Showing 141001 words to 144000 words out of 325075 words
mamakinsa na sake bayyana sosai da ganin Yoohan ?in wai matsayin likita. Koda wasa bai ta?a kawo hakan a ransaba shikam, hasalima ya ?auka Yoohan ?an kasuwa ne kawai.
Yoohan dai ya gaza yin magana, kallon baba malam ?in kawai ya ke ko ?yafta ido bayayi. Baba malam ya ajiye envelope ?in yana duban su Mahmood. "Zaku iya tafiya abinku mun gode". Kamar Abdallah zaiyi magana sai kuma yayi shiru, sai ma alamar su Mahmood suje ?in kawai yay musu da kai. Batare da Mahmood yace komaiba ya nunama yaransa hanyar fita suka fice badan ransu yaso hakanba.
Bayan fitar tasu babu wanda ya iya sake yin magana a office ?in har tsahon kusan mintuna biyu, sai Abdallah ne keta antayama Yoohan harara, Solomon kuma na hararsu gaba ?ayansu. Dan duk haushi suke bashi.
Cikin ?arfin hali Yoohan ya duba Dr Aysha da Solomon. Murya a sar?e yace, "Kuje zan neme ku". Babu wanda yay musu a cikinsu suka nufi hanyar fita kowanne da abinda yake kissimawa a cikin zuciyarsa.
"Dama kai likita ne Yahya?".
Kai Yoohan ya jinjina ma baba malam da yay tambayar, yace, "Eh Uncle".
Murmushi baba malam yayi a karo na farko, yace, "Masha ALLAH, ALLAH ya sanya albarka, yay ri?o da hannunka wajen aikata alkairi ga al'umar MANZON ALLAH ".
Cike da jin da?i Yoohan ya amsa da "Amin" kansa a ?asa dan ya kasa kallon baba malam ?in, harga ALLAH kwarjini yake masa matu?a, musamman ma yanzu da yaga hotunan nan duk da bai tabbatar da ala?ar dake tsakanin baba malam ?in da yarinyar da har yanzu shi ko sunanta ma bai saniba.
Cike da takaici Abdallah yace, "Abba mutum nan fa shineya lalata rayuwar Nu'aymah, ta yaya zamu cigaba da fiskantarsa kamar munajin tsoronsa?".
Da turanci Abdallah yay maganar, dan haka Yoohan yaji komai, ya kuma fahimci komai. Sai dai kafin yace wani abu baba malam ya kalli Abdallah fuskarsa na nuna ?acin rai, sai dai kuma baice komai ba. Yanzun ma shiru Abdallah yay badan yaso hakanba, sai dai yanda yake sauke huci zai tabbatar maka cewar zuciyar ?an mazan a wuya take.
Fuuu ya fice a fusace da ga office ?in. Da ga baba malam har Yoohan duk binsa sukai da kallo............?
______________________
ZAFAFA BIYAR 2021
_______________________
Hafsat miss xoxo??
KIBIYAR AJALI......!
(Sulke baya tareta saita gitta).????
Mamu gee??
MIN ?ALB!!????
Hafsat rano??
ABINDA KE CIKIN ZUCIYA...!!????
Safiyya huguma?? SIRA?IN RAYUWA????
Bilyn Abdull??
SARAN ?OYE????
Duka akan farashi mai rahusar gaske.
Kamar haka????????
?aya___300
Biyu____400
Uku_____450
Hu?u____500
Biyar_____700
Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki????
ACCOUNT NO 0812652655
ACCOUNT NAME- HAFSAT LAWAN GAMBO
BANK NAME: ACCESS BANK.
saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)????
0903 234 5899
IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU????
09033181070
????????????????????
TEAM----ZAFAFA BIYAR????????
ALLAH ka gafartama iyayenmu??????.*_LITTAFIN nan na ku?i ne. Dan girman ALLAH ki daure ki biya kafin ki karanta, idan kuma bazaki iya biya ba ki ha?ura domin ALLAH karki karanta. Idan kuma kin saya dan girman ALLAH karki ya?a mana????_*.
