Showing 231001 words to 234000 words out of 325075 words
sai nayi fa tunda kin sakani na fitar da......"
Wani irin wuntsilowa Aymah tayi ta dafe masa baki tana fa?in, "Na shiga uku ni Zainab, ni dai wlhy babu ruwana". Ta fashe masa da kukan ta?ara.
Wani mugun dariya ne yaji yana taso masa. Amma sai ya danne da ?yar dan karya ?ara tunzurata a samu matsala. Hannu yasa ya janye nata dake akan bakinsa. Fuskarta kuma har yanzu tana a ?oye. "Okay yi ha?uri bake bace nine. Yanzu dai kisan yanda zakiyi dani lokacin salla yayi".
"To ni ya kakeso in maka?".
"Ki koyamin".
Tamkar zata fasa masa sabon kuka tace, "ALLAH ya sani nama fasa zaman hutawar ka maidani Nigeria kawai tunda na warke".
Shi dai dauriya yaketa yi dan kar yay dariya matsalar tafi haka. yace, "To naji, yanzu dai tashi muje ki koyamin yanda zanyi wankan".
"Ni dai babu inda zanje, idan kanaso na koya maka a haka kaje kayi abunka".
"A'a gaskiya, sai dai fa kiyimin practical zanfi fahimtarki. Haka ake malami yayta ragema ?alibi mudun koyarwa".
Shiru tayi ta?i motsawa, taki kuma tanka masa. ya tashi zaune yana fa?in, "Okay shikenan, bara kawai na kira Uncle saina sanar masa abinda ya faru daga nan ya koyamin yanda zanyi wank.......". Zaune ta tashi dingangan ta ?are masa jiki da danne bakinsa da hannunta tana waro idanun dake cike da ?walla.
"Yanzu dan baka da kunya sai ka kira Abbana ka sanar masa wannan abun?". Hannunta ya ture yana marairaice fuska shima. "To yaya kikeso nayi ne Sweet girl? Kinga dai babu damar nayi salla babu wankan nan? Kema kanki nasan fa sai kinyi". Ya kai ?arshen zancensa da kashe mata ido ?aya. Filo ta jawo ta maka masa a hannu sannan ta sauka masa a jiki tana ?un?uni. Duk yanda yaso danne dariyarsa ta gagara sai da yayi abinsa.
Itako data sauka a gadon sai masifa takeyi a ranta tana sharar ?wallan da babu tantama najin kunya ne. Shi dai Yoohan ganin ya samu yanda ya keso tasowa yayi ya biyota inda ta koma ta zauna akan sofa tana sharar ?walla. ?aukarta yay cak zuwa bayin tanata wantsala ?afafu da fa?in ita ya sauketa. Tama fasa koyawar yaje yay Searching a Google ai zai gani. Ko jintama shi bayayi sai da ya direta cikin wajen wankan, zata gudu yay saurin kunna shower ?in. A take tai musu jalab da ruwan data she?o. Ya jawo hannunta ta dawo saman jikinsa. Jin santsin ruwa zai jata ta fa?i dole ta rirri?esa ruwan na sauka musu a jiki. Da wannan damar Yoohan ya kafe gaban rigarta daya ji?e da ruwa komai ya fito yanda ya kamata da kallo. Bata fargaba sai da taji hannunsa a wajen. ?asa tai da sauri tana ture masa hannu. A ranta kuwa al'amarin sake firgitata yakeyi. ?ara ?arfin shower ?in yayi, hakan yasata tilas ta sake mi?ewa tana sharce ruwar dake sakko mata a fuska ko gani da ?yau yana neman hanata. Numfashi ma takai da baki take firzarwa. Shi kansa ruwan ya masa yawa. Amma saboda karta gudu yay ha?uri yana saka hannu yana sharcewa kamar yanda takeyi itama. Sai da ya tabbatar sunyi jagab sannan ya kashe shower ?in. Ya koma hanyar ?ofar wajen wankan ya tsaya. A mamakinta sai gani tai ya fara cire rigarsa. ?asa tai da kanta gabanta na fa?uwa. Ganin wandonsa ya sa?ulo ?asa ta ?ara ki?imewa. Da sauri ta juya bayanta. Hakan ya bashi damar matsawa ya manna bayanta da ?irjinsa.
