Showing 393001 words to 396000 words out of 557259 words

Chapter 132 - πƒπ”ππˆπ˜ATA BOOK1 AND 2 HAUSA NOVEL

HUGUMA   

03 Nov 2025

477

taka har zuwa inda wani boat ke ajiye. Kadan kadan zuciyarta ke bugawa saboda shimfidadden ruwan dake zagaye da wajen fari qal da yake bada wani color me kama da sky blue.

"Ina zamuje saman ruwa kuma?" Ta tambayi kanta tana jin tsoro yana shigarta. Tunda take a rayuwarta wanna shine karo na farko da zata taba shiga jirgin ruwa,duk da wannan din wani irin jirgi ne da zai nuna maka tsadar da yake dashi,tsarinsa daban yake da sauran jiragen da take gani,yana da wata fargajiya da kujerun zama masu daukan hankali.

Bata fahimci maganar da suke ba don cikin harshen Dhivehi suke magana yaren 'yan qasar. Can qasan ranta tana mamakin yadda ya iya harshen haka,a zamanta dashi taji yana yaruka kala kala da batasan yadda ya iyasu ba. Hannunta ya sanya cikin nasa suka fara yin gaba don shiga boats din,saita tsaya ba tare data motsa qafarta ba tana matse yatsunsa cikin nata ba tare da tasan tayi hakan ba. Zuciyarta ke bugawa kadan kadan cikin tsoron shiga boats din,ta yaya zasuyi tafiya saman ruwa?,ruwan ma shimfidadde irin wannan?.

Kallo daya yayi mata ya karanci tsoron da yake idanunta,yayi qasa qasa da muryarsa duk da bajinsu za'ayi ba yace

"You're safe.......idan kina tare dani you are safe......ki shirya zamu koma rayuwa cikin ruwa,har sai sanda kika koyi soyayyar muhammad jadda.....i can't lose you" Yana kaiwa nan ya sake sanyata a jikinsa sosai yana takawa da ita saman katakon da zai qarasa dasu cikin jirgin.

Dole qanwar naqi tsoron ya ladabtar da ita tayi zaune cikin jikinsa,har zuwa sanda suka qarasa shiga,sai a sannan taga irin qawatar da aka yiwa boats din sosai,banda saman ruwan suke da bazata yarda cikinsa suke ba. Bai barta ba sai daya zaunar da ita saman qawatattun kujerun dake a wajen,ya samu wadda ke fuskantar tata ya zauna yana goye hannayensa a qirjinsa idanunshi a kanta. Har yanzun idan ka masa zuzzurfan kallo zaka karanci ranshi yana bace ne,yana kawai qoqarin dannewa ne. Tana jin nauyin idanunsa a kanta sosai,inda zai mata alfarma da ya rage nauyinsu a kanta. Ma'aikacin jirgin ne ya qaraso yana miqa masa wasu qananun blanket guda biyu masu taushi,ya sanya hannu ya karba ya ajiye a gabansa daidai sanda jirgin ya fara motsawa yana harbawa cikin ruwan.

Ido ta runtse tana curewa waje daya,'ya'yan hanjinta suna kaduwa tana jin kaman zata nutse ne a ruwan,sanda jirgin ya tashi sosai ya fara keta ruwan da gudu sai taji kaman kanta zai juye,wannan ya sanyata bude qafafunta ta cusa kanta a ciki zuciyarta na wani irin bugu.

Batasan sanda ya iso gabanta ba,ta daiji lausasan hannayensa saman tafin qafarta. Ta dago idanunta a hankali tana kallonsa,sai ya miqe ya ware blanket din yana lulluba mata,sannan ya koma ya tsugunna a gabanta yana lalubar tafin hannunta. Bata hanashi ba,don tana buqatar wani a kusa da ita,yadda ruwan keyi takejin kaman zasu fada ne,sai ta maida idanunta ta kulle gam.

Tana jin yadda yake murza tafin hannun nata daga gefe,tamkar me dauke da wani sihiri a nasa a hannun......a hankali sai taji bugun zuciyarta yana daidaita,tsoronta yana raguwa sosai.

