Showing 72001 words to 75000 words out of 325075 words
da ko waiwayarta yayiba.
Binsa tai da kallo idanunta na cika da ?walla, babu abinda zaka iya hanga a gareta sai tsantsar damuwa da tashin hankali. Kasa tashi tai a wajen har tsahon wani lokaci. Sai da tai kuka sosai kafin ta iya mi?ewa tabi bayansa.
Yoohan da tuni ya shige ciki yana shiga sashensa ya maida ?ofar ya kulle tare da barin key ?in a ciki dan karma Mom ?in tace zata biyosa. Kai tsaye ?akin motsa jikinsa ya shige ya farayi da wani irin yanayi maiban tsoro. Dan komai yana aiwatar da shine fiye da yanda yakeyi idan yana cikin nutsuwarsa.
Tsahon lokaci ya kwashe a ?akin, duk da yanda yay bala'in fita hayyacinsa saboda wahala ya kasa bari ya huta. Sai da yay wujiga-wujiga da shi, daga ?arshema ya yanke jiki ya fa?i.
A take wasu hawaye masu zafi suka shiga gangaro masa a fuska, ya shiga taunar lip ?insa ?irjinsa na sake zafafa, abinda ke kusa da shi ya rarimo yay wurgi da shi, ya sake ?aukar wani ya ?ara wurgawa. A haka yayta jefe-jefe da kayan ?akin yana hawaye cike da jin ?acin da fushi mara dalili.
Hankalin madam Chioma yay masifar sake tashi fiye da farko. Tunda Yoohan ya fara jefe-jefen nan akan kunnenta ne, taje ta kira su Solomon amma kowa na tsoron shiga ?akin. Waya ta ?auka ta kira papa shima. Bugu biyu kuwa ya ?aga. Da kukanta sha?e-sha?e ta sanar masa da duk abinda ke faruwa.
Duk da papa yasan da yanayin na Yoohan sai hankalinsa ya sake ?ololuwar tashi fiye da da can. Wannan al'amari na Yoohan na bashi tsoro. Sunyi addu'oin a church, sunyi maganin, sunyi na aaibitin amma abu ya?i barinsa. Tunda suke basu ta?a gamo da mai kalar matsalar Yoohan ba. Shi ciwon nasa bawai wani waje ne ke masa ciwo a jikinsa ba, likitocima kansu sun sanar musu su basa ganin kowacce irin matsala tattare da Yoohan ?in, ?wa?walwarsa lafiyarta lau.
UBANGIJI shine yasan gaibu game da matsalar Yoohan. Dan haka kawai yake tsintar kansa da kasa yin barci. Sai ya jera kwanaki sama da biyar bai rintsaba koda kuwa yanajin son yin barci, ada sanda abin ya fara masa sai ake yimasa allurar barci mai shegen ?arfi, a kuma ha?a masa da magani. Idan har akai haka yakan samu barci kona awa ?aya zuwa biyune ya farka. A hankali kuma yana ?ara girma matsalar na hauhawa, sai yazama kobabu ciwon ma baya iya barcin sai yasha maganin ko anyi allura, kuma baya wuce awa biyu zai tashi. Al'amarin sosai ya fara neman ta?a masa rayuwa da karatu, amma da yake yanada ?wazo sai akaita lalla?awa.
A lokacin da karatunsa na likitanci ya fara zurfi sai ya fahimci shan maganin barci da yin allurar barci illace a lafiyarsa da hankalinsa da kuma aikinsa dake cikin manyan burikansa na rayuwa. Ballema da ALLAH ya taimakesa shaye-shaye baya cikin abin sha'awarsa, dan ya jima da fahimtar inhar zaiyi shaye-shaye koda na giyane to bafa zai kai labariba akan burin zamansa likita, sai kuma Asthma da yake da ita, itama ta taka rawar gani wajen sakashi ?yamatar bushe-bushen haya?in samarin zamani. A ?an tsakanin da ya daina yarda amasa allura, ya kuma daina shan maganin barci yasha matu?ar wahala, komawa yay tamkar wani ?aramin mahaukaci, (kunsan rashin barci matsalane). Ya koma babu abinda ya keyi sai ba?in rai, abu ka?an zai hau fushi, baya walwala sam, baison hayaniya, magana ma sai yaso ya keyinta. Karatunsa ma sai ya fara neman yin tangal-tangal.
