Showing 519001 words to 522000 words out of 557259 words
a rayuwa amma ke baki gani ba?,to na rantse da Allah muddin baki sassautawa wannan zuciyar taki ba zakita shan wahala ne,ana aiki yana dawowa baya ba wani ci gaba" Ya fada cikin jin haushinta da takaicinta ya miqe yana barin parlor din bayan ya ajiye duka magungunan da zasu bata.
Idanunta suna kan likitan har zuwa sanda ya kammala ficewa. Numfashi taja sosai tana saukeshi,wani bacin rai yana qoqarin taso mata amma tana danneshi.
"Ba yanzu ba mariya......ba yanzu ba,ki danneshi don ki samu lafiya......ki danneshi don jikinki ya daidaita,akwai abubuwa da dama da kike buqatar aiwatarwa,lafiyarki kuma ita ce jagora,idan babu ita ba abinda zaki iyayi" Ta yarda da wannan sashen zuciyar dake mata wannan bayanin,ta aminta da abinda yake gaya mata. Maganganun likitan sun tsaye mata a rai,lallai ne baisan wacece ita ba.....baisan wacece mariya ba,wato kawai idan baka da lafiya sai abinda ka gani?,idan ba zaka iya yiwa kanka komai ba......idan ba zaka iya cewa komai ba kawai sai abinda ka gani?. Maganar da take nanatawa kanta kenan tana tuhumar wannan ciwon.....ciwon da yayi mata dirar mikiya a sanda ya kasance takun taqi kadanne tsakaninta da arziqinta,takun taqi kadanne tsakaninta da cikar burinta fa......to kuwa me zai hana su kasa fahimtar asiri akayi mata ba hawan jini bane.
Duk inda ta juya ya waiwaya fuskokin yaran take gani,ba daman ta rufe idanunta sai taga yaran guda uku sak masu kama da fu'ad,ajiyar zuciya ta dinga saukewa tana jin wani razana yana kamata.
Fu'ad ya riga daya samu magada,ko mutuwa yayi a yanzu ba a abinda mutuwarsa zata qara mata illa tsira da kaso daya bisa shida na dukiyarsa.......babban sake da kuskuren shine barin yaran suka iso duniya.....kuma duniyarma ta shaida.
Ko sanda ta samu bacci yayi awon gaba da ita su ta dinga mafarki,a mafarkinma su shida suka koma,wani akan qafarta wani a bayanta,wani a zaune saman kanta,wani a gefenta haka dai,na saman kan nata ne ya sheqo mata kashi daya rufe fuskarta da jikinta gaba daya,abinda ya sakata farkawa kenan.
Jikinta rawa yakeyi sosai,ta jiqe da gumi cikin tashin hankali,takai idanunta inda su sahura ke bacci,tanason tashinsu amma bata da wannan ikon.
"Meye fassarar kashi a jiki?,anya ba ajalina aka haifo yaran nan suyi ba?" Ta tambayi kanta da kanta can qasan zuciyarta. Juya mafarkin taci gaba dayi da ma'anoni daban daban,hankalinta kuma yana sake tashi,har sanda Allah ya tashi sahurar ta dubata ta bata ruwa ta sake gyara mata kwanciya. Tanata kallon sahurar,tanaso ta tambayeta fassarar mafarkin kashi,amma ba bakin magana,haka ta maida idanunta ta kulle tana jin zuciyarta tana mata quna,tana Allah wadarai da rashin damar yin magana da bata dashi.
"Mafarkin kashi fa arziqi ne....alheri ne" Wata zuciyar ta gaya mata tana tunasar da ita shekarun baya can sanda fu'ad yana yaro. Tasha yin wannna mafarkin a kanshi,duk sanda ta farka kuwa an yita tafka tsiya kenan ita da abbansu.
"Ni wannan yaron bansan meye tattare dashi ba......kai baka da aiki saidai ayita mafarkin ka shafe jikinka da kashi koka shafeni?,inda Alla yake taimakona wankewa nake zuwa ni nayi a mafarkin ina dalili?,kai kuwa kaida Musaddiq duk yadda zan jaku ku wanke qi kukeyi.....kashi ai masifa ne qazanta ne". Tofa a ranar haka zata yita maganganu,hantara da kyara kuwa ranar fu'ad ya gamu dashi kenan har sai ya fita a gidan ya wuni a layi sannan hankalinta yake kwanciya. Ba fadan da abban baiyi mata ba amma bata ji ba,dole ya kawo idanu ya zuba mata,shi kuma bai taba gaya mata cewa ana tunanin arziqi bane.