Tafiyar mintuna idanunta suka fara hangen wani gini tsakiyar ruwan,mamaki ya cikata har sai data ware idanunta sosai tana duban ginin. Qawataccen gini ne da yake a tsakiyar ruwan,tako ina ruwa ne ba wani qasa a wajen ko wani tsandauri kusa da wajen bare tace ga yadda akayi dabara aka dora ginin.

"The Muraka hotel" Ta fadi sunan data gani an rubuta manya manya sama.

"Hotel?" Ta maimaita sunan qasan ranta,wanne irin hotel ne haka tsakiyar ruwa?,ta sake tambayar kanta a mamakance. Kada dai yace mata nan zasu zauna?,cikin ruwan kaman wasu 'ya'yan aljanu?.

A sanyaye ta aza idanunta a kan fuskarsa sanda jirgin ke tsaiwa daidai wata hanya me kama da gada da ta tabbatar ta nan ne zasu qarasa ainihin ginin hotel din. Girarsa duka biyun ya dage mata da wannan miskilar fuskar nashi,sannan ya miqe a nutse yana zare hannunsa daga nata,ya miqa hannun ya cire mata blanket din sannan ya sake kamata ta miqe tsaye suna fita a boat din yana magana da ma'aikatan.

Wata qaramar mota ce me qafa uku me budadden sama ta tsaya a gabansu,ya kama mata hannu tana taka cikin motar sannan shima yabi bayanta,a hankali driver din ya gaidashi ya amsa masa da yarensu sannan ya tashi motar suka fara ratsa gadar.

Tashin hankali.....ta fada a ranta tana ware idanu tana kallon rayuwa a cikin ruwa. Tun basu qarasa ba ta dinga ganin mutane jifa jifa tsakanin hanyar zuwa hotel din suna al'amuransu hankali kwance. Ita kallon ruwanma kawai dake gefe da gefen gadan ta qasansu daga mata hankali yake,a tsorace take har batasan sanda ta cure a kafadunsa ba.

Boyayyen murmushi ya saki batare daya kalleta ba bare ta gane hakan. Yana buqatar wannan tsoronne dama a tattare da ita,samuwar tsoron shine zai sake kusantata dashi......samuwar tsoron shine zai tattaro masa dukka rayuwarta a hannunsa,a inda ba anni ba amna.....ba farouq ba musaddiq ba kuma saddiq ballantana tayi tunanin zata janye jikinta dashi,zata rayu dashi shi kadai......daga shi sai ita a duniyar da ba wanda ya sansu,a duniyar da bazata iya guduwa ko ina ba.

Gajeriyar tafiya ce ta kaisu bakin qofar shiga hotel din. Luxury iya luxury da ko bakasan abinda duniya ke ciki ba idanunka zasu gaya maka. Wani irin gini na alfarma da zata iya cewa bata tsammaci samunsa a haka ba.

Wayarta dake hannunta tadan kada,ta bude tafin hannunta tana kallon fuskar wayar.

"Welcome to the muraka,the first world's under water villa" Idanunta ta janye daga kan wayar tana maidawa fuskarsa,sai ta kasa cewa komai illa tsoro da take sake jin yana mamayarta.

Binsa kawai takeyi har zuwa reception,inda suka karbi komai ya kuma sake riqe hannunta suna takawa a hankali zuwa dakinsu.

Ta kasa tsaida idanunta guri daya,mamakinta yanata qaruwa yadda take taka wajen tamkar a gida. Tana taka tsandauri alhalin tasan tsakiyar ruwa suke tsundum,ta sake riqe yatsunsa da kyau ko tsoron da takeji zai ragu.

Sanda yake bude qofan living room din dake dauke da bedroom dinsa da toilet harda kitchen mutuwar tsaye tayi. Glass doors ne tako ina da zai baka daman ganin kowacce fuska ta shimfidadden ruwan da suke kai. Luxury suite ne dake da bedroom biyu living room biyu duk da daya take gani a yanzun. Baice mata komai ba yana riqe da hannunta har suka shiga bedroom din.

