Showing 150001 words to 153000 words out of 325075 words

Chapter 51 - SARAN-BOYE COMPLETE

20 Jul 2024

29131

sakaka zubar da mutuncinka gaskiya".
"Karka damu zan kiyaye my son".
Daga haka sukai sallama.

Yoohan da zuciyarsa ke masa zafi da ?una ko sauraren Richard dake jera masa tambayoyi baiyi ba ya tattara kayansa yace masa zai je gida nanda awa biyu zai dawo ya cigaba da duba marasa lafiyan....


*_KANO_*

Alhmdllhi, kamar yanda sukai fata an dace. Dan kuwa Nu'aymah ta farfa?o cikin hankalinta, sai dai ramar da tayi dolene ta baka tausayi, hancin nan ya sake tsaho. Haka ma ta ?ara haske idanun sun fita da ?yau masha ALLAH. Ramarma sai ta sake fiddo mata da ?yawun nata.
Ba ?aramin farin ciki ahalinta suka tsinci kansu ba. Dan tunda farar safiya aka fara tururuwar zuwa ganinta. Ga ?an biki dama sun fara cika gidan musamman dangi na nesa. Ganin za'ayi yawa a asibitin Baba malam ya dakatar da zuwan. Ya sanar musu likitocin sun sanar masa a yau ma zasu sallameta insha ALLAH. Da?ine ya ?ara lullu?e kowa, musamman ma Abdallah da Naser da farfa?owan Nu'aymah ta sakasu komawa kamar an musu albishir da gidan aljanna.

Duk a yanayin da Nu'aymah ke a ciki su Dr Aysha na sanarma Yoohan. Shi da kansa ma ya basu umarnin sallamar Nu'aymah ?in, dan insha ALLAHU ya tabbatar ta dawo cikin hayyacinta. Zata kuma lalla?a jikin har lokacin da za'a fita da ita ai mata aiki a ?wa?walwarta ?in. Kasancewar yayi niyyar zuwa ?aurin auren gidan nasu sai ya bari kawai sai ranar juma'ar ya iso kanon da safe, dan a ranar ta kama za'a ?arama Nu'aymah allura ?aya daga cikin allurorinta.

Sai wajen sha biyu na rana aka basu sallamar, daga Abdallah har Naseer suna a asibitin. hakama Omar malam ?arami Yah Ahmad. Sai Abbah Musbahu. Kai tsaye motar Abba Musbahu Yah Ahmad daya kamota ya sakata. Dan ya kula akan tafiyar babu makawa su Abdallah sai sun nuna hali, shiyyasa ya raba gardamar ma tunkan a fara.
Murmushi kawai Abba Musbahu yayi yana jin da?in abinda Ahmad ?in yayi. Sukuwa duk sai suka ja guntayen tsoki kowa ya nufi motar da yazo ciki. A jere suka bar asibitin kamar wasu ?an kai amarya.
Gidan bawani cika yay sosai ba. Dan dangine kawai irin na nesa sosai wasu daga cikinsu suka iso. Amma duk da haka daka shigo zaka fahimci bayan jama'ar gidan akwai ba?i a ciki. Da yake duk ba'ai tsamanin sallamar yanzu ba sai babu wanda yaji har suka gama fakin. Abbah Musbahu ya kamo Nu'aymah dake kwance a jikin kujera ya fiddota a hankali yana mata sannu.
Kanta kawai take ?aga masa a hankali. Kai tsaye sashen Hajjo ya nufa da ita. Su Abdallah suka take musu baya gaba ?aya. Sun iske sashen ba mutane sosai. Dan Umm ce ke cin-cin dasu dibulan, nakiya, alkaki da dai sauran kayan gara na fulawa da akeyi. Hakan yasa duk ?annenta da ?annen Adda da wasu daga cikin ?awayensu dama matan gidan da yaran manya na ma'auri duk suna can anata aikin a can sashen.
Cikin farin ciki Hajjo da Ananah duk suka shiga musu sannu, idanunsu akan Nu'aymah dake langa?e jikin Abba Musbahu (dama yaya lafiyar kura??). Har cikin ?akin Hajjo Abba Musbahu ya kai Nu'aymah. Nan Hajjo da Ananah suka biyosa. Sake yimata dannu sukayi cike da kulawa da tausayi, sunata jera mata addu'oin samun lafiya mai ?orewa. Itako idanunta akan Ananah dake ri?e da hannunta tanata ?an murmushi. Dan duk zuwan da sukeyi dubata sai yau ne ta ganta. Suna shiri sosai da Ananah, ita?in ?ar gaban goshintace saboda sunan hajjo da taci.
Abbah Musbahu dake kallonsu shima cike dajin da?i yace, "Ananah tayi wanka sai a bata abinci taci, dan likitocin sunce ta fara cin abinci da gaggawa".
"Ba laifi auta. Dan wannan ramar da tayi gara ta?an cicciko, koni tsohuwa na fita ?yan gani ai". Baki Nu'aymah ta turo gaba tana janye hannunta daga cikin na Ananah datai maganar. Abbah Musbahu dake musu dariya yace, "Karki damu mamana, yanzu zanje na ha?o miki kayan da?i kema zaki zama ?atuwa ki fisu. Kuma karki basu ko ?an cinguli kinji".
Murmushi tai tana jinjina masa kai da kallon su hajjo irin bazaku cisa ?in nanba ko.

