Showing 357001 words to 360000 words out of 557259 words

Chapter 120 - πƒπ”ππˆπ˜ATA BOOK1 AND 2 HAUSA NOVEL

HUGUMA   

03 Nov 2025

499

shafa da tafin hannunsa yana satar kallon sabreen ta qasan hannun nasa. Wannan tambayar ta anni sai yakejin kamar gatse yake masa amma ya amsa da

"Lafiya alhamdulillah......yame jikin?" Ya hada kunyars waje daya yana nufin kaita qasa da kuma son janyo hankalin sabreen da ko motsawa batayi ba ballantana ta nuna tasan yana wajen.

"Alhamdulillah" Anni ta amsa masa a taqaice,don ita kanta tuna abun kawai yana sakata cikin wata irin kunya.

Idanu anni ta maida kanta,zuwa yanzu ko ita yarinya ce ta gama fahimtar wanne irin zama sukeyi,saidai tambaya daya data kasa samun amsarta.....ta yaya ta zama zabinsa bayan baya so?.

"Sabreen" Anni ta kirata,kiran daya sanya ta daga kai zuwa ga annin ba tare data kalli sashensa ba. Wani iri yaji.....shi yake da muradin ta fara kalla,shi takeso ta dinga fara kalla kowacce safiya idan yana da ikon hakan.

"Mijinki ya shigo". Lumshe idonsa yayi yana jin dadin kalmar da yadda ani ta fadeta da wani irin taukidi

"Kul.....ba kyau a wajen mace taqi gaida miji......Allah bazaiyi farinciki da hakan ba" Anni ta fada tana jin wani abu yana taba ranta a kansu duka su biyun

"Ya Allah ka taqaita musu jarrabawarsu......kada ka sanya soyayya ta zama wata sabuwar jarrabawa a garesu".

"In sha Allah anni" Ta fada tana dan jin nauyin abinda tayin,bawai a kansa ba.....a'ah akan anni ne. Tsam annin ta miqe tana cewa.

"Bari na duba matar can ko ta dora abincin rana?". Saita nufi qofa a hankali tana ficewa daga dakin harda jan qofar.

Wani dadi ya dinga ratsashi da anni ta basu wannan space din,sai kawai ya harde hannayensa duka biyun saman qirjinsa yana qare mata kallo.

Wani irin kallo ne da yasha banban d kowanne irin kallo,wani irin kallo dake cike da shauqi da matsananciyar soyayyar da yakeji kaman tafi qarfin wannan faffadan qirjin nasa dama tsokar zuciyar dake lullube a ciki. Wani kalan so da yafi qarfin a hada sunan son shauqi dama qauna duka a dunqule waje guda,baima san sunan da zai bata ba. Yana ganin yadda ta maida dubanta kan hadith din tana buda shafin gaba,alamun ta gama da shafin baya kenan. Boyayyen murmushi ya saki wanda ya tabbatar ba zata gani ba,tayi masa wani irin mugun kyau tamkar furen fulawa. Lips dinta ya kalla da kyau,ta sake tsuke dan qaramin bakinnan nata waje daya,da gani kai basai an gaya maka ba akwai fushi kwance cikin zuciyar 'yammatan nasa.

"Zansha tsiwa.....zansha rashin kunya,amma duka ina maraba dasu,akwai kebantacce kuma killataccen gurin da aka tanada saboda su" Ya gayawa kansa da kansa yana jin shauqinsa yana qaruwa a iya kallonta kawai kafin yaji kallon ya daina gamsar dashi,duminta kawai yake da muradin ji,duk da zuciyarsa tana gargadarsa da cewa kuskure ne aikata hakan,musamman a mode din da take ciki,uwa uba kuma cikin dakin anni?. Saidai kuma magnet din dake jansa yafi qarfinsa,bazai iya controlling kansa ba. Tsam ya miqe ya sauka daga saman stool din,ya zube hannayensa a aljihun wandonsa,ya motsa labbansa a nutse.