Baya son zuwa aji, akoda yaushe yafi bu?atar zamansa a hostel shi ka?ai, idan kuma ya fito sai ya koma can gefe guda ya zauna inda mutanema basa gilmawa. Duk da wannan tashin hankali da Yoohan yake a ciki yana nan akan bakansa na daina yarda ayi masa allurar barci ko yasha magani, ya yarda zai jure duk wani matsi da rayuwa zatazo masa da shi dan ya samu ya sai-saita rayuwarsa kodan samun cikar burinsa. Aikam ya jigatu, dan a tsakanin badan Rich ba da ?wa?walwarsa ma zata iya ta?uwa.
A cikin wannan yanayin da ya tsinta kanshi a wata ?asa suka sami hutun sati biyu. A wannan karon sai ya ha?a kaya yace shi zaije gida 9ja hutu. Rich yayi mamaki matu?a, dan yasan burinsu shine bazasu ta?a zuwa gidaba sai sun kammala karatu. Duk yanda yaso tunama Yoohan wannan al?awarin ya?i saurarensa sam, haka dole ya barsa ya shirya ya taho Najeriya. Da yazo Najeriyar ma bata canja zaniba. Dan sai addu'in coci da kullum papa yake kan kaisa ai masa bayan nashi, sai kuma masu magani da basu maraba da a kirasu da matsafa kowa na gwada tasa fasahar.
Ahaka ya kusan cinye hutun babu wani ci gaba, saima gaba al'amarin yakeyi dan yanata ?ara nisanta kansa da zama cikin mutane, ya kuma daina fara'a sam balle walwala. Cikin amincin ALLAH ana saura kwana biyu zai koma makaranta ALLAH ya ha?a shi da wani bawan ALLAH da wani yammaci, ya ?auka mota ya ?an fita daga gida suka kusayin taho mu gama da motar mutumin. Hankali a tashe wa?anda suke a waccan motar suka fito, amma shi Yoohan sai ya?i fita yay zamansa a mota yana cika yana batsewa. Su duk zatonsu wani abun ya samesa, sai da suka bu?e motarsa dansu duba sai suka samesa lafiya lau. Sai dai kuma mutumin kallo guda yayma Yoohan ?in ya fahimci yana tare da damuwa sosai, duk da wani kallon banza dana takaici da Yoohan ke musu sai yay murmushinsa daya ?arama kamilar fuskarsa kwarjini, cikin kwantar da murya ya kama hannun Yoohan ya fiddosa a motar, ya saka drivernsa ya ja motar gefe dan a tsakkiyar titi suke. Danma titine na anguwa babu yawan shiga da fitar motoci.
Da farko Yoohan yaso bijirewa, sai dai kwarjinin mutumin ya cika masa idanu har yaji bazai ta?a iya masa musu ba. Can gefe bawan ALLAH nan yasa suka zauna, ya amshi ruwan da yasa drivern sa ya ?akko masa a mota ya bama Yoohan yace ya sha. Nanma sai bai musaba ya amsa yasha kusan rabin robar yana sauke ajiyar zuciya a jajjere. Sai da ya huta na wasu mintuna sannan mutum nan ya shiga masa tambayoyi cike da nutsuwa da kulawa. Wasu Yoohan ?in na bashi amsarsu, wasu kam sai yay masa shiru.
Duk da bawan ALLAH nan ya fahimci Yoohan ?in ba musulmi bane sai ya dubesa cike da kulawa yace, "Idan na baka wani magani ka gwada zaka amsa kasha?". Kallonsa Yoohan ?in yayi na wasu mintuna yana nazari, kamar bazai amsaba sai kuma can ya ?aga masa kai alamar "eh". Murmushi wancan mutumin yayi a wancan lokacin, ya ?auka goran ruwan da Yoohan ?in yasha ya rage yay addu'oi a ciki ya bashi. Yoohan ya jima yana kallon ruwan kamar bazai sha ba, sai da yaja lokaci mai tsayi sannan ya kafa baki ya shanye. Murmushi mutumin ya sakeyi, ya kama kan Yoohan yay masa addu'oi ya tofa masa. Daga haka yace masa ya koma gida ya kwanta, insha ALLAH yau sai an gaji da dogon barcinsa a gidansu an tadashi. Da izinin ALLAH kuma indai matsalar barcice ya daina fuskantarta sai dai idan hakan yana cikin doguwar ?addararsa.
