Showing 78001 words to 81000 words out of 325075 words

Chapter 27 - SARAN-BOYE COMPLETE

20 Jul 2024

29151

Adawiya canja hanya tayi, inkuwa hakane ai itama tanada wayonta, dan wani abun ma sai dai ta koyama Adawiyar duk da kuwa ta girmeta da wasu wattani. Sake tahowa tai da ?an gudunta ta rungume Adawiya tana fa?in, "Afuwan habibiya, surprise nai niyyar miki shiyyasa na hana kowa fa?a miki".
Le?e Adawiya ta cije dan ta juyama su Hajjo bayane, itama cike da ?acin zuciya ta rungume Nu'aymahn tana magana cikin kuka, "ALLAH saina hukunta ki tunda kika sani kuka". Nu'aymah tai dariya hawaye na sakko mata itama, ta ?ago Adawiyan daga jikinta tana dur?usawa gabanta da ri?e kunnuwanta, "Afuwan hassanata, kaina bisa wuya Please".
Karan farko Adawiya ta saki dariya, itama sai ta dur?usa kamar yanda tayi sunama juna kallon ido cikin ido, Nu'aymah murmushi takeyi, Adawiya kam ta ha?e fuska ganin su hajjo basa ganinta. "Kin ha?ura kenan?" Nu'aymah ta fa?a tana wani ?age ma Adawiyar gira ?aya da sakin mata lallausan murmushin da yay mata tsaye a ma?oshi.
Kasa magana Adawiya dake mata kallon tsantsar takaici da haushi tayi, sai kawai ta rungumeta a jikinta tana gya?a kai........
Gyaran Murya Yah Ahmad yay yana fa?in, "Kunga malamai ya isheku haka, ku barmu mu ?arasa ?ar yunwar azuminmu da sauran yawu a baki dan ALLAH, idan akasha ruwa komaima sai kuyi zamu tayaku da sulhu".
"Fa?a musu dai". Abdallah ya fa?a a wani irin yanayi yana komawa kusa da hajjo ya zauna. ?aramar dariya Hajjo tayi kawai tana ?auke kanta, sai kuma ta kalli Abdallah tana fa?in, "Kaga Audillahi kaini ?akina na huta kaji, bazan iya luguden la??a ba da azumina a baki".
Fuskarsa ?awace da murmushi ya mi?e tare da taimakama hajjon itama ta tashi. Har ?akin da zata zauna ya rakata, tana zama Nu'aymah na shigowa itama. Duk kallonta sukai shi da Hajjon, ta ajiye jakarta tana zama a kujerar dake a ?akin ?waya ?aya tal, batare data kalli Abdallah ba tace, "Yah Ab! Ina yini?". Kallonta yay a karon farko suka ha?a ido, sai ta ?auke nata gefe tana komawa jikin kujerar ta jingina.
"Kunzo lafiya?". Ya amsa mata shima cike da basarwa, dan haka kawai yanzu yakejin zafin abinda ta aikata a ranar ?aurin aurensu. ?in sake tanka masa tayi, hajjo kuwa tamayi kamar bata a ?akin.
?ofa ya nufa dan kai Ahmad nasa masaukin yana fa?in, "Ki taso ki koma ?akin Adawiya, ita hajjo sai ta zauna anan...". Kafinma ya rufe baki cikin sauri tace, "A'a zan zauna anan tare da Hajjon".
Da ga Hajjo har Abdallah kallonta sukai, amma saita ?auke kanta tana ?ata fuska danma kar Hajjon tace dole sai taje. Shima har zai sake magana sai kuma ya fasa ya fita kawai.

"Miyasa bazakije can ?inba? Bayan ?ar uwarki na cike da ?okin ganinki?". Hajjo ta fa?a bayan ficewar Abdallah.
Nu'aymah dake ?o?arin cire kayan jikinta tace, "Babu komai Hajjo, nafison kawai na zauna da ke kodan himma akan ibadar da mukazoyi, sannan nifa ma ittiqafin zan shiga insha ALLAH".
Murmusawa Hajjo tayi kawai tana ?auke kanta batare da ta sake cema Nu'aymah komai ba, itama Nu'aymahn sai ta shige bayi abinta batare data jira amsar hajjon ba.

