Showing 63001 words to 66000 words out of 325075 words
fakin Abban Abdallah da fitowarsu kenan daga massallaci sallar la'asar yayi kici?us dasu Nu'aymahr. Da mamaki ya ?araso ga ?an sandan.
Yayinda suma cike da girmamawa suka nufesa. Kamar ?azun sun gaishesa da mutuntawa. Kafin cikin nutsuwa ?aya daga cikinsu ya fara magana. "Malam ayi ha?uri dan ALLAH a mana afuwa, munzo mu gyara kuskuren da mukayi ?azun akan tafiya da wannan yarinya. Gata mun dawo da ita, dan bata da laifin komai ashe rashin fahimtace aka samu".
Ajiyar zuciya Abbah su Abdallah yayi yana mai jero addu'ar godiya ga ALLAH cikin ransa, tun ?azun da aka tafi da Nu'aymah hankalin kowa ba'a kwance yakeba a gidan, sun kira baba malam yafi sau ashirin dan su bashi ha?uri ya janye shara?in daya gindaya musu subi Nu'aymah amma yama?i ?aga wayar. Gudun kar abin ya zafafa kuma sun kasa gayama Hajjo da tunda ta farka a barcinta wajen sha biyu take faman saka yara su kira mata Nu'aymah tai mata kitso, dan itace ke mata duk sati. Idan kuma tanajin ?an rashin arzi?i tace bazata mataba sai ta biya. Bawai ku?i take nufin ta bataba, furar hajjon ta ?a'ida mai da?in tsiya da kowa ke ?ulafuci a gidan takeso ta bata mai yawa. Dan kullum Hajjo saita za?i wanda ta gadama a gidan take bama furar??.
Sai dai duk wanda ya fita bayan wasu mintuna sai ya koma ya sanarma hajjon Nu'aymah barci take. tun bata damu ba harta fara fa?an wane irin barcine haka Nu'aymahn keyi kamar wacce bata da mafa?i a gidan. Daga ?arshe ta mike da nufin zuwa ta tasota da kanta bayan sallar azhar sai ga Abba Musbahu ALLAH ya kawo gidan. Shine yay mata dabarar hanata yace bara ya aika a duba kidai Nu'aymah bata jin da?ine kokuma batama gidan.
Da wannan dabarar ya wagarar da ita da hirar mahaifinsu har akai sallar la'asar, ALLAH ya taimakesu sun fito kenan da nufin shirya yanda zasubi bayan Nu'aymah koda baba malam ?in zaiyi fushi kuma sai gata ta dawoma.
Godiya yayma ?an sandan, ya kama hannun Nu'aymah da haushin Yoohan bai bartaba har yanzu suka shige Abba Musbahu biye da su. Su Muhammad da suka fito zasu islamiyya ne suka fara cin karo dasu, aiko cike da ihun murna suka shiga fa?in Aymah ta dawo! Aymah ta dawo!.
Hayaniyarsu ce ta fiddo ?an gidan har Hajjo da taji abun banbara?au. Umm ce kawai bata fitoba dukda kuwa tanajinsu daga sashenta, ranta kuma cike yake da zumu?in son ganin halin da ?arta take ciki. Amma saita danne ta cigaba da azkar ?inta na yamma.
Rungumeta iyayen mata sukaitayi, musamman ma Addah da harda ?an ?wallarta tana dudduba jikin Nu'aymahr. Ganin ras babu ko ?warzane sai yunwa da takeji da kuma fushin fuskarta saita sake rungumeta tana godema UBANGIJI daya dawo musu da ita lafiya.
Cike da mamaki Hajjo tace, "Wai mi ake ?oyemin ne halan? Zainabun gidan ubanwa taje da har ake wannan gayar tarbar tata?". Shiru wajen yayi kowa ya kasa bata amsa. A take takaici ya kumeta ta kwanto bakin zaninta ta fara matsar ?walla da juyawa zata bar wajan. Cikin sauri Abbansu Abdallah ya ri?eta yana fa?in, "Yi ha?uri Innah, bafa wani abu baneba, dama wata ?ar matsalace ta faru, to ashema Nu'aymahn bata da laifin komai an samu rashin fahimtane kawai".
"Gidanku Lurwanu. nace kaci gidanku! Yanzu nan ni zaku maida shashasha, tun ?azun nake cigiyar Zainabu a gidannan amma anamin yawo da hankali, ni dama naji a jikina badai lafiyaba, yarinyar da bata iya awa biyu bata shigo sashenaba indai tana a gidanan ace wuni zur banga giccintaba kuma lafiya sumul".
