Showing 84001 words to 87000 words out of 325075 words

Chapter 29 - SARAN-BOYE COMPLETE

20 Jul 2024

29192

manya-manyan ajiyar zuciya yasan da walaki. Amma kowa bai tankamawa ba ya nufi ?aton ?ofar falon nasu na glass da yaja manya ku?a?e masu nauyi koda ba'a fa?aba.

Wani ihun farin ciki Miracle ta kurma dan itace ta fara ganinsa, kafin ta kwaso a guje tazo zata ?ane masa jiki. Sai dai yanda ya wani uban tsumewa ya sakata jan birki a gabansa ta kama hannunsa kawai ta ?an?ame a ?irjinta. A take sauran yaran gidan da ba?in ?ammata da samari yaran Uncles ?insa suma duk suka taso kansa. Basubi takan tsumewar tasaba sukam duk suka rungumesa.
Da ?yar madam Chioma ta samu suka sakesa, itama ta matsa ta rungume abinta tsam yanda takeso hawaye na gangaro mata akan fuska. Hannunsa yasa ya ?an buga bayanta ka?an tare da ?agota yana mamakin hawayen na miye? Batare da yace komaiba ya ciro handkherchief a aljihunsa ya share mata hawayen.
?arasowar su Papa da Uncles nashi uku yasa madam Chioma matsawa suma duk suka rungumesa, hakama matansu. Shikam dai kansa sake ?aurewa ya keyi, dan haka ya tambayesu wai ko lafiya?.
Basu bashi amsaba sai da Madam Chioma data kama hannunsa ta kaisa har saman kujera, Victoria ta kawo masa ruwa dan kowa yasan yafi ?aunarsa sama da kayan za?i. Bai musaba ya amsa yasha kusan fin rabi, sannan ya sake binsu da kallo da sake tambayar yaya akayi wai?.
Gebrail ne ya sanar masa da komai. Hakan ya saka Yoohan ?in dafe kansa dake sara masa ka?an-ka?an yana ?an lumshe idanu. Shi abin nasuma takaici ya bashi sosai. Amma sai baice komaiba. Sanin bazai ce?inba yasa babu wanda ya damu da jiran sai yace ?in. Saima ringu?a da sukai Dining domin yin breakfast ?in da suka kasa yi tun ?azun.
Shi dai Yoohan duk a takure yake matu?a, amma sanin ba?ar masifar Uncle Zamani yasa shi ha?ura ya zauna akai breakfast ?in da shi, wanda shi sam ma baici wani abin kirki ba. Bayan sun kammala sukai sama shida sa'anninsa su uku, sai Rich daya dawo daga nemansa. Amma duk masifar da yay masa akan ?aukar mota ya fita shi ka?ai a wannan halin da yake ciki sai bai kula Richard ?inba. Shima bayan gama masa masifar sai ya watsar dashi ya biyema su Osen kawai da suka baje a falon Yoohan ?in suna kwasar dariya da hirarsu ta sha?iyanci akan ?ammata.
A haka Solomon ya shigo da kwalaben barasar da sukai Order, sai kofuna da ?an?ara. bayansa cikin ma'aikatan gidanne ?auke da tray da aka shiryo gasashen naman kaji a cikinsa wanda zasuyi amfani dashi wajan shan barasan.
Sai da suka jera musu komai yanda ya dace kafin su fice su barsu. Mi?ewa Yoohan yay zai shige bedroom dan ya rage kayansa. Da sauri Godwin yace, "Mr-x ina zuwa?". (Dan haka duk abokansa ke kiransa da shi, Rich kawai yafi kiransa da Doctor) Yamutsa fuska Yoohan yay yana hararsa, dan dama abokin bugawarsa ne, kawai dai dan yau baya cikin good mood ne. "Ina zuwa" ya bashi amsa a ta?aice yana shigewa.
"Wai mike damun Boss ?inka ne?". Joseph ya fa?a yana kallon Richard. Cikin damuwa Rich yace, "Matsalarsa ce dai ta rashin barci ta motsa, nayi-nayi yasha barasa ko nai masa allura ya?i".
Godwin ne yace, "Shegen taurin kan Mr-X ai ba ?arewa yakeba, ni wlhy sonake wataran na samu wata na biyata tai disvirgin ?in gayen nan kozai ware yaji da?in rayuwarsa. Duniya ai sai da jin da?i, amma shi yabi ya wani ?an?ame kansa kamar wanda bai wayeba ko ba'a turai yay rayuwa ba. Minene a giya? Dama da shanta kawai nisha?ine, kuma tunda munada aikin yinmu sai fa lokaci- lokaci muke shanta, ba kuma mai cutarwa ba......."
Katsesa Joseph yayi da fa?in, "Kaga G. Ka barsa, Mr-x tsarinsa kenan shi da ra'ayinsa, koka manta tun muna secondary shi dama komai nasa da ?a'ida ya keyi. so ni banga abin damuwa da har zaku shiga masa rayuwa da yawaba, kubarsa ya tsara ma kansa yanda yake bu?atar ya rayu Ok?".