¡ï¡ï¡ï

"Kuturun ubancan kayyasa! Yanzu wane algungumine mai wannan shirya tafiyar a gidanmu?". Adawiya daketa faman zagaye ?akinta ita ka?ai ta fa?a tana cizar la?e kamar zata hudashi. Ganin babu mai bata amsa ta rarumo waya ta fara neman maman Aaida. Bugu biyu kuwa ta ?aga. Harta fara tsokanarta Adawiyan ta katseta da fa?in, "Maman Aaida yanzu ba lokacin wasa bane, ko kinsan sister ?in nan nawa da zata auri Yah Ab da, ta biyo kakarmu sunzo Umrah tare?".
Da ?arfi Maman Aaida tace, "Na shiga uku, da gaske dan ALLAH?". Adawiya da ranta ya ?ara dugunzuma tace, "Wlhy kuwa. Bama zuwan nata bane tashin hankalina Maman Aaida, kinga kuwa yanda Yah Ab duk ya susuce, gashi kakarmu ?in nan shegen sa idone da ita wlhy".
"Tab, lallai aiki ya samemu, dan kuwa wlhy mukai sanya to ki tabbatar nanda wata ?aya ko sati biyu ma mijinku zai koma na mata uku...."
"ALLAH ya kiyaye" Adawiya tai saurin katse Maman Aaida hawaye na ziraro mata a idanu. Takaicin maganganun maman Aaida ya sakata katse kiranma gaba ?aya tai wurgi da wayar kan gado.
Abdallah dake ?o?arin shigowa ?akin yace, "Lafiyarki kuwa kike wurgi da waya? Kamar ba ku?i akasa aka saya ba!". Da sauri tasaka hannu ta share hawayenta, kafin ta nufesa ta rungume da ?arfi. Saurin tureta yay yana fa?in, "Haba Adawiya, shin wai kina mantawa muna azumi ne? Duk hanyar da zaki raunanama mutum azumi kin santa".
"Kayi ha?uri Yah Ab, wlhy ?okin zuwan Nu'aymah ne ya sakani yin hakan".
"Umyim! Kina ?okin zuwan natane kika barta tafiya ?akin da Hajjo zata zauna ta sauka". Kamar zatai kuka ta kallesa, acan ?asan ranta kuma tamkar ana babbaka wuta, cikin shagwa?a tace, "Damafa jira nake kazo na kawo maka ?ararta ALLAH, nayi-nayi tazo mu zauna anan ta?i, wai batason shiga ha??inmu".
Kafeta yay da idanu kamar mai nazarinta, sai kuma ya ?auke kawai yana ?a?a kansa ya fice batare daya bata amsa ba.
Harara ta raka bayansa da shi harya fice, taja gajeren tsaki, 'Wlhy tunda aka munafunceni sai yarinyarnan ta gwammaci ki?a da karatu a gidan nan, ni kama ?aramin haske akan dawowarta ?akin nan Yah Ab, dan wannan itace babar damar da zan ri?e wajen tarwatsa zuciyarta, saina maidata mahaukaciyar gaske idan da ?aramin haukane a kan nata mtsoww!! Aikin banza kawai'.


Oho, ita Nu'aymah ma batasan tanayiba, dan bata sake le?o falonba har lokacin shan ruwa ya ?arasa, itama Adawiya bata shiga inda sukeba ta ma?ale akan shirya kayan shan ruwa takeyi. Duk da kuwa ba ita ta girkaba. Fita Abdallah yay ya musu order ?in komai daya dace, dan yasan Adawiya bazata iyaba ita ka?ai tunda sunada yawa. Bai kuma kamata asa Nu'aymah shiga kitchen ba daga zuwansu.
Aikin da Adawiya tayi kawai shine shirya abincin a tsakkiyar falo, wanda saida Abdallah ma ya tayata suka tsara komai a inda ya dace.

