Showing 24001 words to 27000 words out of 325075 words
aza kansa bisa cinyarta yana barci. Kan yaron take shafawa a hankali, kanta na kallon p.o.p idanunta na tsiyayar da hawaye.
Ha?iye tasa damuwar yay ya ?arasa cikin ?akin sosai. Harya zauna a bakin gadon kusa da Umm bata motsaba. Ya ?aura hannunsa saman nata dake shafa na Muh'd. Nannauyan numfashi ta sauke da ?ago kanta. Kallon ido cikin ido sukaima juna ita da baba malam ?in. Sai tai azamar saka hannunta na haggu ta share hawayen fuskar tata tana maye gurbinsa da murmushi.
"Sannu da zuwa Abban Nu'aymah. Yaushe ka shigo ban saniba? Gaba ?aya na gajine shinefa nace bara nazo na........." hannunsa yay saurin ?orawa akan bakinta alamar tayi shiru. Yasan ba wani abune ya saka wannan kame-kamenba sai dogon garga?in daya gindaya mata akan karta sake masa maganar Nu'aymah koda da wasa ne. Umm macece ita mai biyyaya da gudun ?acin ran mijinta, duk abinda ya nuna bai masaba ?o?arinta shine dainashi tai masa wanda zai sakashi a farin ciki koda ita zai cutar da tata zuciyar kuwa. Wannan yana ?aya daga cikin abinda ya ?ara mata kima da daraja a gareshi, tare da sake girmama soyayyarta a ranshi.
Mi?ewa yay ya ?auki Muh'd a hankali ya matsar dashi can gefe ya kwantar. Ita dai tana binsa da kallone har ya dawo ya zauna kusa da ita sosai. Kamota yay ya kwantar da kanta a ?irjinsa. A tare suka sauke nannauyar ajiyar juciya. Hawayen da taketa ?o?arin karsu zubo suka ziraro a guje suna sauka bisa jikinsa.
Idanunsa ya lumshe tare da sake kwantar da ita jikin nasa da ?yau, ya zame ?an kwalinta yana shafa kanta dake cike da gashi dogo mai yarfin furfura ?ai-?ai alamar girma ya fara kamata. Sake kwanciya tai sosai da cigaba da hawayenta.
Sunja tsahon lokaci a haka har saida akai kiran sallar la'asar sannan. Itace ta ?agashi da sauri. Hakan yasa ya farka daga barcin daya figesa shima. Tunda abinnan ya faru bai sake yarda sun kwana ?aki ?ayaba tun randa ta kwana babu lafiya. Hakan yasa suke tsananin kewar ?umin junansu. Matsar da fuskarsa yay gab da tata ya sumbaci goshinta da dogon hancinta.
?an murmushi tamasa da sadda kanta a ?asa na alamar jin kunya. Shima yay murmushin yana sauke ?afafunsa ?asa. Batare da yace mata komaiba ya nufi hanyar fita yana fa?in, "Ki tada Muh'd yay alwala mu wuce massallaci".
"To" ta amsa masa tana binsa da kallo.
__________________________________
Ana shiga sallar la'asar jar motar na shigowa cikin layin. Parking yay a ?ofar ?aton gate ?in gidan yana kallon gate ?in massallaci. Kafin kuma ya maido dubansa kan Nu'aymah dake a gefensa hannu da idanunta da baki a rufe tana gyangya?i.
?auke kansa yay ya kashe motar gaba ?aya. Bai fitaba, saima kwanciya yay jikin kujera ya lumshe idanunsa dake a cikin ba?in glasess ?insa.
Kusan mintuna uku da tsayuwarsu Nu'aymah ta farka. Sai dai kasancewar idanunta da bakinta a rufe suke sai bazaka fahimtaba. Addu'a kawai take jerawa a ranta na nema agajin UBANGIJI. Sai da aka fito massallaci mutane suka gama shashsharewa, sai hayaniyar yara ?an islamiyya dake cikin harabar massallacin. Kusan biyar na yamma Baba malam ya fito daga cikin massallacin shi da wani ma?wafcinsu suna magana. Saurin tashi yay zaune da kallon Nu'aymah, yay azamar saka hannu ya ?aye mata salataf ?in da suka rufe mata baki da shi. ?ar ?arar azaba ta saki tana fa?in, "Mugu kawai, ALLAH zai sakamin". Bai kulata ba ya kwance mata idanunta da hannunta suma. Wani irin farin cikine ya saukar mata a rai ganinta a ?ofar gidansu. Tana zumu?in fita ya dakatar da ita.