"Karki zama malama mai yima ?alibanta rowar ilimi fa". Yanda yake maganar yana yawo da hannunsa akan cikinta sai ya nema sake susutata. Tama rasa tunanin da zatayi akan wannan al'amarin nasa mai wahalar fashin ba?i. Tanaji tana gani yay amfani da ?arfinsa wajen zame mata riga da wandon jikinta. Sai dai fa duk yanda yaso cire harna cikin ta?i yarda sam. daga ?arshe ma sai ta saka masa kuka. ?yaleta yayi ganin dai ankai inda ma baiyi zatoba. A haka ta fara ?o?arin koya masa wankan duk dan ta samu ta ku?uta daga wannan dabaibayin da yayma rayuwarta baki ?aya.
Sai da tai nisa a koyawarne ta fahimci ya iya, dama ashe kawai danya bata wahala da kallar mata jikine ya sashi cewa ta koya masan. Wannan haushin ya sakata harya ?arasa wankan ya fita ya barta dan taki yarda tayi ita tana antaya masa harara. Duk da ?aryar datai masa na cewar babu wani wanka daya hau kanta yana fita kuwa sai da tayisa. Dan duk wautarta tasan abinda takeyi tunda tanada ilimin addini. Aiko dai ansha ?un?uni. Tana cika baki da iska ta miko hannu akan ya bata Bathrobe da towel, dan yana a bayin bai fitaba.
Hand dryer ?in hannunsa ya ajiye. Ya ?auki rigar wankan ya kai mata sai dai babu towel. Hannun nasa ma sai da ya sha harara sannan ta amsa. Ganin babu towel ?in kuma taita ?un?uni. Koda ta fito kallo ?aya tai masa ta ?auke kanta ganin daga shi sai towel iya ?ugu zuwa gwiwa. Shiko gashinta dake ?igar ruwa yabi da kallo. A cikin ransa dariya ya sanya mata yana fa?in, 'Yarinya ashe kinada lafiya tunda sa?ona ya isa inda na aikashi?'. A fili kuwa sai ya fuske abinsa. Tai saurin ?aukar towel ta na?e kanta wai dan karya gani.
?arasa hidimarsa yayi ya fito ya barta. Koda ya fito mai ya shafa yay shiri cikin ?ananun kaya. Ba?in wando da pitch color ?in shirt mai dogon hannu. Yana fesa turare ta fito.
"Kiyi shirin fita". Ya fa?a yana ajiye turaren.
Bata tanka masaba. Tai tsaye har sai da ya matsa a wajen sannan ta bu?e akwatin nasu ta ?auki jallabiya ?aya. Bayi ta koma ta sanyo sannan tazo ya jasu salla. Suna idarwa yace ta ?arasa shirin yana zuwa.
Fita yay, ita kuma ta mi?e ta shafa mai, da ?arasa kimtsawa. Tana gamawa kuwa yana dawowa. Zata fara feshi da turarensa ya amshe yana fa?in, "Silly girl ya isa haka dan ba tallanki nazo yima Austrian ba".
Ita dai bata tanka ba. Bakuma ta yarda sun kalli juna ba dan wannan fushin da takeyi tsabar jin kunyarsace kawai ke ?awainiya da ita.
Tsaf suka fito abinsu gwanin sha'awa. Tamkar ka sacesu ka gudu. idan ka gansu sai ka ?auka ?aramar ?ansawarsa ce ma. Yau dinma bata cuci kantaba sai da taita kalle-kalle har suka fito ?aton reception ?in hotel ?in. Zuwa yay yayi signing kamar yanda dokarsu take. Daga haka yaja hannunta suka fito............?
ZAFAFA BIYAR 2021
Hafsat miss xoxo??
KIBIYAR AJALI......!
(Sulke baya tareta saita gitta).????
Mamu gee??
MIN ?ALB!!????
Hafsat rano??
ABINDA KE CIKIN ZUCIYA...!!????
Safiyya huguma?? SIRA?IN RAYUWA????
Bilyn Abdull??
