Showing 177001 words to 180000 words out of 325075 words

Chapter 60 - SARAN-BOYE COMPLETE

20 Jul 2024

29190

aiki tunda nasan can gidan bazasu zauna babu ma'aikata ba".
"Eh duk da haka dai a nema mata. Koba komai zata samu yarenta a cikinsu, ko wani abinne ya dameta ta fa?a mata kafin mu mu sani. Shiyyasama nake ganin ko ha?ura zakiyi ki bata Rabi'atu, tunda kinga ta saba da ita sosai, akwai shakuwa tsakaninsu sannan ita?in ba yarinya bace zata taimakamata da shawarwarin zaman rayuwa".
"To ban?i ta taka ba Abban Nu'aymah. Sai dai kasanfa ko sanda Nu'aymah na gidan nan ba shan inuwa ?aya sukeyi da Rabi ba. Inaga ka fara tambayarta idan tanason a bata ita sai taje. Idan bataso sai a aika mata wata ?in. Dan kasan halin butsutsun yarinyarka ?in nan ba man kai ne da ita ba sam".
Dariya baba malam yay tayi da zancen matar tasa. Daga haka suka cigaba da firarsu duk kusan kashi biyu na firar akan Nu'aymah ne. Da kaji kasan cike suke da kewar ?iyar tasu da begenta. Sai dai dattakonsu ya danne komai suna binta da fatan alkairi a zuci da fatar baki.....

*_ABUJA_*

Nu'aymah bata sake ganin Yoohan ba ko wani a jama'ar gidan har washe gari. Dan tunda ta shiga ?akinta bayan barowa wajen su papa saita kulle harda murza key. Littatafan ta na islamiyya da aka zubo mata cikin kaya ta ?auka taita dubawa a hankali har lokacin barcinta yayi ta kwanta.
Washe gari tunda tayi sallar asuba bata koma ba. Gyara ?akinma tayi har toilet, rashin sabo da zaman ya sata sha'awar fitowa falon shima dan ta ?an gyara ko ta ?arajin ?arfin jikinta ta kuma ?an rage kewa. Tana bu?e ?ofar ?akin nata shima yana bu?e tasa ?ofar............?


yanzu haka an kusa kai ?arhe, gamai bu?ata zai iya garzayawa ya biya??????.

Hafsat miss xoxo??
KIBIYAR AJALI......!
(Sulke baya tareta saita gitta).????

Mamu gee??
MIN ?ALB!!????

Hafsat rano??
ABINDA KE CIKIN ZUCIYA...!!????

Safiyya huguma?? SIRA?IN RAYUWA????

Bilyn Abdull??
SARAN ?OYE????

Duka akan farashi mai rahusar gaske.

Kamar haka????????

?aya___300
Biyu____400
Uku_____450
Hu?u____500
Biyar_____700

Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki????

ACCOUNT NO 0812652655
ACCOUNT NAME- HAFSAT LAWAN GAMBO
BANK NAME: ACCESS BANK.

saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)????

0903 234 5899

IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU????

09033181070

????????????????????
TEAM----ZAFAFA BIYAR????????*_LITTAFIN nan na ku?i ne. Dan girman ALLAH ki daure ki biya kafin ki karanta, idan kuma bazaki iya biya ba ki ha?ura domin ALLAH karki karanta. Idan kuma kin saya dan girman ALLAH karki ya?a mana????_*.

NO. 48

___________________

I'm on Instagram as yerwaincense_and_more. Install the app to follow my photos and videos. https://www.instagram.com/invites/contact/?i=ayfowzb2ah8k&utm_content=6k8ur6p

_YERWA INCENSE AND MORE _
_(Masarautar K'amshi)_

_We've got you covered with our balsamic scented products.. Yerwa scents last longer and linger.. Ba kauri irin na wa'ensu turaren, Chadian kamshi ne na gaske, Kowane irin samfurin turaren wuta munayi, traditional and modern. _

_Akwai Khumrah's kala kala. Kulaccams, Turaren wanka dana wanki dana mopping, Da tsugunno, Jiki da kaya duk muna dasu. Domin mallakar naki tuntub'e ta number shafin dake kasa, Ko kuma Ki duba shafin mu na manhajar Instagram ta: @yerwaincense_and_more. _

