Showing 21001 words to 24000 words out of 325075 words

Chapter 8 - SARAN-BOYE COMPLETE

20 Jul 2024

29169

dan girman ALLAH".
Shiru Addah tai tana sake jinjina ?yawun zuciya irin na Umm, haka take ita komai tana ?aukarsa da sau?i a rayuwarta bata zafafama kanta. Tunda abinnan ya faru babu wanda ya ta?ajin furucinta kosau ?aya akai. Ko a fuska ?o?arin ?oye damuwarta takeyi. Tausayin aminiyar tata kuma ?ar uwarta sai ya sake kamata fiye da da can.

Umm da kanta ta fita taje ta shigo da Adawiya, zaunar da ita tai kusa da Addah itama ta zauna. Su biyu suka shiga yima Adawiya nasiha kamar yanda sukeyi a duka sauran ?a?an Addah uku da aka aurar. Sumayya, Maryam, Badariyya. Sai da sukai mata nasiha sosai kafin Umm ta tashi ta fita ta bar Adawiya da Addahn.

¡ï¡ï¡ï¡ï

Kamar yanda tsari da al'adan mutanen gidan yake bayan sallar la'asar iyayen suka sake ha?uwa aka rufu kan Adawiya da Abdallah akai musu fa?a da nasiha sosai. Tare da gindaya musu sharu?a masu tsauri akan duk wanda wani al'amari mara ?yau ya ?ullo daga wajensa a cikinsu to lallai zai fuskanci ?acin rai da fushinsu sosai. Daga ?arshe aka sake musu doguwar addu'a aka sallami Adawiya da ko sau ?aya batai hawayeba da iyayensu mata.
Umm ta tafi da Adawiya sashenta danta kimtsata, suka bar Abdallah tare dasu Baba Malam da Hajjo da suka sake ?ora masa da Nasiha kasancewarsa shine babba.

?arfe 7:30pm gayyar yaran gidan harna ma'auri su Aysha sukaima Abdallah da Adawiya rakkiya airport dan jirgin 8:30 zasu bi zuwa ?asar Dubai. Sai sunyi kwanaki goma acan kamar yanda Abdallah ya tsarayi da Nu'aymah sannan su wuce Saudia.
A yanzuma dai idanun Adawiya ?ifi-?ifi babu ko ?igon hawaye a cikinsu. Hakan ba ?aramin ?ona ran Addah yayiba. Hakama Momyn Abdallah al'amarin ya bata tsoro, taita kallon Adawiyar cike da alamomin tambaya a ranta, sai dai bata furtaba.

Ko ka?an Yusrah bataji komai a rantaba, dan ko kusa bata kawo Adawiya ma a cikin matsalolinta sa?anin Adawiyar dake jin zafin Yusrah babu gaira babu sabar. Ita Yusrah dama za'a warware nata auren da tayi matu?ar farin ciki. Amma ta ?auka alwashin cigaba da addu'oi tana gayama ALLAH kukanta akan hakan kafin lokacin da akace zata tare.
Basufi zaman mintuna talati da hu?u ba aka sanar da tafiyarsu. Sai yanzune Adawiya ta?anji babu da?i a cikin ranta na kewar ?an uwanta. Amma saita fuske ta shiga binsu ?ai-?ai tana rungumarsu. Da tazo kan Yusrah saita wuce batace mata komaiba. Ba ?aramin mamaki hakan ya bama kowaba, duk suka bita da kallo har Yah Abdallahn. Tsarguwa da tai ne ganin yanda ?an uwan nata ke binta da kallon tuhuma ya sakata bu?e jakkarta ta ?akko wani abu ta nufi Yusrah, hannunta ta kama ta saka mata abin sannan ta rungumeta kamar yanda taima kowa.
A kusan tare duk suka sauke ajiyar zuciya, dan da da yawansu abun yay musu cak a ?irji hatta da ?an uwanta da suka fito ciki ?aya. Musamman Hajarah da taga abinda ya faru a ranar ?aurin auren tsakanin Addah da Adawiyan.
Sallama suka sakeyi da juna. Kafin tabi bayan Yah Abdallah da yay gaba abinsa batare da ya saurareta sun jera tareba kamar yanda taso.