Jama'ar gidan da labari ya kai musu ta hanyar yara sunta zuwa yima Nu'aymah sannu. Sai da kowa ya gama shigowa sannan hajjo ta sakata ta shiga wanka da ruwan data ha?a mata mai ?umi. Yanda take jin jikinta wani irine yasata nutsuwa sosai tai wanka mai ?yau, dan ta kwashe tsahon lokaci a ciki kafin ta fito. Taji da?in ganin jakar kayanta, duk da tana kewar Umm ?inta tanaso ta ganta. Dan kowa ya shigo dubata a agidan banda Umm........ Shigowar Addah, Amal biye da ita da tire a hannu ya katse mata tunani.
Duk sannu suka sakeyi mata. Addah ta zauna gefenta tana jawo akwatin da fa?in, "Daughter tashi kisa kaya ga abinci kici kinji, idan naga ramar nan taki hankalina sake tashi yake yi". Cike da shagwa?a Nu'aymah tace, "Addah nafi yin ?yau a haka fa, dan ALLAH Amal banfi ?yau haka ba?".
Amal dake zuba mata abinci tace, "A'a mudai munfi sonki da ?an jikinki Aymah. Gara ki ciko kafin nanda kwana uku. Yanzu ?an biki kowa ya ganki sai ya tambaya".
"Barta Amal, ?ura zan dinga mata ai". Addah ta fa?a tana ajiyema Nu'aymah kayan da zata saka. Dariya Amal tayi da yima Aymah gwalo. Addah kuma ta taimaka mata ta saka kayan. Da taimakonta taci abincin. Ta bata maganganun ta tasha ta kwanta a gadon Hajjo dan ta ?an huta. Babu jimawa kuwa barci yay ayon gaba da ita.

Sai bayan la'asar Nu'aymah ta tashi. Wanka ta sakeyi da ruwa mai zafi tai salla. Ananah ta kaita falo da kanta ta bata abinci. Ta ?anci kuwa babu laifi, dan abinda take so ne akai mata. A haka Naser ya shigo ya samesu. Cike da kulawa da tausayi yayta jera ma Nu'aymah sannu. Ita kuwa amsa masa take da ?an murmushinta. Baifi zaman mintuna goma ba sai ga Abdallah ya shigo shima. Shima dai kulawar ya nuna a gareta sosai da jera mata addu'oin samun lafiya. Amsa masa tai shima, sai dai babu fara'a sosai kamar Nasir. Haka suka cigaba da zama a sashen suna harar juna har akai kiran sallar magriba. Nu'aymah dai tuni ma ta ?auke kanta ta maida ga tv kamar ta manta da zamansu a falon.
Bata saka iyayenta a rai ba sai dare. Baba malam da Umm tare suka shigo suka dubata, zukatansu cike dajin da?in sau?i data samu. Tare da tausayin gudan jinin tasu mai tsanani. Sun ?an jima anan sannan suka fita, ita kuma ta shiga ta kwanta cike da kewarsu. Badan karsu hajjo suka kamar ta raina musu ba da guduwa zatai wajen iyayenta, sai dai tasan koma taje can ?in ba sakewa zata samu ba dan ba?ine acan ?inma. Musamman dangin Addah da duk biki acan suke sauka dama. Yanzu haka ?akinta kansa tasan da ba?i a cikinsa.

