Showing 156001 words to 159000 words out of 325075 words

Chapter 53 - SARAN-BOYE COMPLETE

20 Jul 2024

29148

?an matsar da kansa kusa da nata ka?an, a hankali yace, "Ki daina magana zan baki magani yanzu zai daina insha ALLAH".
Tabbas taji muryar ba Abbahn ta bane, amma halin da take ciki bai bata damar banbance wanene ?inba sam.
Kallon Ahmad Yoohan yayi, yay masa nuni da box ?in da suka shigo yana fa?in, "Brother Please ko zaka iya ha?amin allurar nan?". "Yes! Doctor babu damuwa". Ahmad ya bashi amsa yana jawo box ?in.
Wata irin zabura Nu'aymah da zancen ya shigarma kunne tayi, batare da sun fargaba suka ganta tsaye bisa ?afafunta jikinta na rawa. "Bana son allura, Abbah! Abbah! banason allura..." ta fa?a a wahale tana ri?e kanta da hannu biyu duka tai baya luuuu zata zube.
Cikin zafin nama Yoohan ya mi?e tsayen shima, hakan yasa Nu'aymah fa?awa jikinsa nata jikin na wani irin karkarwa. Saurin ri?ota yayi shima yana fa?in, "Relax, Please calm dawn!"
Ina batama san yana fa?a ba, kanta kawai take jujjuyawa a ?irjinsa da fa?in, "Banason allura, Abbah banaso".
"Okay shike nan, kinga baza'ai mikiba, ya isa ki daina magana, tana sa miki ciwo kai". Yay maganar da ?aukarta gaba ?ayanta ya maida a kujerar zai kwantar. Sake ru?un?umesa tai, sautin muryarta na ?ara fita da ?arfi wajen fa?in, "Abbah karka bari sumin allura dan ALLAH " ta ?are maganar da fashewa da kuka.
Su dai su Hajjo duk wannan drama dake faruwa suna tsaye ne suna kallonsu, Ahmad dake murmushi yace, "Hajjo kumuje kawai mu barsa da ita, nasan zaiyi duk dabarar data dace yay mata insha ALLAH ".
Cike da gamsuwa suka amsa masa. Allurar ya matsa ya mi?ama Yoohan da Aymah ta kananna?ema jiki kamar mage ta samu katifar audiga. "Gashi, bara mu baka waje kai aikinka Doctor ".
Yoohan zaiyi magana Ahmad ya ajiye syringe ?in da sauri yabi bayan su Hajjo da har sun fice abinsu............?


Likita bokan turai????.


ZAFAFA BIYAR 2021

Hafsat miss xoxo??
KIBIYAR AJALI......!
(Sulke baya tareta saita gitta).????

Mamu gee??
MIN ?ALB!!????

Hafsat rano??
ABINDA KE CIKIN ZUCIYA...!!????

Safiyya huguma?? SIRA?IN RAYUWA????

Bilyn Abdull??
SARAN ?OYE????

Duka akan farashi mai rahusar gaske.

Kamar haka????????

?aya___300
Biyu____400
Uku_____450
Hu?u____500
Biyar_____700

Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki????

ACCOUNT NO 0812652655
ACCOUNT NAME- HAFSAT LAWAN GAMBO
BANK NAME: ACCESS BANK.

saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)????

0903 234 5899

IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU????

09033181070

????????????????????
TEAM----ZAFAFA BIYAR????????

ALLAH ka gafartama iyayenmu??????.I'm on Instagram as yerwaincense_and_more. Install the app to follow my photos and videos. https://www.instagram.com/invites/contact/?i=ayfowzb2ah8k&utm_content=6k8ur6p.


*_LITTAFIN nan na ku?i ne. Dan girman ALLAH ki daure ki biya kafin ki karanta, idan kuma bazaki iya biya ba ki ha?ura domin ALLAH karki karanta. Idan kuma kin saya dan girman ALLAH karki ya?a mana????_*.