"To kiyi ha?uri inna anyi kuskure, amma za'a gyara insha ALLAH".
"Ya zanyi na ha?ura, amma a fa?amin yanda akai to".
Babu musu sukai mata bayanin komai a gaban kowa, suka kuma ?ora da bayanin ?an sandan da suka dawo da Nu'aymah ?in. Ajiyar zuciya kowa ya shiga saukewa a wajen da nuna jin da?in Nu'aymah ba wani laifi tayiba. Daga haka kowa ya kama sabgar gabansa, Addah kuma ta kama hannun Nu'aymah dake yatsine fuska saboda mararta da kamar jira take ta dawo ta fara tsunkula mata.
Umm na zaune tana azkar suka shigo, dukda taji sanyin ganin Nu'aymah lafiya lau saita ?aure fuska ta ?auke kanta. Addah batabi takantaba ta shige da Nu'aymah toilet, ruwa mai zafi ta ha?a mata tace tai wanka ta gasa jikinta sosai. Nu'aymah dake murmushi cike dajin ?aunar Addah ta gya?a mata kai.
Zama Addah tayi a bakin gado tana kallon Umm data ?auke kai, ?aramar dariya tai ta tsokana da son ganin Umm ?in ta manta da komai itama tace, "Wlhy ki gama ?aure-?auren fuskarki nasan ranki fes, ni wlhy yanda kike wani ture Nu'aymah har mamaki kike bani".
Hararta Umm tai ta sake ?auke kanta. Addah ta kwashe da dariya a karo na biyu tana fa?in, "Oho dai, duk abinda da dai zakiyi munsan mune zuciyar taki".
?in tankawa Umm tayi, dukda kuwa abinda Addah ta fa?a ?in shine gaskiya. Tana kawaicine kawai akan nu'aymah dan kar aga rashin kunyarta akan ?ar fari, ?ar farinma wadda ta ?auki tsahon shekaru bata samu ba. Amma kam Nu'aymah itace cikar dukkanin farin cikinta, itace kuma dukkanin hauhawar damuwarta. Shiyyasa take jigatuwa a gidan, dan inma lagontane ma?iya sun gane akan Nu'aymah shiyyasa suke jigata rayuwar yarinyar ta hanyar SARAN ?OYE.
____________________________
*_SAUDIA_*
Ta jima tana kai kawon jiran fitowar tasa amma bai fitoba. Daga ?arshe sai ta fahimci da alama yau bama zai fita yabar gidanba kenan. Zama tai shiru tana ?ullawa da kwancewa a cikin ranta. Ta kusan sake shafe mintuna talatin tana wannan nazari da ?ar ?aramar ?wa?walwarta da ?uruciya ke ?awainiya da ita. Daga ?arshe ta mi?e bisa yarda da shawarar da zuciyarta ta ?orata akai.
?akin nasa ta nufa tai knocking, ta kusa tsayuwar mintuna biyar baiyi ko tariba daga ciki, sai da ya gama shan ?amshinsa sannan ya bata iznin shigowa. Mamaki yay bala'in kama Adawiya ganinsa kwance a saman gado yana danne-danne a laptop, tsabar wula?anci ashema yana jinta ba kamar yanda tai tunanin ko wanka yakeba.
Amma sai ta danne zafin da taji bisa koyarwar Maman Aaida, da kuma son da take masa da akoda yaushe yake hanata ganin laifinsa. Gefen gadon ta zauna murya a sanyaye tace, "Sannu da aiki Yah Ab, nifa na zata koma bakajin da?ine naga yau baka fitaba".
Sai da yaja wasu sakkani kafin yace mata "Sannunki kema" a ta?aice. Duk da hakan bai mataba saita daure bata karayaba, ta sake cewa "Yah Ab wlhy kewar Aymah nakeji dasu Amal, dan ALLAH ka bani aron wayarka na kirasu mu?an gaisa".
Sunan Nu'aymah data sanyane ya sakashi ?aga ido ya kalleta a karan farko, saita narke fuska harda tara ?walla a cikin idonta. Karan farko da tun zuwansu ta bashi tausayi, dan shi?in shaidane bisa sha?uwarta da Nu'aymah. Ya ?an sauke ajiyar zuciya yana girgiza mata kai. "Ni bazaki kira kowa da wayataba".
