Showing 171001 words to 174000 words out of 325075 words

Chapter 58 - SARAN-BOYE COMPLETE

20 Jul 2024

29122

Sashen sa ya koma. Inda ya iske Solomon a falo yana goge-goge. Gaidashi yayi cike da girmamawa kamar yanda ya saba.
Amsa masa yayi yana tura ?ofar ?akin Nu'aymah ya shiga. Solo ya rakashi da kallo tamkar idanunsa zasu zubo ?asa. Oho baimasan yana yi ba, danshi tuni ya shige.
Shashshekar kukanta daya faracin karo da ita cikin kunnuwansa ne ya sashi lumshe idanunsa a hankali ya bu?esu a kanta, cigaba da tsaiwa yayi a bakin ?ofar kawai yana kallonta kamar ya samu television. Ita kam bama tasan da shigowarsa ba, dan gaba ?aya hankalinta da tunani yana kan ta yanda zata samu mafita akan wannan auren ne. Sai ?unbin kewar iyayenta da ?an uwanta dake gaba-gaba wajen tunzura kuka nata.
A hankali ya sauke numfashi da zura duka hannayensa cikin aljihun ba?in wandonsa. Ya fara taka farar ?afarsa dake fes babu wani datti a jikinta saboda tsabar saka kwaba shu da yake a koda yaushe ya ?arasa har gaban gadon dai-dai saitin inda fuskarta take. Har fuska ta rufa bargon. Ka?an yaja gajeran tsaki a ma?oshi, a ransa ko rayawa yake, 'Sai shegen tsiwa a bakinta da ?uruciya'. A fili kam sai ya ?an ran?wafo da zare hannunsa daga cikin aljihu ya yaye bargon daga fuskarta. Bai kai ga kaishi kafa?a ba ta ri?e gam. Idanu ya zubama farar fuskarta da tai jazur musamman saman hancinta da idanunta. Dai-dai da ?ago nata kumburarrun idanun ta zuba cikin nashi. Sai dai sam kwarjininsa ya hanata iya cigaba da kallon tsakkiyar idanun nasa. Hakan ya sakata azamar janyewa tana kumbura baki fal da iska. "Malam ka daina shigamin rayuwa bana so". Cikin yin ?asa da murya yanda bazaiji ba tace, 'Haka kawai a ringa shigoma mutum kai tsaye babu neman izini'.
Baiji maganar data fa?a ba a ?arshe dan da hausa tayi, ta farkoce dai tayi da turanci. Amma a yanda tai maganar yaji a jikinsa rashin kunya ce a ciki. Amma sai ya shareta bai kulata ba, sakin bargon yayi ya ?ora yatsunsa biyu a saman goshinta saboda ganin yanda jijiyar kanta tai ru?u-ru?u.
Saurin ja baya tayi hawaye na sakko mata, "Nifa a daina ta?a ni bana so". Ta fa?a tana hararsa ta ?asan ido da murgu?a baki ka?an.
A karan farko da abin nata yaso bashi dariya, dan haka ya ?anyi luuu da idanunsa tamkar zai lumshesu amma sai ya bu?e yana kauda kai gefe da sakin murmushi. Barin gaban gadon yayi batare da ya sake magana ba. Abincin da aka kawo mata ya bubbu?e. Irish ne da ?wai, sai farfesun kayan ciki, da gasashshen burodi da yaji ha?in salad a tsakkiya. Maidawa yay ya rufe sannan ya mi?e ya fita.
Nu'aymah da duk tana kallon abinda ya keyi ta raka bayansa da harara tana fa?in, 'Mutum babu abinda ya iya sai son ta?a jikin mutane dan kwartanci'. (Hhhhhh?? Aymah tamu ta mutunci, mutum ya sauke sadaki ki kirashi kwarto dan ?arfin hali irin naki??).