________¡ï¡ï¡ï¡ï________

Haka aka cigaba da hidimar biki, ba?i nata sake cika gidan ta kowane sashi. Yayinda jikin Nu'aymah keta ?ara warwarewa. Bata fita ko ina, ko yaushe tana sashen hajjo. Sai dai taci ta ?oshi tasha magani tayi barci. Wani lokacin Amal da Yusrah kan shiga su tayata hira. Adawiya ce dai tunda aka sallamota bata ganiba. Da dai ta gaji da ha?uri ta tambayi su Yusrah. Sune suke sanar mata ai Adawiya nacan gidan kakarsu da ta haifi Addah, wai bata da lafiya. Tun washe garin da aka kwantar da Nu'aymah a asibiti ita kuma ta koma can.
Hakan sosai ya bama Nu'aymah mamaki, dan tasan iyayensu sam basa barinsu matsawa ko nan da can. Duk ?ulafucin da Gwaggo kakarta ta keyi akan ta dinga ?an zuwa mata hutu dole ta ha?ura. Dan ba'a barinsu, sai dai taje ta wunar mata ta dawo. Ko kuma idan bikine suje su kwana da Umm. Amma yau sai gashi wai Adawiya ita an barta zama a gidan kakarta.

?angaren su Abdallah kam duk yanda sukaso ke?ewa da Nu'aymah hakan yaci tura, iyakarsu zuwa su mata ya jiki kamar kowa shikenan. Ita kanta ta?i yarda ta sake dasu.
A daren yau da ya zama saura kwanaki biyu ?aurin auren gidan da daddare su baba malam suka bu?aci ganin Nu'aymah da Abdallah sai Naseer. A sashen marigayi kakansu suka taru, dan canne ka?ai babu kowa a ciki.
Da hanzari Nu'aymah data fito wanka ta zura dogon hijjab akan zanin wanka ta fita kiran da Amal ta sake zuwa tai mata. Ta iske kowa ya hallara ita kawai ake jira, zuciyarta cike da mamakin taron ta ?arasa garesu. Kusa da ?afafun Ananah ta zauna tana gaishe da iyayen nata. Duk suka amsa mata da kulawa suna sake tambayarta ?arfin jikinta.
Kanta a ?asa tace, "Alhmdllh naji sau?i sosai". A kusan tare suma sukace Alhmdllhi.
Abban Adawiya ne ya bu?e taron da addu'a kamar yanda shari'a ta koyar da mu. Bayan sun kammala Ananah ta fara magana akan abinda ya tarasu.
"To da farko dai zan fara da tuna mana muhimmancin zuminci a addinance da kuma al'adance. mu dukanmu anan babu jahili, kowanne ALLAH yay masa nasibi da sani na ilimi dai-dai gwargwadon iko. Harma takai muna koyar da wasu ta hanyar baiwarsa. Dan haka inason mu nutsu, mu kuma fahimci junanmu. Mudai insha ALLAH ?a?a ko jikoki bazasu ta?a shiga tsakanin zumincinmu ni da ?ar uwata da muka rage ba. Sannan kuma ?a?an nasan ?a?a bazau zama silar ruguza naku zumincin ba. To haka nake fatan kuma su Abdullahi karku bari son zukata ya ruguza naku zumincin. Dan haka sakamakon halin da muka fuskanci kuna neman jefa kanku ne ya sakamu yin wani tunanin da ya kamata a kan matsalarku. muke kuma fatan kawo ?arshenta a yau a kuma yanzun insha ALLAH. Sai ku nutsu kusa hankalinku jikinku dan ALLAH".
Kansu duk suka ?aga mata alamar gamsuwa da zancenta. Suka amsa kuma da cewar "Insha ALLAH".
"Alhmdllh" ta fa?a tana maida dubanta ga Nu'aymah data jingina kanta jikin hannun kujerar da Ananah ke zaune tana kallon tattausan carpet ?in dake tsakkiyar falon. "Zainabu!".
"Na'am Ananah". Nu'aymah ta amsa mata tana ?agowa da ?yau.