No. 43

............Ajiyar zuciya ya sauke a hankali jin yanda Aymah take sake tura kanta cikin ?irjinsa. Ya ?an lumshe idanu ya bu?e akan dogon gashinta dake ta uban ?amshi ga ?yallin mai daya sha masha ALLAH. "Silly girl!" ya fa?a a hankali yana kai bakinsa dai-dai kunnenta. Batare da ya jira amsarta ba ya sake mi?ewa da ita ?auke a hannunsa. Zama ya farayi saman kujerar sannan ita kuma ta koma saman cinyarsa da ?yau batare da tasan mi takeyi ba. Syringe ?in da Ahmad ya ajiye ya ?auka, ?an guntun ruwan allurar dake ciki ya kalla, ya ?an yamutsa fuska ka?an da zare hular kansa ya ajiye gefe. Ya sake kallon Aymah ya girgiza kansa, cikin ?warewa da sanin makamar aiki ya kuma turata jikinsa da ?yau tare da ran?wafowa ya ?aura bakinsa akan kunnenta. Wata irin sassanyar iska ya shiga hura mata cikin kunne a hankali, yayinda can kuma hannunsa ke saita inda zai mata allurar batare da ta saniba.
A hankali ta saki wani irin nannauyan ajiyar zuciya da sake shigewa jikinsa, saboda ?amshinsa na sake jan hankalinta. Hakane ya bashi dama tsira mata allurar dai-dai inda ya dace. Da masifar ?arfi ta zabura tare da fasa ?ara ta sake dam?esa da ?yau jikinta na wani irin karkarwa.
Zare allurar yay yana sakin wani lallausan murmushi daya sake fidda annurin fuskarsa. "I am sorry". ya fa?a a hankali cikin kunnen nata.

Ihun Nu'aymah duk sai da ya shiga cikin kunnen su baba malam. Duk rumtse idanu sukayi tausayinta na tsargama zukatansu. Sai dai babu wanda yay yun?urin shiga cikin falon.
A ?angaren Yoohan kuwa idanunsa ?yam akan Aymah dake ta juyi a jikinsa tamkar wata macijiya, sai zufa dake ta faman tsatstsafo mata a goshi. Handkerchief ?insa fari ?al ya fiddo cikin aljihun gaban rigarsa ya shiga share mata zufar, tsahon mintuna biyar suna a haka kafin ta shiga sauke ajiyar zuciya a jajjere, a hankali kuma sai jikinta ya fara saki alamar barci. Cikin ?an?anin lokaci ta fara sauke numfashi. Kwanciyar ya gyara mata a cinyarsa yanda zataji da?i sosai, sai kuma ya kai hannu saman gashinta daya barbaje ya tattaresa cikin hannunsa. Ribbon ?in ya ?auka ya ?aure mata shi a tsakkiya ya nanna?esa da ?yau yanda bazai takura mata ba. Baya yayi ya kwanta jikin kujerar shima, ya lumshe idanunsa da sakin sassanyar ajiyar zuciya.
Shirun da su baba malam sukaji babu motsinsu har tsahon wasu mintuna ne ya saka Ahmad fa?in, "ALLAH yasa dai lafiya naji shiru". ?an murmushi baba malam yayi, ya kalli Ahmad ?in yana fa?in, "Ai tunda kaji mamana tabar kwakwazo na tabbatar anyi alluran".
Kusan a tare duk suka murmusa. Hajjo tace, "Raguwar amarya ba, sai tsiwa a baki amma cikinta fal tsoro, gashi kuma ta zama matar likita sai su ?arata ai". Yanzun kam duk dariya suka ?anyi. Ananah tace, "Ai irinsu dama hakane, zakiga akwai tsiwa amma matsoratane a bugun farko. Ahmadu le?a kagani".
Da to Ahmad ya amsa yana nufar falon. Sallama kusan uku yayi baiji an amsa masa ba. Hakane ya sakashi tura ?ofar a hankali ya shiga. Sai dai daga bakin ?ofa ya tsaya yana kallonsu. A take murmushinsa ya sake fa?a?a.
Bu?e idanu Yoohan yayi a hankali tare da ?agowa zaune sosai yana kallon Ahmad ?in. Sai kuma ya yun?ura ya ?aga Aymah cak daga cinyarsa zai mi?e.
Da sauri Ahmad yace, "No Doctor, kayi zamanka dama na le?one kawai naga idan komai lafiya. To ashema har tayi barci". Yoohan daya ?arasa mi?ewa baice komaiba, sai da ya shimfi?e Nu'aymah a kujerar da ?yau ya gyara mata kwanciya sannan ya ?auki hularsa ya maida bisa kai yana bama Ahmad ?in amsa. "Barrister wannan ?anwar taka ta cika raki da ragwantaka, saboda allura kawai duk ta jigatani tamin Squeezing ?in kaya".
?ar dariya Ahmad yayi yana ?o?arin tattare syringe ?in da komai da sukai amfani dashi. Yace, "A'a Doctor karmuyi haka da kai. Ni na tabbatar maka sai kazo wataran ka sanarmin Aymah jarumace, ballema itama likita zata zama insha ALLAH ".
Idanu Yoohan ya?an waro yana gyara zaman rigarsa, yace, "A hakanne zata zama likita tana tsoron allura tamkar bindiga ?in? Tab za'aga likitoci kam".