No. 38
.............Duk yanda su Abdallah sukaso a tuhumi Yoohan tun a asibiti game da zancen Nu'aymah baba malam ya hana, hakama su Abba basu bada goyon baya ba.
Zuwa yanzu dai Yoohan ya fahimci ala?ar baba malam da patient ?insa. Ya kuma gane Nu'aymah. Sai dai taka maimai abinda bai gama fahimta ba shine hotunan da Abdallah ya kawo masa da tsantsar ?acin ran da yake ganni tattare da samarin gidan su baba malam ?in gaba ?aya harsu malam ?arami da ya fara sabo da su.
Bayan samun damar shiga ?akin da Nu'aymah ke kwance da sukayi ?ai-?ai suka dubata duk da bata farfa?o ba baba malam ya tattarasu su duka suka bar asibitin. Dan Yoohan ya tabbatar musu ba'a bu?atar wani mai jiyya tattare da ita har sai ta farfa?o.
Suna tafiya baifi da mintuna talatinba shima ya amshi key ?in motar Dr Mubarak Solo ya jashi zuwa gidansu baba malan ?in. Kamar yanda yay tsammani ya iske kowa a gida da alama ma zaman jiransa sukeyi. Omar ne ya fito yay masa iso har sashen Hajjo. Hajjo ce kawai a sashen sai su baba malam su duka. Omar ma yana shiga da shi fitowa yayi.
Duk da Hajjo najin haushin Yoohan sai ta danne ta amshesa da fara'a kamar ranar salla dasu Ahmad suka shigo da shi wajenta. Ta kuma kawo masa ruwa da lemo. Yaji da?i kuwa sosai, tare da sake jin ?aunar ?ar tsohuwar har cikin ransa.
Bai iya sakin jiki ya sha ruwan yanda ya kamata ba, ya ajiye kofin tare da sake nutsuwa yana jiran ji daga garesu.
Bayan shu?ewar shiru na wasu mintuna Abba Musbahu yay gyaran murya idonsa akan Yoohan da kansa ke a rissine. Ba bu wani kwalo-kwalo ya shiga zayyano masa duk abinda ke faruwa.
Sosai mamaki ya kusa kashe Yoohan, ya sake tsuke fuska yana girgiza kansa. Idanunsa da suka ka?a sukai jajur ya ?ago ya duba baba malam, "Uncle ni a rayuwar turai da nayi ma ba ta?a aikata haka da wata mace da yardarta ba ma balle anan ?asata. Nasan anyi hakane kawai don shiga tsakanin ala?armu, ko kuma kasancewata musulmi a yanzu. Sai dai kuma ko wanene bai samu nasara ba, dan babu wani ?atanci da za'aimin koda yafi wannan da zai girgiza zuciyata daga barin bautama UBANGIJINA shi ka?ai. Ban musulinta domin kowa ba, ba kuma zan fita domin wani ba. Nasan zaku yarda da ni, Tunda har kuka yarda da dani alokacin da ba addininmu ?aya ba ma, dan ku?in nagartattun mutanene masu ?yawawan zukata. Zan fa?a muku ainahin gaskiyar abinda ya faru". Cikin nutsuwa da ?acin rai ya bayyana musu tun daga ha?uwarsa da Nu'aymah ta farko har zuwa ranar da ya musulinta. Bai iya ?arya ba tun yana kafirinsa, balle yanzun da ya ?ara sanin muhimmancin gaskiya a harshen ?an adam. dan haka ko kissing ?in Nu'aymah da yayi bai ?oye musu ba ya fa?a. Ya ?ora da fa?in, "Zan koma asibiti yanzun insha ALLAH, na muku al?awarin bincike akan cikin da akace itama ya zuba a jikinta, dan sam ni dai banga wannan matsalar tattare da itaba saboda ba akanta na fuskanci matsalarta ba. Amma zan kawo muku hujja a yanzu da yardar ALLAH".
Gaba ?aya sun gamsu da bayaninsa har Hajjo da Abba Musbahu ke fassarama maganar Yoohan ?in dan da turanci yay bayaninsa.