"Malam ?auki akwatinki ki wuce da shi".
Juyiwa tai da sauri tana kallonsa batare da ta saki handle ?in ?ofarba. "Bansan kallo, ki ?au akwatinki nace".
"Minene abin kallo a jikin naka banda ba?in hali da zalunci. Ni dai nasan banbar gidanmu da akwati ba mizaisa kuma na ?auka na shiga da shi..."
"K!!!" ya daka mata tsawa a fusace. Hakan ya sakata dakatawa daga ?o?arin sake bu?e ?ofar ta juya tana watsa masa harara da manyan fararen idanunta masu yalwar gashi. "Minene namin tsawa malam?". Maimakon ya bata amsa sai ya ?aga mata yatsun hanunsa biyu dake a cikin safa yana fa?in, "Kinada za?i biyu. Koki ?auka akwatin nan kokuma wlhy na maidake inda muka fito, kuma wannan tafiyar itace zata zamemiki ta har abada keda gida".
Kafinma ya rufe baki ta mi?a hannu baya ta sungumi ?aramin akwatinta ruwan hoda mai ?yau. Batare data sake jira yace uffan ba ta bu?e murfin motar ta fice abinta.
Sosai gaban baba malam ya fa?i, yabi Nu'aymah dake jan akwati zata shiga gida da kallo harta tura ?ofar ta shiga, kafin ya maido dubansa ga motar data ajiyeta. Akan idonsa mai motar yay reverse yabar anguwar.
Duk yanda yaso danne ransa suci gaba da magana da Alhaji Mani hakan ya gagara. sai kawai yay masa sallama akan yayi ha?uri anjima zasu ?arasa maganar.
Da mamaki Alhaji Mani yabi baba malam da shi harya shige gida da kallo.. Ya ?anyi shiru alamar tunani. Ganin bai hasaso komaiba sai kawai ya girgiza kai shima ya juya ya shiga nasa gidan da masallaci ya raba tsakaninsu da nasu Baba malam.
______________________
ZAFAFA BIYAR 2021
_______________________
Wannan littafi SARAN ?OYE na ku?ine, yana ?aya daga zafafa biyar, idan kana bu?ata kaima wa?anan numbers ?in magana ka biya ku?insa naira 300 kacal dan girman ALLAH. Karka ya?a dan ALLAH idan ka gani??????.
Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki????
ACCOUNT NO 0812652655
ACCOUNT NAME- HAFSAT LAWAN GAMBO
BANK NAME: ACCESS BANK.
saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)????
0903 234 5899
IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU????
09033181070
__________________
__________________
Nu'aymah na isa tsakiyar gidan ta yadda akwatin ta kwasa da gudu zuwa ciki tana ?wala kiran sunan Umm da Hajjo, dan gani takema tafiyar ?ata mata lokaci takeyi na isa garesu.
Ba Umm da Hajjo ka?aiba kowa ma na gidan sai da ya fito, yaran ne kawai da suka wuce islamiyya babu. Samarinma yawancinsu sun dawo daga wajen aiki da makaranta ga wa?anda ke jami'a.
Wani irin tsalle Nu'aymah tai ta ?ane wuyan Umm dake tsaye a ?ofar sashenta tamkar wata gunki. Hakan yayi dai-dai da shigowar Baba malam gidan a matu?ar fusace.
"K!! Nu'aymah! K!! Nu'aymah kina ina?". Baba malam dake shigowa tun daga gate ya fara kwala ma sunanta kira kamar zai ha?iye harshensa.