Hawayen da take ma?alewa suka silalo mata saman kumatu, ta haye gadon sosai kusa da shi, "Yah Ab dan ALLAH ka taimakeni, wlhy ina kewarsu musamman Nu'aymah. Ni tunda nake ban ta?a sati bama tare ba wlhy. Amma yanzu gashi har ana neman ?ulla shekara, wata takwasfa kenan ana shirin shiga na tara. Yah Ab miyasa wai kuke son rabani da itane? Kumata uziri akan laifin ta dan ALLAH, nasan tayi kuskure amma ajizancine. Yah Ab dan ALLAH kabar fushi da ita haka nan ka yafe mata".
Kallon Adawiya yayi cikin ido, kafin ya ?auke yana jan ?aramin tsaki. "Ni na ta?a gaya miki fushi nake da Nu'aymah?".
Saurin ha?iye yawu tayi jin zata saki layi, tace, "A'a baka ta?a fa?aba, to amma yanda ko maganarta bakayi, baka kiranta ai dole zan fassara haka. Yah Ab inhar zaka yafema Nu'aymah namaka al?awarin saina sake farauto maka soyayyarka a ranta. Ko wanene shegen Ameer ?in nan saita barsa da izinin ALLAH. Kaga tunda Yusrah bata tare ba ita saika lalla?a su baba malam a warware aurenku a ?aura maka da Nu'aymah. ALLAH koni da muka tare zan iya ha?ura na barmata tunda dama akwai wanda nakeso".
Duk da bai ?ago ya kalletaba maganganunta da alama sun fara tasiri a ransa. dan kuwa cak ya tsaya daga latsa lap-top ?in yana saurarenta kawai. Kamar zaice wani abu sai kuma ya fasa ya kalleta. "Miya hanaki zuwa makaranta yau?". ya jeho mata tambayar bisa ?o?arin kauda wancan zancen na farko.
Baki ta tunzura masa gaba tana matso hawaye, "Banajin da?i, kuma kewar su Nu'aymah na damuna. Ni wlhy idanma ba tare da itaba karatunma jakanta zantayi harsai an maidani gida ko an kawota nan munyi tare".
Karan farko a tarihin zamansu ya sakar mata murmushin da rabon data gansa tunkam a maida auransa kanta. Ya kai hannu ya lakace mata hanci yana fa?in, "A kawota nan ku hautsinamin kai da rashinjin ku". Wani da?ine ya lullu?e Adawiya, ta ?yal?yale da dariya tana gyara zama da fadin. "Wlhy Yah Ab harma ka tunamin wani abu, akwai wata tsiya da muke tafkama Hajjo ni da Aymah har yanzu bata ta?a saniba".
Tashi yay zaune sosai ya zuba mata idanu alamar bata duka hankalinsa yana saurare. Aiko hakan ya kuma tsundumata a kogin farin ciki ta shiga bashi labarin rashinjin da sukema Hajjo dama na makaranta. Tun yana iya murmushi kawai harya ware yanata kwasar dariya. Dan rabin iya shegen nasu duk Nu'aymah ce oganniyar yinsa. Cikin ?an?anin lokaci ya ware yana magana da bata labarin Shima abinda Nu'aymah kan masa wataran. Ya shiga bu?o mata videos kala-kala nata ita da Nu'aymah suna rashin ji batare da tasan wanene yake ?auka yana tura masaba.
Hummm ashe kan Adawiya na ja????????.
_________________________________
Tunda suka bar police station ?in waya yake da Rich.. Ya sanar masa cewar ya gama masa booking jirgin tafiya Kenya, hakama wanda zai biyo daga nan kano ya dawo Lagos ?in.
Magana yayma driver da ke shirin ?aukar hanyar Abuja akan suje airport. Duk da sunji wayar da yakeyi shi da Solomon da har yanzu haushin Nu'aymah bai barsaba shima, sai dai hakan bai musu da?i ba. Dan sunso ace Abujar za'a koma ko hakan ya taimakesu wajen Madam Chioma da Papa da sukasan sunacan suna jiran isowarsu da Nu'aymah.
Suna isa Airport ?in ya sallamesu akan su tafi kada suyi dare a hanya, su kuma shi da Solomon zasuyi zaman rabin awa na jiran jirgi.