Bai fi mintuna hu?u da fita ba ya dawo hannunsa ?auke da kofin tea ruwan hanta, yanda turiri keta fita ta samansa zai baka tabbacin shayi ne..
A gefen gadon ya zauna daf da ita. Hakanne ya sakata matsawa da sauri. Baki ya?an ta?e, batare da ya kalleta ba yace, "Oya tashi". "Na maka mi?" ta bashi amsa tana satar kallonsa. Kofin tea ?in kawai ya mi?a mata batare da ya sake cewa komai ba.
"Tab, toni nace maka zansha tea ne? Na ?oshi".
"Silly girl"
ya fa?a yana hararta a karo na farko. Ya sake tsuke fuska da fa?in, "Malama tashi kiyi breakfast kona juye miki shayin nan ta hanci".
Tuni idanun Aymah suka ciko da ?walla, cikin rawar sanyin da yake ?aruwa mata tace, "To ana dole ne? Nace na ?oshi ba sai ka barni ba". Komai bai sake ce mataba, sai dire kofin yayi a saman bedside drawer ?in ya mi?e. Fita yay da ga ?akin. Da sauri Aymah tace, 'ALLAH ya hanaka ikon dawowa mai zubin masu jajayen kunne, da wani kansa kamar she?ar angulu'. (Wlhy ke da shi Aymah ni dai ba ruwa na??).
Ganin abinda ya dawo da shi a hannu ya sakata mi?ewa zumbur jikinta na rawa. Shiko ko kallon inda take ya ?iyi sai ?o?arin ?are syringe ?in daya shigo da shi ya keyi. Ya sake zama a bakin gadon yana ?alle bakin kwalbar maganin, tare da saka kan allurar jikin syringe ?in ya zu?e ruwan allurar da ya kusa rabin syringe ?in. Ajiyewa yay a gefenta bayan ya gama, sannan ya ?akko kofin shayin ya mi?a mata batare da yace komai ba.
Da iya gaskiyarta take ziraro da hawaye, zuciyarta sai bugawa take da sauri-sauri. Tabbas a rayuwarta allura na ?aya daga cikin abinda take tsoro fiye da hasashen mai karatu, sai kuma duhu. Wa?an nan abubuwan ko a tunani batason tunasu suna tayar mata da hankali. Hakan yasa hannunta har karkarwa yake wajen mi?a hannu ta amshi kofin shayin. Nanma baice da ita komai ba ya sakar mata. Tiren kayan breakfast ?in ya ?akko gaba ?ayansa ya ajiye saman gadon a gabanta. Bayan ya bu?e mata koma ya ?ago ya kamata tana jan allurar daya ajiye alamar so take ta ?oye.
Da ?yar ya iya danne dariyar data zo masa a ma?oshi. ya sake tsuke fuska yana balla mata harara. "Idanma kin ?oye inada gomanta a ?akina, kinga kenan kinyi na banza. Na baki 20minutes kacal naga tray ?in nan empty".
Hannu tasa ta sake share hawayen da suka ciko mata idanu, cikin ?un?unin da bazaijiba tace, 'Tunda ga jaka rumbu uwar zira lauma an kawo maka ko'. A fili kuwa du?ar da kai ?asa tai kamar ta ALLAH??.
Hannunsa ya ?ora saman nata da har yanzu ke ri?e da syringe ?in ya zare abarsa. Gefensa ya ajiye tare da gyara filos ?in dake birjit a saman gadon ya kwanta rigingine. Wayarsa ya ?auka ya hau dannawa tamkar ya manta da ita a ?akin.
?agowa goma Aymah zatayi harara ashirin take antaya masa. Ba?ar magana kuwa da gorin hawa mata gado da yay tayi yafi sau ?ari babu ?aya tana tunzura baki gaba. Daka ganta kasan tsoro ne fal ranta kawai da neman fa?a da tafi ?warewa a yi. Shi dai bai sake bi ta kanta ba duk da yana jin ?un?unin da takeyi da harar da take masa. Sai dai kasancewar hausa takeyi bai damu da abinda take cewarba. Da yake dama yunwar ta keji sai gashi ta shanye tea ?in duka dan ya mata da?i. Harko da ayyanawa take a ranta 'Wai buzun nan ashe ya iya ha?a shayi' (Kai wagga ?iya ta baba malam ALLAH dai ya gyara????). A sauran abincin kuwa bread kawai taci, dan yanda aka ha?ashi ya mata ?yau a ido da da?i a baki. Wai saida ta gama ci kuma sai cewa tai, 'ALLAH dai yasa ba arnakun nan suka yishiba na wage baki ina turawa kamar a ha?i?iya'. (Ke dai kika sani??).