Da haka suka fito Ahmad na dariyar zancen Yoohan, shiko Yoohan ya fiske abinsa tamkar ba shine yay maganar ba.
Kusan duk a tare su Abbah ke tambayar jikin Nu'aymahn. Ahmad yace, "Ku kwantar da hankalinku ita harma ta tafi duniyar barci. Dama ihun na allura ne".
Duk kallon Yoohan sukai cike da farin ciki, suka shiga jera masa sannu da godiya. Shi dai kansa a ?asa yake fa?in, "Uncle karku damu aikina ne ai. Insha ALLAH zata tashi kamarma komai bai faruba dan amfanin allurar kenan. Sai dai a dinga kula dan abu ka?an ita yanzu zai iya birkita ta, ru?anin kuma shine ba'a so dan zai maida cigaban da ake murnar samu bayane. komai a ringa mata shi da lallashi".
"Insha ALLAHU za'a kiyaye. ALLAH ya saka maka da alkairi, ita kuma ALLAH ya bata lafiya yasa kaffara ne".
A tare suka amsa da amin, harsu hajjo da Ahmad ya fassara musu abinda Yoohan ?in ya fa?a.

A cikin gida kuwa dai hidimar bikinsu suke tayi, babu wanda yasan abinda ke faruwa da Nu'aymah sai sha?i?an Umm da suke a bedroom ?inta kawai. Suma kuma tunda Umm taje ta sanar musu likitan da zai duba Aymah yazo duk sai suka samu kwanciyar hankali.
Bayan wucewar Yoohan duk suka shiga har falon baba malam suka ganta. Hakan ya ?ara musu nutsuwa sosai, dan haka suka dawo ?akin Umm suka cigaba da hirarsu ta zuminci tare da tattaunawa akan auren na Aymah.
Koda suka koma can baba malam da kansa ya ?auki Nu'aymah dake barci hankali kwance ya maida bedroom ?insa. Sannan ya fito shi da ?an uwansa suka fice massallaci gabatar da sallar magriba.

