Showing 135001 words to 138000 words out of 325075 words
neman kufce mata tace, "A kaita asibiti, koma minene sai a yisa da ga baya, ciki kuwa harda neman yaron shima. Da yawan mutane wannan suke tsoro ga taimako, shiyyasa bahaushe ke fa?in kasa mutun inuwa ya saka rana. Ko a fuska bazaka ta?a tunain yaron nan zai aikata makamancin hakanba duk da kuwa a farkon shigarsa jikinmu kafiri ne. Ashe ya lullu?e mune kawai yazo jikinmu ya cutar damu, da alama dama yarinyar nan ya biyo bawai alkairin da muke tsammani daga garesa ba. To kansa yay mawa, ALLAH kuma ya saka mana da gaggawa indai muna da ha??i a kansa".
A tare duk suka amsa mata da amin. Banda baba malam da yay wani ?an murmushi ya ?auke kansa kawai. Abdallah ne ya ?auki Nu'aymah dake a san?ame ya fita da ita bisa umarnin Hajjon.
_________________
An musu ?ar?ar gaggawa saboda halin da Nu'aymah ke a ciki. Musamman ma da suka sami mace ce Doctor ?in dake dutyn lokacin.
A yanda suka ga likitocin na kai kawo ?akin da aka saka Nu'aymah hankalinsu ya da?a tashi sosai. Duk kuma sanda wani ya fito suka tambaya baya basu amsar komai yake wucewa da sauri. Tun suna ?aukar al'amarin ?arami har suka fahimci yanada girma sosai, dan Doctors har uku sun ?aru bayan ta farko. Sai faman yin ?us-?us kuma sukeyi a tsakaninsu.
Cikin ?arfin hali Abba Musbahu ya dubesu yana fa?in, "Bayin ALLAH inaga idan yarinyar nan ta rasa ranta ne ya kamata ku sanar mana, dan kunata sake ?aga mana hankali da rashin cewarku komai da kai kawon nan naku".
?aya da ga cikin likitocin ne ya sadda kansa ?asa cikin girmamawa yace, "Ai mana afuwa malam, ba muna ?oye muku komai baneba. Kawai muna akan aikine shiyyasa, amma insha ALLAHU zakuji komai nanda ?an mintuna ka?an".
Shiru wajen yayi babu wanda yace komai, sai dai a zukatansu sam basu gamsu da zancen likitan ba.
¡ï¡ï¡ï
Tunda aka fita da Nu'aymah asibiti baba malam ya koma sashensa. Zaune yake a study room ?insa saman wata kujera da ke ?an lilasa idan yana kanta. Duk da rana ce ?akin yayi duhu sosai kasancewar bai ?aga labule ko guda ?aya ba a ?akin. Bai kuma kunna fitila ba sai ?an hasken da ake gani ka?an kasancewar na hasken rana. Kwance yake a jikin kujerar idanunsa a lumshe ya fa?a duniya mafi nisan zango a tunani.
Tun daga daren jiya har zuwa yanzun zuciyarsa a ru?ani take. Ru?ani irin wanda ?wa?walwa bata iya rarrabe gaskiya da ?arya, fari da ba?i, haggu da dama........
Motsin da yaji a kusa da shine ya sakashi bu?e idanunsa da ?yar. Umm ce ya gani cikin ?an hasken da ?akin ke da shi. tsaye take a gefensa dafe da kanta alamar tana a cikin matsala. Zumbur ya mi?e ya ri?ota ganin tana layi, ga hakki tanayi kamar wadda tayi gudu a cikin sahara.
Kujera doguwa dake a ?akin ?wara ?aya kacal ya nufa da ita, ya kwantar da ita jikinsa sai tsuma ya keyi. "Jannat miya sameki?".
Duk da halin da take a ciki itama sai da tausayinsa ya kamata jin a yanda yay magana. Tasan ?arfin hali kawai ya keyi tun jiya akan al'amarin nan, amma shima a ru?anin yake. Hannunsa ta kamo da ?ayan hannunta, ?ayan kuma na akan ?irjinta da ke mata azabar zafi tamkar zai bu?e.
