Showing 174001 words to 177000 words out of 325075 words

Chapter 59 - SARAN-BOYE COMPLETE

20 Jul 2024

29167

?auka waya yay kiran Joy. Ring biyu kuwa ta ?aga. Ko gaisuwar datai masa bai amsa ba yace, "Dafa min Noodles". Daga can tace, "Okay Brother, and egg?". Bai amsata ba, sai duban Aymah da yayi, wadda ya tabbatar tana jinsu tunda a Hans free ya saka. Kanta kawai ta ?aga masa ta ?auke idonta daga garesa. Amsa ya bama Joy ?in da fa?a mata inda zata kawo ya yanke wayarsa.
Daga haka ?akin ya ?auki shiru, shi dai wayarsa ya keta latsawa, ita ko tana zaune a stool ?in mirror ne kawai tana kallonsa ta ciki fuska a kumbure. Ba komai ke cinta ba sai kewar gida da yunwa. Damuwace fal ranta, a kallo ?aya kuma zaka tabbatar da hakan.
Knocking ?in da akayi ne ya sakashi fa?in "Shigo" a ta?aice batare da yako ?ago daga abinda yakeyi ba. Gabansa Joy taje ta ajiye tiren batare data kalli inda Aymah take ba, "Broth gashi, nikam inata mamaki, wai kai ne da cin Noodles yau a gidannan?".
Wani mugun ta?e baki Aymah tayi ta ?auke kanta daga kallonsu, a ranta kuwa rayawa take saita saita kan joy ?innan a layi idan har tace zatai mata hauka. Dan duk da ta girmeta sosai ai ita yanzu matar yayanta ce dan ?aniyarta. (Madam son girma??lol).
Yoohan kam da ya gama sauraren Joy a ta?aice yace, "Thanks". kawai. Duk da Joy tasan halinsa, ba kuma yau ne farauba sai na yau ?in yay mata zafi saboda agaban Nu'aymah ne. A hasale ta nufi ?ofa tana harar inda Nu'aymah take. yanda ta fisgi ?ofar ?akin da zata rufe ne ya sakashi ?agowa, sai dai kafin yace komai ta bar wajen da gudu.
Shiru yay baice komaiba, sai idanunsa daya maido kan Nu'aymah. "Kizo kici zamuje ki gaida Momy da Papa". Batare data dubesa ba tace, "Badai mai wancan za?o-za?on farcen bace ta dafa min ko?". Yanzun kam sosai Yoohan yake kallonta, a ransa yake fa?in, 'Yarinyar nan muguwar ?ar matsala ce wlhy'. A fili kam fuska ya ?ara tsukewa yana tsatstsare ta da idanu. "Kina ?atamin lokaci malama, inada abu mai muhimmanci a gabana". Kanta ta maida gefe tana ?ya?e baki, cikin ?un?uni da hausa tace, 'Da waye ya gayyatoka anan balle ka ?agan hanci'. Ta ?are maganar tana tasowa inda yake. dan harga ALLAH wata shegiyar yunwa kecin hanjin cikinta.
Shikam baima sake bi takanta ba, ya cigaba da sabgar gabansa a wayar. Ba ?aramin danne zuciya Aymah tayi ba wajen zaman cin indomie ?in nan. Dan babu abinda ke zuwa mata a cikin rai sai farcen dake a hannun Joy za?o-za?o da tarin gashin dokin da akai mata kitso da shi kamar jikar bammali. Ko rabi kuwa bataci ba ta ture gefe.
Kallonta yay fuska a tsuke, cike da ?osawa yace, "Wazai ci miki wannan ?in?". "To oho, ni dai na ?oshi, yama zaka saka wancan mai farcen da Attachment ?in kamar ?iyar bammali taimin girki. Wanda naci ma da wahala ya zauna dan amai nakeji dana tunota. Ga uban bleaching tayi sai ?arni takeyi".
Sosai yaji zafin abinda take fa?a akan ?ar uwarsa, amma sai yake mata uzirin ?uruciya ce kawai ke ?auwainiya da ita. Watsar da ita yay bai sake duban ko inda take ba har tsahon mintuna uku. Kafin ya mi?e yana zura wayarsa a aljihu. "Muje" ya fa?a a ta?aice yana yin gaba abinsa.
'Tab! Wai kaji haushi ne dan na fa?a abinda ke raina? Aiko aiki ya sameka, dan bazan ga abin maganaba nai shiru bakina yay wari. Da wani kansa kamar mulmulen furar hajjo'. Tai maganar tana mi?ewa. Dan itama zaman ?akin ya fara isarta kuma. Tanason taga gidan yaya yake?. gyale ta ?auka da yay dai-dai da atanfar ta biyosa. A falo ta samesa tsaye, batare da yayi magana ba yay gaba ta bisa a baya suka fice.

