Showing 27001 words to 30000 words out of 325075 words
shiru tana kallonsa kawai.
"Naje massallaci". ya fa?a a ta?aice yana juyawa ya fita daga ?akin. Binsa da kallo Umm tayi harya ?ace mata sannan ta ?auke kanta hawaye na ziraro mata.
¡ï¡ï¡ï¡ï
A ?angaren Hajjo Doctor ya bama Nu'aymah dukkan taimakon daya dace kamar yanda ya saba a duk lokacin da ciwon nata ya motsa. Sai dai yau ta jima bata farfa?o ba. Dan sai da sukaje sukai sallar magriba suka dawo sannan ya ?arasa ?an dabarunsa cikin amincin ALLAH ta farfa?o.
Godiya yayma UBANGIJI tare da fita ya sanar musu ta farfa?o. Dan yau ana idar da salla gaba ?ayansu suka baro massallaci, baba malam ne kawai yay zamansa. Matanma suna idar da sallar duk nan suka sake dawowa harda yaransu da dawowarsu islamiyya sukaji komai.
Bayan Doctor ya kammala komai ya bu?aci tattaunawa da su Abbah. Da ?yar suka samu Baba malam ya baro massallaci yazo.
Doctor ya gyara zamansa cikin girmamawa a garesu yace, "Gaskiya wannan karon jikin Nu'aymah yayi tsamari. Kunsan matsalarta ba'aso abu yana firgitata da tsanani. tsawa da duhu suna gaba-gaba wajen girmama ciwonta da ?arfafa shi".
Hajjo ce tai saurin fa?in, "Hakane likita, duk munsan wannan, kuma ana ?o?arin kiyayewa. Yau ?inma kuskure aka samu kasan ajizanci na ?an adam. Yanzu minene mafita?".
"To Hajjo ALLAH ya kiyaye gaba, amma kam yau abin yaso yin tsamari sosai a gareta, dan yanzu haka zancen da nake muku sam bata cikin hayyacinta, fatanmu dai ta dawo hayyacinta lafiya batare data manta komaiba ma bayan ta farka".
Da matsanancin tsoro suke kallonsa, sai dai kowa ya kasa magana. Da sauri yace, "Bamu da tabbacin hakan, komai na ALLAH ne, mucigaba da mata addu'a insha ALLAHU zata farko cikin ?oshin lafiya. Dama inada shawara ne, dan tun kwanaki naso zuwa da zancen sai nai tafiya kuma, yau kwanana shidda kenan da dawowa ma, zan kuma iya komawa a koda yaushe dan na samu gurbin ?aro karatu a ?asar Australia ne".
A tare sukace, Masha ALLAH, ALLAH ya sanya albarka ya bada ikon karanto abu mai amfani".
"Amin ya rabbi, nagode sosai".
Abbah Musbahu yace, "Muna surarenka. Wane shawarace da kai?".
"Dama akwai wani likita babba kuma ?wararre, dan kam ALLAH ya hore masa baiwa ta fannoni da dama inhar a ?angaren likitancine. To wani abokina ya tabbatar min har masu irin ciwon Nu'aymah yana basu taimako. Matsalar ?aya ce, shine ganinsa. Ganinsa nada matu?ar wahala dan yana aikine a Nigeria da wajen Nigeria. Ko a yau zai iya shigowa kano ya duba marasa lafiya ya fice, zuwa dare kuma kaji bama ya ?asar gaba ?aya".
"To ai mu Doctor ko biyansa ya kama muyi sai muyi dan yazo ya duba ta". Cewar Abban Abdallah.