Abun ya tsaye mata akan jariran,tanason gasgatawa amma kuma tana qaryata hasashen nata.
β
Sati biyu sukayi a madeena kaman yadda fu'ad ya tsara. Cikin sati biyun yake sanya ran sabreen taji qarfin jikinta,hakanan yaran sun sake qwari.
Hakanne kuwa ya kasance,zuwa lokacin sabreen din ta warke sosai saboda irin kulawar data samu daga kowanne bangare,duk da cewa anni tun suna da sati guda ta koma Nigeria. Tana da buri sosai na hadawa yaran gagarumar walima,saidai taje ta tarar amna ta gama shirya komai da taimakawar musaddiq. Wani irin gagarumin suna da akayi sati guda ana shelarsa,sunan da duniya ta jima bataga irinsa ba.
Cikin sati gudar nan fadin irin dukiyar da fu'ad ya sadaukar ma bata baki ne,irin yawan kyauta da yayi abun ba'a cewa komai,mutane da dama ya fidda da prison,mutane masu yawan gaske ya biyawa bashi,mutane masu yawa ya siyawa gidajen zama,mutane masu yawa ya dauki nauyin aurar da 'ya'yansu,a cikin dangi kuma ya sake ninka adadin mutanen da ake bawa kujerar hajji da adadin ninki uku. Mutane da yawan gaske ya dauka nauyin maganinsu da samar musu lafiya,hakanan ya qara yawan adadin marayun da nauyinsu ke wuyansa. A sannan sai ya ke qara jin yana da kyau idan sabreen ta koma hankalinta su zauna,foundation yake da sha'awar ya bude mata saboda taimakon iyayen marayun da marayun kansu.
Yayi kyautar kudaden da shi kansa baya lissafawa. Duk duniya sai data shaida muhammad jadda an haifa masa abinda yafi so.....muhammad jadda ya samu abinda yafi qulafuci,duka kuma yayi ne saboda nunawa ubangiji godiyarsa a gareshi.
Kwanaki uku kawai da suka rage suna suka baro birnin madeena da boundles of joy dinsu,suka sauka kanon Nigeria.
Tun a airport tasan lallai haihuwa wata baiwa ce,wata abace ta daban dake cike da ni'ima baiwa da kuma tarin albarka da bata da iyaka.
Tamkar tawagar matafiya haka sukayi zuga zuwa gida,ko dama fu'ad din idan yana qasar motocinsa sukan kasance ne cikin convoys koda yaushe......saidai a yanxun yawan adadin ya ninku.
Sanda suka isa gida ma mutane 'yan sannu da zuwa da barka suka samu,saidai kusan duk wanda ke cikin gidan me fada aji ne,don haka cikin gayu da nutsuwa komai ke gudana,don sai data shiga daki ta sake wanka ma,aka warware yaran suma aka sakeyi musu wanka aka shiryasu cikin wasu lausasan kaya masu zuwa complete set dinsu ruwan sararin samaniya me haske. Nannys ya dauka musu qwararru tun daga madeena din,wadanda raino suka karanta gaba daya. Salwa da sameena,ba cikakkun larabawa bane,saidai acan aka haifi iyayensu suma aka haifesu,har kuma suka soma girma a yanxun,don kowacce tayi shekara kusan talatin da biyar biyar. Asalin kakanninsu 'yan nigeria ne......mata ne kamilallu da suka san rayuwa,sukasan kuma raino da abinda ake nufi da tarbiyya.
A iya rayuwarta idan aka gaya mata akwai ranar da rayuwa zata sadata da manyan mutane irin wadannan zata qaryata.....mummunar qaryatawa kuwa,don tasan tabbas wutsiyar raqumi tayi nesa da qasa idan har ba ta dalili ko silar fu'ad din ba.