Baba malam ya ?anji nauyin zuciyarsa ya ragu sosai da bayanin Yoohan, a yanzu kuma hankalinsa ma yafi kwanciya da binciken Yoohan ?in fiye da na likitocin farko. Sannan tunaninsa ya fara karkata akan wani abu da ban kuma.
Ko mintuna goma Yoohan bai ?ara a gidanba ya fice ya koma asibiti. Sam baiji zafin su baba malam ba akan wannan maganar. Sun ?arama mutunci a idanunsa ne, haka yake son iyaye su kasance akan ?a?ansu. Ya sake fahimtar addinin musulinci addinine abin koyi, domin yana ?yamatar abinda wasu addinan su a wajensu ado ne, Wayewace. Hasalima zuciyarsa wani hasashe take masa daban akan wannan ?ullin da akai musu. Duk da bai tabbatar ba amma zuciyarsa na kinsa masa papa.
Tare suka koma asibiti da su Abdallah da har yanzu su dai basu wani gamsu da Yoohan ?inba.
Shi da Doctor Aysha suka gudanar da duk wani bincike akan Nu'aymah da har yanzun tana cikin halin sumar allurar da sukai mata. Dr Aysha ta tattara komai zuwa lab ta dan?ama wanda ta aminta da shi. Daga haka ta dawo ta sanarma Yoohan.
Kansa kawai ya iya ?aga mata, dan yana lafe jikin kujerarsa ne idanunsa a lumshe. Fuskar nan tasa kuwa a tsuke take matu?a. yana cigaba da nazarin komai dalla-dalla. Babu abinda ya iya ta?ukawa a wannan yinin sai zuwa salla idan lokaci yayi da le?a Nu'aymah da suke tsumayen farfa?o warta a kowane irin lokaci.
Misalin ?arfe biyar saura na yamma Dr Aysha ta kawo masa duk results ?in bincikensu. Ko bu?ewa baiyi anan ba ya mi?e da shi ya fito, su Abdallah da suka zame masa bodyguard shi da Nasir da Ahmad biye da shi.
Har zuwa yanzun su baba malam duk suna gida suna jiransu. Yanzun dai sa?anin ?azun, duk mazan gidan ne suka taru banda ?ammatan da yaran da su Umm, dan hajjo ce ka?ai mace ma a cikinsu. A maimakon Yoohan ya bu?e yanzun ma sai ya bama Abdallah damar bu?ewa dan ya tabbatar musu zai gane.
Tun a result ?in farko Yoohan yaji sa?anin abinda yay tsammani. Hakama sauran ?an gidan, aka tafi na biyu dana uku, Abdallah baima ?arasa na ukun ba Yoohan ya mi?a hannu a hankali ya zare file ?in da takardun results ?in ke a ciki yana binsu ?ai-?ai da kallo. Tabbas babu ?arya dai-dai Abdallah ke fa?a. Dan kuwa duk Results ?in sun nuna Nu'aymah tasan ?a namiji, ta kuma ?auki cikin sati shida da wasu kwanaki, cikin kuma tayi ?arinsa kwana biyu kenan.
Dimmm kan Yoohan yayi na ?an wani lokaci, sai kuma ya sake duba duka takardun sannu a hankali. Su baba malam dai babu wanda yay magana sunata binsa da kallo. Sai Abdallah ne da Naseer ke jifansa da wani mummunan kallo tamkar zasu hau kansa da duka.
A harzu?e Abdallah yace, "Yanzu kuma wace ?arya zakai mana dan ka kare kanka?". Yay maganar yana ri?o rigar Yoohan.
"Abdallah!!!!" Abbansa ya daka masa tsawa yana mi?ewa. Ransa a ?ololuwar ?ace yace, "Sake sa".