*_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_*
08187255862


𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓 𝐀
_Zafafabiyar_

ΜΆBΜΆOΜΆOΜΆK ΜΆ2

β±§Ι„β‚²Ι„β‚₯β‚³

π™‹π˜Όπ™‚π™€ 81


_An tambayi nana Aisha R.A,menene dabi'un manzan Allah S A W,sai tace: dabi'unsa alqur'ani ne(ma'ana yadda qur'ani ke koyarwa da fadin kalolin kyawawan dabi'u dukka haka halayen fiyayyen halitta S A W yake)_



81


"Sabrrrrr" Ya kirata da sautin nan dake ratsa kunnuwanta ya aike da wani saqo me sauri zuwa kwanyarta. Ko motsawa batayi ba bare ya kula da taji kiran ko bata ji ba,sai ya sauya shawara shima,ya cire hannunsa daga aljihun wandonsa ya fara takawa inda take zaune.

Sarai taji takowarsa,amma sai takejin bata da wani sauran abinda zataji tsoro tattare dashi. Batasan gaibu ta gayawa kanta ba sai da taji hucin numfashinsa dab da fuskarta,kafin ta daga kai ya sanya hannu ya zare littafin ya sanyashi a gefanta,ya kuma maida gurbinsa da kansa. Yayi kwanciyar rigingine ne,fuskarsa na kallon sama tana kuma kallon fuskarta,ya hade hannayensa a qirji kaman me sallah,ya tsurawa qirjinta ido daya fuskanci zuciyarta ce take bugawa shi yasa ya fara dagawa sama da qasa kadan kadan.

Boyayyen murmushi ya saki.....tana da raunanniyar zuciya me cike da tsoro,saidai,kuma fushinta taurin kanta da kafiyarta kaman suna so su rinjayeta.

A tsorace take ainun da yadda ya kankane mata cinta,bata so kuma tayi masa magana sam sam,tana jin bai cancanci kalaman bakinta ba. Haduwar jikinsa da nata sai ya tuna mata da wanzuwar fareeda data gani yammacin jiya cikin jikinsa,abinda ya hadu da fushinta ya sake zafafan zuciyarta kenan ta tattara lausasan tafukan hannayenta zata ture kansa daga cinyarta. Hannuwansa ya saka ya riqesu yana kallon tsakanin haskensu da taushinsu da tun a idanu ma suka nuna hakan.

"Kin cewa anni zaki dinga gaisheni....kuma tamkar alqawari ne,bayan ta fita kuma kin karya alqawarin da ko minti uku bai cika ba.....na taso da kaina don nazo na gaidaki sai kuma ki koreni?,kinyimin adalci kenan?". Idanunta ta zuba masa a zafafe kalmar adalcin daya fada tana bata haushi. Shikam har yayi maganan adalci idan akazo batu a kansa?.

Batajin zata bari yaji koda kalma guda a bakinta,don haka ta gwammace hadiye takaicinta,ta maida kanta gefe bata furta komai ba tana qoqarin zame kansa daga cinyarta. Ganin haka sai ya juya da zafin nama ya koma rub da ciki,still kanshi yana kan cinyarta. A wannan karon ma sai ya qaro da sanya hannayensa ya zagayo bayanta dasu ya mata zobe kanan ya sakata a Tsakanin hannayensa.

"Good morning my sweetest women..........ina fatan kin tashi lafiya?" Ta fada yana sauke wani irin ajiyar zuciya gami da lumshe Idanunsa yana mamakin yadda take saka zuciyarsa bugawa haka.

Duk da baya dubanta haka ta zubewa qeyarsa me kwantacciyar suma idanu,tana jin gaba daya ya zame mata qarfen qafa. Duk wani motsi da zatayi don qwatar kanta sake qanqameta yakeyi sosai,hatta da tafukan hannayenta ya mannesu cikin nasa,ya saki ajiyar zuciya sannan yace

"Ina fatan kowanne ciwo da kika ji ya zame miki silar samun rahamar ubangijinki.......na gode......na gode.....na gode sau babu adadi da killacemin kanki da kikayi......na gode da kika qaryatamin zancan mutane a kanki.....kika kuma bani tabbacin da bandashia baya" Kaman susa bisa ciwonta haka maganganunsa suka zame mata,ta qwace hannun nata da qarfin zuciya irin nata tana ture kansa,amma sai ya sake rungume hips dinta sosai kaman zai maida kansa cikinta.

"Duk yadda zakiyi qoqarin korata daga rayuwarki wannan din mafarki ne......bazan iya ba......bazan iya barinki ba koda na second guda ne,indai zan iya rayuwa babu ruhi ko numfashi......tabbas zan iya rayuwa babu ke.....ke din ruhina ce.....numfashi na ce.....kuma jinin jikina,a cikinsu wanne ne idan babu rayuwa zata tabbata da cikakkiyar ma'anarta?"