Allah ya zuba mata wani iri kwarjini da cika ido sabreen din tun asali,tana kuma da wata irin nutsuwa da kamewa......wannan ya sanya ta saje sosai a cikinsu.
Irin gifts din data karba a ranar kadai sai daya sanya kanta ya kusa kullewa. Da gaske masu kudi suna sha'aninsu,da gaske masu arziqi suna sha'aninsu......da gaske rayuwa mataki mataki ce. Gifts data samu a yau idan a rayuwarta ta baya aka gaya mata ana kyauta da irin wadannan kudaden ko kayan zata qaryata,zata kalli wanda ya bata wannan labarin tace masa ya rage qarya......ya kuma ji tsoron Allah,sai gasu zube a wani daki daban,wanda ma'u tace a nan zata tarawa yaran komai nasu.
Ana magariba ta rufe ganin kowa don tanaso ta bawa fu'ad lokacinsa.......tanaso ta bashi kulawa kaman yadda ta soma tsarawa rayuwarta. Yaran ta sama su salwa suka sake daukewa,aka sake fesa musu wanka da wasu baby set din da akayi musu order dinsu musamman daga wani babban kamfani dan qasar turkiyya. Akwai wani tambari na musamman jikin rigunan dake dauke da THE JADDA'S jikin rigar Kowannensu,hula da takalmi da safan hannu dana qafa duka irin guda sak da kayan da abun daukan nasu dake da adon gold a jiki.
Daga wanka ta fito itama,wanda take lullube wajen dinkin da wani leather haka tayi wankanta sannan ta tsane jikinta da kyau kafin ta bude.
Tururin zazzafan ruwan dake tashi da wani sassanyan qamshin turaren wanka na incense by kabo daughter jikinta yake fiddawa. Wani irin nishadi takeji......tana masifar son qamshi har batasan waye yafi wani ba tsakaninta da fu'ad din. Duka gidan a dumame yake da qamshin incense by kabo daughter,wanda kowanne sashe da daki na gidan qamshinsa daban yake fiddawa.
Manyan mahaukatan botikai tasa akayi mata kusan kala goma,kowanne kuma qamshinsa daban yake fiddawa.
Kanta ta busar ta kuma turareshi da kabbasar gashi duka daga kamfanin incense by kabo daughter,ta tajeshi tana qoqarin kameshi da banda taji an riqe hannayenta a tausashe ta baya.
Murmushi ya subuce mata jin yaqi magana,ya kuma tsaya cak yaqi ya bata alamun da zata gane shine. Motsa labbanta tayi a hankali tana dora hannunta ta baya saman nashi.
"Koda bayan na dauki shekaru da mutuwa ne......koda bayan na zama qasusuwa ko qasa cikin qabarina......muddin zaka wuce ta gurin zan fahimci cewa kaine ka wuce,don takun takalmanka zai zama ya fita daban dana kowa". Wani irin abu yaji yana ratsashi,sabreen dinsa ta fita daban da kowa.......ta iya kalaman da suke sanyashi kullum kwanan duniya yake jin kansa yana sake kumbura,kullum kwanan duniya yakejin yafi kowanne d'a namiji sa'ar mace.....kullum kwanan duniya yakejin ba za'a sake haifan mace kamanta ba.
Juyo da ita yayi suna fuskantar juna,idanunsa cikin nata yana ganin ta sake masa wani ajiyayyen kyau.
"Na dauka zaki tsorata ai" Ya fada a tausashe yana sanya hannunsa ya matsar mata da wani siririn gashi daya fito ta gefen fuskarta gefe. Murmushi ta kuma sakar masa tana juya idanunta.
"Tsoro?" Ta tambayeshi tana murmushi,sai kuma ta miqa hannunta gefan fuskarsa tana shafa kwantacciyar sumar dake wajen.
"Wannan jarumin mazan......wannan uban na 'yan ukun nan masu sunaye masu daraja......ya fidda kalmar tsoro kwata kwata daga rayuwar marainiyar nan.....ya cikata da qauna da aminci da soyayya.....ya sanyata cikin wata masarauta dake cike da tsaro......ya kewayeta da amintattun mutane......ya kuma sake bata wasu ruhikan har uku da zasu rayu da ita" Kasa magana yayi illa jawota da yayi ya rungumeta tsam cikin jikinsa.