Zare hannunsa yayi daga nata,yaja baya yana zube hannunsa a aljihun wandonsa yana dubanta.

"Ga first bedroom.....muje kiga dayan,saiki zabi wanne zaki zauna a ciki" Yayi maganar idanunsa suna lumshewa yana jin wani abu ya soma fusgarsa a kanta. Fararen idanunta ta aza masa,ita sam batasan ma yadda zata kwana cikin wannan ruwan ba,hannunsa ya miqa ya sake riqo yatsunta yana fita a dakin.

Daga wani sashen daban suka iske stairs da sukayi qasa,ya ware yatsunsa yana zurasu cikin nata ya jawota jikinsa sosai sannan suka fara takawa zuwa qasan.

Idanunta ta fidda sosai zuciyarta na harbawa da mugun gudu ganin suna nutsewa qasan ruwa. Tsoronta ya sake ninkuwa tana kallon yadda sukeyin qasa ta bangon glass da ginin yake dashi. Jikinta duka ya dauki rawa ganin yadda halittun ruwa ke linqaya a cikinsa suna wucewa abinsu hankali kwance ta bangon glass din.

"Hamm......" Ta motsa bakinta don kiran sunansa amma saita kasa. Ya jita sarai,kuma yana jin tasirin tsoro sosai a muryarta da jikinta duk da bai waiwaya ya kalleta ba. Idonsa ya lumshe yana son sake jin sunan HAMMA a bakinta wanda sau daya tak ya taba ji ta ambata a wancan ranar. Ba inda zai kawota ya boyeta yadda yake so......ya dora mata karatun da yakeso irin nan din. A nan ne kawai yake da tabbacin cire wannan tsiwar tata gaba daya ba tare da yayita cusa kansa zuwa gareta ba. Yaji dadin samun information din tana da tsoro wasu lokutan,wannan ya sake bashi qwarin gwiwar ci gaba da zama a Maldives ko don saboda ita.

"Nidai.....wannan gurin" Ta sake fada muryarta na sake tsinkewa saboda hango wani babban kifi yana matsowa kusa da glass din.

"Wayyo Allah na" Ta fada da qarfi tana ruqunqumeshi cikin jikinta da wani irin tsatsauran riqo daya sakashi sakin wata qatuwar ajiyar zuciya. Wani irin riqo ta masa da ya tabbatar inda a hayyacinta take ba zata masa shi ba,ya ware idonsa yana duban abinda ya tsoratata. Wasu irin kifaye ne guda biyu masu girma da suka matso dab dasu kaman masu sansanasu,sai suka juya abinsu suna wucewa gami da kada jelarsu. Qaramin murmushi ya subuce masa,inda wannan ne a the Muraka ya fara bata tsoro to tabbas wata babban dama ce a wajensa,zasu kuma qulla kyakkyawar abota da tsoro din.

Duk da sun tafi amma bai tadata a jikinsa ba,don yadda ta maqale shi din shi yayi masa,sai yaji wani sashe na nauyi da bacin ran da yakeji yana kwaranyewa.

"Is okay.....sun wuce fa,ba abinda zasuyi miki..... You're safe na gaya miki" Ya fada cikin sauti na rada dab da kunnuwanta,abinda ya sanya tsigar jikinta tayi wani irin yarfawa kenan.

Fuskarta ta daga a narke tana dubansa,duban da yayi kusanci da yawa a tsakaninsu har suna musayar numfashin juna,tadan taka zata ja da baya ya riqo bayanta ta hanyar tarota da tafin hannunsa yana sakar mata wani irin abu cikin idanun nasa.

"Stay close to me" Ya fada can qasan maqoshinsa yana qoqarin danne feeling da yakeji yana taso masa a kanta. Yana gayawa kansa ba yanzu ba......ba yau ba.

Bata taba jin kasala irin na yanzu ba,saita sauke dubanta daga kansa saidai fuskarta da yanayinta gaba daya ya fidda wani quruciya tata sosai,har ya fara contemplating akan ainihin shekarunta.