Tun daga bakin ?ofar sashesa take ?arema gidan kallo, babu ?arya gidan ya ha?u, musamman idan kana sama kake kallon tsarin falon ?asa. Hakama idan kana a ?asa kake kallon upstairs ?in. Ga koma tsaf babu wani datti alamar dai ana kula da tsaftar gidan yanda ya kamata. A yanzu haka ma'aikatan gidan daketa shara da goge-gogen yamma sai risinawa suke suna gaishesu. Shi ka?ai yake amsawa. Ita kam binsu kawai take da kallo da takaicin ganinsu ?attan maza.
Ta saman upstairs ?in suka nufi sashen Momy dake jikin na papa. Corridor ne mai ?an fa?i da ?ofofi uku a cikinsa. sa?anin Nasu da zaka iske falo. Knocking ?in ?ofar tsakkiya yayi. Daga ciki wata murya ta amsa. Juyowa yay ya ?an kalleta sannan ya tura ?ofar. Ita dai biye take da shi. Yanda taji yace, "Excuse me" itama Excuse me ?in tace a hankali.
Murmushi madam Chioma dake waya da ?awarta tana bata wasu dabaru ta saki saboda ganin rabin ranta. A yau ?in nan duk da zafin zazza?in nan da takeji sai taji a ranta garama da take yinsa. Dan koba komai a dalilin zazza?in ta samu kusanci da lokacin yaronta mai tsaho tare da ita. A gaba ?aya yinin yau sai zirga-zirga ya keyi a kanta da son ganin jikinta ya dai-daita. ?azuma da taita langare masa yafi awa biyu zaune tare da ita.
A hankali kuma sai fara'ar fuskar tata ta fara gushewa saboda ganin abinda ke a bayansa.......
"Masha ALLAH Mom sau?i yazo sosai" ya fa?a yana zama a gefen gadon nesa da ita ka?an batare da ya lura da canjawar fuskar tata ba. Nu'aymah kam dake mata kallon ?asan ido taga komai da madam Chioma tayi, murmushin farko da canja fuskarta da tai saboda ganinta. Dai-dai Aymah na zama bisa sofa ?in ?akinne Momy ke bama Yoohan amsar maganarsa. "?arfin haline kawai my boy, dan dana tashi ma kamar zan kiraka kazo ka sake dubani sai nayi tunanin ko baka a gidan ne?".
?an murmushi kawai yayi batare da yace komai ba, saboda gaisheta da Nu'aymah keyi. Shiru tayi kamar bazata amsaba, ita kuma Aymah daga gaisuwar nan guda ?aya bata sake wata ba.
"Mom tana gaisheki fa". Ya fa?a yana kallonta. Daburcewa ta nema yi, dan batai zaton zai saka baki ba. Cikin kame-kame tace, "Oh Daughter Am sorry, hankalina nakan Son, kina lafiya?". Cike da mamakinta Aymah tace, "Alhmdllh" daga haka taja bakinta tai tsit fuska babu walwala. Itama Madam Chioma bata sake bi takan Nu'aymah ba. Gaba ?aya hankalinta naga Yoohan. Sai takalarsa da zance take ya?i magana ?wa?w?wara, daga guntun murmushi sai um sai a'a. Ita Aymah ma abin dariya yaso bata. A ranta sai gulmar ?an da uwar takeyi tana kwasar dariya. A fili kuwa fuskarta babu ko ?igon walwala a cikinta. Ta tsume abinta kamar tama manta da su a ?akin.
Sosai Yoohan yake lure da ita, amma idan ba shiba bazaka ta?a fahimtar hankalinsa na gareta ba. Agogon hannunsa ya kalla yana fa?in, "Momy bara muje ta gaida Papa nasan ya shigo yanzun".
"A to muje sai na rakaku ai" ta fa?a tana mi?ewa. Da sauri Yoohan yace, "Haba Momy, keda ke fama da kanki". "Karka damu ai da sau?i" ta fa?a tana bin bayan Aymah da tunda ya ambaci tafiyar har ta kai ?ofa. Bayansu kawai yabi yana mamakin halin Momynsa.