"Me zan mallaka miki my world......me zan miki da zai sake fahimtar dake girman matsayinki a raina.....me zan miki?".
"Kaci gaba da sona saboda Allah,kaci gaba da qaunatata don girman zatin Allah,ka kula dani......ka kula da yayana da rayuwata.....sannan ka rayu dani ni kadai". Dagata yayi.yana murmushi gami da duban fuskarta,kafin yace komai ta rigashi.
" Ina da.tsananin kishi.....amma akanka kadai.....banajin zan iya rabaka ko sharing dinka da wata".
"Kin riga kin sameni.....kin sameni har abada ke kadai sabreen.....xanta maimaita miki hakan har sai ranar da kika gamsu dari bisa dari".
"Na yarda dakai" Ta furta tana kallon tsakiyar idanunsa
"Na yarda dake fiye da yadda kika yarda dani" Ya fadi yana sauke mata tattausan kiss.
Knocking din qofar shi ya maida hankalinsu kan qofar.
"Xan iya shigowa hamma?" Muryar amna ta qaraso dakin bayan tadan buda qofar kadan
"Bismillah" Ya fadi yana takawa zuwa qofar dakin.
Babies biyu ne rungume a kafadarta,ya miqa hannu ya karbi daya yana tayata dashi. Tare suka shigo dakin,ya qarasa gaban sabreen ya tsugunna zai miqa mata shi,kaman yasan an iso gaban mamanshi ya saki kuka.
Murmushi ya saki yana bude fuskarsa,ya kalleshi da kyau sannan ya daga kansa yana dubanta.
"Farouq ne......" Murmushi itama tayi tana maida kallonta kan fuskarsa.
"Gyara zaman na baki shi". Saman cinyarta ya dora mata shi sannan ya saka mata pillow yadda zata jita comfortable. Baya ya koma ya zauna sosai yana kallonsu cikin burgewa,yadda take shayar dashi hamza yana gefanta hannunta saman sumar kan hamzan.
"Hamma" Ta kirashi a shagwabe.
"Giwar hamma" Ya amsa mata har cikin ranshi yana jin ta cancanci wannan sunan.
"Nifa na shirya"
"Zuwa ina?" Ya tambaya yana kallonta.
"Zamuje ni dakai mu kaiwa maamah yaran nan ta gansu......bata gansu ba bata sansu ba". Shuru ya danyi yana juya maganarta,hakan ya kamata suyin,to amma shi yana tsoron dabi'ar maamah,baisan da wanne irin kallo zata dubi yaran ba,yana tsoro kada kallonta kadai ya cutar masa da yaran. Saidai kuma ya tabbatar sabreen din tana da zurfin tunani da hangen nesa,ba zata yi abinda zai zamewa yaran cutarwa ba......hakanan ya yarda da ita dari bisa dari.....161
"Is okay" Ya fada a taqaice yana miqewa
"Bari na watsa ruwa kafin lokacin ki sallami sojojina ko?abbana ne kawai ba'a kawo ba" Ya fada yana kashe mata ido daya. Rolling nata idanun tayi tana murmushi.
"Ba laifi"
"Wannan abun yana kasheni my world......anya zaki taimakamin na barki har ki warke?" Ya fada yana karya wuya. Yadda yayi wani kalan tausayi ya sakata sakin dariya
"Eh to,ai anni tana nan dai......sannan momma ma gobe zata iso". Sarai ya fahimci me yake nufi,sai yadan bata rai,ya tako zuwa kusa da ita.
"Karki yadda a zame mana katanga tsakaninmu......bazan iya jurewa ba,idan kuma har na gaza jurewar komai ma zai iya faruwa" Ya qarasa maganar yana aje mata wannan zazzafan kallon nasa da taji ya tsarga mata itama tun daga tsakiyar kanta har tafin qafafuwanta. Daidai sanda kira ya shigo wayarta,ya matsa a hankali ya dauko mata wayar.
"Bibo da yarinyarta sunzo,saidai na hanata ganinki,don har yanzun ban gama nutsuwa da ita ba,bazan kuma bari kowanne abu da ban gama nutsuwa dashi ba ya iso gareku" Ya furta yana saka mata wayar a hannunta.