"Sooraj inaji a jikina mutuwa zanyi, a wannan karon zuciyata bazata iya ?aukar wannan al'amarinba. Abban Nu'aymah akwai ru?ani a cikin zancen nan, amma ni kaina na kasa banbance mai gaskiya tsakanin ?armu da likitocin nan. Idan da ace likita ?aya ne ya fa?a sai muce ko ha?a baki akayi da shine, amma kaga harsu uku, ?ayan ma bamu santa ba tunda asibiti suka sameta. Sannan Sooraj a kwanakin cikin nan da aka ambata ya kasance jikin Nu'aymah ban ta?a ganin wani alama na mai ciki tattare da yarinyarta ba, babban tashin hankalina kuma shine tabbas watan da ya shige na azumi banga Nu'aymah tayi jini ba har suka wuce saudia, wancan watan kuma a farkon wata tayisa. Kasan dai ita jininta baya ?oyuwa a gidan nan saboda lalurar da yake zuwa mata da shi. Sooraj na shiga ru?ani wlhy".
Ta ?are maganar da fashewa da kuka.
Shima sai ya ji hawaye na ziraro masa batare da ya shirya yin hakan ba. Dan zuciyarsa ta karye gaba ?aya. Ya rungumeta a jikinsa sukayi mai isarsu kafin ya ?agota yana kallon yanda take faman dafe ?irjin nata har yanzun.
"Jannat bazaki mutuba, bana fata ki tafi ki barni cikin wannan tarna?in, nima zuciyar tawa ba iya ?auka zatai ba. Ki daure dan ALLAH muyi imani da ?addara. Amma kamar yanda kike cikin ru?ani a wannan al'amarin wlhy nima haka nake a ciki. Na ?iyasta duka zuwan Yoohan cikin gidan nan gaba ?aya ban iya tunano ta yanda har ya samu ke?ancewa da Nu'aymah ba. Wlhy zuciyata ta kasa yarda Nu'aymah da Yoohan zasu aikata wannan ?arnar. Idan kuma nace ban amince sun aikata ?inba yaya xanyi da wa?an nan hujjojin bayyanannu kuma Jannat? Ya ALLAH ka bayyanar da gaskiyar al'amarin nan koda a cikin Zukatanmu ne ya Rabbi".
Haka sukaita hawaye har sai da baba malam ya fahimci Umm na neman rasa numfashin ta. Sake ru?ewa yayi ya shiga girgiza ta jikinsa na rawa. Yama rasa miya kamata yay mata, kiran sunanta kawai yake iya yi da iya ?arfinsa.
Hakanne ya jawo hankalin su Hajjo da ke zaune jigum-jigum suna jiran jin halin da Nu'aymah dake a a sibiti take a ciki. Har rige-rigen shiga sashen sukeyi, gashi duk mazan gidan sun wuce asibiti tare da Nu'aymah, dama baba malam ?inne kawai ya rage.
A hankali inuwar mutum dake a jikin windown tana kallon su baba malam ta kafar labule ta janye daga wajen. Hakan yay dai-dai da fara shigowar matan gidan. Babu wanda hajijiya bata kusan kwasa ba ganin da gaske Umm bata numfashi, ga baba malam yau duk jarumtarsa da kawaici yana zirar da hawaye............
_____________¡ï¡ï¡ï
A asibiti bayan sallar la'asar Doctors ?in suka bu?aci ganin wasu a cikin su Abba. Su duka ukun suka shiga office ?in, aka bar su Abdallah kawai a waje.
Sai da aka nuna musu wajen zama kafin likitar mace tai ?an gyaran murya tana kallon sauran ?an uwanta uku likitocin. Kawuna suka ?aga mata alamar bata damar magana. Ta amsa musu da kai itama tana sake gyara zamanta.