Da sauri Nu'aymah ta saki Umm jikinta na wani irin rawa, dan abin yazo mata a yanda batai zatonsa ba. Akwatinta dake yashe a ?asa ya shura da ?afa yana fa?in, "Zoki ?auka ki koma inda kika fito kafin harshena ya furta miki abinda har ki ?are rayuwarki zai zame miki musiba".
Idanu sosai Nu'aymah ta zaro waje jikinta na sake ?aukar tsuma. Muryarta na rawar fitar kuka tace, "Abba......" Katseta yay a tsawace yana nuna mata hanya da yatsansa.
Ba'ita mai laifin kawai ba, kowama yayi tsuru-tsuru a gidan hatta dasu Abba Rudwan sun kasa magana, dan sunsan ran yayan nasu a matu?ar ?ace yake. Hajjo ce kawai zata iya sakashi ko hanashi a irin wannan yanayin. Gashi kuma bata fitoba, ?ila wanka takeyi.
"Ba dake nake magana ba ne?!!".
Fashewa da kuka Nu'aymah tayi ta dur?ushe ?asa. "Abbah wajen wa?anda suka sacenin kakeson na koma?". Tsaki yaja mai ?arfi, dan yama ?auka maganarta raini da iya shege.
"Lallai Nu'aymah kin girma! Ashe wayonki da iya tsara abubuwa har ya kai haka ?arfi? Ki sanar mana kinbi saurayi saboda kar a aura miki Abdallah sannan ki dawo mana da wani sabon rainin wayon saceki akayi?. To idan saceki akayi uban wanene ya rubuta sa?wannin da kika barmana? Wanene kuma ya sacekin? Wanda naga ya ajiyeki yanzu shima wanene?. Duk sai ki bamu wa?anan amsoshin muna saurarenki?".
Kai Nu'aymah ta shiga girgizawa tana hawaye. "Wlhy Abbah bansan komaiba akai. Bansan su wanene ba? Bansan wanene wanda ya ajiyeninba nima? Sannan ban ajiye sa?on komaiba ga kowa wlhy".
"Nu'aymah!!!". A tsananin tsawace baba malam ya kira sunanta. Sai da hantar cikin kowa ta ka?a da tsawarsa. Itama tai baya ?asa wanwar jikinta na ?ari na tsabagen tsorata. Dan bata ta?a ganin fushin mahaifinta irin hakaba duk da tasan yanada zuciya.
Nufarta yay tamkar wani mayunwacin zaki, sai famar huci yakeyi jikinsa na tsuma.
Da sauri Abban Abdallah da Abba Mustapha suka sha gabansa yana gab da isa ga Nu'aymahn. Kareta sukayi yanda bazai ko iya ganinta ba balle ya ta?ata.
Sake ?aci ransa yay, ya kallesu da jajayen idanunsa da ?walla suka taru a ciki. kamar zaiyi magana sai kuma ya fasa, ya juya zai zagayesu ya dam?eta.
Caraf aka ri?e masa hannu. Dan haka ya tsaya cak batare da ya shiryaba. Hajjo data fito yanzun nan saboda tsawarsa da taji ta kalli hannunsa data ri?e da tana sake tamke fuska batare da tayi magana ba.
A take dukkanin jikinsa yay sanyi la?was, sai wata irin zufa data shiga tsatstsafo masa a goshi. Sun kai kusan mintuna biyar a haka ana kallon kallo tsakanin duka ?an gidanma. yayinda Umm tunda Baba malam ya shigo ta sulale ta koma ciki tana hawaye.
Da idanu Hajjo tai masa magana da yaren da tun yana yaro ya haddace sa, kafin ta saki hannunsa a hankali ta nufi Nu'aymah dake dur?ushe ?asa tana kuka har yanzun. su Abbah zagaye da ita suma har yanzun suna bata kariya daga baba malam. Kamata hajjo tai ta mi?ar da ita ta rungumeta a jikinta. Nu'aymah ta ?an?ame Hajjo sosai tana jan numfashi da ?yar. A hankali kuma sai idanunta suka fara lumshewa, kafin kowa ya farga tama sume.