"Ai anan gizo ke sa?ar Malam. Dan ko nawa za'a biyashi bazaizo gida duba mara lafiya ba. Dolene sai dai mutum yaje yay tanadin ganinsa kamar kowa, zai baka date ?in da zaka gansa idan har ciwonka yakai shi zai dubaka, idan kuma yaga akwai mafita zai ha?aka da wani likitan da zakaje ka gani. Date ?in da za'a rubuta maka kuma dole a sannan ne zaka gansa babu alfarma. Kwanaki yaron president ya samu wata babbar matsalar da sai shine ake fatan ya dubasa ko za'a dace. Har jirgi aka aika ya ?akkosa daga wata ?asar dan kawai yazo ya dubashi amma yace suje su sai kati subi layi kamar yanda kowa keyi shi bazaije ba. Kuma dole hakan akayi".
Babu wanda bai jinjina wannan al'amari ba a cikinsu, sukai shiru kowa na tunanin mafita kuma. Ganin haka Ahmad yace, "To Doctor idan babu damuwa ai muma sai kai mana hanya mubi hanyar data dace ?in na ganin nasa kawai, ko'a ina yake mu zamu bisa insha ALLAH. Fatanmu dai a dace".
"Hakan shine dai-dai. Ga Number ?aya daga ma'aikatansa zan baku sai ku nemesa, insha ALLAH zai muku ?arin bayanima fiye da nawa ma, ga kuma ta abokina ma duk zan ha?a muku shima likitane zaku iya neman taimakonsa koda ni na wuce ne".
Rubutawa yay ya mi?ama Hajjo dake a kusa da shi, ita kuma saita mi?ama Baba malan da tun shigowarsa baiyi ko tari ba. Bai musaba ya amsa ya ajiye gefensa da nufin idan ya tashi sai ya ?auka yaje ya adana. Doctor ya tattare file ?in bayanan ciwon Nu'aymah waje guda ya sake mi?ama Hajjo yana fa?in, "Da wannan zaku gansa dole, dan ?a'idarsa sai yaga bayanan ciwon mutum na baya inhar ya ta?a ganin likita akan hakan".
Nanma godiya suka sake masa. Hajjo ta sake mi?ama baba malam. Amsa yay ya saka Numbers ?in da aka bashi a cikin file ?in ya ajiye.
Kasancewar lokacin sallar isha'i yayi duk sai suka fice har Doctor. Bayan an idar da salla Doctor ya sake dawowa tare dasu Ahmad ya shiga ya ?ara duba Nu'aymah. Sai da ya sake tabbatar da komai ya zauna sannan ya fito yay musu sallama akan insha ALLAH da sassafe zai dawo yaga jikin nata. Idan kuma sunga da wata matsala komai dare su kirashi.
Sun masa fatan alkairi da godiya ya tafi.
_¡ï__¡ï_
Baba malam bai shigo gidan ba sai kusan goma saura, dan ya tsaya sunyi karatu ne. Sashen Hajjo ya fara shiga ya duba Nu'aymahn. Har sannan barci take, dan haka ya ?auka file ?in nata ya fice da shi zuwa sashensu.
Duk abinda Umm take masa bata fasaba. Yanda kuma bai mata magana akan Nu'aymahr ba itama batace da shi ?ala ba har suka kwanta.
______________________
ZAFAFA BIYAR 2021
_______________________
Wannan littafi SARAN ?OYE na ku?ine, yana ?aya daga zafafa biyar, idan kana bu?ata kaima wa?anan numbers ?in magana ka biya ku?insa naira 300 kacal dan girman ALLAH. Karka ya?a dan ALLAH idan ka gani??????.
Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki????
ACCOUNT NO 0812652655
ACCOUNT NAME- HAFSAT LAWAN GAMBO
BANK NAME: ACCESS BANK.
saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)????
0903 234 5899
IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU????
09033181070
_______________________
WASHE GARI
_______________
Alhmdllh Nu'aymah ta tashi jikinta da sau?i, kuma kamar yanda kowa yay fata bata manta da komai ba kamar yanda Doctor yayta jin tsoro. Hajjo ce ta taimaka mata tayi wanka. Yusrah ta kawo mata abinci tama zauna da kanta ta ringa bata. Ta ?anci babu laifi, dan Yusrah lalla?ata ta dingayi ita da Hajjo.