Biki yayi biki masha ALLAH, dan Addah ta samu alkairi sosai daga wajen abokan arzi?inta. Hakama sauran matan gidan bisa al'adar biki da kowa ya sani suma sun samu rabonsu ga abokan arzi?ansu. Harma da Umm da kowa sai yanzu yasan harda gudan jininta. Ana idar da sallar isha'i kuma aka shiga shirya amare. Hajarah da Kubrah. Nu'aymah dai babu wanda yay magana maybe ba yau ba kenan.
Kamar yanda kowa ya sani baba malam shike raka duk ?a?ansu gidan aure. Babu wani gayyar ?an kai amarya. Duk wanda yake da bu?atar ganin ?aki yakanje da rana bayan ?aurin aure ko washe gari idan amarya ta kwana a gidanta. To gasu Hajarah ma tsarin bai canja ba. Dan ana idar da sallar isha'i su baba malam duk suka shigo gida. Sashen Hajjo aka kai amaren, Hajarah nata kuka kamar zata shi?e. Kubrah kam idanunta ?yar cikin lifayar da aka na?a musu. Sai uban ?amshi suke kamar gidan turare.
Duka iyayensu da sha?i?an ?an uwa suka taru a sashen Hajjo aka shiga musu nasiha. A yanzunma dai Hajarah kuka take, Kubrah kam kanta dai a ?asa tana saurarensu. Bayan nasihar da akai musu da garga?i mai ratsa jiki akai musu doguwar addu'a da fatan alkairi sannan aka fito dasu. Da motoci uku kacal za'a kai amaren. Motar farko amaren ne a baya sai baba malam da Omar da zaiyi driving. Mota ta biyu iyayene mata na ?angaren Addah su hu?u, sai yayun Umm biyu, su kuma Malam ?arami ne zai jasu. Sai motar ?arshe da Yah Ahmad zai ja ita kuma tsoffin iyaye ne dangin su baba malam a ciki su biyu, sai Umm da momy da amaryar Abba Musbahu. Motar ?arshe, Abban Abdallah, Abba Musbahu, Abubakar da zai jasu, Uncle Kabeer mahaifin Nasir, sai Uncle Babangida shima dai sha?i?insu ne.
Haka suka fita a jere ana bin amare da addu'ar tafiya a sa'a. Dama mafi yawan ?an biki na kusa duk sunata guduwa suma. Zuwa goma na dare sai hayaniyar gidan ta ragu sosai, wasu sunyi barci, wasu sun tafi.


¡ï¡ï¡ï

Su baba malam sun fara mi?a Hajarah ne dan itace ?arama. Gidanta mai ?yau da tsari a anguwar GRA, kowa ya yaba da addu'ar zaman lafiya da zuri'a ?ayyiba. Sun sami tarba ta mutuntawa daga dangin ango su bakwai da sukazo tarbar amarya daga can gidan surukan Hajarah. Kasancewar sunsan dokar su baba malam ?in suma cikinsu harda maza uku. Bayan sun ?an zauna a falo akai addu'a baba malam ya kama hannun Hajarah har cikin Bedroom ?inta ya kaita, zaunar da ita yay a bakin gado yay mata addu'a da saka mata albarka. Ya juyo zai tafi ta ri?e hanunsa. Tsayawa yay tare da juyawa jikinsa duk a sanyaye yana dubanta. Haka yake shi, yanada son yara, shiyyasa har ?ayan ?an uwan nasa ?aunarsu yake har cikin ?argonsa. Duk kuma sanda yay irin wannan rakkiyar sai yayi ?walla dajin ?acin rabuwa da yaran nasu ta dalilin aure ?anin mutuwa.
Hajarah data bu?e fuskarta ta share hawayen dake silalo mata. Cikin dasashshiyar muryarta tace, "Abbah dan ALLAH inason in ro?eka wani abu". Kansa ya jinjina mata, yace, "Komi kikeso zan miki inhar baifi ?arfina ba Hajarah, dan haka fa?amin koma miye kinji". Sake share hawayenta tayi tana jinjina masa kai. "Abbah dan ALLAH idan yah Abdallah yace bazai maida aurensa da su Adawiya ba karku takura masa". Jimmm baba malam yay yana kallonta. Sai kuma yace, "Uhm Hajarah miyasa kika bu?aci hakan? Bayan kinsan shi ?in mai laifine". "Abbah zan fa?a maka dalilina amma ba yanzu ba, dan ALLAH kuyi mani wannan alfarmar, suma su Abba zan kirasu duk na ro?esu har Hajjo".
Numfashi baba malam ya ?an sauke, sai kuma yace, "Karki damu zan duba na gani, kibar kukan nan haka karya saki zazza?i. ALLAH ya baku zaman lafiya".
Daga haka ya fita ya barta tana cigaba da rabzar kukanta.
Daga gidan Hajarah saina Kubrah. Itama dai gidan ya ha?u masha ALLAH. Sai dai ita tana da abokiyar zama harda yaranta uku. Amma kowa da sashensa dan gidan babbane. Itama dai an tarbesu da mutuntawa. Baba malam kuma ya rakata har nata ?akin ya ?ara mata addu'a sannan ya fito suka wuce gida kowa aka barsa da halinsa kuma.