Hajjo da taji ta mata nauyi tai ?o?arin ?agota amma ta kasa. Gabantane ya fa?i tace, "Kai Mustapha zoku duba yarinyarnan kamarma bata da rai".
Ai kafinma ta rufe baki sun kama Nu'aymah da hanzari. Yaraf tai baya jikin Abban Adawiya alamar dai da gaske bata numfashin. Sake tashi hankalin kowa yayi, duk sauranma suka matso suna ambaton Innalillahi....
?aukarta Abban su Adawiya yay ya nufi sashen Hajjo sauran biye da shi. Yana kwantar da ita bisa kujera Ahmad na mi?o ruwa daya ciro a fridge. Amsa Abban su Abdallah yay ya zuba a hannu sannan ya shafama Nu'aymah a fuska. Ko motsi bataiba balle ai tunanin farfa?owar ta. Sake tashi hankalinsu yayi. Ahmad da Malam ?arami suka dur?usa da saurin kama ?afafunta suna murzawa, suma su Abba hannayen Nu'aymah suketa faman murzawa. Amma abin tashin hankali ko motsi bataiba har lokacin.
A yanzu kam kowa ya fara tunanin ciwon Nu'aymahr ne ya motsa, dan haka Abba Musbahu da bai jima da shigowa gidanba yay saurin fa?in, "Inaga a kira Doctor ?inta, kamarfa ciwontane ya motsa".
Cikin kuka Hajjo tace, "Kirashi Musbahu, dan ALLAH ka kirashi da sauri. Innalillahi......... Zainabu karki mutu ki barmu kinji". Kukan Hajjo ba ?aramin sake ?aga hankalinsu yayiba, matan ma sai faman share hawaye sukeyi.
Duk abinda ke faruwa akan idanun Baba malam ne dake tsaye a jikin daga ?ofar falon Hajjo yana kallonsu. Kallo ?aya zakai masa ka fahimci yana cikin tsananin tashin hankali. Nu'aymah zuciyarsa ce, yana dannewa ne kawai, amma bazai yuwu ya bari son da yake mata ya hanashi hukuntata akan kuskurenta ba, dan yasan icce tun yana ?anye ake tan?warashi, idan ya bushe karyewa yakeyi.
Sun cigaba da ?o?arin ganin ta farfa?o kafin Doctor ya iso, sai dai fa ko motsi babu wani sashe na jikinta dake nuna alamar zaiyi ma...........?
Tashin hankali??, kumuje zuwa.
_____________________
SAHFAT PREORDER!
______________________
Wani kaya sai amale ka ?auka??.
SAHFAT PREORDER maida tsohuwa yarinya.
Kaji masu kawo kayan adon gida dana jiki ?an gaske.
*_Ina mata masu ?an bana bakwai? ko uwargidar da ake shirin kawoma ?ar bana bakwai?. Kai hardama matan gayu ?an ?walisa masu son sabunta gida da kayan ado ?an waje masu sau?in farashi da nagarta!._*
_To ku garzayo dama ta samu, dan SAHFAT PREORDER sune na ?aya a wannan fanin. Idan kayan kitchen kikeso masu ?yau da nagarta a farashi mai sau?i kuma zaki samu a Sahfat preorder. Idan kayan sakawa kikeso na manyan mata ?an gayu suma akwaisu babu ?ayarya. Jaka ko takalma na nunawa tsara suma ba'a barsu a baya ba harma da mayafai. Hakama kayan ?aki basu da tsara_.
Ni shaidace domin dukkan kayana ta hannunsu nake samu nima. Ku garzayo kuma a dama daku dan nasan zakuyi alfahari da hakan insha ALLAHU.
Kiyi magana ta wannan Number 08142957548 insha ALLAH zaki samu ?arin bayani ?ar uwa.
*_Siyen nagari??, maida ku?i gida?? sai SAHFAT PREORDER??????????_*
_____________________________
ZAFAFA BIYAR 2021
_______________________
Hafsat miss xoxo??
KIBIYAR AJALI......!
(Sulke baya tareta saita gitta).????
Mamu gee??
MIN ?ALB!!????