Cike da girmamawa a garesu tace, "Dama munason muku bayani ne akan abinda ke faruwa idan bazaku damu ba". Babu wanda ya iya ce mata komai a cikinsu. Dan haka ta cigaba da fa?in, "Maganar gaskiya yarinyar nan tana cikin mawuyacin hali, duk yanda mukaso ceto rayuwarta ma mun gagara, dan aikin yafi ?arfinmu. Amma a yanzu dai abinda muka iya kawai shine jawo numfashin ta da wasu na'urori kafin a samu mafita. Muna da likitan da zai iya duba matsalarta, sai dai kuma ganinsa shine tashin hankalin musamman da ya kasance yau kwanakinsa goma sha ?aya kacal da barin nan, sannan aikinsa yana da ?a'ida bana waje ?aya bane balle muce muku kai tsaye ga inda zaku iya samunsa. Amma yanzu dai in ta?aice zance matsayinku na iyaye a garemu masu daraja da kima bazamu iya ganin matsala a gareku ba mu kauda idanunmu, dan haka munyi ?o?arin nemansa dan muji ko zai iya mana alfarmar ganinsa amma bai ?aga wayar ba, sai dai mun kira amintaccen sa da ke a garin Lagos a yanzu haka ya tabbatar mana zai bincika mana shi, idan har ya amince zaizo zamu iya ganinsa a koda yaushe. idan bai aminceba yana da wani uzurin kuma shi zaizo ya ga yarinyar ko zai iya bada wata mafita akan matsalar tata dan shima babban likita ne".
Cike da gamsuwa da bayaninta duk suka kar?a mata da "ALLAH yasa a dace" tare da musu godiya sosai akan wannan taimako da sukai musu. Daga haka suka tashi suka fito kowa yana addu'ar dacewa a cikin ransa da jin tausayin ?iyar ?an uwan nasu dama ?an uwan nasu shi kansa fiye da ko yaushe a yau.
Kamar da wasa sai ga su Abbah sun shafe fin awanni bakwai amma babu labarin likitan da ake tsumayen jira. Su kuma likitocin basuce musu komaiba. Haka suka cigaba da zama jugum-jugum suna addu'oi a zukatansu har tsahon wani lokaci. Shigar lokacin sallar la'asar ne ya sake tadasu suka nufi massallaci, bayan an idar da salla suka sake fitowa suka sake zaman jiran tsammani.
Wata cikkakkiyar awa biyu suka sake sharewa gangariya, Abban Abdallah na ?o?arin mi?ewa zuwa office ?in Doctor ?in nan mace mai suna Doctor Ai'sha yaji yaya ake ciki? sai ya hangota tana fitowa da ga office ?in nata fuskarta washe da murmushi.
Kafin ya samu damar mata magana yaga ta nufi ?ofar fita da hanzarinta. Kamar zai bita sai kuma ya fasa, ya cigaba da tsaiwa a wajen yana jiran ganin ko zata dawo.
Tsayuwar tasa tayi dai-dai da shigowarsa cike da takunsa na ?arfi da lafiya, wanda idan baka saniba zaka iya ?auka tsabar isa ce da izza ke ?awainiya da shi. Amma sam ba haka baneba, halittar tasa ce kawai haka.
Kansa du?e yake sakamakon file ?in Nu'aymah da ke a hannunsa yana dubawa. Ya ?an rame, hakan ya saka sake fiddo hasken fatarsa da ?yawun da ALLAH yay masa. Ga wani annuri na hasken ibadar ALLAH tattare da shi, wanda ya sake ?aukaka ?warjininsa da cikar haiba kai kace farin watane ?an daren sha biyar. Kamar kullum sanye yake cikin suit, na yau ?in sun kasance Coffee color, sai farar shirt da ke a ciki babu necktie, dan ma?allan Shirt ?inma kusan uku a bu?e suke.