Richard yace, "Hakane Joseph, amma idan ka lura shima fa bawai jin da?inne baya bu?ata ba, kawai shi dai ya ?auki burin duniyane ya ?aura akan aikin nan namu, a tunaninsa duk abinda zai sha zai iya shagaltar da shi akan aikinsa, sannan mata ma zasu iya takura masa su hanashi yin rayuwarsa da ?yau, kunsan mutum namu ?an hutune, ko mace bata fa?a masa son jiki ba".
Dariya suka kwashe dashi gaba ?aya suna mai ha?a kofunan da suka zubama barasa a ciki alamar chssss.
Hakan yayi dai-dai da fitowar Yoohan daga ?aki, ya canja kayansa zuwa wando da riga duk blue na kamfanin adidas. Duk da hayaniyar tasu bai sonta haka ya zauna a cikinsu dan gaba ?ayansu childhood Friends ?insa ne, kuma ?an uwansa na jini dan duk ?a?an ?annen papa ne, sai Osen ne kawai ?an aboki shima kuma iyayen nasu sun zama kamar ?an uwa, sai kuma Richard shi kuma abokinsa. Amma tare sukai secondary school dukansu, hasalima duk ajinsu guda.
Osen ne ya mi?a masa cup duk da yasan ba sha zaiba. Aiko Yoohan ?in ya yamutse fuska da girgiza masa kai tamkar mai ?yan?yamin giyar ma. Dariya suka sanya masa suna zuba masa sha?iyancin da suka saba, tare da labarin da?in da ?ammatansu ke jiyar dasu harma da karuwai dan dukansu ji suke da ?an ku?a?e a aljihu. iyayensu kuma sun tara, sanna suma ?in gwasaken kansune sosai. Shiyyasa suke zuba tsiyarsu a garin Abuja da Lagos kamar babu gobe.
Duk abinda sukeyi saboda Yoohan yaji haushine yay budurwa, dan har maganar ?ammatansa dake bala'in sonsa suke kawowa harda Miracle, tare da ko?a ?yawunta dama na sauran ?ammatan da Yoohan ?in shi yake nuna kullum basa gabansa.
Joseph yace, "Mr-x daga yau ka fara taka tsantsan da G-boy, dan ya shirya yanda za'a maka fya?e, kaga sai kasan zaman da zakai da shi".
Mangare ?eyar Joseph Godwin yayi yana fa?in, "Munafiki, halan giyan ya fara kai maka karo zaka ha?ani da shi". Dariya suka kece da ita duka. Yoohan dake harar Godwin ?in yace, "Barma wani kare kanka naji sanda kake fa?a ai, an fa?a maka ni irinka ne da baida damuwa saita kwana da mata. Please, try and change your habit kaima".
Nanma dariya suka sanya, dan sunsan kam G-boy shege ne akan mata, duk yanda zai yaudareki ya biya bu?atarsa ya sani. Rich yace, "Calm dawn my Doctor, duk randa ya aikata maka haka zuwa zakai kawai ka tona masa asiri wajen babien sa, dama gata da shegen kishi kamar taci wuta a cikinta......."
Osen dake ?o?arin yagar nama yace, "Ashe ka ganota, nifa haushi take bala'in bani, amma G-Boy sam baya ganin laifin hakan da take masa, da kayi magana saiya nuna cewar son da take masa ne".
Ajiyar zuciya Yoohan da warin giyar ya fara hawar masa kai ya saki, ya mi?e a hankali ya ?auki basket ?in da aka zubo musu kwalaban giyan ya nufi hanyar fita. Da sauri suka shiga kwala masa kira akan ya kawo musu abinsu, amma baiko juyoba ya fice yama kullesu ta baya ya sauka ?asa. Canma iske su Papa yay suna ?ora tasu suna hira da dariya harda su Momy suma sha suke. Sosai ransa ya sake sosuwa, sai kace ba yanzu papan ya gama wa'azi a church ba. Tsaki yay ciki-ciki ya wucesu batare da ya tanka musu ba yana ?walama Solomon kira.
Da gudu ya shigo kuwa, ya mi?ama masa basket ?in kawai babu bayanin komai ya fice a falon. Garden ya nufa. Sai dai kuma yana shiga ya hango su Miracle a cikin swimming pool suna wanka. Cike da farin ciki duk suka zuba masa idanu, kowacce kwa?ayinta a kansa na fitowa fili saman fuskarta. sai dai kuma tuni ya juya yana jan wani tsakin takaici. Wannan taron yasa sam bayason zama gidan ranar lahadi, yanzu haka zuwa anjima gidan sake cika zaiyi da wasu ba?in kuma. Solomon ya bama key ?in ?ofar sashensa daya kulle su Rich, yace yaje ya bu?esu, shi kuma ya fice gidan a ?afa duk da kuwa rana ta fara ?agawa kuma akwai ?an zafi............?