SARAN ?OYE????
Duka akan farashi mai rahusar gaske.
Kamar haka????????
?aya___300
Biyu____400
Uku_____450
Hu?u____500
Biyar_____700
Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki????
ACCOUNT NO 0812652655
ACCOUNT NAME- HAFSAT LAWAN GAMBO
BANK NAME: ACCESS BANK.
saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)????
0903 234 5899
IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU????
09033181070
????????????????????
TEAM----ZAFAFA BIYAR????????
ALLAH ka gafartama iyayenmu??????.[6/24, 12:35 PM] +234 901 860 0202: *_LITTAFIN nan na ku?i ne. Dan girman ALLAH ki daure ki biya kafin ki karanta, idan kuma bazaki iya biya ba ki ha?ura domin ALLAH karki karanta. Idan kuma kin saya dan girman ALLAH karki ya?a mana????_*.
No. 61
...........Da Solomon sukaci karo a jikin wata dalleliyar mota tsaye. sai baturen dake cikin Uniform ?in hotel ?in. Da girmamawa Solo yake gaisheta da sake tambayarta ?arfin jiki. Cike da takaicin zamantowarsa tamkar jelar Yoohan ?in ya sakata amsawa a ta?aice. Yoohan ya bu?e mata da kansa ya taimaka mata ta shiga. rufewa yay, ya zagaya inda baturen ya bu?e masa shi kuma ya shiga. Baturen ne ya shiga a matsayin driver, Solomon kuwa gefensa. wannan abu ya zafi Nu'aymah a rai. Kenan duk inda mijin nata yake dole wannan basamuden sai ya kasance da shi?. Dolene tasan matsayin wannan bibbinin kuwa. Galla masa harara tayi lokacin da drivern ke harba motar a titi suka fice daga harabar hotel ?in.
Idanu Yoohan ya lumshe da jingina kansa da kujera. Ya saki ajiyar zuciya, a ransa yana ayyana 'hakan shine kawai mafita a gareni. idan ba ?an fitar mukaiba bazan iya barin yarinyar nan ba. komai zan iya aikatawa kamar yanda zuciyarsa ke bani ?warin gwiwar game da ita'.
Nu'aymah dai ta fahimci motar hotel ?ince ya ara. Sai dai batasan ina suka nufaba. Dan haka ta ware idanu da ?yau tana sake kallon tsarin garin na Vienna da ya gama ha?uwa da ababen more rayuwa kala-kala. Duk da ranta cike yake da taikaicin tafiya tare da Solomon, kai harshi kansa Yoohan ?in haushinsa takeji akan Solo.
Sun fara zuwa wani ha?a??en wajen Saloon, bata fahemci hakanba kuwa sai da suka shiga ciki. Ta kallesa tana yamutse fuska, "Mi zamuyi anan?". Kallonta kawai yake shidai fuska a tsuke shima. Dan shi ka?ai yasan a halin da yake ciki. Sai dai yana mamakin miya ?ata mata rai haka? Ya fahimci tun fitowarsu cikin hotel ?in wajensu Solo ta ciskule fuska, sa?anin farko da kunyarsace kawai tattare da ita.
Bai bata amsaba, sai ma ma'aikatan wajen da sukazo musu tarba ta mutuntawa. Da Garman language yay musu bayanin abinda suke bu?ata. Hakan yasa Aymah bataji komaiba. Saima mamakin dama yanajin yaren data fahimci mafi yawan ?an garin sunfiyi kenan?. Bata da mai bata amsa, sai jan hannunta da ma'aikaciyar tayi zuwa sashen mata. Binsu yay har ciki, shine ya za?a duk abinda za'ai mata. Nu'aymah dai ta zubama sarautar ALLAH ido tana kallonsu. Shiko ya?i yarda su ha?a idon. Yana gama za?a ya biyasu ku?insu. Sai shi kuma ya nufi na maza dan yana bu?atar gyaran fuska da yankan farce.