Doctor Aysha na daga gefen damarsa duk da ya?an zartata ka?an a tafiyar kasancewar ya fita tsayi, da alama bayani take masa akan matsalar. Sai Solomon dake ?auke da jikkarsa a hannu, da Doctor Sa'ad da wasu likitoci biyu da Nurse kusan hu?u na biye da bayansa. Har suka zo suka gitta Abban Abdallah bai ga fuskarsa da ?yau ba, dan har lokacin kan nasa a sunkuye yake ga file ?in. A dai-dai ?ofar ?akin da Nu'aymah ke ciki suka ja birki, su Abdallah da duk suka zuba nusu ido duk suka mi?e, sai dai kafin wani cikinsu yace wani abu. Ya tura ?ofar ?akin ya shige har lokacin hankalinsa nakan file ?in.
Iya shi da Doctors ?in suka shiga, yayinda Solomon da Nurses ?in suka ja birki a bakin ?ofar.
Sai da ya ?arasa gab da gadon da Nu'aymah ke kwance sannan ya ajiye file ?in ya kai dubansa gareta, bai ganeta ba sam, saboda na'urar da aka saka mata mai taimakama numfashinta fita. Ya ?an ran?wafo kanta ka?an ya kai hannu ya zare na'urar mai ha?e da oxygen. Ba ?aramin tsirgawa zuciyarsa tayi ba, amma saboda son sake gaskta abinda yake tunanin sai ya zare Glasses ?in idonsa da ya ?ara ?awata fuskar tashi. 'Kamar dai itace' ya ayyana a zuciyarsa cike da kokwanto.
A fili kam sai yay saurin maida mata na'urar saboda ganin yanda ?irjinta ke sama da ?asa da sauri-sauri ga jikinta na vibration har gadon kansa na motsawa. Luuu ya ?anyi da idanunsa ya lumshesu ya sake bu?ewa a kanta. murya a cinkushe ya dubi Doctor Aysha a ?an fa?ace ya ke fa?in, "Anyi matu?ar sakaci da lafiyar yarinyar nan da har take neman shiga matakin ?arshe, ina mamakin yanda mutane suke abu tamkar basu san muhimmacin lafiya ba. Mtsoww!!. Su Iyayenta fa?".
Dr Sa'ad ne ya bashi amsa da "Haka suke wlhy Doctor, sai kuma an mutu suce likitoci ne da sakaci bayan tun farko sune da matsalar su........."
Cikin sauri Dr Aysha ta katse Dr Sa'ad ?in dan bata son ya sake tunzura Dr Yoohan, "Ayi ha?uri sir, duk family nata suna waje, duk da kasancewarsu manyan mutane suna tare da ita tun ?azun fiye da awa tara wlhy".
Baice komaiba, ya dai sake kai dubansa ga Nu'aymahn, sai kuma yay azamar ?auke kansa batare da nasan dalilin yin hakan ba. Juyawa yay zai fita. Doctor Aysha tai saurin ?aukar file ?in da ya ajiye su ka sake bin bayansa ita da su Doctor Sa'ad da ke ta faman cika yana batsewa saboda haushin kare dangin Nu'aymah da tayi.
Yanzun ma bai duba kowa ba a cikin su Abdallah yay wucewarsa. Duk da kallo suka sake binsa suma, yayinda Abban Adawiya yaso gane sa, sai dai baiyi magana ba jin suma su Abban Abdallah basu ce komai ba.
Da ga shi sai Solomon suka shiga office ?insa, komai ?al yake, dan tunda Dr Aysha ta tabbatar da zuwan nasa ta saka aka sake tsaftace office ?in duk da dama ?a'ida kullum sai an share an goge. ?aramin ?akin hutun dake cikin office ?in Solo ya ?arasa. Ganin nanma komai dai-dai yake yanda yasan Yoohan ?in na bu?ata sai ya ajiye jikkar ya fito.
Tsaye ya iske sa yana ?o?arin zame rigar suit ?insa, har Solomon ?in ya kai ?ofar fita ya tsinkayi muryarsa ya na fa?in, "Kiramin Dr Aysha".
"Okay sir".