"Hummm!! Wasa farin girki Adawiya??????".

___________________
NU'AYMAH
______________

Tun randa aka barota daga gida bata sake sanin halin da take a ciki ba sai washe gari da yamma. Farkawa tai a tsananin firgice. Sai dai nauyin masifa da kanta yay mata na azabar ciwo ya sakata sakin ?ar siririyar ?ara da dafe kan nata da hannu bibbiyu tana sakin numfashi a wahale.
Sake ?o?arin bu?e idanunta tai da ?yar saboda nauyin da sukai mata suma. Tabi ?akin da take ciki da kallo mai ?aracin haske, sai dai ba dun?um yakeba. Katifa ce kawai a ?aki da wasu lalatattun akwatuna guda uku kalar ruwan ?asa. Sai takalma na maza da aka jera a gefe kusan ?afa shidda. Sai hanger a jikin bango anyi hanging farar jallabiya ta maza guda ?aya da wanduna uku duk ba?a?e. Sake lumshe idanunta tai ta bu?e a hankali dabin jikinta da kallo.
Hijjabin tane dai a jikinta har ?asa da ta saka lokacin da zata fita neman wayarta. Ta kai hannu da ?yar ta laluba jikinta. Towel taji wanda shima shine tasan ta ?aura a jiyan, sai dai yanzu ya kwance duk ya zazzame daga ?irjinta ya dawo saman cikinta.
Juya mata da garin ya farayine ya sakata yin baya ta sake kwanciya a katifar hawaye masu a zabar zafi na silalo mata a saman kumatu. A haka ta cigaba da kwanciya tana zirarar da hawayen jikinta duk babu wani ?arfi. Tafi mintuna talatin da kwantawa sannan aka bu?e ?ofar.
Kasa bu?e idanu tai balle taga wanene ya shigo ?in, tsahon mintuna biyar kafin ta bu?e idon ka?an ta saukesu akan wanda ke tsaye jikin ?ofa sanye da ba?a?en kaya, hatta da hannunsa akwai safar hannu ba?ake. Hakama fuskarsa da facemask, idanunsa kawai take iya gani. Suma ganin kallon da take masa ya sashi ciro glasess ya toshesu.
Basket ?in dake ri?e a hannunsa ya tako gaban katifar ya ajiye batare da yace da ita uffanba ya juya ya fita. Maida idanunta tai da ?arfi ta rumtse zuciyarta na zafi. Kukanma yanzu sai ya kasa fita mata. Haka ta cigaba da zama a wajen har bayan mintuna kusan goma da fitarsa. Sai kuma ga mace ta shigo sanye cikin dogon hijjab har ?asa. Itama fuskarta sanye take da ni?af.
Batare da tama Nu'aymah magana ba ta kamata ta tayar. Bata da wani ?arfi ko iya yin magana, dan haka ta cigaba da bin matar kawai a yanda taso. ?ofa ?wara ?aya ?arama dake a cikin ?akin suka nufa, sai da suka shiga Nu'aymah ta fahimci toilet ne. Fas yake babu ?azanta a cikinsa, saima ?amshin omo da hypo daketa tashi.
"Kiyi wanka". Matar ta fa?a a ta?aice batare da ta jira amsar Nu'aymah ba ta fice abinta. Da kallo kawai Nu'aymah ta bita, sai dai bakinta ya mata nauyi ta gaza cewa uffan a yanzunma. Kamar bazatai wankanba sai kuma wani tunanin yazo mata. Rabonta da salla tun ta isha'in jiya. Ga shi a yanzu da alama har anyi sallar la'asar ma. Tana bu?atar ?arfin jiki sosai, hakan kuma bazai yuwuba sai tayi wankan.
Cikin ?arfin hali ta zare dogon hijjabinta da towel ?in, duk da tsaftar ban?akin a ?arare tai wankan. Taji ?arfin jikinta sosai, sai faman sauke ajiyar zuciya takeyi a jajjere. Alwala tayi ta fito tana daddafa bango, dan akwai yunwa tattare da ita.
Da mamaki ta kalli kayanta da aka ?aura a saman katifar, ta bi ?akin da kallo kamar ?azun, babu kowa sai kayan a ajiye da kuma kwanikan abincin dake cikin basket ?in suma an fiddosu ?asa an ajiye.
Bata da wani za?in daya wuce canja kayan tai sallolin dake kanta. Harta kammala rama sallolin babu wanda ya sake shigowa, ta kwanta saman abin sallar tana hawaye da tunanin ko wane hali yanzu Umm da Abbanta da Muh'd dama duka sauran ?an gidansu suke ciki a yanzu na rashin ganinta?. Yah Abdallahn ta, tasan zaifi kowa shiga tashin hankali bayan Umm da Abbanta. 'Minayi suka kawoni nan? Su wanene su? A ina nake?'. Ta fa?a a fili tana sake fashewa da kuka. Taja tsahon lokaci tana ribzar kukanta, har kanta yana masifar sara mata fiyema da ?azun. Barcine ya fara figarta na wahala. Jin motsin shigowar mutum ya sakata tashi zaune zumbur. Matar ?azunce, yanzuma batai mata magana ba ta ?akko kwanikan abincin ta kawo gabanta da mata alamar taci.
Yunwa Nu'aymah takeji sosai, dan haka batai musu ba taja abincin tahau cinsa. Taci sosai har matar tai mamakin hakan. Matar ta mi?e zata fara tattare kwanikan Nu'aymah ta kalleta cike da rashin tsoro tace,
"Su wanene ku? Miyasa kuka kawoni nan? Minai muku kuma?".
Kallonta matar tayi sosai, amma sai batace da ita komaiba ta tattara kwanikan tai ficewarta.
Tashi Nu'aymah tayi ta nufi ?ofar da sauri, sai dai tana ta?awa tajita a kulle, fashewa tai da kuka ta koma saman katifar ta sake kwanciya tana sambatun kiran Umm da Abbanta da Yah Abdallah.