_Kyau, arha, inganci , sai yerwa incense. Muna tura kayanmu ko'ina a fadin nigeria da waje.. Ayi following, Da liking dinmu a Instagram handle dinmu dake sama._


No. 48

..............Kallo ?aya tai masa ta kauda kanta. Dan daga shi sai wando gajere fari dako cinyoyinsa bai gama rufewa ba. Sai singlet kalar gwaiduwar ?wai hannunta mai fa?i fiye dana singlet data sani. Shikam dai kansa tsaye yake ?are mata kallo cikin kayan barcin wando da riga pink masu taushi. Duk da basu kama mata jiki ba sun mata ?yau, musamman daya kasance kanta ko hula babu. Gashin dake a ?aure a tsakkiya duk ya zazzame a gaba ya tashi.
Cike da ?osawa da kallon ?urillar da yake matan tace, "Good morning". Kamar dama abinda yake jira kenan. Ya janye idanunsa daga kanta yana sakin handle ?in ?ofar da fa?in, "How are you feeling now?". "Alhmdllh". Ta amsa dai-dai lokacin da yake tura glass ?in dake bangon kudu a falon ?ofa ta bayyana. Ita duk zatonta ma an sakashine kawai domin ado. Amma sai taga ya shige ?ofar ta koma da kanta ta rufe. Shiru tayi tana ta kallon wajen kamar wata sokuwa.......
"Good Morning Maa!".
Aka fa?a a bayanta. Da sauri ta juyo danjin muryar gardi. Solomon dake ta wani ?ata fuska yay saurin sunkuyar da kansa ?asa bayan ya gama ?are mata kallo tun shigowarsa. Wani irin mugun takaicine ya turnu?e Nu'aymah, taya ?aton banza da shi zai shigo musu babu wani neman izini. Lallai dolene ta saitama ma'aikatan gidan nan zama, dan bazata ?auki wannan iskancin ba sam. Da ?yar ta iya ha?iye bala'in dake a harshenta. Murya a da?ile tace, "Ince dai lafiya?". "Yes maa! Zanyi sharane. Dan nine mai yima oga gyara". 'Zan saita muku layi kai da ogan ai' ta fa?a da hausa tana zuba masa harara kamar idanunta zasu fa?o. Shi dai Solomon bai ji mita fa?a ba, amma yana kallon harar da take zuba masa. Kuma harga ALLAH sai yaji wani irin shakkarta da ganin ta cika masa idanu da kwarjininta duk da kuwa inda aure yayi sai ya haifi wadda ta fita ma.
"Kaje bana bu?atar sake ganinka ka shigo mani nan, ka ajiye min kayan sharan hannuna zai iya yin komai".
"Okay maa! I'm sorry".
Banza tai masa, sai harar da taketa cigaba da antaya masa hannayenta ri?e da ?ugunta kamar mai shirin yin dambe. Kamar wal?iya Solo yabar falon. Ta dafe goshi cike da takaici. 'Shegu dangin ?an sama jannati, duk saina muku sabon kaciya tunda idonku bai iya daina kallon mutane. Yanda kasan mayu, suyi maka ?uri da idanu'.
Haka taita banbamin jaraba ita ?aya kamar wata zararriya. Ta gyara falon tsaf harma kitchen da ba komai aka ta?a yi aciki ba. Ta kwaso turarenta na ?amshi ha?in da miss xoxo tai mata ta baje ko'ina da su, (Da gaske masoya, duk mai bu?atar turarurrukan su khumrah da makamantansu ya tuntu?emu zai samu. Kuma a kowane gari kake muna aika kayanmu insha ALLAH) sannan ta ?ora da Air Fresheners ?in data gani. Yanda gidan ke tashin ?amshi tuni zai saka ka barci baka shirya yi ba. Yunwan da takejine ya sakata nufar inda taga an shirya kayan tea cikin wata drawer glass dake a dining ?in. Sai da ta gama ?arema kayan shayin kallo da su biscuits dake ciki kala-kala, sai su cornflakes, gya?a soyayya a cikin kwalabe, dabino, zuma, kayan ciye-ciye ne dai iri-iri wasuma ko ganinsu bata ta?a yiba. 'Oh ALLAH, amma guy ?innan mugun makwa?aici ne yasin. Kaga yanda ya ha?a kayan ?walama kamar wani sa'an Muhammad. Amma dai anji jiki yasin'. Tana mita tana zagurar wa?anda ta gani a bu?e tana jefawa a baki (makwadaitan sun ?aru kenan??lol).