Jiki a sanyaye sukai musu sallana da addu'ar a dawo lafiya suka fito daga airport ?in. Yoohan da duk yake a galabaice da gajiya da yunwa ya ?o?arin kiran papa suyi magana dan baya bu?atar kuma wani abu makamancin hakan ya sake tasowa. Sannan ya lura da tsoron dake a fuskokin Guards ?in nasa harma Solomon dake a tare da shi. Irin kuma wannan tsoron suka baro d.p.o da shi shima.
Duk da yanda papan ke masa wayar cike da ?oki ga Yoohan ba haka bane. Sama-sama yake bashi amsar duk tambayar da yay masa wadda gaba ?ayanta akan lafiyarsace.
Sai da ya bari papan ya kammala kafin yay masa magana ta nutsuwa akan case ?in Nu'aymah, ya kuma nuna fushinsa sosai akan matakin da papan yaso ?auka akan ?aramar yarinyar da ko hankali bata gama mallaka ba.
Daga can sai papan ya danne nasan haushin ?ata masa shiri da Yoohan ?in yayi akan Nu'aymah ya koma lallashinsa dan baya ?aunar fushin ?an nasa kamar yanda Madam Chioma ta tsana itama. Ya jima yana lallashinsa dan har lokacin da jirginsu ya gama shirin ?aukar masu tafiya sannan sukai sallama. Wayarce ma ta ?auke hankalin Dr Yoohan daga uwar yunwar dake cin hanjinsa da gajiya..............?
Ku ?ara ha?uri dani fa dai dan ALLAH ????.
_____________________
SAHFAT PREORDER!
______________________
Wani kaya sai amale ka ?auka??.
SAHFAT PREORDER maida tsohuwa yarinya.
Kaji masu kawo kayan adon gida dana jiki ?an gaske.
*_Ina mata masu ?an bana bakwai? ko uwargidar da ake shirin kawoma ?ar bana bakwai?. Kai hardama matan gayu ?an ?walisa masu son sabunta gida da kayan ado ?an waje masu sau?in farashi da nagarta!._*
_To ku garzayo dama ta samu, dan SAHFAT PREORDER sune na ?aya a wannan fanin. Idan kayan kitchen kikeso masu ?yau da nagarta a farashi mai sau?i kuma zaki samu a Sahfat preorder. Idan kayan sakawa kikeso na manyan mata ?an gayu suma akwaisu babu ?ayarya. Jaka ko takalma na nunawa tsara suma ba'a barsu a baya ba harma da mayafai. Hakama kayan ?aki basu da tsara_.
Ni shaidace domin dukkan kayana ta hannunsu nake samu nima. Ku garzayo kuma a dama daku dan nasan zakuyi alfahari da hakan insha ALLAHU.
Kiyi magana ta wannan Number 08142957548 insha ALLAH zaki samu ?arin bayani ?ar uwa.
*_Siyen nagari??, maida ku?i gida?? sai SAHFAT PREORDER??????????_*
_____________________________
ZAFAFA BIYAR 2021
_______________________
Hafsat miss xoxo??
KIBIYAR AJALI......!
(Sulke baya tareta saita gitta).????
Mamu gee??
MIN ?ALB!!????
Hafsat rano??
ABINDA KE CIKIN ZUCIYA...!!????
Safiyya huguma?? SIRA?IN RAYUWA????
Bilyn Abdull??
SARAN ?OYE????
Duka akan farashi mai rahusar gaske.
Kamar haka????????
?aya___300
Biyu____400
Uku_____450
Hu?u____500
Biyar_____700
Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki????
ACCOUNT NO 0812652655
ACCOUNT NAME- HAFSAT LAWAN GAMBO
BANK NAME: ACCESS BANK.
saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)????
0903 234 5899
IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU????
09033181070
????????????????????
TEAM----ZAFAFA BIYAR????????