"Ya isa......ka dagani" Ta fada adan tsaurare saboda wani irin nishi da sauti da yake sakar mata daya sanya ta fara daina gane komai,wata irin tafiyar tsutsa yakewa tafukan hannayenta da take jinta har cikin qasusuwa da bargonta.

"Ka daga ni ko na maka ihu na kira anni......." Murmushi ya sakar mata hankalinsa kwance ba tare daya motsa ko ya fasa abinda yakeyi ba

"Ki taimakeni ki kiramin ita......wataqila zata tayani gaya miki irin matsayin da me jadda ya baki.....ita din uwace dake fuskantar kowanne yare da 'ya'yanta zasuyi magana dashi". Da gaske yake mata,bataga wani alama ko kadan a tattare dashi na razani ko tsoro ba,saima sake gyara zamansa da yakeyi saman cinyoyinta kamar ya samu wata DUNIYARSA a wajen.

"Zan sake maimaita miki.....zanta baki haquri.....zanta baki damar horani har zuwa sanda zaki huce........amma karkiyi zaton akwai wani kalar bore da zakiyi da zai sanya na haqura dake.....kece rayuwata.....banajin bugun numfashi na yana fita da sunan kowacce mace a duniya sai ke" Ya qarasa fadin maganan yana sake qanqameta.

"Wayyo dinki na" Ta fada da qarfi,abinda ya sanyashi miqewa a gigice a kuma razane yana riqeta da kyau.

Ya bude baki zaice wani abu ta sanya duka hannuwanta ta tunkudeshi sai gashi ya tafi da baya ya fadi. Ba wani abu da taji na zafi ko ya samu dinkin nata,tayi hakanne dama kawai don ya saketa.

Baiyi wani qoqarin tashi ba saima sake bajewa da yayi yana sakar mata murmushi

"Next time ba zaki nasara ba" Daidai nan anni ta turo qofar a gaggauce saboda sautinta kaman da taji. Shigowar anni ya sakashi miqewa da sauri,yana dan kade jikinsa a kunyace. Yadda anni ta zuba masa idanu yasan tuhumarsa takeyi ba tare data jefa masa kalmar tambaya akan tuhumar tasa ba. Ta janye Idanunta ta mayar kan sabreen

"Lafiya?" Tambayar ta yiwa sabreen nauyi,batasan me zatace mata ba,sai tayi qasa da kanta ta kasa amsa mata.

"Zaka iya tafiya abinka,amma kasan ba'a takurawa mara lafiya right?" Tuni ya Fahimci me anni ke nufi,sai kawai ya gyara hannun rigarsa yana fadin

"Afwan" Ya juya yana fita a hankali bayan ya saci kallon sabreen din data kasa cikakken motsi.

Gabanta anni ta qaraso a hankali,taja stool din daya tashi akai ta zauna tana dubanta.

"Sabreen" Ta kirata a tausashe. Da qyar ta motsa labbanta tana amsawa sa

"Na'am" Tana lanqwasa yatsunta,ta tabbatar idanun anni sunkai kan littafin da fu'ad ya aje a gefanta,wanda duk wanda ya kalla zaice ita ta aje din don yafi kusa da ita.

"Ki lallaba jikinki ki warke yadda ya kamata,kada ki yarda kiyi sakacin da dadin bakinsa zai sanya ki bashi dama ya lalata abinda ke jikinki.....dukkaninsu 'ya'yana ne....kuma nasan halin kowa......shi namiji da kike gani dukkaninsu halinsu daya,abu kadanne ya banbanta wannan da wancan" Anni tayi maganar kanta tsaye.

Tsoro da kunya suka cakudu suka sanya hawaye taruwa idanunta,kunyar kada anni ta dauka wani abun suka aikatawa,ko ta bashi daman yin wani abu da ita. Muryarta yana raurau,idaΓ±unta cike da hawaye ta daga kai tana duban gefan annin.

"Wallahi Allah anni ni ban......"