Tun daga wannan ranar kullum hakan ta cigaba da faruwa, zasu kawo mata abinci sau uku a rana, matarnan zatazo ta gyara ?akin ta wanke mata bayi da kayan data cire. Sannan ta ha?a mata ruwan wanka ta sakata cin abinci. Tambayar duniya tai mata bama bata amsa, haka shima namijin idan zai shigo sau goma tai masa magana baya ko mata tari. Iya kacinsa ya le?o ya ganta ya koma.

Haka Nu'aymah ta cinye kwanaki goman nan cikin matsanancin damuwa da tashin hankali. Babbar damuwarta halin da ahalinta zasu shiga na rashinta. Musamman ma Umm ?inta da Abbanta da Yah Abdallah da Hajjo. Tayi kuka harta gaji ta bari ta koma gayama UBANGIJI kukanta. Dan tasan shine mai rahama mai jin?ai. Ya fita sanin dalilin da yasa ya jarabceta da wannan al'amari a daren ?aurin aurenta da yayanta masoyinta.

Ranar data cika sati biyu a ?akin bayan sallar la'asar sai ga matar nan, kamar kullum yauma batai mata magana ba, saima kwashe kayanta data cire tai ta fita dasu. Bayan kamar mintuna goma sai gata ta dawo ?auke da hijjabi wankakke gogagge. Mi?ama Nu'aymah tai da mata alamar ta sanya. Babu musu Nu'aymah ta fisgi hijjabin daga hannunta tana watsa mata harara ta sanya. Ita sam bata wani jin tsoronsu, damuwarta kawai family nata.
Matar bata kulataba, bayan ta saka hijjab ?in ta zagaya ta bayanta ta ri?e mata hannaye. Fisgewa Nu'aymah ta fara ?o?arin yi amma ta kasa saboda ?aure hannayen da matar tayi. Kafin ta samu damar magana namijin ya shigo shima. Gaban Nu'aymah yaje ya tsaya tare da fiddo ba?in ?yalle a aljihunsa ya ?aure mata idanu.
Duk tsiwar da take masa bai kulataba balle ya tanka. A haka suka fita da ita a ?akin batare da tasan ina za'a kaitaba.............?