Haushi ya hana Aymah yin magana har aka fara wanke mata kanta. Ganin babu kitso dai yasa bata damuba. An mata wankin ?afa da gyaran farce, sannan aka kaita wani ?aki wai na gyaran jiki ne. Nu'aymah dai taga abinda ya girmeta, har tsoron shiga wa?an nan injina ta ringayi, a ganinta idan aka ?auke wuta mutum na ciki kuma ai shikenan labarinsa ya ?are. 'Kai wannan mutumin ba kawoni yay kuwa a marka?eniba ma?' ta aiyana a ranta tana ?un?uni da hausa. Su dai ma'aikatan ba jinta sukeba. Hakan yasa suketa aikinsu kawai. Anyi mata gyaran jiki na musamman da ita kanta tasan eh ta gyaru ?warai da gaske. Aka kuma kaita wani waje wai tausa nankuma za'ai mata. 'Babbar bala'i' ta fa?a a fili cikin su?utar baki. 'Amma wannan mai jajayen kunnen ya gama sakamin rayuwa a gaba. Yoni nace masa ina bu?atar duk wannan ne ko mi?'. Haka taita zuba mita ana mata tausa. gashi kuma sai faman lumtse idanu takeyi alamar tanajin da?in jikinta. Bayan kammala tausan an maidata wajen gyaran jiki, daga haka aka ?arasa gyara mata kanta. Ha?a??un wando da riga aka kawo mata ta saka ?yautar da shagon ke badawa kenan idan suka maka aiki mai tsada irin haka. Badan taso ba ta amsa ta saka. Ta yana gyalen jallabiyar ta akai suka fito inda Yoohan ke zaune yana jiransu. Dan shi tuni an kammala masa.
A tare suka zubama juna ido. Kowanne yana zancen ?yawun da ?an uwansa yay masa a zuciya. Sake tashi hankalin Yoohan yayi matu?a, wata sabuwar bu?ata da tafi ta farko sai ?ara bijiro masa takeyi. Nannauyan numfashi ya furzar da yin luuu da idanunsa da launinsu na fari ya sirka zuwa ja. Sai da ya lumshesu sannan ya sake bu?ewa akanta. Da ?yar ya iya mi?ewa tsaye zuwa gareta. Ita dai kanta a ?asa tun kallon datai masa na farko da yaba ?yawun da gyaran fuskar da yay yayi masa, dan an canja masa style ?in sajensa. bata ?ara yarda ta dubesaba saboda kallon ?urullar data ga shima yana mata. Hannu yasa a hankali ya zame gyalen daga bisa kanta yana kallon gyaran gashin nata. Ya kama jelar gashin dake ?aure a tsakkiya ya murza cikin hannunsa tare da sha?ar ?amshin da gashin keyi. Duk yanda yaso furta wani abu a harshensa ya kasa hakan....
Maganar ma'aikaciyar wajen ce ta katsesa daga ?o?arin kamo fuskar Aymah da yayi niyyar yi. Ya juyo yana kallonta. Bag ?in hannunta mai tambarin wajen nasu ta mi?ama Nu'aymah fuskarta da murmushi tai musu godiya na zuwa masana'antarsu. Guntun murmushi Aymah tayi mata kawai ta amsa. Kallon jikkar yayi ya maida dubansa ga matashiyar matar. Yay mata tambayar da Aymah batasan ta minene ba, kai kawai ya gya?a mata da kama hannun Nu'aymah suka fito Reception, wata hanya sukabi bayan taga ya karanta rubutun wajen da ita dai ba ganewa takeba tunda ba turanci baneba. A shagon kaya ta gansu, yanda baiyi maganaba itama batayiba. Sai hannunta daya ri?e yanabin kayan da kallo. Yayinda ma'aikatan wajen ke musu barka da zuwa.
Kujera aka bata ta zauna shi kuma yana duba abinda yazo nema. Kallon shagon ya ?aule mata hankali har batasan dami-dami ya ?aukaba. Sai da yazo gabanta da riga a hannu ne ta kallesa. ya kamota ya mi?ar tsaye yana magana a hankali. "A ?asar mutane ma sai kin nuna ke bakanuwa ce?"..