Amin afuwa jiya ciwon kai ya hanani sukuni na kasa typing ?in????.

_____________________________
ZAFAFA BIYAR 2021
_______________________


Hafsat miss xoxo??
KIBIYAR AJALI......!
(Sulke baya tareta saita gitta).????

Mamu gee??
MIN ?ALB!!????

Hafsat rano??
ABINDA KE CIKIN ZUCIYA...!!????

Safiyya huguma?? SIRA?IN RAYUWA????

Bilyn Abdull??
SARAN ?OYE????

Duka akan farashi mai rahusar gaske.

Kamar haka????????

?aya___300
Biyu____400
Uku_____450
Hu?u____500
Biyar_____700

Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki????

ACCOUNT NO 0812652655
ACCOUNT NAME- HAFSAT LAWAN GAMBO
BANK NAME: ACCESS BANK.

saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)????

0903 234 5899

IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU????

09033181070

????????????????????
TEAM----ZAFAFA BIYAR????????

ALLAH ka gafartama iyayenmu??????.
[4/6, 6:47 PM] +234 901 860 0202: No. 23

................Tun sakkowar Yoohan daga sashensa Momy tai saurin ajiye kofinta na barasa, dan Yoohan ya da?e da hanata shan giya, kuma ta masa al?awarin dainawa. Sai dai wani lokacin damuwar da take ciki kansa tasha abinta musamman da daddare idan zata kwanta barci. duk da dama wani mai yawa take sha ba. Binsa tai da wani shegen kallo tamkar idanunta zasu fa?i ?asa, yayinda fuskarta ma ta nuna shau?i sosai fiye da yanda suke zaune. Yun?urawa tai zata tashi amiyarta madam Monecca tai saurin ri?e mata hannu tana girgiza mata kai cikin hikima. Duk da bataso hakanba saita koma ta zauna tana sauke wasu tagwayen ajiyar zuciyar da harsu Papa da fira ya ?aukema hankali basusan da wucewar Yoohan ?inba suka juyi suna kallonta.
"Lafiya Darling?" papa ya fa?a cike da kulawa a gareta. Murmushi ya?e ta masa da cewar "Babu komai, bara na?an rage kayana dai sun fara min nauyi". Murmushi yay mata da aika mata kiss daga inda yake. Ta mi?e tana fadin, "Thanks Honey".
Rakata da idanu yay cike da so da ?auna harta haye sama sashen bedrooms ?insu. Sai da ta wuce da kusan mintina goma kafin Madam Monecca ta mi?e itama tana neman excuse ?in zuwa toilet. Duk da kowa yasan dama amintarsu tafi zuwa ?aya da madam Chioma babu wanda yay zargin komai a sauran matan. Sai ma maida hankalinsu ga hirar mazajen su da sukayi kawai.