_____________________
SAHFAT PREORDER!
______________________

Wani kaya sai amale ka ?auka??.

SAHFAT PREORDER maida tsohuwa yarinya.

Kaji masu kawo kayan adon gida dana jiki ?an gaske.

*_Ina mata masu ?an bana bakwai? ko uwargidar da ake shirin kawoma ?ar bana bakwai?. Kai hardama matan gayu ?an ?walisa masu son sabunta gida da kayan ado ?an waje masu sau?in farashi da nagarta!._*

_To ku garzayo dama ta samu, dan SAHFAT PREORDER sune na ?aya a wannan fanin. Idan kayan kitchen kikeso masu ?yau da nagarta a farashi mai sau?i kuma zaki samu a Sahfat preorder. Idan kayan sakawa kikeso na manyan mata ?an gayu suma akwaisu babu ?ayarya. Jaka ko takalma na nunawa tsara suma ba'a barsu a baya ba harma da mayafai. Hakama kayan ?aki basu da tsara_.

Ni shaidace domin dukkan kayana ta hannunsu nake samu nima. Ku garzayo kuma a dama daku dan nasan zakuyi alfahari da hakan insha ALLAHU.

Kiyi magana ta wannan Number 08142957548 insha ALLAH zaki samu ?arin bayani ?ar uwa.

*_Siyen nagari??, maida ku?i gida?? sai SAHFAT PREORDER??????????_*


_____________________________
ZAFAFA BIYAR 2021
_______________________


Hafsat miss xoxo??
KIBIYAR AJALI......!
(Sulke baya tareta saita gitta).????

Mamu gee??
MIN ?ALB!!????

Hafsat rano??
ABINDA KE CIKIN ZUCIYA...!!????

Safiyya huguma?? SIRA?IN RAYUWA????

Bilyn Abdull??
SARAN ?OYE????

Duka akan farashi mai rahusar gaske.

Kamar haka????????

?aya___300
Biyu____400
Uku_____450
Hu?u____500
Biyar_____700

Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki????

ACCOUNT NO 0812652655
ACCOUNT NAME- HAFSAT LAWAN GAMBO
BANK NAME: ACCESS BANK.

saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)????

0903 234 5899

IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU????

09033181070

????????????????????
TEAM----ZAFAFA BIYAR????????

ALLAH ka gafartama iyayenmu??????.
[3/10, 7:27 PM] +234 901 860 0202: *_Typing??_*