Kamar Yah Ab ya kashe Yoohan haka yakeji, amma kasancewar an musu tarbiyyar jin maganar magabatansu sai ya saki Yoohan ?in da shi sam hankalinsa ma bawai yana tare da su baneba. Dan gaba ?aya zuciyarsa ta shige a wani sabon nazari ne. ?an hanka?ashin da Abdallah yayine ya sakashi dawowa hayyacinsa. ?agowar da zaiyi sai idanunsa suka sauka jikin Windown falon hajjo. Inuwar mutum ya gani, yay ma wajen kallon kusan seconds goma kafin wanda ke a tsaye ya farga ana kallonsa yay saurin barin wajen. A take kan Yoohan ya kawo masa wuta kasancewarsa mutum mai kaifin tunani da basira.
Kallon sashen da baba malam yake yayi, ya ?anyi luuuu da idanunsa da haskensu ya ?an sirka yana wani bahagon murmushi, kamar zai lumshe su sai kuma ya ?u?esu a hankali. Cikin muryarnan tasa mai kauri da amo data hadu da ?acin rai a yanzun yace, "Uncle wannan tatsuniyar akwai marubucinta kusa da mu daf. Amma mizai hana ka bani damar yankar ticket ?in fara game da shi? Dan ni bana wasa a saman ruwa tunda ba masinci bane. Nafi yarda da shiga ?ar?ashin ruwan kasancewata mai yawan bincike akan ma'adanai. Kasan masu iya magana kance idan ka hango biri bisa tsumagiyar reshe ba gangancine ya kaisa ba, tsabar ?warewa ce a iya hawan bisa. Ko zaka amince ka bani aurenta idan ta girma?".
Kowa a falon sai da ya zaro idanu waje, harma da masu zabura. Nasir da Ya Ab kam ai dingangan suka tsaya akan ?afafunsu tare da hassalowa lokaci guda kamar zasu ha?iye Yoohan da ko kallo basu ishesaba. Sai dai kafin su ?arasa Abban Adawiya ya daka musu tsawa. Tilas suka ja burki badan rayukansu sunso hakanba.
A karon farko baba malam yay tattausan Murmushin da har ha?waransa sai da suka bayyana. idanunsa ?yam akan Yoohan. zamansa ya gyara da ?yau yabi duk jama'ar falon da kallo, su Abban Adawiya ma duk murmushin sukeyi, hadda hajjo da malam ?arami ke fassarama maganar yoohan ?in.
Murmushi baba malam ya sakeyi a karo na biyu, kafin yace, "Yoohan maganar aure ba abin wasa bace a musulinci, dan haka bazan iya baka amsar bukatarka a yanzun kai tsaye ba. Amma kaje zanyi magana da ?an uwana, duk hukuncin da muka yanke zamu sanar maka insha ALLAHU".
Duk da Yoohan yaso samun amsar baba malam take a wajen sai kawai ya jinjina masa kai alamar ya amince da hakan. dan haka ya mi?e yay musu sallama ya fice abinsa yana jifan Naser da Abdallah da wani irin kallon na ban ?yaleku ba kuma, kamar yanda suma suke binsa da kallon kishi da tsana.
A yanzun kam zamu iya cewa komai ya harmutse musamman a gidan su Nu'aymah. Dan tun bayan barin Yoohan gidan baba malam ya kasa zaune ya kasa tsaye da fashin ba?i akan kalaman yaron mai hikima. Kai kawo kawai yake a bedroom ?insa tamkar mai safa da marwa. Hakama Abdallah da Naser hankalinsu a matu?ar tashe yake, dan su dukansu suna tsananin son Nu'aymah har cikin ransu. Umm kam da hajjo bama a maganar halin da suka tsinci kansu a ciki. Umm ba maganar wa Nu'aymah ya kamata ta aura bane damuwarta. Abinda likitocin keta tabbatarwa ga ?iyarta shine tashin hankalinta. Itace ta haifi Nu'aymah, itace tai mata tarbiyya, sannan a gabanta ta tashi har zuwa yanzu da ake akan rikicin. Tunda take da yarinyarta bata ta?a kamata da kuskuren sauka akan turbar tarbiyyar data ?orata ba. To tayaya za'ace hakan ta faru? Kanta ya kulle gaba ?aya, tama rasa wazata gaskta tsakanin likitoci da Nu'aymah. Dan zuciyarta ta?i aminta ?arta zata aikata haka, to sukuma likitocin mizaisa su musu ?arya? Ta yama zasu musu ?arya bayan sun kasance daban-daban?.