A lokacin Yoohan ya tashine kawai ya bar wajen amma ko godiya baima mutuminba dan bawai ya yarda da zancensa bane, tunda shi yasan fa?i tashin da iyayensa keta famanyi akan matsalar. Shi kuma mutumin bai damuba sai kallo kawai ya bisa da shi a ransa yana fata da sakankancewa UBANGIJI zai amsa masa addu'arsa tai tasiri akan Yoohan ?in.............?
_____________________
SAHFAT PREORDER!
______________________
Wani kaya sai amale ka ?auka??.
SAHFAT PREORDER maida tsohuwa yarinya.
Kaji masu kawo kayan adon gida dana jiki ?an gaske.
*_Ina mata masu ?an bana bakwai? ko uwargidar da ake shirin kawoma ?ar bana bakwai?. Kai hardama matan gayu ?an ?walisa masu son sabunta gida da kayan ado ?an waje masu sau?in farashi da nagarta!._*
_To ku garzayo dama ta samu, dan SAHFAT PREORDER sune na ?aya a wannan fanin. Idan kayan kitchen kikeso masu ?yau da nagarta a farashi mai sau?i kuma zaki samu a Sahfat preorder. Idan kayan sakawa kikeso na manyan mata ?an gayu suma akwaisu babu ?ayarya. Jaka ko takalma na nunawa tsara suma ba'a barsu a baya ba harma da mayafai. Hakama kayan ?aki basu da tsara_.
Ni shaidace domin dukkan kayana ta hannunsu nake samu nima. Ku garzayo kuma a dama daku dan nasan zakuyi alfahari da hakan insha ALLAHU.
Kiyi magana ta wannan Number 08142957548 insha ALLAH zaki samu ?arin bayani ?ar uwa.
*_Siyen nagari??, maida ku?i gida?? sai SAHFAT PREORDER??????????_*
_____________________________
ZAFAFA BIYAR 2021
_______________________
Hafsat miss xoxo??
KIBIYAR AJALI......!
(Sulke baya tareta saita gitta).????
Mamu gee??
MIN ?ALB!!????
Hafsat rano??
ABINDA KE CIKIN ZUCIYA...!!????
Safiyya huguma?? SIRA?IN RAYUWA????
Bilyn Abdull??
SARAN ?OYE????
Duka akan farashi mai rahusar gaske.
Kamar haka????????
?aya___300
Biyu____400
Uku_____450
Hu?u____500
Biyar_____700
Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki????
ACCOUNT NO 0812652655
ACCOUNT NAME- HAFSAT LAWAN GAMBO
BANK NAME: ACCESS BANK.
saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)????
0903 234 5899
IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU????
09033181070
????????????????????
TEAM----ZAFAFA BIYAR????????
ALLAH ka gafartama iyayenmu??????.[4/2, 1:36 PM] +234 901 860 0202: *_INA MASU NEMAN INDA ZASU SAMU INGANTATTUN:_*
*_HERBALS APHRODISIAC NA GARGAJIYA BANA HADIN BATURE BA MAI SIDE EFFECT..?_*
*_TO KU SAURARA KUJI, DOMIN NESA TAZO KUSA.._*
*_ZEE HERBALS APHRODISIAC!_*
*_ZEE HERBALS APHRODISIAC!!_*
*_ZEE HERBALS APHRODISIAC!!!_*
*_MUNZO MUKU DA INGATTTUN KAYAYYAKI WANDA ZASU GYARA CIKI DA WAJE_*
*_MUNADA SUPPLEMENT MASU GYARAN JIKI DANA FATA, WANDA ZASA SAKI KIYI SHEKI FATAR KI TAYI LAUSHI. TAYI LUWAI! LUWAI! TAMKAR TA JARIRAI_*
*_AKWAI SUPPLEMENT NA KAYAN MATA WANDA ZASU GYARA KI, KIJI KI TAMKAR BUDURWA, SUPPLEMENTS DINMU BASU DA SIDE EFFECT, DOMIN AN HADO SU NE DAGA INGATTATTUN ITATUWA, WATO NATURAL PRODUCTS NE ACIKI._*
*_KAI BA ANAN KADAI MUKA TSAYA BA, MUNA DA INGATTUN KAYAYYAKIN MATA WANDA KESA KISHIYA KWAFA, WANDA DUK INDA SARAUNIYA TAKAI KIN WUCE, WANDA ZASU TSATSO MIKI MARTABAR KI DA KIMAR KI_*.