"Shshssh.....bance kiyi rantsuwa ba sabreen,kome meye ya faru babu haramci a ciki,mijinki ne halal din juna kuke......amma nasan halin maza sarai.....akan wannan wajen komai ma zasu iyayi.....kusan a nan aka sanya hankalinsu,a nan ne kuma ke kike da power din iya sarrafasu yadda kikeso.... Dole ki bashi kulawa ta musamman,don ke nan ne naki mulkin yake......a yanayin da kike ciki dinnan kuma ba wani abu bane don ya miki dadin baki ya karba,tsaf kika bashin amshewa zaiyi.....amma sabuwar wahala kuma takice". Gaba daya kunya ta sakata saka hannunta ta rufe fuskarta tana sakin kuka,ya cuceta ya sakata jin nauyin anni,ya sanya anni tana tunanin wani abu a kanta

"Wallahi Allah anni......ni ba komai da......"

"Kul....ni ban tambaya ba,namiki bayanin da zai amfaneki ne,nace kuma ki kula,bance ki fadamin sirrinku ba,maza oya......goge hawayen" Anni ta fada tana tashi zuwa gaban dressing table,ta kuma jawo wata locker dake jiki ta ciro wasu kwalaye guda biyu ta dawo wajen sabreen din wanda ta sanya gefan mayafinta tana share hawayen daya zubo mata. Ba zata sake yarda ko fuskarta ya gani ba bare yasa anni ta zargeta,idan shi baida kunya ita akwai kunya a jininta.

"Daga gobe wannan sabun dashi zaki dinga amfani wajen tsarki,idan kikayi sati daya akwai saqon da zai iso zan baki ki amfani dasu,zan miki bayani suma idan sun iso".

" Na gode" Ta fada tana jin kunya tana dawainiya da ita,amma sai ta lura ita anni ko a jikinta,tamkar yadda uwa zatayi magana da 'yartane wadda shaquwa da fahimtar juna yayi nisa a tsakaninsu.

Kyakkyawar farfajiyar gidan ya fita yana tasbihi qasan ransa,ranshi fes da wani irin farinciki da yaji yana samun mazauni a zuciyarsa. Tabbas ya sake yarda...kudi ko wadata ko wani jin dadi na rayuwa bata taba cika saida macen aure.....cikar kamalar namiji itace aure ya yarda da wannan. A tsakanin jiya da yau,duk da birkitaccen yanayin da komai yazo masa sai yake jinsa a wani cikakken mutum me cikar kamala da mutuntaka,duk wani nauyi dake kowanne gaba na jikinsa kaman an sanya ruwa an wanke masa. Kwanyarsa a yanzu a cike yake da tunanin yadda zai gina kyakkyawar rayuwar auratayya ne kawai,gidan dake cike da soyayya da kuma qaunar juna.....irin qaunar da zata maida gidansu tamkar dausayin aljanna ta duniya. Bai damu ko kadan da dukka wadannan boren nata ba,yayi imani na wani dan lokaci qanqani ne,kuma zata yishi ta gama......komai zai daidaita. Yayi alqawarin dimautata da zazzaqar soyayyar da zata mance kanta gaba daya,ko tanaso ko bataso,ko ta yarda ko kada ta yarda......zai nuna mata qarfin qwajin zuciya da nasa salon na sace zuciyar d'iya mace,a banza ma yake aikata hakan ba tare da yasan yaushe hakan yake faruwa ba?,ballantansa wannan me license?.

Zamanshi kenan cab ya tsaya a qofar gidan nasu.ba wani me maida hankali bane shi kan abubuwan da basu shafeshi ba,don haka ya maida kansa ga wayarsa yana duba sunan da yayi saving number CP s.nuhu. a yanzun yana jin wani qaimi da wani irin priority a kansa na tunkarar dukka badaqalar daya baro a Nigeria. Indai har ya sameta a cikakkiyar mace budurwa wadda mutuncinta bai samu koda rawa ba balle tasgaro to tabbas dukka mutanen can akwai daga inda suka bullo,akwai kuma mabanbantan dalilai da suka shigo da ita rayuwarta. Me suke buqata?,wanne dalilai ke garesu?.


*_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_*
08187255862



𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓 𝐀
_Zafafabiyar_

ΜΆBΜΆOΜΆOΜΆK ΜΆ2

β±§Ι„β‚²Ι„β‚₯β‚³

π™‹π˜Όπ™‚π™€ 82



_Manzan Allah S A W yace: Bawa zaizo ranar qiyama da tarin ayyuka da kuma tarin lada,yana murna zai shiga aljanna sai Allah ya dakatar dashi,ga tarin mutane da baisan daga ina suke ba.....dukansu masu neman haqqinsu ne a kansu a wajen Allah,yaci dukiyar wancan.....ya zagi wancan.....ya zalunci wannan,ana biyansu da haka da haka sai ya wayi gari bashi da komai cikin ayyukan ladansa,bayan ayyukansa sun qare za'a koma ana diban zunubin mutanen a maimakon biyansu da ladansa ana lafta masa,daga qarshe sai ya tashi baida komai sai tarin zunubai,sai Allah yayi umarni wa mala'iku su jefashi a wuta( Allah ka tsaremuπŸ™πŸ½)_