Ganin ta kammala Yoohan ya mi?e zaune sosai yana ajiye wayar hannunsa. Trayn ya sauke ?asa, batare da ce mata uffan ba ya matso daf da ita sosai har suna jin saukar numfashin juna. Zabura tayi da sauri zata matsa ya ri?ota. Baya bu?atar hayaniyarta a yanzu saboda jikinta yay masifar zafin zazza?i, shegen taurin kanta ne kawai ya hana bakinta da bai rabo da tsiwa yin shiru. Baki ta bu?e zata fara masa tijara ya mannesa da nashi tare da sake jawota ya matseta a jikinsa tsam. ?arfin ba ?aya bane, hakan yasa duk mutsu-tsunta ko gezau baiyiba balle tasaran kubuta. Syringe ?in daya ?ura ruwan allura ya ?auka, batai auneba sai jin shigarta tayi cikin tsokar jikinta. Tabbas da bakinta baya cikin nasa ba ?an gidan ka?aiba har ma?wafta sai sunsan ta kwana a gidan yau. Dan allurar malaria ce daya fahimci shike saka mata zazza?in yay mata, allurar kam tana da azabar zafi, dan saita ratsa kowacce kafar magudanar jini da ?argon mutum kafin a hankali ta fara bashi nutsuwa.
Wani irin mugun ?an?amesa tayi jikinta na rawa. Harma ya zare allurar yana murza mata wajen bata dawo hayyacinta ba. Bakinsa ya janye a cikin nata a hankali yana sauke wani wahalallen numfashi da gajerun ajiyar zuciya a jere. Itakam kuka ta fashe da shi jin ta samu bakinta, sai ?ara ?an?amesa take kamar zata koma masa ciki saboda yanda zafin allurar ke gauraye duk jikinta. Ha?arsa ya ?aura saman kanta yana ?an murmushi da lumshe idanunsa. Hannayensa a bayanta yana shafawa a hankali alamar lallashi.
Sun sami tsahon mintuna biyar a haka sannan ta tureshi da ?arfi tana janye jikinta baya. Cikin kuka kashir?an tace, "Wlhy sai ALLAH ya mana hisabi da kai tun a duniyarnan tasa. tunda ai cakai idan naci abincin bazaka minba shine ka karya al?awari. Na rantse saina fa?ama Abbana" ta goge bakinta da bargo tana cigaba da fa?in, "?azami kawai mayen bakin mutane".
Shi dai komai baice mataba. Kallonta kawai yake da narkakkun idanunsa masu cikar gashi da haske. Tana cigaba da masifarta da goge baki yaga ta fara ajiyar zuciya da lumshe idanu alamar gyangya?i. Basuyi mintuna bakwai ba a haka ta ?ingire barci. Kansa ya?an girgiza kawai. A kan la??ansa ya furta "Yeyyey girl, mai bakin tsiwa".
Sauka yay daga kan gadon ya zagaya ?ayan gefen gadon data koma tun turesa da tayi. Kwanciyar ya gyara mata, ya fara ?o?arin zare hijjabin jikinta. Amma kasancewar barcin baiyi nisa ba, sai ta shiga ture masa hannu cikin kasala irin ta mai barci. Dur?usawa yay gaban gadon ya ri?e hannun nata cikin nasa. idanunsa ?yam akan ?ya?y?yawar fuskarta da komai ya dace da ita. Bata zare hannun nataba daga cikin nasa tabbacin barcin ya fara nauyi. Sai ajiyar zuciya da take faman saukewa a jajjere. Sai da ya ?ara bata mintuna kusan uku kafin ya kai dubansa ga hannunta data matse nasa. Zanen ?unshin ya ringabi da kallo yana ?an murzawa da babban yatsansa a hankali, abin ya masa ?yau sosai, sai dai a ?asan ransa tunani yake badai tattoo bane ba?. Jin ta ?an motsa ya juyo ya kalleta. Yanda ta wani ta?e baki a cikin barcin kamar zatai kuka sai abin ya so bashi dariya. A fili ya furta "Trouble maker" yana lumshe idanunsa ya sake bu?ewa a kanta.
Gudun kar hijjabin ya sha?eta ne ya sashi cire mata shi cikin dabara. Sai kuma yaci karo da bata da riga sai zani data ?aura. Kallo ?aya yay mata ya janye idanunsa yaja bargon ya lullu?a mata.
Oho, ita dai duk batasan yanayi ba, barcinta take zazza?in na sauka mata a hankali. Sai da ya gama bin ?akin da kallo tsaf sannan ya fice a ransa yana yaba ?o?arin iyayenta. Dan ko kujerun da aka zauba musu a falon yasan ku?i sosai aka zuba wajen sayensu.