¡ï¡ï

Sosai Solomon yaji zafin abinda Aymah tayi masa, ya kuma ?auki alwashin sai ya saita ta a layi duk da matar ogansa ce. Da wannan takaicin yaje kitchen ya amshi tatattun kayan itatuwan Yoohan ?in a wajen Blessing data kammala ha?awa. Ta waccan ?ofar yabi ya shiga Gym ?in. Inda ya tarar Yoohan ko rabin motsa jikinma baiyi ba. "Good Morning sir". Ya fa?a ransa har yanzu najin zafin Aymah. "Morning?". Yoohan ya amsa masa yana dubansa da tunanin ko baida lafiya ne. Yanzun ma cike da ?acin murya yace, "I'm Good sir". Komai Yoohan bai kuma ce masa ba. Ya cigaba da harkokin gabansa har ya kai lokacin da yake tsayawa. Towel Solo ya miko masa. Amsa yay yana furzar da huci ya ?arasa kujerar zamansa ya zauna. Solomon ya karaso ya mi?a masa juice ?in. Sannan ya ?auka remote ya kunna television.
Sai da Yoohan ya sha kusan rabin juice ?in, hankalinsa nakan program ?in yace, "Ka bama su SJ kayan dana ce?". "Sir wane kaya? Bansan ka ajiye kaya na basu ba ai". Da mamaki Yoohan ya juyo ya ?an kallesa, sai kuma ya maida ga television ?in yana fa?in, "Baka gyara min ?aki ba kenan?".
A take abinda Aymah tai masa ya dawo masa a rai. Murya a cinkushe yace, "Sir naje zan gyara Madam ta hanani. ta kuma min garga?in ma karna sake shiga sashen gaba ?aya".
"Madam? Wace madam?".
Yoohan yay maganar da tsatstsare sa da idanu. Kan solo a ?asa yace, "Madam Nu'aymah". A take ya zayyane masa duk yanda sukayi da Aymah kafin yazo nan wajensa. Ya zata zaiga ?acin rai tattare da ogan nashi, dan ya saka aiki a?i masa ko wani ya hana a masa yana ?aya daga cikin abinda ya tsana, ko madam Chioma ce sai ya nuna ?acin ransa koda ba zaiyi magana ba. Amma a mamakin Solo sai yaga Yoohan ?in yayi wani ?an munafukin murmushi yana ajiye kofin hannunsa. Batare da yace komaiba ya shiga zare takalman ?afarsa. Yana kammalawa kuma ya mi?e ya fito solo na binsa da kallon tsoro dan ya wuce na mamaki kam.