Koda suka fito Aymah tsayawa tai baya suka wuce gaba tunda sune ?an gida. Sun shiga sashen papa dake da falo babba, dan har yafi nasu girma ma. bata cuci kanta ba, koda suka zauna sai da ta ?arema kowace kusurwa ta falon kallo lokacin Momy ta shige bedroom ?in papa dan basu sami kowa a falon ba. Yoohan kuma yanata latsa waya.
Lokacin da suka shigo shima papan ta ?asan ido ta gama ?are masa kallo tsaf. Shima ?ya?y?yawa ne kuma fari, dan suna kama da Yoohan, sai dai Yoohan ya fisa ?yau da ?warjini da ?uruciya. Da alama dai Yoohan ?in ya kwaso kamannin wanu bayan shi. Papa na zama Aymah ta zamo ?asa ta zauna. Ba Yoohan ba har Madam Chioma hakan da Nu'aymah tayi ya bata mamaki. A ranta kuwa ayyanawa take, 'Wato ni wannan ?ar shilar yarinyar ta raina kenan?, ina zaune sama tana zaune itama a ?akina'.
Maganar papa ce ta katse madam Chioma. Cikin fara'a sosai yake amsa gaisuwar da Aymah ke masa, harda ha?awa da ?ar tsokanarta. Itako tanata zuba murmushi kanta a ?asa. Tambayoyi ya rin?a mata dake nuna kulawarsa a gareta. Hakan ne ya sakata ?an sakin jiki da shi tana bashi amsar da duk ya bu?ata.
Shi dai Yoohan ma abin sai ya bashi mamaki, dan koshi bata sakin jiki da shi kamar hakan. Papa daketa murmushin jin da?in yanda Aymah ta saki jikinta da shi ya dubi Momy yana fa?in, "Darling a tattaro min duk members na gidan nan da masu aiki, zan gabatar musu da daughter in-low ?ina. Itama na gabatar mata da su.
Cikin ?an yatsine fuska madam Chioma ta mi?a hannu ga wayar landline dake a table ?in jikin kujerar da suke zaune ita da papan ta hau danne-danne. Kira tayi, bayan an ?auka daga can tace, "Joy, ki sanarma kowa na gidan nan yazo Master parlor yanzun nan".
"Okay maa!"
Joy ta amsa daga can tana ajiye wayar.