A bakin gado Madam Monecca ta iske Momy zaune ta dafe kanta. Ta ?arasa kusa da ita ta zauna, cikin harshen nasara take tambayarta damuwarta?.
?agowa Madam Chioma tai idanunta cike da hawaye tana kallon ?awarta, tace, "Monecca! Ina cikin damuwa sosai akan Yoohan, gaba ?aya ya sake canjamin, ?an kusancin da nake murnar ya ?ara shiga tsakaninmu a yanzu neman hanyar kakkka?ar da shima ya keyi. Rungumarsa ma yanzu bayason yaga nayi, sai kiga ya kama ?acin rai. Nifa na gaji da ?oye-?oyen nan, dan gashi Honey harya fara tunanin wai yay masa maganar aure......"
"Aure!?" Monecca ta fa?a cikin tashin hankali.
"Ki bari kawai, jiya da yay maganar naji kamar na bindige shegen nan nama huta da wahalansa, Monecca zan fitoma Yoohan a mutum kawai da bu?atata, duk da kuwa nasan shegen taurin kansa".
Cikin sauri Madam Monecca tace, "Karkiyi haka, dan zaki samu babbar matsala. kidai bari muyi tunani akai. Wai ita Mira bazata koma gidansu ba ne. sai naga kamar itace ke ?auke masa hankali?".
Cikin dariyar da Madam Chioma batai niyyar yiba tace, "Miracle fa? An gaya miki kalloma ta ishesa ne a gidan nan. Dama fa Zamani ne keta son ganin Yoohan ?in ya aureta. kuma ni na gama fahimtar shima akwai tasa manufar akan hakan, shi kuma Yoohan ?in duk da ?yan Miracle ?in bata gabansa shiyyasa nima zamanta a gidan bai ta?a damunaba".
?an ta?e baki Monecca tayi tana hararar Madam Chioma a kaikaice. a ranta kuwa rayawa take duk rintsi saita bi hanyar mallakar Yoohan ?in, dan itama wani Masifaffen sonsa take, tana dannewa ne a gaban ?awar tata kawai. Sun tattauna sosai ta yanda suke ganin ya dace a samu Yoohan ?in a hannu. Kafin su fito wajen sauran ?an uwansu a cigaba da hira.

Haka gidan ya cigaba da kar?ar ba?i har dare, dan yau ranace ta ziyara a garesu, musamman ma gidan papa daya kasance babban mutum a wajensu.
Yoohan bai dawo gidanba sai yamma lis, ya samu giyar dasu Osen suka sha ta ?an sakesu, harma sun fito daga sashensa Solomon ya shiga ya gyara. Duk suna harabar gidan zaune dan wasu abokan nasu sun ?aru saboda jin Yoohan ?in na gari, shima sai kawai ya zauna a wajensu duk da ba firar yakeba sosai.