*_AKWAI INGATTATTUN MAGUNGUNA, NA CUTUTTUKAN DA SUKA SHAFI DAN ADAM DAMA JINNU.. KAI DAMA WANDA BAMU AMBATA BA.. ZEE HERBALS APHRODISIAC (MASARAUTAR INGATTATTUN MAGUNGUNA KENAN)_*
*_KYAU, ARHA, INGANCI, RAHUSA... SAI ZEE HERBALS APHRODISIAC_*
*_MANHAJOJIN MU NA SOCIAL MEDIA: KAMAR INSTAGRAM DA WHATSAPP DAMA NAMBAR TARHON MU: DOMIN SHIIGA KUGA IRIN KAYAYYAKIN MU TUNTUBE MU TA_*
_INSTAGRAM LINK DIN MU:_
www.instagram.com/zeeherbalsaphrodisiac
_WHATSAPP LINK DIN MU:_
https://Zeeherbalsaphrodisiac.whats.bz
_NAMBAR TARHON MU_
08169380189
*_KARKA BARI A BAKA LABARI GWARA KA BAYAR.. KIZO A DAMA DAKE YAR UWA, KI ZAMO DAYA DAGA CIKIN KASAITATTUN MATA MASU AJI.. MUNA GARIN KATSINA, SANNAN KAYAN MU MUNA BADA SU AKAN FARASHIN SAYA 'DAI DAI KO SARI.. MUNA TURA KAYANMU A KO'INA A FADIN NAJERIYA._*
__________________________________
No. 20
..............Aiko ALLAH ya amsa masa, dan cikin amincinsa Yoohan na komawa gida bai rufa awa ?aya ba wani irin barci mai da?i da saka kwanciyar hankali yay awan gaba da shi. Sai ga Yoohan da ya kwanta tun kusan shida na yamma bai farkaba sai goma na safiyar washe gari.
Wannan al'amari ya bama Yoohan da su Papa mamaki, suka shiga masa tambaya akan yaya akai yay barci jiya?. Bai ?oye musu komaiba ya basu labarin ha?uwarsa da mutumin da bai sani ba, bai kuma san inda zai sake samunsa ba a yanzun. Duk da sunji da?in hakan sai suka nuna rashin damuwarsu da sanin wanene mutumin ko inda zasu samesa, saboda kawai sun fahimci musulmi ne. Yoohan ?in kuma ya koma inda suka ha?u da mutumin har kusan sau hu?u bai samu koda mai kama da motarsaba ma balle shi ?in. Haka ya ha?ura badan yasoba ya koma makaranta.
Wannan shine dalilin samun sau?i sosai daga matsalar Yoohan, ya koma yana barcinsa lafiya lau kamar kowa, sai dai lokaci-lokaci abin nasa kan buga, idan kuma ya juyo yana tsintar kansane cikin mawuyacin hali na ba?in rai da fushi da tsangwamar kansa. Dama gashi dalilin hakane sanadin maidashi mutum mara fara'a da son hayaniya.
To a yanzu gashi al'amarin nasa ya sake motsawa, duk da yakan jima baiyiba ma. Yau kwanakinsa uku kenan da dawowa ?asar, amma ko barcin mintuna goma ya kasa ?aukarsa. Yanda yake ganin rana haka yake ganin dare. Ya mugun fita hayyacinsa a kwana ukun nan, ya daina magana da kowa, abincima ya masa yajin aiki sai abinda ba'a rasaba yake ?anci idan yaji yana neman halaka a banza.
¡ï¡ï¡ï¡ï
Cikin murya mai cike da lallashi papa ke kiran sunan Yoohan ta jikin Window da suke a tsaye shi da Madam Chioma. Duk da yana jinsu bai fasa wurgi da abinda duk yaci karo ba a ?akin, har wani sashe na gilas ?in dake zagaye da ?akin ya tsage, dan ya jefa ?arfe ne ya bigi gilas ?in dake a matsayin bango ?akin.
Sai da ya jigata dan kasan sannan ya zube a ?ara yana wani irin sauke ajiyar zuciya mai ?arfin daban tsoro.. Duk da hankalinsu ya ?an kwanta ganin yabar jefe-jefen basu daina kiran sunansa da ro?on ya bu?e musu ?ofarba cike da lallashi. Shi kuma yayi banza dasu tamkar baisan da zaman nasu a wajenba.