________¡ï¡ï¡ï_______

A kano ta dabo kam ba?i sun isa gida lafiya da shatara ta arzi?in da suka samu. yanzun kam gidan ya koma shiru duk ba?i sun kama gabansu, hakan yasa suma duk basu wani yi zaman awa bibbiyu ba a gidan duk suka tafi. Sai Ananah kawai da ba yaune ranar tafiyar tataba ita. Amma jikokinta da sauran ?a?anta duk sun koma katsina tun jiya...........?


_Kuyi manage da wannan bajin da?in jikina nakeba, mura tamin ram????_.


Hafsat miss xoxo??
KIBIYAR AJALI......!
(Sulke baya tareta saita gitta).????

Mamu gee??
MIN ?ALB!!????

Hafsat rano??
ABINDA KE CIKIN ZUCIYA...!!????

Safiyya huguma?? SIRA?IN RAYUWA????

Bilyn Abdull??
SARAN ?OYE????

Duka akan farashi mai rahusar gaske.

Kamar haka????????

?aya___300
Biyu____400
Uku_____450
Hu?u____500
Biyar_____700

Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki????

ACCOUNT NO 0812652655
ACCOUNT NAME- HAFSAT LAWAN GAMBO
BANK NAME: ACCESS BANK.

saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)????

0903 234 5899

IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU????

09033181070

????????????????????
TEAM----ZAFAFA BIYAR????????*_LITTAFIN nan na ku?i ne. Dan girman ALLAH ki daure ki biya kafin ki karanta, idan kuma bazaki iya biya ba ki ha?ura domin ALLAH karki karanta. Idan kuma kin saya dan girman ALLAH karki ya?a mana????_*.

No. 47


________

I'm on Instagram as yerwaincense_and_more. Install the app to follow my photos and videos. https://www.instagram.com/invites/contact/?i=ayfowzb2ah8k&utm_content=6k8ur6p.

INA MA'ABOTA KARATUN LITTATTAFAN HAUSA? WANDA ZAI NISHADANTAR DAKU, YA FADAKAR, YA KUMA TSUNDUMA KU A KOGIN LOBAYYAR KAUNA? TO KU MATSO KUSA... DOMIN MUNZO MUKU DA ALBISHIR DIN WANI GANGARIYAR LITTAFI.. DAYA NE TAMKAR DA DUBU.. YAZO DA WANI SALO NA DABAN WANDA ZAI SANYAYA ZUKATAH.._

_LITTAFIN *UNCLE NE...* LITTAFI NE FIRST OF ITS KIND, DA YAZO A WANNAN SHEKARA TA 2021. AN BAJE KOLIN BASIRA A BOOK DIN UNCLE NE.._

_"Wait... Dakata hafsat Rano, Kina nufin NIMCYLUV, dai shararriyar murubuciyar nan itace tazo da wani salon rubutun..?.."_

_"Kede bari Billyn Abdul.. Tsaya kiji kanun labarin a tak'aice..*NIMCYLUV* Tace book din a ta'kaice labarin *UNCLE NE* ne yana tafe:_

_Da farko yana mata kallon uwa wacce ta haife shi kuma jigon rayuwarsa, ashe itace silar rushewar rayuwarsa??yarinyar da yakewa kallon ?anwa uwa ?aya Uba ?aya ita aka wayi gari ta zama MATAR SA?????¡â? ?addara ta ha?ashi da (Ahlil kitab) kiristan ya bata farin ciki, kulawa, soyayya, harya samu ta musulunta, Dalilinta sbd al'?awarin aure da yyi mata,ashe ba sonta yake ba??yaje birnin NUFAR domin kai masu tayin Muslunci, sun amince da hakan amma shara?in dole ya kwanta da ?arsu,?????¡â?gashi bashi da cikakkiyar lfy mazantakarsa bata aiki?? ashe mahaukaciya ce ta haife shi.._