"Zainabu wannan zaman nakine. Dan haka inason ki nutsu waje guda ki tsai da hankalinki. Maganar abinda ya duk ya faru mu ajiyesa mu barsa. UBANGIJI yana kallon kowa yana kuma sane da komai. Duk da bamu gaskataba zukatanmu basu bar rawa da ciwo ba akan batun, amma muna nan akan bincike ainahin gaskiyar al'amarin dan bazamu bari ya wuce a banza ba saboda kiyaye gaba akan na baya. Shiyyasa muka yanke shawarar da mu kanmu muke da tabbacin zata sama mana nutsuwa da ke kanki. Ga Abdullahi nan, ga kuma Nasiru nan. Dukansu ?an uwanki ne kuma masu sonki da fatan zama dake a matsayin matar aurensu. Kamar yanda a wancen karon bamu tauye ha??inki ba, a wannan karon ma bazamu tauye ba. Dan haka munason a yanzu basai anjimaba ki nuna mana wanda kike so tsakanin Abdullahi da Nasiru domin samar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a cikin zuri'ar mu".
Wani irin fa?uwa gaban Nu'aymah yayi, ta dubi Nasir ta dubi Abdallah sai kuma ta maida idonta kan iyayen nasu. Muryarta na?an rawa tace, "Ananah kuma a yanzu?".
Hajjo tace, "?warai da gaske Zainabu, a yanzu zaki nuna mana za?inki, dan muna bu?atar salama da zaman lafiya".
Zuciyarta na wani irin harbawa ta sake duban su Abdallah. Yanda duk suka zuba mata idanu cike da tashin hankali sai itama suka sake ?aga nata hankali ?ololuwa. Saurin maida kanta ?asa tai tanajin anya kuwa zata iya?. A take rauninta ya sake bayyana bisa fuska tamkar yanda suma duk suke a raunane zukatansu na rawa da barazanar son faso ?irazansu su fito.........
Abbah Musbahu ne ya katseta da cewa, "Mamana ke muke saurare, ki daure ki fa?a mana abinda ke a ranki kinji, kinga dai bazaki auri maza biyu ba, dan haka karkiji komai ki za?i ?aya a cikinsu mu zamu fahimceki suma haka. Zakuma mu saka muku albarka a cikin al'amarin".
Kuka Nu'aymah ta fashe da shi, bakinta na sake rawa tace, "Ab...a... Abbah ni dukansu ai ina sonsu".
Baba malam da tun ?azun baice komaiba yace, "Zancen banza kenan. Ai munsan dukan kina sonsu, hakanne yasa mukace ki za?a tunda ai baki ta?a ganin ana auran maza biyu ba ko!".
Bayan ta ?an zabura ka?an ta ?ara mannewa da jikin Ananah. Sai ?an girgiza kanta take hawaye na zubo mata da sauri-sauri.
Cikin taushin murya Abban Abdallah yace, "A'a yaya ayi mata a hankali. Mamana ki kwantar da hankalinki kinji, ki fa?a mana a cikinsu dawa zaki iya zaman aure a yanzu? Dan bazamu bari a cuta ma rayuwarkiba insha ALLAH. idan ma dukansu basu miki ba falillahil-hamdu, mu a garemu ba komai bane, sai ki kawo wanda kike so koda ba'a cikin zuri'armu yake ba. Zamu duba nagartarsa idan ya cancanta zamu basa ke".
Kanta ta jinjina masa tana share hawayenta. Ta ?ago a hankali ta zubama su Abdallah dake kallonta idanun. Kowannensu a kallo ?aya zaka fahimci ro?onta sukeyi da idanu ta za?esa. Hakanne ya sake saka zuciyarta sake raunana. Cikin rawar hannu data jiki ta nunasu da ?an yatsa.
Gaba ?aya falon inda hannunta ya nuna sukabi da kallo..............?