Solo ya fa?a da sauri yana ficewa. Hanging ?in rigar yayi bayan kujerarsa ta zama, sannan ya fara ?o?arin kunna Computer ?in da ke a saman desk ?in na sa. Yanda yay matu?ar zuba idanunsa ga Computer ?in zai tabbatar maka abunda yake yi a ciki yana da matu?ar muhimmanci. A haka Dr Aysha ta turo ?ofar bayan tayi knocking ta shigo, dan tasan ba lallai ta samu amsa ba musamman a irin wannan lokacin da ta tabbatar hankalinsa gabaki ?ayansa nakan patient ?in da ke jiran taimakonsa.
Batare da ya ?ago ya kalleta ba yace, "Matsalar yarinyarnan babba ne, sai dai zan mata wani ?aramin theatre yanzun, dan haka ku shiryata zuwa theatre room". Ya mi?a mata file ?in gabansa yana cigaba da fa?in, "Wannan mahaifinta zai saka hannu anan, ko mahaifiyarta ko mijinta. Kuma dole ?aya da ga cikinsu ake bu?ata kawai".
?an jimm Dr Aysha tayi. sai kuma komi ta tuna oho, ta gya?a masa kai da fa?in "Okay sir". Daga haka ta fice shi kuma ya mi?e ya nufi ?akin da ke a cikin office ?in.........?
______________________
ZAFAFA BIYAR 2021
_______________________
Hafsat miss xoxo??
KIBIYAR AJALI......!
(Sulke baya tareta saita gitta).????
Mamu gee??
MIN ?ALB!!????
Hafsat rano??
ABINDA KE CIKIN ZUCIYA...!!????
Safiyya huguma?? SIRA?IN RAYUWA????
Bilyn Abdull??
SARAN ?OYE????
Duka akan farashi mai rahusar gaske.
Kamar haka????????
?aya___300
Biyu____400
Uku_____450
Hu?u____500
Biyar_____700
Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki????
ACCOUNT NO 0812652655
ACCOUNT NAME- HAFSAT LAWAN GAMBO
BANK NAME: ACCESS BANK.
saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)????
0903 234 5899
IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU????
09033181070
????????????????????
TEAM----ZAFAFA BIYAR????????
ALLAH ka gafartama iyayenmu??????.*_LITTAFIN nan na ku?i ne. Dan girman ALLAH ki daure ki biya kafin ki karanta, idan kuma bazaki iya biya ba ki ha?ura domin ALLAH karki karanta. Idan kuma kin saya dan girman ALLAH karki ya?a mana????_*.
No. 37
............A tsaitsaye ta iske su Abba gaba ?aya yanzun kam. Cikin girmamawa ta ?arasa garesu. Fuskarta ?auke da murmushi tace, "Congratulations, mun samu nasara babban likitan da ganinsa ke da matu?ar wahala ya amshi gayyatarmu".
Cike da jin da?i suka shiga fa?in Alhmdllh.
Da ga haka ta bu?aci magana da su Abbah. Babu musu suka bita office. Bayani tai musu akan ?a'idar saka hannu da Dr Yoohan ya sanar mata, Abba Musbahu ne ya nuna ai suma iyayen Nu'aymah ne idan sun saka hannun babu damuwa, tunda yayansu baya a kusa, gashi kuma tace za'a shiga aikin ne da gaggawa........
Ita dai kasa ce musu komai tayi dan suna da girma da kima a idonta, sannan kuma ta tabbatar tunda Dr Yoohan yace a cikin ukun ?aya ake bu?ata dolene hakan za'ayi. Ganin shirun da tayi ne ya saka Abban Adawiya fahimtar akwai matsala, dan haka sai ya kalli ?an uwansa, "Inaga kawai mu kira Yayan kamar zaifi fa'ida, dan sun fimu sanin muhimmancin shar?anta hakan".
Duk sun gamsu da bayaninsa. Abban Abdallah ya ciro waya yay kiran Baba malam. Kirannasa ya shiga wayar baba malam ?inne dai-dai lokacin da Umm da Hajjo ta shafama ruwa a fuska