kwanta,itama tabi sahunsu a