Koda aka kira salla ruwa da dabino kawai suka ?anci, sannan suka gabatar da sallar magriba. Daga hajjo har Nu'aymah basu za?eba akan abincin, sukai zamansu gefe suna tsumayen tayi daga Adawiya. Itako hankalinta ma baya garesu, tana can tana ?ullama zuciyarta abinda zata aikata a wajen shan ruwan idan an zauna danta cusama Nu'aymah takaici. Shiyyasa ta fara ?o?arin shiryama Abdallah nashi tunkafin su shigo.
"A'a Hajjo ya naga baku fara bu?a bakin ba?". Abdallah da ke ?o?arin ?arasowa cikin falon sosai ya fa?a idonsa akan Nu'aymah dake danna waya. Wando da rigane marasa nauyi a jikinta, sanin basu ka?ai bane ya sakata ?oro hijjab a sama wanda yaje mata har gwiwa.
Murmushi hajjo dake kallon Adawiya cike da nazari tayi, sai kuma ta maida kallonta ga Abdallahn tana fa?in, "Ku muke jira mana, dan zaifi da?in ci ai". Cike da jin da?i ya kama hannunta ya sumbata, kafin ya zauna kusa da ita yana gaisheta da mata barka da shan ruwa. Nu'aymah dake a ?ayan gefen Hajjo itama tace, "Barkanku da shan ruwa". Ahmad dake ?o?arin zama kusa da Abdallah ne kawai ya amsa, sai hajjo data ?wace wayar tana harararta da fa?in, "Sai yanzu kika san damu?".
"Waini miyasama na biyoki?". Nu'aymah ta fa?a cikin haushin amshe mata waya tana tura baki cike da shagwa?a. Hajjo da Ahmad sukai dariya, hajjo tace, "Tambayi kanki mana, ja'ira kawai".
Adawiya da abun sam bai burgetaba, ta kalli Abdallah da gaba ?aya hankalinsa akan Nu'aymah yake. Haushine ya sake turni?eta, murya a cinkushe tace, "Yah Ab ga abincinka". Kallo ?aya yay mata ya ?auke kansa. "Gasu hajjo da suke ba?i baki ha?a musuba sai ni da ko shigowa banyiba........?"
Katseshi Hajjo tai da fa?in, "Kaga barta, ai abincinma so nake a ha?esa a babban tray mu ha?u tare mu sami ladan juna".
'Tab?i jan' Adawiya ta fa?a a ranta tana jin wani tu?u?in ba?in ciki, a fili kuwa sai ta kafe Abdallah da ido a zatonta ko zaice wani abu. Duk da ya ganta sarai baice uffanba, saima ?auke kansa yay abinsa.
Hajjo da duk take lura da motsin kowa tace, "Zainabu zuba abincin, ki ha?e da wanda Adawiya ta zuba duk a ha?u kowa ya saka hannunsa".
Murmushi Nu'aymah tayi a karon farko, ta gyara zamanta tana fa?in, "Angama Hajjaju uwar masu gida, uwar gida ran gidan malam Hashimu ?an jibiya".
Sosai Abdallah, Ahmad da Hajjo suka sanya dariya da kirarin na Nu'aymah. Hajjo ta ran?washeta akai tana fa?in, "Ja'ira". Adawiya kam wani ba?in cikine ya kumeta a rai, harta kasa daurewa ta mi?e.
Abdallah yace, "K kuma ina zaki?". Da ?yar ta iya ha?iye kukanta tace, "Zan ?akko abune a kitchen". Bata jira amsarsa ba tai gaba.
Wani shegen murmushi Hajjo da Nu'aymah suka saki, wanda kowa da manufar nasa.

Hawaye sosai Adawiya tayi a kitchen, sai dai gudun kar wani ya biyota yasata saurin wanke fuskarta ta ?akko ruwa ta fito.
Koda ta dawo babu wanda ya tanka mata, saima ?o?arin kai abinci suke a cikinsu. Yayinda Abdallah duk Motsin Nu'aymah na gunada ne a idonsa. Itama Nu'aymahr dai hankalinta na a kansa. Sai dai tana ?o?arin fuskewa ita babu mai ganeta.