ALLAH ka gafartama iyayenmu??????.[3/30, 1:19 PM] +234 901 860 0202: *_INA MASU NEMAN INDA ZASU SAMU INGANTATTUN:_*
*_HERBALS APHRODISIAC NA GARGAJIYA BANA HADIN BATURE BA MAI SIDE EFFECT..?_*
*_TO KU SAURARA KUJI, DOMIN NESA TAZO KUSA.._*
*_ZEE HERBALS APHRODISIAC!_*
*_ZEE HERBALS APHRODISIAC!!_*
*_ZEE HERBALS APHRODISIAC!!!_*
*_MUNZO MUKU DA INGATTTUN KAYAYYAKI WANDA ZASU GYARA CIKI DA WAJE_*
*_MUNADA SUPPLEMENT MASU GYARAN JIKI DANA FATA, WANDA ZASA SAKI KIYI SHEKI FATAR KI TAYI LAUSHI. TAYI LUWAI! LUWAI! TAMKAR TA JARIRAI_*
*_AKWAI SUPPLEMENT NA KAYAN MATA WANDA ZASU GYARA KI, KIJI KI TAMKAR BUDURWA, SUPPLEMENTS DINMU BASU DA SIDE EFFECT, DOMIN AN HADO SU NE DAGA INGATTATTUN ITATUWA, WATO NATURAL PRODUCTS NE ACIKI._*
*_KAI BA ANAN KADAI MUKA TSAYA BA, MUNA DA INGATTUN KAYAYYAKIN MATA WANDA KESA KISHIYA KWAFA, WANDA DUK INDA SARAUNIYA TAKAI KIN WUCE, WANDA ZASU TSATSO MIKI MARTABAR KI DA KIMAR KI_*.
*_AKWAI INGATTATTUN MAGUNGUNA, NA CUTUTTUKAN DA SUKA SHAFI DAN ADAM DAMA JINNU.. KAI DAMA WANDA BAMU AMBATA BA.. ZEE HERBALS APHRODISIAC (MASARAUTAR INGATTATTUN MAGUNGUNA KENAN)_*
*_KYAU, ARHA, INGANCI, RAHUSA... SAI ZEE HERBALS APHRODISIAC_*
*_MANHAJOJIN MU NA SOCIAL MEDIA: KAMAR INSTAGRAM DA WHATSAPP DAMA NAMBAR TARHON MU: DOMIN SHIIGA KUGA IRIN KAYAYYAKIN MU TUNTUBE MU TA_*
_INSTAGRAM LINK DIN MU:_
www.instagram.com/zeeherbalsaphrodisiac
_WHATSAPP LINK DIN MU:_
https://Zeeherbalsaphrodisiac.whats.bz
_NAMBAR TARHON MU_
08169380189
*_KARKA BARI A BAKA LABARI GWARA KA BAYAR.. KIZO A DAMA DAKE YAR UWA, KI ZAMO DAYA DAGA CIKIN KASAITATTUN MATA MASU AJI.. MUNA GARIN KATSINA, SANNAN KAYAN MU MUNA BADA SU AKAN FARASHIN SAYA 'DAI DAI KO SARI.. MUNA TURA KAYANMU A KO'INA A FADIN NAJERIYA._*
__________________________________
Mo. 18
..............Ran papa na zafi da ?una ya ajiye wayar, hakan da yay ya sake fahimtar da Madam Chioma cewar akwai damuwa.
"Lafiya Daddyn Yoohan?". Ta fa?a da yarensu cike da za?uwa. Banza yay mata kamar bazai tankaba, sai da yaja tsahon lokaci kafin ya sanar mata yanda sukayi da Yoohan ?in. Itama abin ya sosa mata rai, amma saita bama mijin nata shawara akan ya barshi kawai. Karkuma su sake ?aukar kowanne irin mataki akan yarinyar har sai Yoohan ?in ya manta da zancen sannan.
Wannan shawarar ta masa da?i sosai, harya kai ga jawota jikinsa ya rungume yana kissing ?in wuyanta. Fakar idanunsa tai ta zuba masa harara tana yamutse fuska da?an turesa daga jikinta irin kamar da wasa ?in nan.
Shikuma ya?i ya bari saima ?ara wuta yakeyi. "Darling!" ta fa?a tana fisge jikinta da ?an fushi, ganin ya saketa kuma saita ?yal?yale da dariya tana mi?ewa ta nufi ?ofa da gudu tana fa?in wai ta masa wayo. Mi?ewa yay zai bita ta ida ficewa da gudu taja ?ofar ta rufesa a ciki.
Ha?e fuska tayi tamkar an aiko mata da sa?on wani ya mutu yanzun nan tana harar ?ofar. Jitake a ranta lokaci yayi da zata fitar da abinda ke ranta tsahon shekaru. Taja gajeren tsaki tana barin wajen ta nufi ?asa inda take jiyo hayaniyar su Miracle dake casar rawa a falon sun ?ure ki?an daya kara?e gidan.
________________________
*_SAUDIA_*
Shirin Adawiya ya saka suka wuni cikin da?in rai yau ita da Abdallah. Dan dakansa ya sakata tai musu girki kamar yanda tai masa al?awarin yimasa irin girkin da Nu'aymah tafi iyawa kuma tafi so. Shiko