______________________________
*_SAUDIA_*

Duk da Adawiya na ?o?arin ?oye halayenta hakan bai hanata sakin layi a wasunl lokutan, dan babu abinda ke sakata takaici da ?unar zuciya kamar yanda Nu'aymah ta?i nuna damuwarta akan duk abinda take mata. Gaba ?aya Nu'aymahr ma ta maida hankalinta ga ibada ne kamar yanda ta ?auro niyya tun daga gida.
Tayi mugun yin watsi da shirmen Adawiyar dan ta gama karantarta tsaf akan lamarin nata, to dama tasan tun suna secondary ma Adawiya tasha ha?ata fa?a da ?awayensu, ta kuma koma ta no?e ta nuna ba ita tayiba. Amma sai bata ta?a nuna mata ta gane komaiba akan hakan, dan duk sanda taje ta sanarma Umm Adawiya ta mata kaza sai Umm ta lallasheta da nasiha da nuna mata muhimmancin ha?uri da ?an uwa. Hakanne ke da?ile Nu'aymah daga ramuwa ga Adawiyar gashi har hakan ya zame mata jiki.
A wannan tsukun kuma data fahimci Adawiya ta canja sabon salon halaye sai itama ta canja takunta a kanta tana binta da gashi cikin ruwan sanyi, a ranta tana zargin kenan dama Adawiya na son Yah Ab komi?. A duk sanda tai wannan tunanin takanyi ?o?arin ganin ta ?aryata zuciyarta, dan bata ta?a ganin alamar hakan ba ga Adawiya a dacan baya. A ganinta yanzu dai da?in aurene yasa take ganin tafita kusanci da Abdallahn shiyyasa take shirya ya?arta a kansa.

Yau ma kamar kullum Nu'aymah na ?an yin barcin rana a falo, dan da daddare tafi maida hankalinta ga ibada ne, Abdallah ya shigo gidan. Adawiya ta wuce makaranta. daga hajjo sai Nu'aymah. Da tare suke da Hajjon a falo zaune suna ?an hira sai barci ya kwasheta, itama hajjon saita nufi ?aki ta kwanta danta huta.
Kafe Nu'aymah da idanu Abdallah yayi ko ?yaftawa ba yayi, ya ?araso inda take yay tsaye kanta yana cigaba da kallonta tamkar mai nazarin wani abu. Cikin barci Nu'aymah taji alamar tsayuwar mutum a kanta. A ?an firgice ta bu?e idanu saboda barcin nata baiyi nisaba sosai. Ganin Yah Ab tsaye a kanta ya sakata sake zabura tana binsa da kallon tuhuma itama. Sai kuma ta kumbura baki tana ?auke kanta cike da takaicinsa.
Fuskarsa a ha?e ya zauna a kujerar da take kwance, hakan ya saka Nu'aymah saurin mi?ewa sosai tana fa?in, "Yah Ab minene haka wai?".
"K kika cancanci wannan tambayar ai?". Ya fa?a shima yana mi?ewa yasha gabanta fuskarsa a ha?e, ya cigaba da fa?in, "K harkin isa ki dinga wula?antani akan wani banza can Nu'aymah? Kinzo inda nake amma sai wani basar dani kikeyi".
Cikin rashin fahimta take kallonsa, kamar zatayi magana sai kuma ta fasa ta ra?ashi zata wuce. Sake shan gabanta yayi yana mazurai, "Nabaki izinin tafiya ne?".
Idanunta cike da ?walla tace, "To idan na zauna mizan maka? Kodan kaga nazo na zauna a gidanka kakeson ?untata rayuwata?". Hannu ya ?aga tamkar zai ?wa?a mata mari sai kuma ya fasa ya dun?ulesa yana taune lip ?insa jikinsa na tsuma. Yace, "Uban wanene Ameer?".
Cike da takaici Nu'aymah ta kallesa ta watsar, kamar karta bashi amsa sai kuma mamakin abin nasa yasa ta kallesa da ?yau. "Ban gane mikake fa?a ba Yah Ab?". A hasale yace tayaya zaki gane mara mutunci. Nu'aymah wai harni zaki iya gudammawa a daren aurenmu saboda wani jaki? Kinsan ba?ya sona miyyasa kika yarda aka saka mana ranar aure?".
Sallamar Adawiya da batai zato ko tsammanin Abdallah zai dawo gidan a wannan lokacinba ya hana Nu'aymah da mamaki ya kume bashi amsa. Turus Adawiyan tayi tana kallonsu, dan wanda bai saniba zai ?auka ne wata maganar arzi?i sukeyi da juna.
Binsu take


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login