A haka dai suka kammala bu?a bakin, yayinda kowa yaci komai dai-dai misalin da bazai cutu ba. Duk da akwai gajiya tattare dasu haka suka rarrafa zuwa massallaci sukai isha'i da asham. Kafin su dawo kowa ya nema makwanci.
Abin mamaki sai ga Adawiya tayi shiri ta tafi kwana ?akin Abdallah.

(??ta wajena Adawiya gara ki dage ki samu kan, gaskiya fa, dan naga su o'e anzo saudia da shirin Snatching mijin mutane.????????)

_______________________________
*_NIGERIA_*

"Wai tunanin mi kiketayi ne haka da zurfi Darling? indai akan Yoohan ne na samo mana mafita".
Da sauri Momy ta juyo tana kallon papa da ke maganar da yarensu, bakinta har ?an rawa yake wajen tambayarsa wace irin mafita ya samo?.
Sai da ya rungumeta kafin yace, "Mu lalla?ashi ya auri Miracle kawai". A wani irin zumbur ta mi?e zaune tamkar wadda maciji ya sara. Ta nuna Papa da yatsa tana fa?in, "Kasan mi kake fa? kuwa Darling? duka-duka shekarar Yoohan ?in nawa da kake maganar yay aure? Indama son Miracle ?in yake to da sau?i, amma kana ganin yanda yake mata a gidan nan ai ko".
Tsuru papa yay yana kallon yanda matar tasa ke masifa kamar zata ha?iye harshenta, sai da takai ayar zancenta tana wani huci sannan yay saurin jawota jikinsa yana girgiza kansa. "Ki fahimceni mana, idan Yoohan yay aure matarsa zata dinga ?ebe masa kewa a duk lokacin da ya shiga irin wannan damuwar, kum......."
"Kaga nifa bani da lokacin wannan maganar, ka barni barci nakeji". Ta fa?a ranta a ?ace da ?wace jikinta taje gefen gadon ta kwanta. Da kallo kawai ya iya binta har na tsahon lokaci, kafin shima ya kwanta ?in yana sauke tagwayen ajiyar zuciya. A cikin ransa kuwa ya ?udiri aniyar lalla?ata ita da Yoohan ?in har sai sun amince da ?udirinsa.

*_WASHE GARI_* safiyar lahadi, tunda safe jama'ar gidan suka shiga hada-hadar shirin fita church, dan papa ma tun da sauran duhun safiya ya fice shi.
Rich daya fito wanka ya kai dubansa ga Yoohan dake zaune kan sofa, ?afafunsa mi?e akan table, ya jingina bayansa kansa na kallon sama. Duk da idanunsa a lumshe suke ya tabbatar ba barci yake ba.
"Doctor ya kamata ka tashi kai shiri mu shiga church ko? Idan mun fito sai mu ?an zaga gari danni yau da yamma zan koma Lagos".
Shiru Yoohan bai motsaba, duk da kuwa sarai yanajin Rich ?in. Sai da ya ?ata wasu mintuna kafin ya bu?e idanunsa da sukai wani irin kumburowa, fatarsu tayi jaa sosai alamar jin barci tattare da shi, hakama fuskar tayi jajur sosai abin tausayi. Mi?ewa yay batare da yayi magana ba, ya wuce toilet yana ?an ?ingisa ?afarsa da bata gama sakiba, sai dai hakan kuma sai ya bama tafiyar tasa wani style daban kamar mai tafiyar izza.
Baija dogon lokaciba ya fito ?aure da towel ruwan gwaiduwar ?wai. Babu kowa a ?akin dan Richard ya gama shirinsa ya fice. Ya ?arasa gaban mirror, shafe jikinsa yay da mai da kayan ?amshi tamkar yanda ya saba, kafin ya nufi wajen kayansa. Fararen suit ya ?akko yana ?an yamutsa fuska da kallonsu. Sai kuma yabar wajen dasu zuwa gaban gado. Tsaf ya shirya a cikin suit ?in da sukai masifar zama masa a jiki, tare da fiddo surarsa mai jan hankalin mata dama mazan kansu. Necktie ?in ya ?auka a hannu tare da jacket ?in suit ?in, dan shi kam har yanzu ?aura tie na masa wahala. Gaban mirror ya sake komawa ya feshe kansa da kalolin designers ?in turarurrukansa, kafin ya ?au sar?a ?aya a cikin sar?o?insa na Cross da taji zallar diamond tanata ?aukar idanu ya saka. Ya ?auki agogo ya ?aura tare ?an wani abin hannu na gayu ya ?aura a ?ayan hannun, ya kuma manna ?an kunnensa a kunne ?aya. Yayi ?yau sosai, duk da kuwa fuskar a tur?une take matu?a. Amma yanda yau ya gyara kansa da sajensa sai yay ?as da shi kamar ka suresa ga gudu.