??Munga Idi Aymah wa?! ???.



ZAFAFA BIYAR 2021

Hafsat miss xoxo??
KIBIYAR AJALI......!
(Sulke baya tareta saita gitta).????

Mamu gee??
MIN ?ALB!!????

Hafsat rano??
ABINDA KE CIKIN ZUCIYA...!!????

Safiyya huguma?? SIRA?IN RAYUWA????

Bilyn Abdull??
SARAN ?OYE????

Duka akan farashi mai rahusar gaske.

Kamar haka????????

?aya___300
Biyu____400
Uku_____450
Hu?u____500
Biyar_____700

Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki????

ACCOUNT NO 0812652655
ACCOUNT NAME- HAFSAT LAWAN GAMBO
BANK NAME: ACCESS BANK.

saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)????

0903 234 5899

IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU????

09033181070

????????????????????
TEAM----ZAFAFA BIYAR????????

ALLAH ka gafartama iyayenmu??????I'm on Instagram as yerwaincense_and_more. Install the app to follow my photos and videos. https://www.instagram.com/invites/contact/?i=ayfowzb2ah8k&utm_content=6k8ur6p.


*_LITTAFIN nan na ku?i ne. Dan girman ALLAH ki daure ki biya kafin ki karanta, idan kuma bazaki iya biya ba ki ha?ura domin ALLAH karki karanta. Idan kuma kin saya dan girman ALLAH karki ya?a mana????_*.


No. 42

.............Wani irin zabura Yah Ab yayi tamkar wanda yay gamo da mala'ikin mutuwa. A tsananin razane yace, "Nu'aymah kina nufin Naseer?!!".
Fashewa tai da wani sabon kukan tana jijjiga masa kanta. "Yah Ab kayi ha?uri, yanzu shine ya fi cancanta da hakan a gareni, kai ma dan ALLAH ina ro?onka ka maida matanka. Dan ALLAH ka kare mutuncin danginmu, karka bari wannan ya zama sanadin rusa zuminci ko saka ?iyayya a tsakaninmu. Kayimin afuwa mu rungumi ?addara, UBANGIJI ya fimu sanin hikimar dake a cikin hakan. Dan........"
Da sauri ya ?aga mata hannu jikinsa na wani irin tsuma na yun?urowar zuciyar tasu ta gado. Ya duba iyayensu da duk sukai tsit suna kallonsu tamkar babu su a cikin falon. Sai kuma ya duba Naser dake ta zuba murmushi idanunsa a lumshe bakinsa na motsawa alamar addu'oin godiya ga UBANGIJI yake jerawa. Batare da yace komai ba ya juya zai fice.
"Abdallah!".
Baba malam ya kirashi cikin muryar rashin wasa.
Cak ya tsaya, sai dai bai iya juyowa ba. Cikin bada umarni Hajjo tace, "Dawo ka zauna". Hawayen da suka cika masa idanu ya share. Kafin ya juyo a hankali ya dawo inda yake da, ya sake zama batare da yayi magana ba.
Kallon Nu'aymah dake kuka hajjo tayi. "Zainabu tashi kije mun gama da ke. Ki kuma share wa?an nan hawayen ki kwantar da hankalinki, dan munsan abinda mukeyi". Kai kawai ta jinjina mata tana mi?ewa. Batare da ta sake duban inda su Abdallah suke zaune ba ta fice a falon jikinta duk a sanyaye. Zuciyarta kuwa wani irin zafi take mata tamkar ana gasa mata ita bisa garwashin wutar gasa balangu.

¡ï¡ï<>¡ï¡ï

Tun wannan zama da akayi Nu'aymah bata sakeji daga bakin kowa ba a gidansu. Dan zuwa yamma ma gidan sai ya sake cika ma?il da ba?i dake ta sake ?ullowa ta kowanne irin kusurwa saboda walimar da za'a gabatar daga ?arfe hu?u. Hakama su Yah Ab bata sake ganin kowa ba a cikinsu, harma iyayen nasu. Garama Abba Musbahu taji muryarsa bayan


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login