Cikin mintuna ?alilan kowa ya shigo falon, hatta da maigadi bai zaunaba, kulle gate ?in yayi ya taho. Shi dai Yoohan kamarma baya cikin falon. Babu wanda ya damu da shariyar tasa tunda sunsan halinsa kenan. Victoria ce ma uwar surutu taje jikinsa zata zauna ya harareta. Da sauri ta canja mazauni tana tura baki gaba na shagwa?a.
Sai da kowa ya nutsu sannan papa ya fara magana. "Na taraku anan ne domin na sake tabbatar muku da ?aruwar member da family ?inmu ya samu duk da nasan kun sani. Karku ganta ?ar ?arama kuce zaku ?auketa ?asa da ku, har wani raini ko abu mara ?yau ya faru a tsakaninku. Duk wanda ya aikata hakan zan sa?a masa da sa?awa mafi ciwo. Dolene kowa na gidannan idan ka cire su mama da Darling dake matsayin kakanni a gareta da Uwa kowa ya bata girmanta. Saboda mata ce ita a wajen John, kowa kuma yasan a gidan nan bayan ni John shine uba, dan shine babban ?ana abin alfaharina. Sunanta Zainab, amma ana kiranta Ayimah. My daughter ko ba haka bane?" ya ?are maganar yana kallonta. Murmushi Aymah tayi, batare data ?agoba ta gyara masa da cewar, "Nu'aymah".
Sake maimaitawa yayi duk da dai yanzunma bai fa?a dai-dai ba. "Nasan dai baku manta da shara?in John ba. Zainab ?ago kanki zan nuna miki kowa da sunansa anan kema".
Babu musu kuwa ta ?ago, dan ganinsu cike da falon baisa taji ko ?arba a ranta saboda tun fil azal ita ALLAH yayita mutum mara tsoro. "Wannan itace mamana sunanta Mama debora. Itace ta haifeni tare da ?annena. Maza mu uku, mata su biyu. Gasu nan" ya nuna ?annensa biyu mata dake zaune a wajen. Maman Favour, da maman Destiny. "Akwai maza biyu suma zan nuna miki su idan sunzo. Sai wannan itace Maman Darling. Momyn John kenan gata nan" ya nuna madam Chioma da mamanta. Daga haka ya dawo kansu Joy, Gebrail, Abraham, Victoria ?annen Yoohan kenan. Sai Miracle ?iyan ?an uwansa Uncle Mike. Sai Aunty Blessing kuku, daga haka ya koma kansu Solomon daki-daki da ayyukansu a gidan duk ya sanar mata har zuwa kan maigadi.
Cikin murmushi tace, "Nayi murnar ha?uwa da ku duka".
A tare suma duk suka amsa mata da hakan, duk da dai da yawansu ba har cikin zuciya bane ba. Sun fa?ane kawai saboda tsoron Yoohan da duk abinda sukeyi yayi kamar baya falon.

Sallamar ma'aikatan gidan ya farayi, kafin ya sake duban family nasa ya shiga musu nasihar zaman lafiya (Su papa kenan??lol). Daga haka ya sallami su Miracle ma daketa antayama Aymah harara ta ?asan ido ita da joy. ya rage daga shi sai su mama debora da su maman Destiny. A gabansu ya fiddo keys ?in mota guda biyu ya mi?ama Nu'aymah ?aya.
"Dota wannan shine wedding gift ?inki daga ni. Kai ma John ga naka. ALLAH ya sanya muku albarka a cikin aurenku". Da hannu biyu Aymah ta amsa bayan taje gabansa ta dur?usa. Tai masa godiya sosai. A ranta kuma tana addu'ar ALLAH ya shiryesa idan yana da rabo, idan baida kuma ALLAH yay maganinsa. Shima oga Yoohan ya amshi nasa. Tare da rungume papansa yana mai nuna masa jin da?insa da wa?annan ?yaututtuka shi da matarsa. Bu?e masa hannaye madam Chioma tayi wai itama ya bata hug.... Kafa?a ya ma?ale mata yana fa?in, "Sai kin bamu naki gift ?in sannan".
Kusan a tare duk falon akai dariya. Banda Aymah da sam abin ita bai birgeta ba. Dan haka kawai madam Chioma duk da mahaifiyar mijin nata ce batai mataba ko ka?an. Su mama debora ma duk sun bama Yoohan ?yauta, amma basu bama Aymah ba. Ko a jikinta ita kam, dama bata bu?ata. Ganinma lokacin salla yayi saita mi?e tana fa?in ita zataje tai salla lokaci yayi.
Papa ne kawai ya amsa mata. Sai Yoohan da ya bita da kallo saboda ganin yanda tai maganar kanta tsaye babu wani inda-inda a ciki. Harga ALLAH ta birgesa, dan da watace sai tai ta nuku-nu?u musamman data san su ?in sun rinjayeta a gidan.
Ko kallon inda yake bataiba tai ficewarta, dan tasan zata gane hanya abinta. Acan downstairs ta hango su Miracle sun baje suna kallo, ta girgiza kai da ta?e baki tana fa?in, 'ALLAH ka rabamu da gafalalliyar rayuwa dai'.
Sai da ta tsaya a falon ta gamai masa kallon tsaf tana jinjina yanda ya ha?u, da jin ?aunar iyayenta. Ganin zata makara salla ta nufi hanyar bedroom. Tana bu?e ?ofar zata shiga aka bu?e ta falon. Kallon inda ?ofar take tayi, ganin shine ya sakata ?arasa shigewa batare data nuna alamar tasan da shigowar tasa ba. A fili ta furta, 'Ai nazata tuban mazuru kayi, bazaka taso kayi sallan ba'.
Oho, shidai baisan tanayi ba. Dan ?akinsa shima ya shige kai tsaye dan gabatar da sallar, tunda an ja masa makara bai tafi massallaci ba.