Kamar yanda kowa na gidan yazo ya dubata da safen haka Baba Malam da Umm ma sukazo suka dubatan. Sunji nutsuwa sosai a zukatansu ganin jikin nata Alhmdllh. Sai dai kowansu bai nunaba a fuska, sunma ha?e mata gabas da yamma.
Hakan ba ?aramin sake ?aga hankalin Nu'aymah yay ba, harta kasa ha?uri ta shiga tambayar Yusrah ko wani abu ya faru bayan barinta gida ne? Dan ita tayi zaton idan ta dawo zataga kowa na murnar dawowar tata. Amma saita samu sa?anin hakan, sai ma kalaman baba malam na jiya keta mata kaikawo a cikin rai.
?asa Yusrah tayi da kanta hawaye na cika mata idanu, haka kawai ta tsinci kanta da jin kunyar Nu'aymah ?in mai tsanani. "Yusrah dan ALLAH kimin bayani mana? Ina Yah Ab da Adawiya duk bamma gansu ba". Nu'aymah tai maganar cikin sanyin murya na alamun rashin jin da?in jiki.
Saurin mi?ewa Yusrah tayi ta juya mata baya zata bar ?akin. Nu'aymah ta ri?e hannunta itama da sauri. Hannu Yusrah tasa ta goge hawayen dake rige-rigen sakko mata a kumatu batare data juya ta kalli Nu'aymah ba.
Dai-dai nan Hajjo ta shigo tare da Doctor da yazo sake zuwa ganin jikin nata.
"Kai lafiyarku?".
Hajjo ta fa?a ganin Nu'aymah da Yusrah duk suna hawaye.
"Ba komai Hajjo". Yusrah ta bama Hajjo amsa tana zare hannunta daga cikin na Nu'aymah. Kamar hajjo zata sake magana sai kuma tayi shiru suka bama Doctor damar duba Nu'aymahn. Yaji da?in ganin jikin nata normal, sai dai yanason mata allura yana tsoron rikicinta da zasu kwasa. Nu'aymah ta mugun tsanar allura a rayuwarta, indai akace za'ai mata allura to lallai an taro match kuwa. Dan sai kowa yaji a gidan harma makwafta.
Kallon hajjo yay murya ?asa-?asa yace, "Hajjo ko za'a kira mana su Ahmad ne kusa. Allura zan mata kinsan kuma sai ansha ya?i".
Sosai hajjo ta waro idanu waje. Ta?an kalli Nu'aymah data kwanta idonta na kallon fanka dake juyawa a hankali. Sake kallon Doctor tayi, itama a hankali tace, "bara dai a dubamin cikin iyayen nasu tunda duk basu fita ba".
Kansa ya ?aga mata ya tashi ya fita falon dan ya ha?a allurar. Itama Hajjo biyosa tayi.
Kusan mintuna biyar da fitar tasu duk suka dawo harda Baba malam dake cikin shirin fita. Batare da yayi maganaba ya kama Nu'aymah da kansa ya tayar zaune. Kallonsa take cike da so da ?aunar mahaifin nata. Amma yanda yay kicin-kicin da fuska sai yake ?ara tsoratata. Ganin yanda ya jata jikinsa ya rungumene ya saka ?irjinta bugawa. Dan tun tana yarinya inhar taga ya mata irin wannan rungumar to lallai allura za'a mata. Saurin ?agowa tai ta kalli Doctor daya ?oye hannunsa a baya. Jikinta ne ya fara tsuma, zatai magana Baba malam ya balla mata hararar da ta sakata maida kanta jikinsa ta kwantar.
Rikici sosai akasha kafin Doctor ya mata allurar, ba ita kanta ba har baba malam da hajjo masu ri?etan saida ta tarama gajiya. Doctor kam har ?ar zufar wahala yakeyi a goshi, a ransa yana sake jinjina daru irin na Nu'aymah.