"Tsoro nakeji......ka maidani wajen anni" Ta fada da wata shagwababbiyar murya da batasan ta yita ba.

Wani qawataccen murmushi ya saki,ya saketa yaja hannunta zuwa wata lafiyyar sofa dake wani corner na dakin zai zaunar da ita,saidai suna zuwa dab da wajen wasu gungun kifaye suna iso zasu wuce. A zabure ta taka tana sake fadawa jikinsa ta riqeshi da kyau,muryarta da zuciyarta suna karyewa.

"Ka gani ko?" Ta fada kaman zata saki kuka. A wannan karon duk yadda yake danne dariyarsa sai da ta fito da wani irin nutsatsen sauti. Riqet yayi da kyau yana qarasawa da ita gefan gadon ya zaunar da ita,ya koma gabanta ya tsugunna a nutse saman qafafunsa. Kanta ta daga sama,still ruwa ne sosai a saman nasu da wasu halittun ruwan suna rayuwa abinsu hankalinsu kwance,fuskarta a kwabe a kuma narke ta kalkeshi,saita nuna gurin da yatsa tana tabe baki kaman qaramin yaro zai saki kuka.

Gaba daya yanayinta yaji ya tashi kansa.....dukka quruciyarta da tsoronta sun gama bayyana,abinda bai taba gani ba tattare da ita,hakan ya bashi wani irin farinciki da sai daya sanya fuskarsa cikin tafin hannunta yana boye dariyarsa. Baisan haka muraka zai bashi farinciki ba......tabbas da ya jima da kawosu gurin,wannan tsoron yakeson gani cikin idanunta.

Daidaita mode dinsa yayi yana kallonta.

"Meet my gaze" Ya furta da natsatsiyar muryarsa yana cire wasa a yanayinsa. Kaman yadda ya buqata haka ta tattara hankalinta dama idanunta cikin nasa. Bata taba zaton zata iya dogon kallo cikin qwayar idanunsa ba sai yau. Batasan me ya riqeta ba har ta iya kallonsa na tsahon wannan lokacin,saidai tsakanin mintunan taga abubuwa masu yawa cikin idanun nasa......taga kuma abubuwa masu yawa. Wani irin kyawawan idanu da yau ta fara karantar hakan,tsahon wasu mintuna suna yiwa juna kallon qurilla wanda dukkaninsu da yanayin daya haifarwa da kowa,hannunta ya sake riqewa sosai yana murza a nutse

"You're under my watch....I'll shield you.....i promise to keep you safe.....take my word for it" Ya fada yana bata tabbaci.

"Yaushe zamu koma gida?" Ta fada cikin sanyi da wannan tsoron dake gilmawa cikin idanunta. Dan qaramin murmushi ya sake mata wanda ya sanyata qifta idanunta sau biyu akan fuskarsa.

"Is in your hand......." Idanunta ta fidda waje tana waresu a kanshi

"Ni kuma?" Ta tambaya cikin rashin wayo. Kafadarsa ya dage mata

"Yes......" Ya fadi tare da ajiyar zuciya,muryarsa ta sake zama low sosai,yayi qasa d qwayar idanunsa yana kallonta.

"I crave love and affection in my life,i need someone to talk to,someone who cares......ina da anni ina dasu musaddiq,amma inajin still akwai wani ruhi da nake da buqata daban bayansu cikin rayuwata......Can you fill that role?" Ya jefa mata tambayar yana sake tsareta da kallo.

Karon farko da takejin wani abu daban a kanshi. Yana dasu anni amma yana kewar wani abu.....me yasa dukka zancansa babu maamah a ciki?,me yasa duka wannan qaunar da shaquwa da take gani tsakaninsu da maamah bata ganinsa tsakaninsu dasu?.

"Don't stress yourself" Ya fada yana miqewa gami da zame hannunta cikin nasa.

"Which apartment you prepare?,up or down?" Ya tambayeta yana goye hannunsa a qirji yana son ci gaba da ganin drama dinnan tata.