________¡ï¡ï¡ï¡ï________

"Wai nikam murmushin mi kike tayi hakane Jannat? Tun jiya ina lura dake Murmushin nan ya kasa barin ?ya?y?yawar fuskarnan taki".
Murmushin Umm ta sake yi tana kallon mijin nata da take ?unbin so da ?auna. Sai da ta mi?a masa kofin ruwan data zuba masa kafin tace, "Wlhy idan na tuno Nu'aymah tabar gidan nan sai naji wata irin nutsuwa da kwanciyar hankali. Duk da ina fargabar inda ta tsinci kanta kuma a yanzu. Sai dai inaji a raina bazata bari a cuta mataba acan tunda tasan su?in su wanene. Amma a gidan nan da bakasan wanene mai SARAN ?OYE ba tayaya zakai taka tsantsan da al'amarinsa. ALLAH ya ?arama Hajjo tsahon rai da nisan kwana. Dan nasan ita ?in babbar garkuwa ce a garemu a gidan nan. Kaga yanzu saimu gani, yarinyarmu ce ba'a bu?ata a gidan? Komu kanmu ne?".
"Gaskiyarki Jannat, koni inajin nutsuwa ta musamman a zuciyata tun bayan ?aura auren mamana. UBANGIJI shine masani akan wannan auren na Yahya da mamana ya ?umsa. Dan maybe da ?aya daga cikin su Abdallah ta aura salamar da muke mata fata bazata ta?a samunta ba. Sai ma wasu sabbin fitintunu ne zasu cigaba da bayyana ?ilama har sai mun rasata gaba ?aya. Amma kinga a yanzu aurenta da yaron nan zan jefa tsuntsu uku ne da dutse ?aya".
"Tsuntsu uku kuma Abban Nu'aymah?".
"?warai kuwa Jannat. Na farko zan ?ara ?arfafa gwiwar Yahya akan musulinci, zata taimakesa akan dukkanin ilimin da yake bu?ata na sanin musilinci. Na biyu Mamana zatayi ibadar aure, ta kuma samu lafiya da kulawa mai inganci akan lalurarta. Na uku zataimin wani aiki da zuciyata ta kasa daina min kokwanto a kansa. Maimakon inji na ajiye batun, kullum sai sake jin ?wa?ayin tabbatar da gaskiyarsa nakeyi".
"Ikon ALLAH, Abban Nu'aymah minene shi kuwa wannan al'amari?".
"Zan fa?a miki shi Jannat, ki bani lokaci na gama neman za?in UBANGIJINA akansa sannan".
"To UBANGIJI yayi jagora Abban Nu'aymah, ALLAH kuma ya tabbatar da alkairi a cikin al'amarin".
"Amin ya rabbi Umm-Muhammad. Yanzu yaya batun mai aikin da mamana ta bu?ata?".
"Karka damu za'a nema insha ALLAH, bandama rigima irin tata mizatayi da wata ?ar


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login