_bukhair da muslim_


82


Tun yana daga cikin motar idanunsa suka sauka akan fuskar fu'ad din. Wani irin murmushi da ya fito tun daga qasar zuciyarsa ya wanzu a fuskarsa. Tabbas aure rahama ne kaman yadda mata suke rahama ga rayuwar wanda ya dace dasu. Daga inda yake yana iya hangen wani annuri na musamman na fita daga miskilar fuskar nan da ba'a lamunce mata murmushi ba a kowanne lokaci sai lokaci lokaci idan shi da kansa kuma yaso hakan,amma a yau yana ganin wani sakewa akan fuskar daya tabbatar koshi me fuskar ba lalllai yasan da ita ba.

"That's my bro muhammad fu'ad jadda" Ya fada qasan ransa yana taya fu'ad murna gami da kama murfin motar ya fito. Ci gaba yayi da kallonsa ba tare dashi ya sani ba,idan har za'a tambayeshi mutum na farko dake bashi mamaki a duniyarsa fuad dinne.......mutum na farko da rayuwarsa tamkar madubi ce a wajensa.....mutum na farko da tausayinsa bai taba raguwa a ransa ba fuad dinne. Yana da sauqi kayi masa mummunar fassara idan bakasan halinsa ba,bakasan wanene shi ba,amma kuma kuna wuce wannan level din dashi zaka fahimci mutane irinsa a duniya qalilanne.

"Ka kama kanka farouq.....banda tsokana da yawa,kafi kowa sanin wayeshi" Ya gayawa kansa da kansa saboda yadda yakejin wata dariya nason fara taso masa tun bai qarasa wajen da fu'ad din yake ba

"Ka wuceshi kawai kaman baka ganshi ba indai kasan ba zaka iya riqe dariyarka ba" Wani sashen na zuciyarsa ya bashi shawara don da gaske dariyar nan bayajin zata riqu. Yafi yarda da shawarar zuciyarsa ta biyu,don haka ya zaro wayarsa yahau kiran fannah ba tare daya shirya ba,a sannan harsu amna sun wuce cikin gidan.

Baisan adadin sau nawa murmushi ya kubcewa fuskarsa ba. Duk da waya ce a hannunsa amma ba abinda yake gilmawa idanunsa sai ita din. A wannin da suka shude masa sunyi masa wani irin tasiri da har ya mutu ba zasu taba goge masa ba. Wasu irin mintuna na musamman da suka fara cikin fushi suka kuma qare da wani abu me matuqar ban mamaki da bai taba kawoshi ba a ransa.

Bai lura da saqon ba don haka cikin sauqi hannunsa ya danna saqon ba tare da ya shirya ba

*_Kada ka taba tunanin zaka subucemin.....kada ka taba tunanin zaka kubcemin........a shirye nake nayi komai don na mallakeka.....ciki kuwa harda taba alaqar dake tsakaninka da KARUWAR da kake kira matar aure a gareka,fareeda khaleed mustapha_

Wani irin kallo yakewa saqon yana sake karantashi daga farkonsa zuwa qarshensa,

"Karuwa?" Ya maimaita sunan da wani irin yanayi da yakejin kaman ana yankar naman zuciyarsa.

"Fareeda?" Ya sake maimaita nata sunan yana jin wani irin fushi yana taso masa. Fareeda da ire irenta baya jin zai dagawa waninsu qafa da kalmar KARUWA ta fita a bakinsa muddin suna nufin kalmar ne akan SABREEN. Zaiyi shari'a da kowa a kanta......zai kuma tsaya mata akan duk wanda ya jefeta da wannan kalmar. Har ya fara laluben number fareeda din kai tsaye Muryarshi kawai yaji ya daga kai yana kallonsa. Farouq ne,shi kuwa da gasken gaske wai bai ganshi ba,ya daga hanci sama yana amsa wayar kanshi a sama yana duban qofar gidan.

Ganinsa kawai sai yaji fushinsa ya soma sassauta,dan uwa kuma abokin kuka tun

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login