No. 7

................Sosai gazawar Umm take ?o?arin bayyana ga kowa. Dan gaba ?aya yinin yau da Nu'aymah ta yisa a ranta. Tun tana kukan zuci kamar yanda ta saba har hawaye suka kai ga fara sakko mata daga idanu.
Wajen misalin biyu da rabi na rana Baba malam ya shigo gidan. Kamar yanda al'adarsa take inhar ya dawo daga wajen aiki sai ya fara zuwa sashen Hajjo yaga lafiyarta. yauma haka ne. Zaune ya isketa a falo Imran na tausa masa ?afa yana kumbura baki dan ta sakashine dole.
Murmushi Baba malam yay da zama a ?asa gefenta ka?an da ajiye mata ledan kayan fruits idonsa akan Imran ?in da shi sam hankalinsa bai kai kansa ba.
"Imran ya naga fuskar a kumbure? Ko dai aikin innah ne ba'a son yi?".
Kallonsa Imran yay da sauri, sai kuma ya saki ?afar Hajjo ya nufi baba malam ?in yana sake tunzura baki gaba. "Baba sannu da dawowa". Kafin Baba malam ya bashi amsa Hajjo ta katsesa. "Dan gidanku dawo ka cigaba, inba hakaba kasan ALLAH nasan ta inda zan rama mai ?walelen ?eya kawai".
Dariya Baba malam yayi yana kallon yanda Imran ?in ya cika yay fam, sai kuma ya kalli Hajjo da itama ta kumbura farar fuskarta da duk tai tamojin tsufa tana zubama Imran ?in harara......
"Ni wlhy na gaji Hajjo, kumafa Momy jirana take zan mata aika".
"Oh! Uwarka ta fini kenan?.."
Baba malam yay saurin ha?iye dariyarsa da matsawa kusa da ita gab ya kama ?afar tata ya aza saman ?aramin filon kujera. "Kinga Inna manta da shi kinji, idan shima yana tsoron ?atama mamarsa nima ai gani tare dake ko?".
Murmushi tayi kamar ba itace da fuska a kumbure ba. Sai kuma ta watsama Imran ?in harara tana fa?in, "Tashi ka fitarmin a falo to kirikun banza, indai nice ai inada ranata yaro".
Tashi Imran yay da sauri dan ganin Hajjo ta kwakuso filon kujera da alama dukansa zatayi. Sai da yaje bakin ?ofa sannan ya juyo. "Ai dai gobe idan ALLAH ya kaimu zamuyi komawarmu Abuja......."
Kafin ya rufe baki ta tilla masa filon, kwasa yay da gudu ya fice yana ?yal?yala mata dariya.
"Wlhy ?an malam ?a?anku sun fetsare musamman ma ?arshe-?arshen nan. Kaga akace maka Imran da Muhammadu da Jafar sunfi kowa rainanima a gidannan". Hajjo ta fa?a a ?ufule.
Cike da girmamawa da lallashi baba malam yace, "To kiyi ha?uri inna zan musu fa?a kinji, yanzu dai ?afar ciwo take miki ne?".
"Ka?an take ciwon dai, na neman man zafin daka siyomin shekaranjiya na rasa inda yake, na tabbata cikin ?a?anku wani ya ?aukesa. ?ilama Zainabu c......." sai kuma tai shiru ta kasa ?arasawa saboda tunawa da tai Nu'aymah ma bata gidan. To ita ka?aice ke mata yanda ta gadama a cikin jikokinta a zauna lafiya a gidan. Dan suna mugun ?asawa da Nu'aymah saboda duk aikin da ta sakata yimatashi take. Hatta da wanki Nu'aymah ce kema Hajjo. Hakama gyaran sashenta. Sai ko Adawiya itama suna?an shiri, amma ?a'ida kullum sai sunyi fa?a.
?an murmushi baba malam yayi mai ciwo, dan shima a kullum ?iyar tasa tana a ransa. Ya sauke ajiyar zuciya da fa?in, "Karki damu innah insha ALLAH zansaka Abubakar ya saya miki idan zai baro company. Sannan zanma Doctor Kabir magana yazo ya duba ?afar, idan kuma asibitin zamu koma to".
Jikinta a sanyaye ta ?aga masa kanta, harya mi?e bata iya sake cemasa komaiba. Sai da yaje gab da fita sannan ta kira sunansa. "?an malam!". Juyowa yay da sauri yana ?o?arin ha?iye abinda ya tokare masa ma?oshi da amsawa da "Na'am Innah".
"Har yanzu babu labarin Zainabu dai ko?".
Murmushin ya?e yay mata wanda yafi kuka ciwo, ya ?an girgiza mata kansa da fa?in, "Innah tasan inda taje ta ?oye kanta ai. Randa ta bu?aci ganinmu da kanta zata nememu, ki kwantar da hankalinki wannan yabar damunki".
Bata iya cewa dashi komaiba yanzuma. Dan damuwa ?arara ta hango a saman fuskarsa da cikin idanunsa. Amma dan ?arfin hali sai yay mata murmushi sannan ya juya ya fita.

Tamkar wanda aka zarema lakar jiki haka ya isa sashensa. Da tsarabar da yayo ta fruits ya fara cin karo a falo alamar driver baiga kowaba ya ajiye a nan. Ya ?anbi ledojin da kallo kafin ya ida shigewa cikin corridor ?in da ?akunan barcin su Umm suke. Kansa tsaye ?akinta dake can ?arshen dogon corridor ?in ya nufa, yay sallama kusan uku a ?ofar ?akin babu amsa, sai kawai ya tura ?ofar ya shiga da sallama.
Tsaye yay cak a ?ofar ?akin ri?e da handle ?in kofar yana kafe Umm dake zaune a saman gado, Muh'd na kwance ya


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login