Har yanzu Aymah na a falon, dan tsabar ?warewa a ?wa?ayin da take cema wani yana yi ita kofi ma ta ?akko ta ha?a madara da zuma da yawa, tasa ruwa ?an ka?an. Ta kwaso biscuits kala-kala kusan shida tazo ta zube a dining tana faman ci da lumshe idanu. Dan babu ?arya biscuits ?in duk sunyi uwar ha?uwa.
Cak Yoohan dake ?o?arin fitowa ya tsaya kawai yana kallonta da ma?aukakin mamaki da al'ajab. Yayi tsayuwar kusan mintuna uku yana kallonta da ita da falon da ?amshinsa ke neman saukar masa da kasala kafin ya cigaba da takowa a hankali ya iso inda take. Kamar zaiyi magana sai kuma ya wuce a binsa zuciyarsa fal mamakinta. Ya tabbatar ta gansa amma ta basar.
Tunda ya tura ?ofar ?akinsa yaga yanda ya barsa haka yake sai ya juyo bai shiga ba. Wajen Aymah dake cigaba da party ?inta ya dawo. Yanzun kam a bisa tsautsayi ta ?ago kanta, dan batai tunanin shine ya dawoba duk da taji ?amshinsa sai suka ha?a ido. Saurin kauda nata tayi tana tura biscuit cikin baki.
Shikam yana tsaye hanayensa duka cikin aljihun wandonsa, cikin ?asa da murya sosai, kamar baya son yin maganar yace, "Hy Smally, tuda kin korarmin maimin aiki sai ki je ki min dan bana iya wanka a toilet ba'a wanke ba".
Kamar Aymah zata sharesa sai kuma ta kasa, dan yanda yay maganar ?asa-?asa da kiranta sumoli yaja hankalinta wajen son maida masa murtani. Sai dai kuma tana ?agowa ta sami fuskarsa a tsuke mayun idanunsa kuma ?yam a kanta kamar zasu ha?iyeta. Kumbura baki tayi da fa?in, "Wlhy niba smally bace, dan ko a yanzu dai shekarata goma sha bakwai da wata tara".
A ransa yace, 'Ai fa sai sha bakwai ?in'.
Ta cigaba da fa?in, "Kuma da kake cewa na korar maka mai aiki, ta yaya zanbar wannan ?aton gardin yana tsayamin a kai kamar wani mala'ikin dake tsaron ?ofar wuta. Baga ?annenka nan ba wani yazo ya gyara maka".
Harga ALLAH maganarta ta bashi dariya, amma sai ya danne. Takawa yay gab da ita. Hakan yasa ta mi?e zumbur tana ajiye ledar biscuit ?in hannunta, ta tura kujerar baya danta samu hanyar guduwa. Caraf ya ri?o hannunta ta fa?o jikinsa. Duk da yaji ?an zafin yanda ta fa?o masa bai damuba. Sai ma hannunsa daya ?ora akan ?ugunta ya sake matsota ta manne masa sosai.
"Ouch!! Wannan muguntar fa?". Ta fa?a tana ?o?arin ?ago fuskarta dake saman ?irjinsa gab da ha?arsa, dan har ?an gashin gemunsa na gogar gashin kanta. Kallon ido cikin ido sukaima juna. Tana ?o?arin son kauda nata amma ya hana, da wani irin yanayi yace, "Miyasa ke bakinki baya iya daina magana? Kowacce amsa kinada ita?".
"To sai in zauna a ringa cutata, ku mutane ai kunason mutum ya zama banza ku dinga takashi kamar wani tiles kuna wucewa".
Shi sam bama ya fahimtar mi take fa?a, hankalinsa gaba ?aya yana kan bakinta ne da idanunta da suka ciko da ?walla. Hakan yasa baice mata komaiba, sai saukar babban ?an yatsansa taji akan gefen bakinta. Saurin kauda fuskarta tai ?o?arin yi tana zaro ido. yayinda shi kuma ya ?aga mata yatsan yana nuna mata ?ur?ushin biscuit daya goge mata. Ha?iye abinda zata fa?a ?in tayi da ?o?arin san zamewa daga jikin nasa. Babu musu ya saketa kuwa.
Da?ar ta fa?a saman kujerar da take zaune da. "Wayyo Abbana!". Ta fa?a saboda zafi da taji.
Dafe tebirin yayi da hannu biyu ya ran?wafo kanta har tanajin saukar numfashinsa. Cikin kunnenta yace, "Silly girl, wannan shine maganin masu bakin magana kamar akku".