Harararsa tayi dai-dai yana kamo hannunta ya zura mata hannun rigar coat ?in ta mata data gama ha?uwa sai wani irin shegen ?amshi takeyi. Bakinsa ya ta?e ya kamo ?ayan ma ya zura mata ya gyara mata rigar da ?yau. Takai mata har gwiwa kuwa, hakan yasa ta rufe mata jikin yanda yafi bu?ata, dan yaji a ransa bazai iya barinta yawo da kayan da wajen saloon ?in suka bata ba.
Ta ?ara ?yau kuwa sosai masha ALLAH, shi kansa ya kasa ?auke ido a kanta. Ku?in abinda ya ?auka ya biya suka fito a wajen. Inda suka bar su Solomon zaune a harabar wajen nan suka iskesu suna shan coffee. Solomon dake satar kallonsu ta gefen idi yace, 'Yarinya sai shege ?yau kamar aljana. Shiyyasa gaba ?aya oga ya susuce a kanta'.
Oho Aymah batasan yanayiba. Dan tuni ma ta bu?e mota ta shige ko jiran Yoohan ?in ya bu?e mata yayi batai ba. Da kallo shima ya bita dan ya fara fahimtar kamar haushin Solomon takeji. Bai dai tabbatar ba, dan haka shima ya shiga motar. Su Solo ma duk shiga sukai suka bar wajen.
A yanzunma da suka tafi kanta ta juyar tana kallon garin. Shi dai Yoohan nata kallonta ta ?asan ido da nazarinta har suka ?arasa wani garden ?in hutawa. Wajene da masoya kawai ke kai kawo abin za??yau da burgewa. Sun bar su Solomon acan wajene, shi da ita kawai suka shiga ciki. Inda ya zazzagaya da ita wajejen abubuwan tarihi, sukai hotuna ta sha kallo kuma. Yoohan bai da kuzari gaba ?aya. Yanata dauriyane kawai, dan a rayuwarsa bai ta?a jin matsananciyar sha'awa irin ta yau ba. Ji yake kamar idan bai akasance da mace ba zai rasa ransa. Itako Aymah gani take shegen miskilancinsa ne ya motsa kawai. Shiyyasa ta tattarasa ta watsar gefe. Ko abu ya faru sai dai taita ?un?uni a ranta da gulmarsa a zuciya. A waje sukai sallar la'asar, magriba da isha'i. Sun ?anyi ciye-ciyensu da Aymah ke ganin wasu ?azanta. Duk dan lokaci ya?an ?ara ja sai da Yoohan ya bari tara na agogon ?asar yayi sannan suka dawo hotel ?in su.
Masifaffen ciwon cikin daya taso masane ya sakashi cemata taje ciki yana zuwa zaije asibiti duba wani maralafiya. Bata damuba. Ta kwashi kayan da suka sayo tai ciki. Can ya samu ?asan wani rumfar ya zauna dan dama babu asibitin da zaije. So yake ta?anyi nesa da shi ko zaiji sassaucin abinda ya keji game da ita. Sai dai kuma ina, rikicewa ma al'amarin ya sake neman yimasa saboda kaiwa da kawowa da matan turawan keyi ta wajen tamkar tsirara. Bai rufa mintuna ashirinba dole ya tashi a wajen ya nufi cikin ?akin jikinsa na rawa.
Shigowarsa dai-dai da fitowar Nu'aymah da sanin bayama hotel ?in gaba ?aya ya sakata fitowa daga ita sai guntun towel iyaka cinya. Daga ita har shi turus sukayi. Aymah dai ru?anin ganinsa babu zatone ya sakata ?amewa waje guda ta kasa ko motsi. Shiko tashin hankalin halin da yake a cikine ya sakashi tsura mata idanu jikinsa na wani irin tsuma. Ya rasa wane kalar tashin hankaline yake ciki a yau shi kuwa?.
Sum-sum ta wuce gaban Wadrobe batare data ?ara yarda ta dubesa ba. Shima sai ya ?arasa shigowa ya nufi bayin dan watsa ruwa ko zaiji sanyi a ransa da gangar jikinsa.
Da sauri-sauri tai shirin barci. Sai dai doguwar riga ta saka ta tada salla dan basuyi shafa'i da wutiri ba. Tana yin sallamar shafa'i ya fito. Bata kallesaba ta mi?e zatai