Papa ne ya tuna da extra keys ?in sashen nasa, dan haka yabar wajen Window da sauri zuwa bedroom ?insa. Mintuna ?alilan sai gashi ya dawo cike da farin cikin samo keys ?in. Hakama Madam Chioma saboda da?in da taji har kiss taima papa tare da rungumesa. Zagayawa sukayi domin bu?e ?ofar, sai dai kuma key ?in ya?i shiga alamar yabar wani key ?in a ciki. Ransu duk a jagule suke bin ?ofar da kallo, madam Chioma har hawayenta sun dawo kwarara.
Solomon ne ya kawo shawarar bin ?ofar can baya dake sada mutum da ?akin motsa jikinsa kai tsaye. Su ru?ewama ta sakasu mantawa da ?ofar. Da sauri suka zagaya tacan, cikin amincin ALLAH kuwa suna gwada key ?in da suketa kokwanton ba nata bane sai gashi ya bu?e musu.
Har rige-rigen isa garesa kuwa sukeyi. Duk da yana jinsu bai motsa ba, sai da sukasha fama, dan Yoohan akwai taurin kai dama, da ?yar ya yarda suka tadashi zuwa ?akinsa. Madam Chioma da kanta ta shiga toilet ta ha?a masa ruwan wanka mai ?umi sosai. Kafin ta dawo inda papa ke rungume da shi yanata faman lallashinsa da masa magana mai da?in gaske, wadda ko ba'a fa?aba da alama tana tasiri ga Yoohan ?in.
Zama tai kusa dasu itama, ta mi?a hannu ta ri?o na Yoohan ?in tana murmushin jin da?in ganin ya nutsu, matsawa tai jikinsa sosai zata rungumesa kamar yanda papa yay masa, sai ya ?wace hannunsa ya mi?e zumbur. Cike da basar da abinda ya fahimci zatayin ya nufi toilet yana ?ingishi, dan da alama yaji ciwo a ?afar tasa ne.
Duk binsa da kallo sukai ita da papa, yayinda ranta ya sosu sosai akan yanda Yoohan ?in keyi mata a duk lokacin da ta nufi yimasa makamancin wa?an nan abubuwan. Tarasa dalilinsa na yimata hakan, 'shi kodai ya fara tunanin.......' sai kuma ta kasa ?arasawa ta girgiza kanta alamar ba haka bane. Dariyar papa ta sakata saurin kallonsa. Ya ?age mata gira da matsowa shi ya rungumeta yana fa?in, "?anki fushi yakeyi dake yau, kinga yama?i yarda ki rungumesa. ni zo na rungumeki".
Fuskarta a yatsine ta?an turesa, cike da salon yaudara ta matsa baya da juya masa keya irin maganarsa ta ?ara mata haushin nan. Shiko ya sake matsowa jikinta ya rungumeta ta baya yana dariya ?asa-?asa. "Wasa nake miki Momyn Yoohan, shima nasan yanayin da yake cikine kawai ya sakashi aikata miki hakan".
Duk da haushin da take ciki sai maganar papan ta?an sanyaya mata rai, dan ita ada tunaninta ba haka yake kawo mata ba. Juyowa tai idanunta cike da ?walla, muryarta na rawa tace, "Darling! Anya kuwa bazamu nema mutumin nan daya ta?a yimasa maganiba shekarun baya da suka wuce sannan muna farko-farkon zuwa Abuja?".
Papa dake kallonta ya ?an ?ata fuska yana nazarin maganarta, sai da yaja tsahon lokaci kafin ya amsa mata. "Shawaranki mai ?yaune momyn Yoohan, sai dai kuma a ina zamu samesa? Shi kansa Yoohan ?in bana tunanin zaima iya ganesa idan ya gansa ai".
Kafin ta samu damar bama papa amsa Yoohan ya fito daga toilet ?aure da towel, dan duk zatonsa sun fita. Turus yaja ya tsaya yana kallonsu fuska a tur?une.
Ahankali madam Chioma ta sauke idanunta akan bu?a??en jikin yaron nata dake ?auke da wata lafiyayyar farar fata mai santsi da ?aukar idanun mai kallonsa. Basai an fa?aba a kallo ?aya zaka fahimci shi ?in ya tashi cikin kulawar rayuwa da jin da?i, dan sam babu alamar rama tattare da shi......
Jikinsa ya fara ja da baya yana ?ara tamke fuska, hakan