Hawaye na silalo mata akan fuska ta sa hannu kan damtsen hannunsa ta turesa. Fuskarsa ?auke da murmushin mugunta ya ri?e hannunta, "Tashi muje ki gyaramin ?aki kona sake ?agaki sama na dire a kujerarnan har sai........ " Sai kuma yay shiru bai ?arasa ba
Zatai magana ya ?ora yatsansa saman bakinta yace, "Shiiii!!!!". Sai kuma yaja hannunta dake cikin nasa ya mi?ar da ita. Tanaji tana gani ya jata har ?akinsa. Ganin ya nufi hanyar da take ?yautata zaton toilet ne ta tirje da fa?in, "Nifa bana shiga toilet babu ?an kwali".
Baice komaiba, sai sakin hannunta da yay ya nufi Wadrobe ?insa, sai gashi ri?e da babban handkerchief. Gani tai kawai ya warwaresa yay masa linkin ?ankwali ya ?ora mata bisa kai. Tsaf ya ?aura mata shi kuwa duk da bawai ya bu?e bane da ?yau yanda ya kamata, amma dai ya rufe gashin. Sake kama hannun nata yay zuwa cikin toilet ?in.
"Ki fara wanke nan, wanka zanyi na fita". Daga haka ya saketa ya fita.
Dubansa tayi kamar zatai magana sai kuma tai shiru dan harya gama ficewa. Tsaf ta gama bin toilet ?in da kallo, dan babu ?arya ya ha?u, gashi an zuba kayan toilet ?in irin kalar, garai-garai ?in nan kamar ?an?ara, sai dai sunfi ?an?ara duhu dan sunyi ?an kalar ash da fari-fari. Komai tsaf a tsare inda ake bu?atar ganinsa babu wani dattin da yake fa?a akansa bazai iya wankan ba. Da yake neman aikin yin take saboda jikinta da yay mata nauyi sai gashi ?ara gyarashi tsaf, kamar taje ta ?akko turaren toilet ?in da miss xoxo ta ha?a mata mai shegen ?amshi na wanke toilet sai kuma ta fasa. A cewarta kada ta cika za?ewa ya ?auka ya sameta ne a ?agas.
Fitowa tai ri?e da ?ugu alamar ta gaji, Yoohan dake zaune a kujerar dake tebirin karatunsa ya ?ago yana kallonta jin tana nishi. Dan shi a zatosa ko fa?uwa tayi a toilet ?in ma. "lafiya?".
Baki ta kumbura gaba da fa?in, "Na gaji ne, bayana kamar zai ?alle".
"Ka?anma kenan, tunda kika koramin mai mini ai". Ya fa?a yana ?auke kansa daga gareta ya maida ga lap-top ?in gabansa da yake aiki a ciki. Haushin maganar tasa ya hanata tanka masa, ta ?arasa ga makeken gadonsa ta fa?a a kai tana fa?in, "Wash Umm na gaji, nima bara na rama hawar min gado da kayi".
Mi?ewa yay idonsa a kanta. Batare da yace mata komaiba ya nufi bayi yana wani murmushin daya zo masa babu shiri. Harga ALLAH ta burgesa da tai aikin, dan baiyi zaton zatayin ba saboda sanin tsiwarta. Iyawarma baiyi zaton ta iya ba. Amma daya shiga bayin sai yagama gyaran natama yamafi na Solomon ?in.
Sai da taja kusan mintuna uku a kwance tana sha?ar ?amshinsa daya manne bedsheet ?in, kafin ta mi?e ta fara gyarawa duk da harga ALLAH ta gaji da gaske. Amma batason ya fito ya isketa. Kuma tanama bu?atar zuwa tayi wanka itama dan cikinta dam yake da ciye-ciyen da tayi.

Tana tsaka da mopping kuwa ya fito. Kallo ?aya tai masa tai azamar maida kanta ?asa ta du?ar tana ?un?unin wai mara kunya ne mutumun nan. Yasan da ita amma ya fito da towel.
Oho shi baimasan tanai ba. Dan mirror ya nufa bayan shima ya mata kallo guda ya dauke kansa. kansa tsaye yake komansa duk da kuwa yasan tana cikin ?akin. Ta gama tana fesa fresheners data gani shi kuma ya ?akko kaya zai saka. Juyowar da zatayi idonta ya sauka a kansa yana ?o?arin ?waye towel ?in. Cikin subutar baki tace, "Babbar bala'i a gabana?". Kafinma ya fahimci mitake nufi ta jefar da roban freshener ?in ta kwasa da gudu ta fice.
Da kallo ya bita


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login