A ?angaren Yoohan kam yana fita yaci karo da Solomon. Bai wani zaman tunanin yanda akai ya biyisaba ko inda ya samo motar da yazo ?aukarsa kawai ya shiga kusa da mazaunin driver.
A tsorace Solomon ya dubesa, kamar zaiyi magana sai kuma yay shiru. saurin zagayawa yay mazaunin driver ya tada motar suka bar anguwar. Har suka isa hotel babu wanda yace uffan a tsakaninsu. Solo yay masa rakkiya har ?akin da ya kama masa. Yana ganin ya shiga shi kuma ya koma da baya. Wayarsa ya zaro yay kiran papa. Bugu biyu kuwa Papa ya ?aga saboda muhimmancin da Solo yake da shi a wajensa. Cikin girmamawa ya gaishe da shi, kafin suyi magana mai tsajo wadda bilyn ku bataji saboda da yare Solo ke magana. Sun kusa mintuna talatin sannan Solomon ya yanke wayar yana wani cizon lips da yin ?wafa.
?arar waya ce ta saka Yoohan dake zube saman gado idanu a lumshe ko takalmi bai cire ba bu?e idanunsa. Kasancewar ring ?in daya sakama iyayensa da banne yasa ya fahimci papa ne. Sai da wayar ta kusa katsewa sannan ya ?aga. Ya saka a kunne batare da yayi maganaba.
Daga can Papa yace, "Yoohan kana lafiya?". "Uhhm!" Yoohan ya amsa a ta?aice. Papa da keta ?o?arin danne fushinsa yace, "Ni bansan lokaci daka fara zama ma?aryaci ba. Ni nasan dagajin muryarka akwai matsala ai, dan an kirani daga asibitinku an sanarmin duk abinda ke faruwa". Kamar Yoohan zaiyi magana sai kuma yay shiru abinsa yana sake tsuke fuska. Takaici ya kuma kume papa, yace, "John kana jina kuwa?". Yanzunma kamar bazai amsa ba, sai kuma ya nisa muryarsa a har?e yace, "Papa inason nayi aure! Kuma ?iyar Sheikh Sooraj Hashim jibiya zan aura, sai dai yarinyar ta cika ?ankanta".
Wani irin bugawa ?irjin Papa yayi a lokaci guda. Tamkar wanda aka ?wa?ama guduma a saman kai ya mi?e zumbur da fa?in, "What?!. John! Are you Mad?!!". Yanda papan yay maganar da tsananin tsawa ne ya saka Yoohan janye wayar daga jikin kunnensa yana matse idanu tam-tam. Sai kuma kawai ya yanke wayar yay wurgi da ita ta tarwatse ?asa kamar wani zararre. Harya ?an zabura zai mi?e sai kuma ya koma baya ya sake zubewa a gadon yana ambaton addu'ar da Manager Hamza Ibrahim da a yanzu suka sake zama abokai sosai ya koya masa. Ita ya shiga maimaitawa a cikin ransa. Cikin amincin UBANGIJI a hankali yaji ?irjinsa ya fara rage nauyi, sai kuma wani irin barci ya fara fisgarsa a hankali.
Gaba ?aya papa ya haukace a gaban abokansa da ?anninsa. Dan suna a tare lokacin wajen wani meeting ?insu na manyan ?auyensu, dan dama yaje ?auyensu ?inne tun jiya da daddare saboda meeting ?in mai muhimmanci ne suka shirya yi.
Uncle Godwin ne ya kama hannunsa ya zaunar da shi yana fa?in, "Hah Friend. Please calm dawn ".
Papa ya furzar da wani zazzafan huci jikinsa na wani irin tsuma, ya doka sandar hannunsa a ?asa yana cizar lip