"Na tabbatar maka bibo tayi nadama zuwa yanzu,don ba komai yake damunta ba tuncan baya sai kishi da hassada"
"Zan duba na gani" Ya amsa mata yana takawa a hankali zai fita a dakin,ta maida kallonta kan wayar.
Kawu rufa'i ne,ta dan saki murmushi tana daga kiran.
"Sannu d'iyar arziqi......sannu d'iyar albarka......wadda aka haifa tsiya tana bacci". Dariya sosai kawun ya bata.
"Ina wuni kawu barka da dare"
"Barkanki kadai,an samu kai qalau?"
"Alhamdulillah kawu"
"Ubangiji ya rayasu yayi musu albarka......ai nace kinyimin daidai da kika bugo yara uku tun a karon farko......wa yaqi arziqi?,waye zaiyi sanya a gidan arziqi?,ina me miki wasiyya,duk sanda kika tashi haihuwa dinga ajiye masa hudu hudu uku bibbiyu,idan da hali karkiyi d'an d'aya ma sam". Dariya ce taso kubce mata,amna ta danneta,saidai hakan ya nuna a muryarta.
"To ai kawu abun na Allah ne,shi yake bada iya adadin da yakeso".
" Eh amma ai yace ku roqeni zan amsa muku ko?,qarshen watannan zamu shiga qasa me tsarki,farouqu xai fara cika alqawarinsa.......zam zage nayita roqo miki.haihuwar haka haka din" Wannan karon saida tayi dariya sosai.
"Kawu Allah ya bamu masu albarka wadanda zamu iya dasu".
"Ke!,kana da wadata da arziqi irin na mijinki harka dinga tunanin kalar yaran da zaka iya dasu?,yo ko yawan taron arfa kika haifa masa ai yana da abinda zaiji dasu". Kai ta girgiza tana murmushi.
"Kawu......tarbiyya ba'a nan take ba,kace ameen kawai"
"To ameen sarkin tsari......nace ba?" Ya fada yana komawa serious.
"Ina jinka kawu"
"Ina iya tahowa zaman dab'aro?". Idanu sosai sabreen ta bude dariya tana son qwace mata.
"Kawu kaifa kawuna ne,kuma namiji ne kai,ai mata suke zaman dab'aro,inama laifin ace inna A'i?(matarsa)".
"Ke komai yanzu a zamanance akeyinsa,ta yaya zan turo A'i gani?,bayan ba abinda bazan iyayi miki ba?,ni damuwata na kula da d'iyar ahmadu,na rama halascin da ya yiwa rayuwata" Ta fuskanci da gaske kawu yake,saita gyara muryarta.
"Kawu kada ka damu,mun dauko masu kula da yaran musamman,sannan kuma ga masu aikin gidan na ainihi".
"Duk da haka ba za'a barki haka ba,xan aiko A'in ta zauna miki kona kwana arba'inne na al'ada"
"To kawu Allah ya saka da alkhairi ya qara zumunci" Ta fada tana jin dadi qasam ranta. Ko ba komai zata ce ga wani daga dangin mahaifinta,duk da zuwa yanzu 'yan uwa ne kowa keta kutsowa da b'arkowa don nuna kulawarsa da bajintarsa akan haihuwar,tun suna madeena ma kafin sukai ga dawowa.
Wayar ta sauke tana murmushi sanda take tuno baya,drama dinsu da kawu wadda kusan kullum sai an yita,rayuwa kenan.....komai yayi farko said qarshe,kuma dukkan tsanani yana tare da sauqi tabbas.
Farouq yayi bacci,saita ajiyeshi kusa da dan uwansa hamza,ta miqe ta soma shiryawa,tana yi tana duban fuskokinsu. Ita kadai murmushi yana subuce mata,tana jin qaunar yaran har a cikin jininta. Duk sanda ta kallesu su ukun a jere reras saita samu kanta cikin mamakin yanzu wadannan din daga jikinta suka fito?,yanxu wadannan din 'ya'yanta ne?,mallakinta ne?,yanzu wadannan din jininta ne?,jinin muhammad fu'ad ne?.