____________________

A ?angaren Yoohan kam tunda suka baro gidan su baba malam sai ya koma Hotel ?in da su papa suka yada zango. Babu yanda baba malam baiyiba akan su sauka a ?aya daga cikin gidajen ba?insu amma papa ya ?i fir. Wajen ?aurin aurenma da yake jirgin 12 suka shigo suna isowa ana idar da sallar juma'a, hakan yasa saida ma aka ?an jirasu kafin su iso wajen ?aurin auren daga airport. Yoohan ne kawai yazo tun goma na safe. Bayan an ?aura auren aka ?unguma har dasu hall ?in da su baba malam ?in suka tanada domin gudanar da walimar cin abinci. Anan akaci aka sha cike da farin ciki. Babu wanda zai kalli baba malam da papa yace akwai wani abu na rashin jituwa a tsakaninsu. Suma su papan sun sake sosai a cikin mutane bazaka ta?a cewa ga daga addini ko ?abilar da suka fito ba. Musamman ma daya kasance a cikin manyan mutanen ?an ?aurin aure akwai wa?anda suke da ala?a dasu sosai musamman ma ?an siyasa. Wasuma papan ya sake gayyatarsu bayan gayyatar da baba malam yay musu.
Bayan an kammala walimar ne mafi yawan ba?in suka kama gabansu, su kuma su papa da tawagarsa suka nufi hotel bayan sun?i amsa tayin baba malam. Hakan yasa yanzun acan Yoohan ya iskosu. Sai dai kasancewar jirgin ?arfe bakwai da rabi zasu bi zuwa Abuja duk ya iskesu sun fito shi ma suke jira. Basu wani zauna zaman ?ata lokaci ba duk suka shiga motocinsu. zasu kaisu airport ?inne su dawo su kwana da safe suma su ?auki hanya. Dama da safe suka taho kafin su papan.
Ko mintuna goma cikakku basuyi da zuwa airport ba jirginsu ya lula birnin tarayya abuja. Inda a canma dai ?aukarsu akazo akayi. Abokan papa kowa ya nufi gidansa, papa da Gebrail, Richard, Joseph, Godwin, Osin, Uncle Marcel, Uncle Anthony, kuma suka nufi gidan papan. Sai Solomon jelar Yoohan??.
Sun iske gidan a hargitse da rikicin da suka bari su Mama Debora nayi akan auren Yoohan ?in. Fa?a mai lasisi sosai akasha tsakanin tsofin biyu. Kuma duk akan sufa basu yarda jikansu ya aure bahaushiya mai salla ba. Momy da papa ya gama sanar mata komai akan manufar auren tanata ?o?arin fahimtar da su duk da kuwa jitake kamar tafi kowa shiga tashin hankali, amma sun ?i fahimta. Sai kiran dangi suke na nesa a waya suna sanar musu. Miracle kam yanke jiki tayi ta fa?i a sume dama tunkan su Yoohan su wuce. Akace kuma ya dubata ya tsallake yay ficewarsa batare daya ko tanka musu ba.
Hakan daya aikatane ya sake fusata kakanninsa sabon wutar bala'i ya ?ara ruruwa. Sai asibiti aka kai mira bayan wucewarsu ?aurin auren.

Tunda Yoohan ya shigo idonsa ya sauka akan kakannin nasa sai ya sake tsuke fuska fiye da yanda take. ?auke kansa yayi ya nufi upstairs duk da yaga yanda suka mi?e zumbur suna kallonsa cike da wutar masifa.
Cikin yare, mama Debora ta shiga ?wala masa uban kira kai kace gidan zata fasa. Ko waiwayensu baiyiba ya bu?e ?ofarsa ya shige bayan ya amshi babbar rigarsa a hannun Solomon dake biye da shi a tsorace. Ruf ya rufe ?ofar ya murza mata key yama barshi a ciki dan kar wani yay tunanin amfani da wani key ?in.
A falo ya zube yana sauke numfashi da jan dogon tsaki. Jin an fara buga ?ofar tasa da ?arfi ana masifa ya kuma jan wani tsakin ya mi?e ya nufi bedroom ?insa.


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login