Tunda baba malam ya maidata ya kwantar ajiyar zuciya kawai taketa faman saukewa hawaye na zirarar mata da gudu. Hajjo ta zauna inda baba malam ya tashi ta ?ago kan Nu'aymah ta aza bisa ?afarta tana shafa mata dogon gashinta.
Sauran magungunanta Doctor ya ajiye yayma hajjo sallama suka fice shi da Baba malam.
Hajjo ta jima tana lallashin Nu'aymah kafin ta samu tayi shiru barci ya saceta. Amma har cikin barcin tsabar rikicinta ajiyar zuciya taketa faman saukewa a jajjere. Haka dai hajjo ta lalla?a ta kwantar da ita da gyara mata kwanciya ta tashi ta fice.
______________________
ZAFAFA BIYAR 2021
_______________________
Wannan littafi SARAN ?OYE na ku?ine, yana ?aya daga zafafa biyar, idan kana bu?ata kaima wa?anan numbers ?in magana ka biya ku?insa naira 300 kacal dan girman ALLAH. Karka ya?a dan ALLAH idan ka gani??????.
Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki????
ACCOUNT NO 0812652655
ACCOUNT NAME- HAFSAT LAWAN GAMBO
BANK NAME: ACCESS BANK.
saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)????
0903 234 5899
IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU????
09033181070
_______________________
______________
DUBAI
________
Amarya Adawiya da ango Abdallah sun isa ?asar dubai lafiya, sai dai gaba ?aya ya canja tsarin daya shiryama kansa da Nu'aymah. Ya dai kama musu babban hotel kuma a ?aki ?aya. A randa suka isan kuma ya sace wayar Adawiya ya ?oye batare data saniba.
Ita dai duk abinda yake mata bai ?ata mata rai, ha?e fuska da ?in mata magana tunda suka taho baisa taji haushinsaba balle sonsa ya ragu mata a zuciya. Saima ?aruwa da ya sakeyi tanajin kamar ta ha?iyesa.
Gadon ya bata ta kwanta shi kuma yasa bargo a ?asa yay kwanciyarsa. Da asuba ya rigata tashi, yay wankansa yay shiri tsaf. Sai da ya kammala komai sannan ya tadata. Mamaki ya kamata matu?a ganinsa cikin shirin fita, sai dai kuma babu fuskar tambayarsa.
Murya a sha?e yace, "Duk abinda kike bu?ata ki kira zasu kawo miki". Daga haka bai sake tofa komaiba yay ficewarsa daga ?akin yaja mata ?ofar. Ta jima zaune a wajen tamkar wata gunki har gari yay haske sosai kafin ta sakko jiki a sanyaye taje tayo alwala. Duk da hakan da yay mata babu da?i sai bataji haushinsaba. Haushin Nu'aymah nema ya kamata, dan a ganinta zaman dataine cikin zuciyarsa yasa baya ganin kowa da gashin mutunci sai ita. Aiko ta ?auki alwashin sai ya manta wata banza Nu'aymah a zuciyar tasa har abada balle kuma wata Yusrah da tasan bata a gabansa.
"Hajiya Adawiya, ke dai kike ki?anki kike kuma rawarki????".
Haka ta yini ita ka?ai, daga kallo sai cin abinci da kwanciya. Gashi ta nema wayarta ta rasa, sai kawai tunaninta ya bata kota barta a gidane kokuma ta yaddata a jirgi Yah Abdallah ya ?auke mata. Ta barsa akan idan ya dawo zata tambayesa.
Abdallah bai dawo hotel ?inba sai kusan 11 na dare, harkokin kasuwancinsa ya yini yi hankalinsa kwance. Baiyi zaton iske Adawiya ido biyu ba. Amma a mamakinsa sai ya sameta zaune dirshen tana kallo. Sannu da zuwan data masa kawai ya amsa ya ?auke kansa. Ya ?auka kayan barci ya nufi bathroom. Tana nan zaune ya fito tsaf da shi. Nanma bata ishesa ko kalloba ya zauna a ?aya daga rukunin kujerun ?akin yay kira a kawo masa tea. Babu jimawa akai knocking ?ofar. Adawiya ta mi?e jiki na ?ari zataje ta bu?e ya ?aga mata hannu. Da kansa ya tashi yaje ya amso ya dawo yay zaman sha bayan ya kunna laptop.