Hafsat rano??
ABINDA KE CIKIN ZUCIYA...!!????
Safiyya huguma?? SIRA?IN RAYUWA????
Bilyn Abdull??
SARAN ?OYE????
Duka akan farashi mai rahusar gaske.
Kamar haka????????
?aya___300
Biyu____400
Uku_____450
Hu?u____500
Biyar_____700
Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki????
ACCOUNT NO 0812652655
ACCOUNT NAME- HAFSAT LAWAN GAMBO
BANK NAME: ACCESS BANK.
saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)????
0903 234 5899
IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU????
09033181070
????????????????????
TEAM----ZAFAFA BIYAR????????
ALLAH ka gafartama iyayenmu??????.
[3/12, 6:01 PM] +234 901 860 0202: *_Typing??_*
No. 8
...................Doctor na isowa aka maida Nu'aymah bedroom ?in Hajjo. duk fita sukai suka bashi waje yay aikinsa yanda ya kamata. Sai Abubakar da aka bari kawai dan ya taimaka masa da wani abun idan ya bu?ata.
Sunyi jigum-jigum a falon Hajjo, kowa da abinda yake tattaunawa da zuciyarsa wadda ALLAH ka?ai yasan minene a cikinta.
Juyawa baba malam yay a hankali ya fice daga sashen. Sashensu ya nufa dan sai yanzune hankalinsa ya kai ga rashin ganin Umm tare da su. Babu kowa a falon, ya nufi bedroom ?inta canma babu kowa. Fitowa yay ya nufi nasa ?akin ko tana can. Sai dai kuma nanma babu kowa. A ?an ru?e ya dawo ?akin Muh'd. Muhammad ?in kawai ya samu yana canja Uniform ?in islamiyya dan yanzun suka taso. Baima gansaba, sai da yace, "Muhammad ina Umm ?inku?"
Jiyowa Muhammad yay da sauri, fuskarsa da ?an damuwa yace, "Abba nima ban gantaba, na shiga ko ina bata nan kuma yunwa nakeji".
Shigowa sosai Baba malam yay cikin ?akin idonsa akan Muhammad ?in. "Yunwa kuma Muhammad? Bakaci abinciba ka fita ne?".
"Abba lokacin nasha fura wajen Hajjo na ?oshi, yanzu kuma zanci".
Kama Hannunsa Baba malam yay suka fita kitchen da tsammanin zaiga Umm a can. Sai dai kuma mai aikinta kawai suka samu tana gyaran kayan miya. Cike da girmamawa ta gaida Baba Malam ?in. Amsawa yay yana cirar tuffah dake cikin fruit tray ?in da suke sakawa. ?arasawa yay wajen fanfo zai wanke Saude tai saurin fa?in, "Baba malam kawo a wanke". Baiyi musu ba ya mi?a mata tuffa ?in guda biyu daya ?auka. Sake bin kitchen ?in yay da kallo kafin yace, "Ina Jannat ?in take na ganki ke ka?ai kina aiki?".
Saude data wanko apple ta ?aura a ?aramin filet tace, "Nima na shigo ban gantaba, dama naje can ?asan layine na sayo mata daddawa data bada. To nadawo kuma na duba kamar ta fita, shine nace bara na gyara ko kayan miya kafin ta dawo". Shiru Baba malam yayi gabansa na fa?uwa. Amma sai ya danne ya kalli Muhammad dake saurarensu. Filet ?in tuffa ?in ya mi?a masa yana fa?in, "Kar?a wannan kaje kaci muje salla mu dawo saika zauna cin abincin".
Kai Muhammad ya ?aga masa da amsar filet ?in. Yaron nagaba yana biye da shi har suka fice. Sake komawa yay ?akin Umm ?in dai zuciyarsa na bala'in harbawa. Tsaye ya isketa gaban Wadrobe tana fiddo kaya da alama wanka tayo. Ya sauke ajiyar zuciya da fa?in 'Alhmdllh' a fili. Hakanne yasata juyowa da sauri dan bataji shigowarsa ba. Kamar zatai magana sai kuma tai