"_Kai lalle akwai runguntsumi acikin wannan littafi.. Ba za'ayi babu ni ba, Domin Za'a sha lagwadar romon dadi. shin tayaya ake biya Hansatu?_"

_"Ai ta Abdul..LITTAFIN *UNCLE NE* Naira 300 ne, Idan kuma kana son vip inda za'a ake posting sau biyu a rana kuma za'a baku littafan data rubuta na ku?i sai ka bada 600 mai ma kon 1k.. number asusu wato bank account details: 0116886423 : account name sulaiman Na'ima S. Bank name: unioun bank: Sai a tura shedar biya ta 08119237616... A nuna mata ?auna ta hanyar turowa ta account????kamar yadda Za'a faranta maku a littafin UNCLE NE_
_(Best romantic love story of the year//Had'adden labarin kauna na shekarar 2021)_



No. 47

...........Sosai Nu'aymah tasha barcinta. Dan sai gab da la'asar ta sake farkawa. Yanzun kam Alhmdllh garas take jinta, sai dai jinta take wata fiyau tamkar iska zata ?auketa ta yada saboda rashin nauyi. Wanka ta fara yowa da alwala. Tazo tai salloli sannan ta kimtsa ?akin duk da bayyi wani datti ba. Tunda ta bu?e kwanikan dake saman tray ?in da ke bisa centre table sau ?aya bata sake ba. Sai ?un?uni da ta dingayi akan ita bazataci wannan jagwalgwalon abincin ba yasin. Dan duk da uban naman dake cikin miyar baiko birgeta ba.
Tsaf tai shiri cikin riga da sket na atanfa. Kayan sun mata ?yau sosai. Tana cikin saka turare aka turo ?ofar. Saurin juyawa tayi danjin babu wani knocking balle a kai ga sallama. Haushi ya tu?eta ganin Yoohan ne. Ta ?auke kanta tana ?ata fuska.
Yoohan da waya ke manne a kunnensa alamar magana ya keyi da wani shima ?in dai kallo ?aya yay mata ya ?auke idonsa, zama yay a kan sofa ya cigaba da sauraren abokin wayar tasa dake masa bayani daga can. Ita Aymah ma harta fara tunanin ko wani sabon wula?ancine ba wayar yake ba. Dan ya kusan mintuna sha biyar wayar na kunnensa amma baice komaiba.. Dai-dai ta ?ago ta kallesa taji ya ?an sauke numfashi, sai kuma ya fara magana a hankali cike da nutsuwa. Harga ALLAH bazata ?oye ba muryarsa na mata da?i. Ita bata bu?e yanda zaka tsorata mai sauraro ba, ba kuma ta sirance kamar ta mata ba. Tana fita da kauri da amo musamman daya kasance shi ma'abocin magana ne a nutse.
Haka ta dinga satar kallonsa harya kammala wayar. Ya cire daga kunne yana ?ago idanumsa kanta. "Am sorry, Assalamu alaiki". Ya fa?a yana janye idanun kanta lokaci guda. Amsa masa tayi fuska a tsuke, kamar zata ?auke kanta sai kuma ta sake dubansa. "Nifa yunwa nakeji".
Da mamaki ya kalleta, sai kuma ya duba tray ?in dake a jiye a wajen. Tabbas bana safe bane. Kulolin ya bu?e batare da yace mata komaiba. "Shi wannan abincin kuma fa?". Ya fa?a yana kallonta. Baki ta kunbura tana wani sake tsuke fuska, "Yoni bazanci wannan abincin ba, dan ban iya cinsa ba".
Shiru ya ?anyi yana kallon abincin shima. Eba ne da wata miya da suke kira Abak Atama soup (miya ce da mutanen Akwa ibom state suke yinta) taji uban nama sai ?amshi takeyi. Tabbas yasan da wahala ta iya ci ?in, tunda abincine irin nasu. "Mi zaki ci to?". Yanda yay maganar a da?ile ne ya sakata sake jin haushinsa, tai masa harar gefen ido. Kamar bazata fa?a ba sai kuma tace, "Noodles".
Batare da ya ?ara kallonta ba ya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login