Sunja tsahon lokaci zaune, Adawiya nata faman kallonsa kamar ta samu television, shiko aikinsa yakeyi tamkarma ya manta da ita a cikin ?akin.
"Uhhm Yah Ab dan ALLAH ko kaga wayata?". Cak ya tsaya daga aikin da yake yana sake tsuke fuska batare da ya kalleta ba. Ba komai ya jawo hakanba sai Yah Ab datai kiransa da shi. Dan Nu'aymah itace ta fara kiransa da suna har kowama ya ?auka. itace kuma ke kiransa hakan a koda yaushe. Kamar zaiyi magana sai kuma ya fasa. Ya girgiza mata kansa kawai ya cigaba da abinda yakeyi.
¡ï¡ï¡ï¡ï
Haka suka cigaba da tafiya a kwanakin da duk suka gabata na barinsu ?asarsu. Adawiya duk a takure take, dan Abdallah kullum da sassafe yake fita, bazai dawoba kuma sai sha ?aya. amma soyayya ta rufe mata idanu ta kasa jin zafin hakan da yake mata.
Shiko gaba ?aya ya ?auketa yasa a kwandon shara ya maida hankalinsa ga kasuwancinsa kawai, dan a maimakon kwana goma da ya shirya yi a ?asar ya maidashi kwana shida zasu wuce.
Tun a randa Nu'aymah ta dawo gida yay mafarkin hakan da daddare, aiko tunda asuba yay kiran Number Ahmad. Cike da farin ciki Ahmad ?in ya sanar masa komai, dan dama shima yana da shirin kiran nasa, so yake kawai jikin Nu'aymah aga yanda zai kasance a washe garin.
Karan farko da tun faruwar al'amarin nan Abdallah yay sassanyan murmushi hawayen farin ciki na cika masa ido. Jiyake tamkar an tsundumasa aljanna yau. Yana katse kiran ya kira Momy itama. A lokacin dawowarta kenan daga sashen hajjo taje ta duba Nu'aymah itama.
Bayan sun gaisa cike da so da ?aunar juna irin ta ?a da uwa, ya tambayi lafiyar kowa a gidan sannan cike da zumu?i yace, "Momy ashe Nu'aymah ta dawo?".
Jimm tayi kamar bazata amsa masaba, sai kuma tace, "Uhmm! ta dawo jiya".
"Kai Alhmdllhi Momy, yanzu zanje na saya mana tickets kuwa mu dawo, in ALLAH ya yarda wannan karon bazan sake ta sake ku?uce minba Momy, a yau ?in nan ina durowa koda magriba ne sai an ?aura mana aur......"
"Kai! Shashasha dakata min. To idanma mafarki kake maza ka farka ka dawo hayyacinka. Wai kai Abdallah wane irin sakaran banzane halan? Ka fita idanuna tunkan na rufesu da kai a ciki wlhy. Bara makaji na maka mai kankat. Wlhy tallahi idan naga ?afarka a ?asarnan batare da ni nace kazoba ALLAH ya isa ban yafe maka ba....."
"Momy!!" ya fa?a cikin tsananin tashin hankali.
"Yes! Abinda kaji shi na fa?a. Idan zakai ha?uri da wa?anda aka baka kayi. Hauka akeyi da za'a manna maka mata har uku ?an family ?aya uban ?an son zuminci? Itama Yusrahn ina nan ina nema maka hanyar barinta wlhy. Adawiyar dai ta tsira tunda ALLAH ya sota ka baro ?asar da ita da wuri. Idan suma sunada nasu za?in nima inada nawa ai, amma aka nunamin fin ?arfi da ?an uwantaka. Kai kuma shashasha da