Tun fara sakkowarsa daga benen Mom da Rich, Solomon dake a falon duk suka zuba masa idanu, sake ?aure fuska yayi yana ?arasa sakkowa. Saurin tararsa Solomon yay da kofin coffee daketa turiri akan tray, yace, "Good Morning sir". Kansa kawai ya ?aga masa yana gya?a kai, tare da ?aukar coffee ?in ya nufi Mom da ta tsatstsaresa da idanu tun sakkowar tasa, sai dai fuskarta sam babu walwala. Tayi ?yau sosai abinta tamkar zata gasar sarauniyar ?yau. Necktie ?in hannunsa ya mi?a mata batare da yayi magana ba, saima kofin coffee ?insa da yakai baki yana cur?a kamar bayaso.
Tsaye ta mi?e, duk da ya fita tsaho, amma da yake tana kan tudun dining ne saita samu damar kaiwa wuyansa cikin sau?i. ?aura masa tie ?in tayi, tare da amsar jacket ?in ta koma bayansa. Hannunsa guda ya mi?a mata ta saka masa, ya sake mi?a ?ayan ma ta saka, sannan ta zagayo gabansa tana gyara masa da ?yau.
Ta ?an saki murmushi tana masa wani narkakken kallo, kafin takai hannunta saman fuskarsa ta shafa kwantaccen sajensa dayin magana ?asa-?asa kamar mai ra?a. ?anja baya yay yana zame hannunta, murya a cinkushe yace, "Thanks Mom".
Kafin ta samu damar yin magana ?annensa dake fitowa cikin nasu gayun suma suka shiga gaishesa ?aya bayan ?aya. Hannu kawai yake iya ?aga musu yana cigaba da shan coffee ?insa cike da basarwa.
Ganin yanda Mira ke binsa da wani shu'umin kallone ya sakashi mi?ama Solomon kofin duk da bai ?arasa ba, batare da yayima kowa magana ba ya nufi hanyar fita abinsa cike da takun nutsuwa da ?asaita sai kace wani jinin mulki.
Dukansu baya suka take masa, yayinda Gebrail yay saurin kaiwa inda yake yana ri?o hannunsa. Batare daya kallesaba yace, "What happend?". Murmushi Gebrail yayi yana susar kai, cikin ?an in ina yace, "Brother Yoohan ku?i nakeso Please".
Yoohan baice komaiba, ya zare hannunsa daga cikin na Gebrail ?in, ?arasawa yay jikin motar da yaga Rich tsaye yana waya. Da sauri ?aya a cikin Guards ?insa ya bu?e masa yana gaishesa. Hannu kawai ya ?aga mar ya shige. Richard ma shiga yay ta ?ayan gefen, Solomon da driver ma suka shiga. Cike da ?oki Gebrail da yasan matsalarsa ta yanke ya shiga motarsa shima tare da su Mira da taso bin motar Yoohan ?in. Sai dai ganin Rich datai tunanin ba a gidan ya kwanaba da, ya sakata ha?ura ta shiga ta Gebrail ?in ita da joy.

Motocin na gama fita a gidan Yoohan ya zaro wayarsa dake cikin aljihu, transfer ?in ku?i masu yawa yayma Gebrail tamkar baisan ciwonsu ba, kafin ya ajiye wayar gefensa ya maida kansa ya jingina da kujera ya lumshe idanunsa.
Har motocin suka tsaya a katafaran church ?in da papa ke


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login