Idanunta ta dan ware a narke tana dubansa kaman ruwan hawaye na kwanciyaπŸ₯Ή,tana tunanin wanne gurinne zaifi mata,ta zauna a qasan ruwa da kifi ya hallakata?,ko ta zauna a saman shima still ruwan dake kadawa yayita kawo mata farmaki?. Qasa cikin ruwa take tsundum da take ganin kaman glasses din da suka zama katangun dakin kaman zasu tsage ruwan ya shigo.....shi kuma saman nisan ruwan da suke ciki kawai ya isheta firgici.

"Is alright......ki zauna a qasan,zan koma saman" Ya fada yana fara takawa. Ai batasan sanda ta hantsilo ta biyoshi a baya ba,ja yayi ya tsaya yana danne dariyarsa.

"Eheennn" Ya fada yana dubanta da salon tambaya. Kasan masa magana tayi,sai qasa da tayi da kanta tana murza yatsunta,haka kawai yau takejin nauyinsa,ita magana ta Allah daga saman har qasan ba inda zata yarda ta zauna ita daya,gani take kaman zata rasa rayuwarta ne. To amma ta yaya zata gaya masa hakan?,fada masa hakan ma ai daidai yake da ce masa su rayu daki daya,idan kuwa zasu zauna daki daya kenan yana nufin suyi sharing komai?.

"We can room mate?" Ya tambayeta a tausashe yana lalubar qwayar idanunta. Tambayan ta mata tsauri,a zahirin gaskiya a yanzun ba wata mafitan da tafi wannan,don dai ita ba zata bari ta zauna ita kadai ba......amma kuma tana juya yadda hakan zai kasance.

"Let's room together" Ya fada yana wucewa zuwa matakalun da zasu maidashi sama. Wannan karon sai da yayi da gasken gaske sannan ya hana dariyarsa fitowa,don duk inda ya aje qafarsa nan take jefawa,bata yarda ma ya koma saman ya barta a dakin can qasan ruwan ba. Tana tsaye ya dauki wani luggage me kyau da batasan sanda aka kawoshi ba da wani kwali na daban.

"Ranar farko zai zama a dakin sama.....rana na biyu underwater nakeso nayi bacci......hakan yayi?" Ya fada yana daga gira daya gami d qarewa tsoronta kallo a fakaice. Kai kawai ta gyada don nata da wani sauran zabi,tsoron da takeji ma ya isheta.

"Okay.....stay here.....zan duba wani abu zan dawo yanzu" Ya fada yana bata tabbaci da idanunsa. Kai ta daga masa,tana kallo ya bude qofan ya ratsa living room ya fice.

A sanyaye ta sauke idanunta ga ruwan da take kallo gashi gata,wai a haka cikin daki kake kaman ka sanya hannu ka kamoshi. Kujerar da aka aje gaban qofar glass din ta matsa ta zauna tana sake ganin kusancinta da ruwan.

"Subhana man kalaqal kalqa wa'ahsahum adad" Ta fada a ranta tana sake jin girman zatin Allah yana kamata. Ba shakka da yawanmu 'yan adam bamusan waye Allah ba,kawai muna fadinsa ne a bakunanmu ba tare da halasto girmansa a zukatanmu ba. Iya halittar ruwan ya ishi bayinsa sake sallamawa lamarinsa. Ta sauke numfashi tana maida kallonta cikin dakin,idanunta ya sauka kan littafin dake ajiye saman dan qaramin table din dake gabanta. Hannu ta miqa ta dauka,ta fara budewa,cikakken bayani ne akan gurin,taswirar dakin da suka kama inda toilet da restaurant da komai yake.

Idanunta ya tsaya cak kan farashin wajen,adadin kudin da zaka biya duk kwana daya tal,dollar dubu hamsin kimanin million saba'in da wani abu.

Idanu ta fidda waje mamaki yana kasheta,zuciyarta ta kasa gasgata farashin,ko a mafarkinta bata

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login